Showing 222001 words to 225000 words out of 395027 words

Chapter 75 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Bello bello ya fado min a rai lokaci guda ranan da bello ya tareni shida abokinshi yana bina da mota lallai wani mai farar mota ya taimake mu ya rage muna hanya.

Amma ban sanshi ba dama shine na juyo ina fadin dama kaine mai farar mota dinnan da facing cap ka dauke mu ?

Yanzu dai kin yarda na sanki a kano ko don naga har yanzu kin dauka zolayanki nakeyi ban taba saninki a can kano ba sai a nan ?

Ban san lokacin da nayi kasa da kaina ba ina murmushi kawai nace amma an dade ban dauka zancen na a ranka ba har yanzu ?

Itace Saudat ko don naga tafiki hankali kuna da son kama da ita saidai kin dan darata abubuwa da dama shine kawai banbancin ku da ita.

Itace Saudat ita ke bin min ga haihuwa sai uwale sai su Abdul da aka haifa a bayana bayan na dawo da zama nan lagos wajen uncle .

Yaya kuke dashi officer har aka bashi rikonshi no need inyi karya a yanzu ga wanan mai wayon tsiyar kilama ya riga daya sani kawai tambaya yakeyi yaji a bakina.

Saina tsunci kaina ina fadin kawai family suke da mahaifinmu bansan ma ya alakar yake ba shine yaje gun kakan mu ya nemi a bashi yaro guda a wajenta.

Sai kakata ta daukeni ita da mama suka bashini dalilin dawowana lagos ke nan wajen su da zama.

Yanzu kuna da connection haka haka na jini yabar rayuwanki ya fara gurbacewa a nan meyasa wasu mutane basu san girman amana bane wai ?

Amana fa ya daukoki yazo garin nan ya barki kina abinda kikaga dama don kanki kamar mara kwabo haka ?

Baki na turo gaba alaman banji dadin zancen daya dauko din ba akan uncle dina donni wallahi uncle bai laifi a gareni gaskiya.

Ba zaki gane bane kin ko san irin sakacin da nake ganin yayi maki a rayuwa ba haka ake daukan amana ba sam ka dauko yaro ka rikeshi tsakani da Allah tankar kaika haifeshi idan baka iya hakan barwa mutane dansu shine mafi sauki a gareka.

Nayi tunanen baku da halaka dashi haka mai karfi saidai yanzu da naji nayi matukar mamakin jin wai akwai zumunta a tsakanin ku ?

Uncle mutumin kirkine haka matarshi don basu daukoni a matsayin yar aiki ba a wajensu ko wata wace basu suka haifa ba yadda kake tunane akaina.

Har gobe ina jin dadin su suna kuma gani darajata suna min komai kamar yadda zasuyiwa wani nasu kaine kake ganin sunyi min sakacin riko wanda avin ba haka yake ba.

Allah kadaine shedana saini dasu kuma ban taba saurayi ko jawo masu maza ko ace na fada wani mumunan rayuwaba a nan Lagos ?

Haka kuma basu kasa gayi min dawainiya ba a rayuwansu har wanan ranan amma kika yarda kina wanan sana,an tare da diyan arnaku ?

Kin san kuwa irin risk din da kikaso jefa kanki ban yarda da hakan da yawancin company sukeyi ba garin nan ka dauki dan mutane idan ya fada wani matsala ka zare hannunka kabar iyayyenshi a cikin kuncin rayuwa ?

Hankalina ya tashi sosai a ranan dana ganki wajen su Alh sambo don nasan ba mutanen arziki bane tun daga wanan ranan na saka a raina zan taimaki rayuwanki in rabaki da wanan sana,an .

Dan kalloshi nayi yace yes tun ranan iam telling you ban barki ba duk inda kika sa kafa ina biye dake ina duban mu,amulanki da komai naki har zuwa wanan lokaci da kika shigo hannuna.

Nasan ba zaki karbi tayina ba da nayi maki a fakaice tun a lokacin na fahinci hakan shiyasa na bi baya na hada da uncle din naki shi kuma ya amince min.

