Showing 279001 words to 282000 words out of 395027 words

Chapter 94 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

koma na kwanta yadda nake da farko.

Sannu a hankali nake jin barcin wahala ya soma dibata har ya dan daukeni din can naji muryan anty a kaina tana fadin maryam ki tashi baki da lafiyane ashe ?

Ido na bude da kyar ina jin wani irin yanayi na saukan zazzabi a jikina takara fadin ki tashi ga oganki nan a waje yana kiranki.

Sai zuwanshine ai nasan kina gidan nan tun dazun kwance na daure na tashi ina yamutsa fuska na mike zaune ina fadin na dawo na samu duk kuna daki lokacin nashigo na kwanta.

Shine ya kirani nake fada mai ina gida banda lafiya ashe zaizo yace ki fito kuje asibiti ta fada cikin wani yanayi mai nuna alaman ranta ya baci dani a lokacin.

Ba sai naje asibiti ba ai kaina kawai ke min ciwo anty shiyazo yayi nocking yace a kiraki so ki tashi kije ki sameshi meye a cikin asibitin ba magani zaki karbo ki dawo ba ?

Dole dai na tashi na shirya wai asibiti duk zuwana garin yaushe na samu gatan zuwa asibiti haka tun ina secondary zuwana lagos din sabo sabo na tama fever haka paapa ya kaini asibiti har yau saidai in dansha magani Allah ya mikar dani ban faye ciwo ba gaskiya.

Tunda na fito ya tsura min ido zance wanan ranan ne kila ya soma ganina da shiga sak ta yar arewa musulma don hijjab din sallahna dake jikina haka na fito irin wanan hijjab din da akayi a baya mai kan alkyaba da wani a sama na bayan na rito sai dan kamun baki haka ansako igiya da aka daure da beads a ko wani gefe nawa dark blue ne mai kyau sosai innan mu ta saya min shi da mukaje arewa taga banda hijjab sosai dana dawo nan na mayar dashi na sallah saboda ya sauka sosai ina jin dadin ibadana dashi kuma.

Yana ganin na karasone ya dan yunkura ya bude min motan gefen daya hakan yasa na zagaya na shiga na zaune ina dago kai a hankali tare da kokarin gaidashi.

To yaya ya rigani fada na amsa da naji sauki ciwon kaine kawai ai wani kallo yayi min yana fadin ciwon kaine kawai baki san ciwon kai alama bace babba ga jikin dan adam ?

Ga Na,ima can nace su kaita asibiti tun shekaran jiya data soma sunki sai yau suke kirana wai jikin nata ya kiya zasu asibiti da ita tun abu na karami zuje basuje ba sai yanzu .

Ke kuma gani again wai ciwo kai ne kawai ya fada yana tayar da motar muka bar haraban wajen nidai ban iya magana ba sai dafe kan da nayi da hannu daya kawai ina lumshe idona.

Ni dai a rayuwana abu biyune na dauka shi zuwa asibiti gata da samun halin hakan ga bawa dan abu kadan ace asibiti aje a kashe kudi a dawo ko don tun farko ban samu gatan haka bane tun a gida oho ?

Na kanyi mamakin irin mutanen da dasunji kyasham a jikinsu yanzune zasu kwasa suje ganin likita a bankado masu magani suzo suyi ta faman sha yana dibge masu jiki.

Idan kaina har yana ciwo haka da yawa nakan shafa rob ne a goshina inyi ta murwa ko kuma in dafe goshin gefe da gefe na dan lokaci ina karanta suratul falaq sau ukku in shafe yadda innan mu ke muna.

Cikin ikon Allah kuma Allah ubangiji ya ban sauki a hakan wanan yasa ban tashi da sanin dadin asibiti ba a rayuwana ba.

Muryanshice tasani bude ido ga tunanen da nakeyi yana fadin kinci wani abune ?

Kai na dan girgiza mai alaman a,a gareshi naji ya danja tsuki yana kawar da kai gefe daya can ya soma fadin ba tare daya duboni ba.

