Showing 90001 words to 93000 words out of 395027 words
Chapter 31 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
a cikin gidan nan zata soma daba min yuka ta nasa min magana iya son ranta akan hakan don haka kabari na fida hakkina a matsayina na ubanshi.
Kai habibu maza kayi shiru kabar ya sauke nauyinsa na uba zuwa ga dansa Alh yana da gaskiya daya dage kan son sanin ainihin inda Aliyu ya samu dukiyarsa don tseratar da mutuncin ahali nan gaba.
Kwarai kuwa malam liman ni kaina naji dadin hakan da Alh yayi tun a ranan da bai tsaya wani ja,in jaba ya fito da wanan maganan tare da kin karban kwandala daga dukiyan yaron nan daya turo mashi.
Duk da ya riga ya karba a baya cikin rashin sani don wanan gidan da Alh yake da iyalinsa a yanzu gidan yana matsayin Aliyune don kuwa shiya famshi gidan a hannun wanda ya saya a wurin Alh.
Wani kallo gaba dayansu suka aikawa Gadanga din dashi na mamaki malam innuwa yace kwarai malam liman gidan nan a yanzu zaman Aliyu yakeyi bana mahaifinsa ba.
Baku mamaki bayan an sayar kowa yasan halin Alh sabo aida mallakinsane da tuni ya turowa Alh yabar mashi gidan da iyalinsa su nemi inda zasu koma.
Sai Allah ubangiji ya gyara lokaci yayi da haihuwa zatayi rananta ina ji na kira Aliyun na labarta mashi komai ya turo da kudi muka bawa Alh sale nasa kai kuma Alh ka karbi saura ciko daya saura lokacin duk a zatonka Alh salene ya sai gidab.
Kallon mamaki yake aikawa dan nasa Aliyu hannunsa sagale daya nuna Aliyun dashi yana nufin kai din Aliyu dai Aliyu ?
Kwarai kuwa Alh yakubu don yanzu duk tunanen da zakayi kan Aliyu ya wuce haka da kake zato ka dai san Aliyu ba zai taba kaice hanyar Allah in tsaya in goyi bayanshi ba haka ?
Ina hakane don kuwa Aliyu ba kaucewa tarbiyan da muka bashi ba a baya yana nan har yanzu saman tarbiyan dakai mashi na tsoron Allah da tunawa da za a koma gareshi watan wata rana.
Nasan zakai tunanen hakan da nake nunawa Aliyu ka dauka mu bamu damu da halin da muka ganshi a ciki ba don zuciyan mu ya kwadaita ga abin hannunsa ko mun nuna rashin kulawa kan duk wani hali da muka ganshi ciki a yanzu.
A,a bamu bar Aliyu hana ba kamar yadda ku nan kuka fita zancenshi karshema kuke yadda cewa ya mutu ya salwance a cikin duniya surin ta,addanci dago kai Alh yakubu yayi ya kallo malam din.
Yace kwarai ba abinda mai dakinka bata fada kan yaron nan ba cikin garin nan bayan wanda ta kuma mai lokacin da yake gida a zaune alhalin ita tayi sanadin daga tsameshi cikin duk wani harka naka da kakeyi da yayan ka gidan nan.
Mu bamu tura Aliyu yabar garin nan ba saida rakiyan malam hamza gashi zaune hamza bai dawo garin nan ba saida yaga tashinsu a lokacin wanda kuma ya kaisu din da danshi muka dauko duk wani bayanai nasa.
Hamza gashi yana bibiyan zancen Aliyu kusan ko yaushe munaji daga gareshi shima haka yana ji a wajen mu mundai kyaleku iyayyensane don kariya garesa.
Saboda abinda ake fada mara dadi akan yaron bayan haka anyi abinda za a ingiza keyarshi ta yadda ba za a kara jin duriyansa ba tun kafin ya tafi muka fahinci hakan duba ga yadda yaron yake ji a jikinsa ana turashi tako wani hali yabar garin nan ya tafi nisa inda ba ajin labarinshi.
Allah yasa akwai shakuwa cikin magana kan a barshi ya tafi ya samu fada muna hakan a lokacin haka yasa muka fahinceshi muka gano akwai matsala.
Munyi shirune a lokacin don ko mun fada a lokacin akwai tsanar yaron a zuciyarka ba lalai bane ka yarda da abinda zamu fadama din kan yaron.
Donshi yasa bamu tsaya neman ku ba muka shiga da fita wajen ganin wancan kullin da akai masa ya karye a saukake .
Allah da ikonsa munyi nasaran hakan koda zamu laluboshi kuma mun samu yayi karfi ga aikin da suka saka kansu a can na ma,adanai tare da sauran albarkatun kasa na Africa tunda sana,an mahaifin shi wancan yaron ke nan.
Munyi murna da hakan sosai da wanan labarin yazo muna gashi a zaune a lokacin shiya hanamu fada maku halinda yake ciki wanda yin hakan yabarwa kansa sanin dalili kuma mun rike mashi sirin hakan.