Ke nan hadin baki kukayi min kaida uncle nayi mamaki yadda yazo min da maganan sam ban dauka ku bane da farko sai ranan dana zo office din nan naga hakan.

Saidai na kasawa uncle magana akan banson aikin nan dole yasa nake zuwa wajen nan aiki daku don wanan aiba fannina bane ?

Amma aikin iya computer kin kuma iya lissafi don me ba zaki iya wanan aikin ba ina yanzu aikin gane mafufina na jawoki ga aikin nan ko ?

Ina fatan zaki daina wancan aikin don Allah hakan ba kimar ki bane ba darajanki bane meye illan wanan da aka killaceki a waje daya ?

Shiru nayi don banda amsa a lokacin ban sanarwa nan gaba sai tuki mukeyi iya bin gari da mukeyi a cikin motar nashi banga inda mukaje ba a lokacin.

Kina son wani abune nakaiki ki saya komu koma office muryanshi naji yana tambayana hakan a lokacin don haka ba tare dana dago ba nace a,a a sanyayye.

Ba zai yuyu ba nasani duk zaki koma kikan tsaya ki sai wani abu ki rika zuwa gidan hakan yakan ban mamaki matuka ?

Yana kuma saka zuciyana a zargin akwai wani abu dake sa kina hakan ko wani lokaci don haka zamu shiga wancan shagon kar kiji komai ki dauki duk abinda kika gani kina so a cikinsa kada mu koma haka hannu sake ajanunki su hanani barci da dare .

Abinda ya fada yasani dan murmushi haka kuma nagama yarda yana bina ko wani lokaci din inba haka ba yaya akayi yasan wanan dabi,an tawa ?

Shagone kamar kina kasan waje don babu daine babu a shagon ni ban ma taba sanin wanan shagon ba sai wanan ranan .

Tare muka shiga shagon dashi ni binshi kawai nakeyi muka nufi wajen turare dashi naga yana neman wani turare can sama ya daukoshi ban yarda na nuna komai ba sai zagayawa yayi dani wani waje babu komai a wajen sai zalla abaya din nan na mata lettes one sabbin yayi ya fara dan hankadawa yana duba meye size dinki ?

Bani amfani dasu ai so bansan size dina ba ai zaki soma daga yanzu ya fada na bishi da kallon mamaki pink orange red brown black white guda shidda ya zabo ya jefa a kwando red made dinkon atamfa nan ma ya zabo ya hada da wa yan nan na farkon sai wasu shoes and bag kala biyu masu bala,in kyau ya hada min dasu.

Wajen kayan shayi ya nufa iein manyan gwagwanin Nido din nan da peak ya dauko guda biyu millo bourvita sai sugar din kwali dasu liptop iri iri abu sai kace a kyauta yake kwasansu.

Muka fito ba don ya gaji da jidan kayan ba muka nufo wajen biya a yadda suke da mutanen kamar sunsan juna nake gani ban gaskanta hakan ba saida naji ance dashi za a lillasafane oga ?

Idan baka lissafa ba kai zaka biya common ban son shirme don Allah ya fada da sauri naga mutumin yana lissafi shi kuma yana danna waya ya mikawa mutumin kati ya cire kudinsa tare da kira mashi pin number din.

Ya juya ga wayan yana fadin Isha kazo nan bakin shagon ku ka karbi wani sako ina wajen aka hada kayan aka fito dashi nikan baukaya na zama a wajen .

Baki ya mutu iya shege ya samu waje ya boye dole na zama yar kallo a lokacin muna fita mutumin na aje mota naji yace ka dauki wanan kayan ku maidashi model daidai size din wanan .

Angama sir ya fada na tsargu sosai na zama speechless kan abinda nake gani a lokacin yaja mota muka fice daga wajen .

Yanzu sai ina akwai wani wajen da kike son zuwa ne kuma yake tambaya no nagode na fada a kunyace yaci gaba da tukin motarshi a cikin gwanewa.

Kada ki kara kiran gida a kan zancen nan ba zancen yara bane ki fitar da bakinki cikin zancen su na manya ya fiku sanin halinta ai shidake tare da ita.