Na rasa wasu irin mutane kike zama dasu haka wai ace har mutum ya dawo ya shigo gida amma wai ba a sani ba yanzu idan wani abu ya faru dake fa ?

Da alama ma mata biyune ai a gidan ko don naga wata bakar mace dogowo ta leko ina magana ta koma ciki na dan jima a waje tsaye ai ina ta horn saida na sauko nayi nocking wanan tazo ta bude nake fada mata.

Itace antyna wacan din abokiyar zamantace haka take ita halinta ko itace wace ta haihu mukazo sunnan danta ko ?

Ban iya bashi amsa ba shiru nayi don abinda ke damuna shima shiru din yayi bai sake magana ba kafin mushiga asibitin ya tsaya wani shago ya fita ya sayo hollandia da cake ya kawo min yana fadin ki soma shan wanan kar ace za ai maki allura.

Jin abinda ya fada wai allura yasa na kalloshi da sauri ya bude motan ya fita yana waya ina jin yana tambaya ko yana ciki ban sandai amsan da aka bashi ba don ya dan matsa daga gurin a lokacin.

Na bude kwalin na dan tsotsa sugar shi na shiga bakina naji kamar zanyi amai cikin daurewa na kara kurba na mayar na rufe naganshi fitowa da wata nurse.

Ta zagoyo gefena wai kamani zatayi bansan lokaci dana balla mata harara ba nace haba mana zan iya tafiya ai nayi gaba abina na barta tsaye tana bina da kallo.

Shiyasa diya masu kudi da matansu suke shagwabe wai tawani zuwa ita kamani zatayi da abin haushi office din likitan muka shiga a tare dashi.

Likitan yarene shima amma akwai sanaiya a tsakaninsu nake gani na zauna yana min sannu tare da tambayata meke damunane wai nace kaina ke ciwo kawai ?

Kinyi period dinki wanan watan tambayan da ya jefo min ke nan naji kamar in nutse a cikin kasa don ni ko antyna da muke tare a yanzu bata sanin lokacin wanan abin balle wani kato haka.

To ma me yake nufi da yi min wanan tambayan haka a gaban wanan mai kwakwafin na daure fuska sosai ban kuma sake dago kaima na dubeshi ba.

Shine ke fadin bakiji tambayan da yayi maki bane toni me zan fada kaina kawai ke ciwo kuma don kukan da nayi jiyane yaja min ciwon kai din nacema idan nayi addu,a zai daina ai yazo yana min wani tambaya na daban kuma yanzu ?

Tambayanahi yayi wai mena fada nagane likitan bayerabe yana cikin mayar mashi da turanci abinda nace ni kuma a lokacin na juya harshe da yarbanci ina fada mai kaina kawai ke min ciwo saboda nayi kuka jiya yaja min hakan.

A,a dama ke yaroba ne nace a,a na daiji zama garin nan so ke hausace kika iya yarbacin haka a bakinki ya fada yana wasu yan rubuce rubuce .

Suna kuma magana da juna naji yana fadin za ai min allura da zai sani karfin jiki sai maganin da za a ban don feverne ke son kamani saboda kukan danayi din.

Ya juya harshe da yarbanci yana fadin in bari ai min alluran zai taimaka min kada abin ya kaini kwance.

Harshe na juya don fahintar daure fuska da yayi lokaci guda wanan kuma nasan don yaren da nakeyi da likitan ne da baiji yasa ya daure fuskanshi din.

Ba sai nayi allura ba bani allura aban magani nasha is okey for me dariya suka kwashe dashi yana ta zolayanshi irin nasu na likitoci ya ce aban maganin mu tafi.

Na rigashi fitowa daga office din ya fito ya sameni na jingina a jikin mota ya shiga nima nashiga ya miko min ledan maganin na karba.

Saida ya soma tafiya yake fadin don an tambayeki zancen period dinki gabana saboda kar na sani zaki juye harshe kina gulmata a gabana ko ?

Gulma kuma na fada cikin mamaki na juyo na dan kalleshi sam bansan me yasa a yanzu banda courge din dubanshi irin farko ba sai kawai na juya naki magana ina kallon titi.