Don ko ita jiddah gata nan ya nuna Alh bamu taba barin tasan musan halinda Aliyun yake ciki ba balle taje ta fada a wani wajen har a san da hakan.
Abu dayane shine duk alherin da zai aiko maku dashi iyayyensa sai mu nuna cewa daga wajen mu ya fito duk da musan Alh da karfin hali bako yaushe zai iya karban kudin daga hannun mu yasa muke dan tsankwara mashi zuwa wani lokacin kuma mu sake bashi a ma banbanta lokuta.
Ya kallo malam hamza yana fadi ga ragowa kudin nan tsoron sanin halishi yasa nabada shawaran a je kudin nan har zuwa lokacin nan.
Mun san kayi gaskiya kuma ko can mun tsanmaci hakan a gareka Alh amma yanzu ga layin shi mr Abraham din zaku iya kiransa idan kuna son jin komai daga bakinshi.
Shi din mutumin kasan bauchine amma mazaune kudu yana sana,an mai da fataucin kayan ma,adane a kasashen ketare .
Tunda Alh yakubu ya dukar da kai a wajen bai dago ba har akayi maganan da za ayi da saura bayanan daya dace na fahinta Alh yakubu ya kasa dago kanshi suyi arba da dan nashi.
Saida shi Aliyun ya soma magana yana fadin duk wani motsi na gidan nan yana a kunnena tunda na dawo kasan nan nake da labarin komai game da gida .
Sai lokacin mahaifin ya dago kai ya dubeshi duban daya kasa jurewa hakan ya sada kanshi kasa don kunyar dan nasa da yake ji a lokacin yadda yau malam innuwa ya tuna mai da abinda ya faru lokacin tafiyan dan nasa .
Bawai ya rasa avin bashi bane haka kawai yake ji a lokacin ya tsani dan nasa ko ganinsa baya son yi don haka koda tafiyan nasu ya taso baijin zai iya ba dan nasa ko kwandala daha cikin dukiyanshi a lokacin.
Haka kuma irin borin da hjy Naito ta tasashi a gaba tayi mai na cin mutunci kan kada yaba Aliyun kudinsa in yayi gaka ba zasu yafe mai ba.
Sai kuma ace yau wanan dan nashi Aliyune ya dawo kasan yake masa abin arziki haka wanda kaf diyan Naito din ko kadan ba wanda yasan zafinsa irin hala balle a tallafa mai.
Ina zuwa Aliyun ya fada ya mike ya bar wajen zuwa dakin mahaifiyarshi daya kagu dasu kebe da ita a lokacin.
Gwani ban tausayi koda yayi sallama ya shiga tana zaune sun hada kai ita da yayanta mata biyu jannensa ke nan ko wanin su idonsa yayi ja saboda kukan da suka taya mahaifiyar suyi a dakin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/27, 10:15 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,
3️⃣0️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15- HAWAYEN KADA🐊 1000.
_Account No._
_*ZAINAB IDRIS MAKAWA*_
2254380105
ZENETH BANK
PHONE NO.
08036959257
Zancen tafiyan mu da mama taji an soma ya daga mata hankali bamu san yaya tayi da diyanta a dakinsu ba akan zancen tafiyan nawa .
Sai ga kakarmu tunda safe tayi sallama a gidan mu muka dinga fitowa daya bayan daya muna gaida ita da kwana da zuwa tana amsawa da izza har aka kawo kaina na fito lokaci daya da mahaifina da shima fitowanshi ke nan da inna taje ta tayar dashi ga umma din tazo.
Suka gaisa kafin ni na daga zan bar wajen ta soma fadin ke akan zancen ki nazo gidan nan don ba zancen komawan ki Ikko din nan .
Hakan da naji yasa naja na dan tsaya anan naji baban mu yana fadin saboda me kuma umma munyi magana dashi Alh Faruq din yace mun saboda zancen ita Mairo zaisa su koma a satin nan mai zuwa don zata fara karatu a farkon watan nan.
Babu zancen komawanta a yanzu don ba ita kadai bane ai yarka don haka kowama yana son cigaba ba ita kadaice za aita turawa tana dangwalo arziki ta dawo suna ci ita da uwarta da yan uwanta su ma sauran dakin ai suna son hakan suma.
Umma wanan zance ina yafito ita Rakiyanne ta bukaci hakan ko ra,ayinkine ke umma nayin hakan garesu don nasan babu dan Rakiya da zaije ya zauna yanawa wata mace bauta kona kwana dayane balle na dindindin irin da mairo tayi har sukaji dadinta.
Su daban ne daba zasu iya hakan ba ita taje tayi haka nace hakan kuma za ayi wanan yar ba zata koma ba wata daga dakin Rakiya zata tafi yanzu.
To ai shike nan umma yadda kikace hakan za ayi din tunda kinga hakan yafi dama ai ita Rakiya din ta tura mairo bani ba umma yanzu kuma taga dacewan zuwan nata yayan ai shike nan ko ?
Ka daiji mena fada ai don haka abar zancen komawan ita wanan din a yanzu ina Rakiya din muji wace zata bayar din a dakinta .
