Showing 150001 words to 153000 words out of 395027 words
Chapter 51 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
cikin harshen hausa nima.
Anzo wajen ya fada a ransa don ya fara aikina kaina na bincike ledojin da aka shake muna da kaya na mika hannu in dauka sai kuma na dakata ina fadin sorry sir meyasa kayi hakan akwai kudi a katina ai a cikin turanci.
Na kula baki son alheri a rayuwanki shiyasa kikewa karamar yarinyan nan fada don ta yarda dani nidin ba mugu bane tasan waje daya muka fito.
Na dan dubeshi kadan sai kuma na juya na mika hannu na dauki kayan ina fadin angode yaron shangon ya miko min dayan ledan sabon sayayyan na rasa yadda zan daukesu a lokaci guda don sunyi min yawa a hannuna da dauka lokaci daya.
Tambayansu yayi ina masu daukan kayansu aka kira yaro daya yace yakai muna bakin mota mukai gaba saurayin ya biyomu da kayan a baya.
Bansan yana biye damu ba saida naji muryanshi a lokacin da nake nufar titi inda zamu samu drop a kaimu gida naji yana cewa yaron ga mota can ya kai muna.
Sorry sir wahalan ya isa haka zamu samu motan da zata kaimu inda zamu a nan bakin titi kin yarda baki son taimako ko ?
Ki bari na rage maku hanya ko don wanan yarinyar please yau akwai rana a garin dan shiru nayi kamar mai tunane sai bance komai ba aka saka komai a cikin motarahi muka shiga yaja muka fice wajen .
Ina kuka nufa na fada mai unguwar ya dauki hanya baice komai ba ya mika hannu ya kunna kira,a mai sautin Ahmed sulaiman kano yana dan bi a hankali.
Har muka juya a round about Amira da taji kira,a saita kama karanto Alhamdu tana tsaye a bayan mota ta raba hannayenta biyu tana karatu.
Zakice bashi yai maganan ba a lokacin yace wanan yarkice tana da matukar wayau sosai ina son yaro haka mai basira gashi tasan karatu akeyi ta dauka na zata da farko aiko ba musulmai bane ku ?
Amma yanzu yarinyar nan ta tabbatar min daku musulmaine ya dan juyo yana satan kallona don ban iya bashi amsa ba don na kule da tambayan nasa dukka biyu daya jefo min lokaci guda.
Jin ban bashi amsa ba ya sake tambaya da yarkice ita meye sunanta Amira na bashi amsa yace nice name Amira yana nufin suna mai ma,ana jagora mace ke nan ko a takaice ?
Yes kawai na iya fadi sai ya juya tambayan daba amsa ga yarinyar yana tambaya Amira ta amsa da yes uncle ya danyi murmushi yace is she mother ?
No no no she is my big sister kamar yadda mamanta ke fada mata ta dora da fadin my mother is at home watching television don shi muka barta tana yi a lokacin da muka fito.
Good girl so you are living with your parents here in lagos yes kawai nace dashi ina maida hankali ga titi don tambayanshi ya fara isana a lokaci.
Kudin hausawane ko yaruba amma kamar na sanki a kano nake gani may be watace mai kama dani don bani bace a nan lagos nake zaune ni tare da iyayyena.
You mean baki san kano ba amma kike hausan yan kano a bakin ki kawar da zancen nayi ina fada da Amira dake batun fado min da turanci akan ta natsu kada ta fadi taji ciwo.
Ya gane banson amsa mashi tambayoyinshi yasa yaja bakinshi yayi shiru muka tafi a hakan can kamar an matse bakina nace dashi ina kara godiya kan yarda da aiki da company da nakewa aiki da sukayi mungode kwarai da gaske and beside kuma ina kara godiya ga wanan sayayyab da yai muna mungode kwarai da hakan a garemu ba matsala yace ai business ne aikinshine hakan kuma ya saye ya sayar inda yaga za a samu riba ba rikici a cikin harka.
Kinyi kankanta da wanan sana,an baki gudun su damfareki su gudu su barki ciki a karshe ?