Wayan shi yayi kara ya dauko yana fadi hello sulaiman yanzun nan zan dawo ina hanya yanzu daga haka ya kashe wayan nashi.

Ba wanda ya kara magana cikin mu har muka shiga company can wajen entrances muka hango sulaiman kafin mu fito har ya karaso wajen motan nashi yana muna sannu ya juyo gareni yana fadin maryam ya jikin da sauki ko ?

Abinka da mace lokaci guda na hade zakice gaskiyane banda lafiya din na amsa a ciki da sauki ko don muna a wajene sai bai tsaya bin kaina ba zakice bashi bane muka gama magana a yanzu don ya fito ya wuce mu few a wajen.

Sai su Ademola ne suka tsayar dashi suna gaidashi tare da fadin sir we don"t know that you niece is here all dis days is now sulaiman is telling us that she is sick ?

She is with us here suka shiga yi min sannu ina amsawa sai min kallon kwam da suke bina dashi har na shige daga cikin abina na barsu wajen.

Ajiyan zuciya na sauke na kai zaune ta hanyar yin tagumi da hannayena duka biyu sannu a hankali na soma tariyo abubuwa da dama gida da waje a cikin zuciyana.

Tabbas mama ta kuntatawa rayuwana dana mahaifiyata ta bautar damu a lokacin da sunan uwargida akan inna bata isa ta shigo mata gida ta dauka taga gidan mike kafa ba.

Wanda wanan hukuncin na mama harni ya shafa da ace mama din irin matan zamanin nan ne da wani irin kazamin rayuwane zasuyi a gidan da sunan kishi.

Sai ya zamanta ta fito cikin irin matan dauri na can baya masu kawaici da hangen nesa masu tawakkali da ruguman hukunci duk yadda yazo masu.

A yanzu wayewa ya saka matan yanzu basu yadda da wanan mulkin na uwargidanci kokarima mace takeyi a auroki bayanta tazo tace kece zata ture waje komai yawan yayanki da miji wasu amaren basu tunane sai kokarin ganin sun raba uwa da yayanta sun bar yara a wullakance gidan ubansu gida ya koma nasu dana yayan da suka haifa kawai agidan tare da jawo yan uwa da kawai wai duk akan kishi mata da yawa ke sayar da lahiransu tun a duniya.

Sun manta kishi zaman amanane a wajensu kada ki cutar kada a cutar dake har ma inkinga kina cutawane a gun miji ko kishiya find way out da darajan ki ba zai zube ba a gidan kema asan mace ceke a dama dake.

Amma sai abinda ke shirin dawowa mata a yanzu shine shirka is hard ki samu macen dake gidan mijinta a yanzu data dogara da Allah kadai bata dan leke kofan malam ?

Wai duk akan namiji namiji nan buhun kaikaine komai dadinki dana miji sai ya kumsawa rayuwanki baki ciki wata rana yar uwa gara ki hakkura din ko zaki nemi tsari kada ki nemi wanda zaki zama sanadin mutuwan auren kishiya don Allah domin ko akwai hisabin zama a gobe kiyama.

Nayi sallah na jima a zaune office din suna wajen meeting dinsu hakan yasa na kira innan mu mukai waya itace take kara min bayanin abinda ya faru tiryan tiryan .

Take fadin baba ya dauki zafi da kowa a gidan tunda ya fita bai dawo ko cin abinci ba ranan dole ai akwai damuwa sabo wani abune dake tafiya a jinin dan adam.

Na dai kara tausan innan mu nace don Allah inna kada ki saka kanki cikin zancensu ki barsu suyi abinsu don sunfi kusa tare kuma kika samesu shima ba dadinshi bane ace ya rabu da mama a wanan shekarun nasu ga yan mata kamar su yaya a gabanta.

Nasan yayi mata hakane don tashiga hankalinta a nan take fada min cewa aiko da alama ta girgiza don yadda tayi ba,a taba tsanmanin hakan gareta ba yayace don malam ya furta kalman saki a gareta take kuka shabe shabe da hawaye tabar gidan nan abin gwanin ban tausayi wallahi yau ba bakin nan da zabure zabure gareta a yau saitaba ko waye tausayi sahurace daki tun dazu tana ciki tana kuka tun safe.