Asibitin nan da kike gani har likitan abokinane a cikinsa baya nan yayi tafiyane duk sanda kike da wani matsala tunda an bude maki file a nan kina iya zuwa koke ko wani dan gidan ku kuzo zai sanar dani komai.

Angode na iya fada yamma yayi sosai a lokacin don naga yanayi yana duban time a gogonshi saiko ga kora anyi mai naji yana fadin ka bari har gobe ina wani abu important yanzu sai na dawo .

Wani gidan saida abinci ya tsaya ya shiga shi kadai ni waje kawai nake nema in kwanta a lokacin don ina jin ba dadi har lokacin a jikina.

Ya fito da ledoji a hannunshi ya saka a bayan mota muka tafi gida ya mai dani yana kara jaddada min da nasha maganin da aka ban zaisa ciwon ya sauka min insha Allahu.

Godiya nayi mai ya miko min ledojin na karba nashiga dasu ciki anty na sama zaune a falo ina shigowa ta bini da ido hadi da sannu da antyna keyi min na amsa.

Wuri na samu na zauna ina aje ledan a gefe daya maganin na mika mata take fadin me ke damunkine wai nace ciwon kaine fa kawai anty amma duk yabi ya wani tayar da hankali haka ?

Kinjiki dai da shirmen banza wanan bashi ake kira da so ba idan bai sonki zai tayar da hankalinshine din halan ?

Na juya ina kawai kwance ina fadin wai so wanda keda matanshi kawai dai yana ban kulawane don muna shiri dashi amma ba wanan a tsakanin mu gaskiya.

Don yana da mata sai akace kada ya nemi wata mata nawa akace maza suyi na bata fuska ina gyara kwanciya ta sake fadin Allah guy din yana sonki sosai maryam.

Ga abu a zahiri a idanunsa lokacin da yazo dazun nace baki dawo ba bakiga yadda hankalinshi ya daga bane wallahi.

Yasan ina gidane tunda munyi waya dashi nace mai nadawo gida shiyasa yazo kinga ba na fada maki yana sonki sosai wallahi har bai iya boye hakan a gaban kowa.

Anty guy din nan dan kanone shima kuma yana da aure fa sannan dan masu haline sosai haka shi kanshi ina ganin yana da kudi ni kaina na kanyi mamakin abinda yasa yake kulani haka a yanzu ?

Wai yaushe zakiyi wayaune maryam koda yake don baki taba soyayya bane kike fadin haka shi so ina ruwanshi dako mutum bai kai class din ka ba ki gane mana kema ?

Balle rigiman mazan arewa ai ba wanan tunanen da kikeyi ke balle shi wanan din dake da abinsa sai kiga mutum ba sana,an kirki amma haka zai tara mata a gida wani shekarunsa bai kai ya kawo ba sai kiji ance matansa ukku ko hudu.

Shiru nayi ina tunane a kasan raina nikan har inason kaina da lafiya ai in raba kaina da mai mata shine zaman lafiyana.

Gara tun wuri ma in taka mashi burki ba wanan zancen so din a tsakanin mu inma abinda take fada gaskiyane to ya daina ya rike matarshi.

Waima ko matar nashi yake fadin yace akai asibiti ban kula ba tabbas itace ma yake magana a kai ke nan itama matar bata da lafiya amma yana nan yana wahala akan wata ?

Lalai maza sai a barsu don idan kina da hankali tun waje zaki fara gane halaiyan namiji ashe gata can kano ba lafiya amma yazo nan yanawa budurwa hidima kuma wai a kaita asibiti.

Hajja yabi ta fito da danta suka zauna a falo lokacin anty ke fadin wai meye kika shigo dasu haka suke kamshine ?

Sai lokacin na sauke ajiyan zuciya na dawo daga tunanen da nakeyi ina fadin shiya sayo min wai inci insha magani ta yunkura ta soma budewa don ganin meye a ciki ?

Abincine lafiyayye har roba ukku sai nama a sauran leda din take fadin ki tashi kici kisha magani a raina nace lalai kunya gadanshi akeyi wani lokaci.