Dam dam gabana ya fadi sau ukku lokaci guda wanda yasa har na dago nayi mai kallo ido da ido na dan lokaci kafin na girgiza kai ina fadin.
Ban tsamanin hakan don da dan mai company muke karatu Allah ya hadani dashine ga wani taimako da yayi min a rayuwana daba zan iya mantawa da hakan ba a raina.
Don badonshi ba a lokacin ba zan cigaba da karatuna ba da nake gab da gamawa yanzu tun lokacin ya sakani a wanan harkan kuma sunayi ban taba jin ance an samu matsala da wani ba.
Amma idan harkan bai kwanta maku ba zaku iya resigning mu nemi wasu kasuwa dama dan sa,ane idan abu bai kwantawa mutum a rai ba ya barshi.
No no no ba haka nake nufi ba sam yarda dake tun farko yasa na shiga harkan nan amma ni ba sana,ata bace har kan mai wanan ne karo na farko da zan gwada a rayuwana.
Wani irin kallo nayi mai na mamaki sai wani irin abu ya ziyarci zuciyana lokaci guda tsorone ko razana dai gashi nan ba zance ba.
Cikin daurewa nake fadin amma ba sana,anka bane kayi kasadanyi da makudan kudi haka masu yawa da alama kana fargaban hakan tunda ba sana,anka bane wanan harkan.
Amma da rashin tayi ake barun araha inji bahaushe ko zan gwada saiki tayani da addu,a ya fada da hausa na amsa da amin shiru nayi don tsoro ya gama rufe min zuciya a lokacin.
A daidai shagon su Bumi nace ya sauke mu yake mamaki a nan muke na amsa da eeh muka sauka mamanta muka samu tana muna sannu da zuwa ya sauke muna kayan ban farga da yaba Amira kudi ba saida maman Bumi ke fadin in karba kada a fisge a hannu ta na karba sin cikin mamaki ina bin motarshi da kallo har ya kusa bacewa a lokacin.
Nan na tare motan da zai karasa damu unguwar mu muka shiga zuwa gida har lokacin ban cikin hayaci don fargaba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/22, 10:03 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
4️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15- HAWAYEN KADA🐊 1000.
_Account No._
_*ZAINAB IDRIS MAKAWA*_
2254380105
ZENETH BANK
PHONE NO.
08036959257
A sabule na isa gidan hankalina baya tare dani a lokacin don maganganun da mukayi da bawan Allah nan ya daga min hankali sosai.
Ban taba kawowa a raina cewa hakan daya fada yana iya faruwa ba ga duk harkallah da mukeyi.
Don kurciya dake dibana a lokacin ko kuma wayau hakane bai kai gareni ba oh don a shayi muna ji muna gani hakan ba bakon abu bane a nan din .
Azo a cuci mutum miliyoyin kudi masu yawa za a damfareshi sai lahira a hadu can don kowa so yake ya gina kanshi a yanzu wasu basu damu da damuwan wani ba sai nasu.
Yau Allah ya tsare idan har haka ya kasance gareni tawa ta kare ke nan don ko dan gidan mu na kano akace a sa kasuwa abiya mutanen nan kudinsu ko rabi kudin baya taba yi balle biya.
Jiki ba kwari nashiga gida inda Amira keta ihu tanawa mamanta gulman mun sayo baby teddy da sweet uwar ke fadin yau ashe kuna da shagali gidan na zauna jagwal a gefenta cikin damuwa ta dubo tana fadin lafiya ?
Zufa nake jin yana karyo min daga kaina zuwa fuska na debe dan hijjab din kaina ina goge fuskan a daidai lokacin amaryan Paapa ta fito sabe da danta.
Ba wanda tayiwa magana a cikin mu ta samu wuri ta zauna ta kurawa tv ido ba yau ta fara hakan garemu ba don sai muna zaune zata zo ta zauna muna bata cewa uffan a cikin mu harta karaci zamanta ta mike zuwa daki.
Haka muma babu mai kulata a cikin dan gara nima akwai ranan data ban danta in kama mata wai zata shiga wanka yana kuka na karbeshi ba magana har tafito baiyi kuka ba ban kuma kai mata shi ba.