Allah sarki dole tayi kuka inna kije ki bata baki don Allah haba dai yarinya in tafi ina suda suke ganin saboda mune aka saki uwarsu aisai ta dauka sheri nazoyi.

A a inna koma me zatace kije dai ki dubata don Allah kiyi hakkuri ke murjafa yau malam yana fada tana bashi amsa wai ashe dama tana har shaye shaye ashe iyayyen sun sani suka boye muna.

Ita wanan wake batunta inna saima tayi abinda yafi wanan ai ba damuwanta bane indai yaya murjane harda barazana tayi min da zata fita wai nasa ido inga abinda zatayi min nace sai alheri don bani ganin komai insha Allah tunda bani nace ya saki uwarsu ba.

Haka tace maku inna tace haka ta fada garam da garam a gaban kowa shine malam ya bata amsa yace iyaka dai ta turo mashi yan daban da suke tambada tare ayi mai duka ko yankan rago dai ko ?

Kiji har yan daba take bo na taba jin labarin hakan amma na barwa raina zancen ban taba nuna mata nasani ba da nice yaya sai unguwar nan kaf ansan da zancen hakan gareni.

Allah ya kyauta Allah kuma ya fita ba zai bata iko a gareku ba insha Allahu na kara bata hakkuri taje ta duba yaya sahura din a dakin tace min taji.

Ajiyan zuciya na sauke ina gyara zama tare da kallon saman office din ina furzo iska yau dai gidan mu ba dadi ke nan haka za a wuni a cikin bacin rai gaba daya gidan kenan.

Shirin fita nakeyi zuwa gida don time din tashin mu ya kusa yayin da har lokacin basu fito daga wajen meeting dinsu ba da alama meeting yayi zafi ke nan a ranan.

Na hada kayana ina shorin mikewa naji sako ya shigo min a wayan na dakata ina dubawa sakone daga gareshi ya turo min wait for me please.

Banda number shi a wayana da nayi serving amma nasan shi din ne a lokacin don a duniya ba wanda zai turo min hakan .

Wanan sakon yasa na koma na zauna yakai tsawon mintuna arba,in a lokacin zuwanshi da kiran innan mu yayi dai da zuwanshi ina daga wayan daidai lokacin ya tsaya irin tsayin gajiya din nan ta hanyar dora hannayeshi a weast dinshi.

Na soma fadin inna yana jin haka ya juya ya ban baya yana sasauta nick tied din dake wuyanshi na soma fadin ya akayi inna baba din ya dawone ?

Bai dawo ba na samu Sahura din bata da lafiya shina na bata Paracetamol tasha a,a inna taje kemis nace hakan wai ba kudi a hannunta.

Ki bata dubu biyar inna sai in turo maki dashi zuwa anjima tana fadin tun jiya na kwashe kudin na turawa wanan matar mai turare okey bari kicewa Saudat zan turo kudi yanzu.

Ya juyo yana fadin ina mota inkin kagama kai na gyada mashi alaman to ya juya ya fice nima dagawa nayi ina sauraren inna har mukai sallama na fito da tarkacena na rufe kofan office din .

A motan na sameshi kamar yadda yace din yana zaune kamar yana neman wani abu a cikin motan na fito na zagaya na shiga don a bude motar take.

Yayi key muka fara fita daga wajen shiru banyi magana ba shima haka na dab lokaci sai can ya juyo yana fadin don me kike barinsu babu kudi ?

Meye amfanin neman kudin da kikace kinayi a nan din dan kallon mamaki nayi mai sai kuma na juya nayi shiru bance dashi komai ba.

Ki ban number da za a tura masu kudin da sauri na kalloshi da mamaki bakiji bane ki ramin number yanzu ?

Na dan gyara tare da nisawa na zaro wayata a cikin jakkata na fara neman account din Saudat da nake tura masu kudi a ciki idan zanyi sako.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login