Ba nuna komai ga hakan zatace wai in tashi inci insha magani yau da a hannun iyayyena nake konasha giyar wake aiba zance an sayo min abinci daga waje ba don insha magani ba.

Ai ban kare wanan tunanen ba nashiga wani lokacin da take fadin Amira ta dauki plate ukku a kitchen yarinyar ta sheka ta dauko ta saka naman a ciki tana fadin Amira mikawa Yabi wanan ta mika mata wanda ta sakawa yabi din.

Itako ba kunya ta karba tana fadin nama muka samu haka ashe da rabon mu ciki angode maman Amira don kadama tace ni ?

Saida sukai nisa da yagan kajinsu suna ci kowa na hira da danshi ta dago tana fadin kici mana kada yayi sanyi gashi da zafinsa sosai yanzu .

A lokacin na yunkura ina fadin zanci ina son inyi brush ne in nayi sallah inci insha maganin na mike na dauki ledan maganin zuwa daki.

Uwar wani dai ba uwa bace inji manya koda yake haline kowa da nasa ba wani dogon bincike a kaina su dai kawai rayuwan akasawa gaba ke nan .

Harma idan wani sharholiyace nakeyi su sam ba a jikinsu ba wanan ko zata iya ba yarta tarbiya kuwa abinda nake tambayan kaina ke nan na shiga dakin nawa.

Alwala na shiga nayi na fito na tayar da sallah bayan na idar ina zaune Amira ta biyoni da abincin da sauran abubuwan tace min mamanta tace inci kafin in kwanta na karba ina godiya ta fita.

Kadan naci nasha magani na koma na kwanta tare da rufe idona ina son inyi barci a wanan lokacin amma nasan zai kira idan ya kira din sai in kwanta inyi barci.

Ina zaune ina jin dan dararamun mutanen gidan duk da dai bansan akan me suke dariyan ba a lokacin aiko wayan da nake jira ya shiga kara .

Dayan biyune ko sir Aliyu ko Saudat a lokacin na mika hannu na dauko shine a layin nayi sallama ya amsa yana fadin to ya karfin jikin yayi sauki ko me tsoron Allura ki bari ai maki allura ki samu lafiya kinki saboda tsoro ?

Dan murmushi nayi nake fadin ya jikin anty can kano ko mummyna zance tunda matarkace ai ta zama mommyna ke nan ita ma.

Wa ke nan kike nufi hjy mummy kowa ita ai kinsan dama haihuwa tayi a lokacin na kuma fada maki tun lokacin mun samu brother Ahmad.

Nauyi naji nake fadin bafa ummah ba matarka da kace itama ance bata da lafiya dazun a hanya ai Na,imace kuma matata Ni,ima kanwata fa nake fada maki zakuyi sa,a da ita ai.

Sai kuma naji yace humm, meye matsalanki da matane wai maryam da kullum kike tambaya a kanta ?

Babu kawai itama ina sontane kamar yadda kake sonta tunda dai matar daddyna ne ai dole in so ta ki ko kyauta idan kinyi hakan bari zan kawo maki ita har gida ku gaisa tunda kina sonta ai.

No dan Allah da wasa nakeyi kada ka kawota please a takaice kinji saukin ciwon kan naki ke nan tunda har kika tsaya tambayan jikin wata yanzu ?

Bari kawai zanzo da ita har gidan naku ku gaisa ya sake fada nace ta dawo ke nan yace dama ina taje ai tana gari batayi tafiya ba ?

Don Allah dai ka barta kada kazo da ita yace why nace saboda zataji ba dadi idan ka kawota wajena ina dai gaidasu .

Maryam na amsa da na,am kina kishin matana ke nan nace saboda me don kawai na tambayeta to idan baki kishinta ki bari nazo maki da ita ku gaisa ku san juna kinga sai kuyi fara zumunci tun yanzu ?

Ni zan kwanta na fada na dora da fadin nasha magani kila yana sa barcine barci nake ji sosai wallahi okey ya fada yace na dai gane baki son zancen zamuyi nan gaba good night ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/2, 9:41 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊 8️⃣5️⃣ 🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login