Antyna,ko bata,ko kallon inda yaron yake balle ta nuna tasan dashi a gidan dole ko wace uwa wanan abin ya taba mata zuciya amma halin kishine ba abinda bai saka mai raunin imani yi saidai wace ubangiji ya kareta ya tsarkake mata zuciya akan hakan.
Amirah dake faman damu na fito da teddy din uwarta ta gani yasa na sauke ajiyan zuciya tare da mika hannu na bude katon ledan na ciro mata na mika mata ita da uwar suka hau ihun murna kallo daya Yabi tayi ta kawar da kanta garemu .
A hankali na mika hannu ina zaro duk sayayyan da nayowa yaron na dagwara mata turare da wani hand bag mai kyau dan na kula da wani tsohon hand bag take dawainiya na mike na nufeta ina fadin.
Maman boy ga tsaraban boy da naki nan antyna ta dago ido tana bina da kallo Yabi ta juyo da dan mamaki makale a fuskanta tana fadin tsaraban har mune ashe ?
Kai masha Allah anko gode na zube a gabanta na barta ta fara budewa tana gani na juya gun antyna na mika mata ledan dana sayo mata nata gaba daya izuwa lokacin ta dan saki fara,a a fuskanta tana budan ledan amma bata bude duk a fili kowa ya gani ba.
Wanan sayayyan mutumin da Amira na fara cirewa ina duba don a lokacin ba zance ga abindake cikin ledan nashi ba .
Manyan ledan sweet biyu na fitar sai irin biscuit din nan da ake jerawa a cikin kwanko guda biyu sweet din ma na foreign company ma,ana na waje na yan gayu.
Hannuna ya fara zaro manyan designers din turaren mata acikin kwalinsu masu kyau na dinga ajesu a gefe daya sai dayan ledan dake shake da kayan shayi na kasar waje masu kyau da tsada.
Mamakin da zuciyana ya kumsane kakara a fuskana wanda muryan antyna ya katseni da tambayan data jefo min da wanan sayayya haka mai tsada ?
Da alama kin samu kudi masu yawa maryam a cikin harshen yarbanci take fadin hakan gareni na bata amsa a cikin hausa ina sauke ajiyan zuciya nace.
Wani kwangila na samu anty wanda na samu mahaukacin kudi gareshi kinsan tsarin wajen mu yadda yake ka kawo customer mai kyau abinda za a baka mai yawa.
Na kawo masu wasu yan arewa da zasuyi business din mai shine suka ban kaso mai yawa daga cikin abinda suke ban haka ka,idan yake.
Ikon Allah idan ka kawo masu sayen kaya sai a baka wani abu mai tsoka ke nan Yabi ta tsoma muna baki a cikin hiran namu.
Haka wajen namu yake aikin mu ke nan dasu mu tallata company yawan masayan daka samu shi zai baka kaso mai tsoka is depend ga yadda kasuwan yazowa mutum dai.
Yoo ashe da ake fada a lagos ko shago kikai masayan kayansu daga arewa sai sun baki kaso mafi tsada a matsayin tukwaici zancen nan gaskiyane ?
Hakane sunsan darajan sana,a idan ka iya suna bukatan masaya wanan yasa suke promo ga yaran shagon don kowa ya dan samu.
Shigowan Paapa dake bin mu da kallon mamaki ganin irin zaman daya sama anyi wanda yasan karshe fitinane saidai ba alaman fitina ko bacin rai ga fuskokin matan nashi a lokacin hakan yasa akalan idonshi komawa gun kayan dake baje a falon banda nawa da fidda ba a leda madara da sauran ganyen shayin na mikawa yabi daya sauran na mike na tattara zan bar wajen.
Umar kaga anty yara tasayowa yan uwanta damu wanan tsaraba haka mai yawa ta fada fuska sake tana kallon mijin nasu .
Maryam tayo wanan sayayyan haka mai yawa wanan ai ba karamin kudi ta kashe ba a nan ya fada yana mika hannu ya karbi teddy din da Amira ke mika mashi nata.
Ya juyo ya kallon antyna yace a ina ta samu kudi haka masu yawa tayi wanan sayayyan fuska ta daure tana fadin amma ai kasan irin aikinta ko ?
Ko na sani ina da right da zan tambaya tunda a karkashin ikona take garin nan bakaga abu kayi shiru irin haka ba wanan is many mana kayan nan zasu kai ,,,,,,
Ai yanzu take muna bayani indata samu kudin wai ashe idan ka kawo wanda yasai kaya mai yawa shine ake ba mutum kaso mai tsoka to ita ta kawo ansaya aka bata kudi mai yawa haka.
Ga namu da Maha!
Tana tura mashi ledan zuwa gabanshi yabi ledan da kallo kafin ya nisa kadan ya juyo gun antyna yana fadin amma zata dinga wasa da kudi haka bata tanadi ta turawa iyayyenta tunda suma suna cikin bukatan haka ?
Donta saya muna shine wani abu maryamce fa maryam dake da mugun wayau tsiya kawai ka barta she knows all dis tasan me zatayi ai.
Look what ever she is she need our support tunda shekarunta baikai ta hango wani abu a rayuwanta ba and kuma dole idan mun gani mu sakata a hanya.
Irin wanan abubuwan ba ido zamu sa mata ba we have to ask her yadda ta samu kudin da abinda ya kamata ace tayi da kudin so that her parents will know don gaba mu san abinda zamu fada masu daga inda tabi take zaune tace hakan kuma gaskiyane indai zaman Allah da Annabi kakeyi da mutum shine zama tunda yarinyace ita har yanzu.
Me kike nufi da fadan haka So, ni ba zaman Allah da Annabi nakeyi da ita ba ke nan ko to sai ki koya min yadda akeyi tunda kinzo ?
Shout up please kada ku kawo min wanan halin naku a nan ba zan dauka ba ke maryam ya fara kwala min kira mai nuna alaman ka taba zuciyar mutum a lokacin don a jere ya jera min kira ukku lokaci guda.
Nafito ina karba a zatona fada zaiyi kayan amaryanshi yabi ko danshi saidai ina zuwa na dan duka ina gani Paapa ya juyo yana fadin .
Yauwa!
Naga kaya yanzu suke nuna minsu angode amma don Allah maryam tsakaninki da Allah ina kika samo kudi haka kikayo wanan sayayyan tashin hankali wanda koni na miji ba zan iya sayo wanan abin haka ba a yanzu lokaci daya.
Kallo na kawai antyna dake cika tana batsewa nan ta soma fadin ato na fada mashi bai yarda ba sai kiyi mashi bayani yadda zai fahinta ai.
Akan me fa na tambayeta cikin dan girmama ta nuna da hannu tana fadin Paapa yace yana son yaji yadda kika samu kudi haka da kikai wanan sayayyan masu yawa ?
No a wajen da nake advertises ne uncle na kawo masu wasu hausawa da zasu dinga daukan mai a karkashin company shine da aka shirya suka ban share dina.
Ke kinsan abinda kike fada kuwa a gabana maryam a ina kika shiga kika samo irin mutanen nan wai ashe kinyi nisa haka ban sani ba innalillahi sai yakai hannunsa ya shafo fuskanshi zuwa kai yana shafawa ya sauke ajiyan zuciya mai sauti ya sake kallona yace.
Wanan babban del ne fa kike zance maryam umm,hhh hakane Paapa dama ai na fada ma muna masu tallane sai su bamu dan kason mu a gurin aikin baban Ozil din shike da wurin man ai.
Ozil ozil idan anyi magana kice Ozil who d hell is Ozil in dis town kinsan irin kasadan da kika jefa kanki kuwa idan mutanen nan suka gudu da kudin mutane kece za a kama fa maryam.
In anyi magana kice Ozil kinsan gidansu ne ko kinsan garinsu wawiyar yarinya kawai mara hankali ke baki tunanen hakan ya faru.
Kaina girgiza alaman