Tasawa mama kira ta amsa dama tana kusa ta fito but tace gani ai mama to kin daiji me nace ai saiki fada muna wace zata tafi a cikin yayan dakin naki ?
Tau bamu gama shawara dasu ba tukun har yanzu don kowansu ya nuna yana son zuwa sai umma din ta tare da fadin kinsan dai mutum dayane zata a cikinsu dai ?
Na sani amma bari na koma naji inda shawara ya tsaya sai naga baban mu yana murmushi muna hada ido naji yace jeki abinki mairo Allah yai maki wani mafita dayafi wanan din.
Na amsa da Amin ina mikewa tsaye don barin wajen to lalai kan don ba zancen komawa gaskiya tunda wasuma suna son hakan ba ita kadai bace kuma ?
Raina ya baci sosai da jin huluncin umma din da bansan meyasa take nuna muna irin halin nam ba tankar mu din ba jininta bane wani lokaci idan tayi muna wani abin.
Ba abinda ya dameni kamar zancem karatuna don haka ina shiga daki na zauna nayi shiru a waje daya bakin gadon dakin mu.
Me zaisa ki sakawa kanki damuwa akan hakan abinda kika samu a wajensu Allah yasa ki more ai kowa da halinsa ake zama dashi don sun ba shi zaisa ita antyn naki ta rabu dake ba ai.
Inna zancen karatuna ya dameni sai kuma Amira da rashina zai jawowa damuwa shine kadai abin damu in bashi ba me zaisa in damu da hakan .
Ko banza hakkuri nayi nakai haka a gidn tare dasu tunda mahaifiyar anty kamar Annabi da kafiri muke da ita tace bata kaunar duk wani dan kano.
Nan na soma ba inna labarin da ban taba fada mata ba tun zuwana akan irim rayuwan da nakeyi a can sai lokacin saudat ta dago tana fadin.
Wanan duk makircin mamace bakiji me umma ta fada ba yanzu dama sun riga da sun shirya hakan a tsakaninsu zuwa dai tayi yanzu ta fadawa baba din.
Ba sai su anty din sun yarda zasu dasu ba ni duk wanan abin a shirme na daukeshi ai ba gidan ita umma din bane da zata zo ta yankewa mutane hukunci tunda safe haka.
To ki dai iya bakin,ki don Allah kin san dai halin umma a kansu yanzune zaki ja muna zagi a wajenta don haka kowa ya kama bakinsa banson ji kuma.
Ke Ai da kika shige daki da yaran kuna kus kus dasu zagina kukeyi kome a dakin ?
Naga inna ta mike da sauri tayi waje wajen umma din tana fadin ,a,a umma mu zageki kuma muce maki me umma ?
Nina sani tunda ina nan waje nasan dai abinda kukeyi ke nan a dakin tunda anga na kafa dokan da kowa zai samu inga kara ai ita batayiwa yarki bakin ciki ba lokacin da zata tafi din.
Meye na bakinciki cikin zancen nan inna da ita da yar uwarta ai duk wanda yaje daidaine don ba bare a cikin su da ita ba zancen da nayi kan maganan ku a dakini.
Ta murga baki irin na tsofi tana fadin a daiyi ni dai nasan ba ita daya bane balle yadda yarinyar nan ta dawo garin nan tana kyali wa zaiki hakan ga nashi sai wani kuma yaje ya dangwalo arzikin shima ai.
Dan yayan muryan da taji daga dakin mama yasata fadin me kuma wai ko kunki shirya kankune kuma kufa matsalata ke nan daku ba natsuwa.
Ai barsu su zaba din kawai inta fito ta fada muna mai zuwa wanan karon baba ya fada umma din tace balle kasan halin Rakiya magana ba magana kan dan wanan magana tazo muna da kuka kan bata yarda ba sai aje da yan dakinta kuma nace ai tun farko haka naso amma taki yarda sai yanzu.
Umma hali dai kejawa mutum alheri a rayuwa ko ita din da taje ai halinta yasa ta zamo hakan har suke kaunan junan su sukai sabo haka da ita.
Na dawo mama ita Sahura tace zata itama murjan haka amma yanzu gasu suji bafa wai zuwan ba wace zataje tayi abinda ake so din.
Ke nan kin kasa tamkwasasu tun a daki ita wanan kan ai nake ganin tayi girma ga zuwa saidai ita murja din dai naga kamar da dan dama abu daine naki Rakiya yaran nan sunkai muzalin aure ba yau ba gaba dayansu sa,oinsu duk suna dakin mazansu a yanzu .
Ina ke ina tura yara haka kuma zuwa har ikko nan ma yaya aka kare dasu don Allah balle har gari kamar ikko bafa talla ko saida abinci bane ?
Umma in baiyi a barshi naga itama Mairo din ai sa,ointa suna dakunansu a yanzu bai zama magana ba sai na wa yan nan din yanzu ?
Allah baki hakkuri Rakiya abinda na hango na fada tunda kinga haka yafi aishike nan ko sai a tsayar da wace zata kafin tafiyan nasu.
Shi kuma farukun zan samu yaya a gidanta in sheda mata sauyin da aka samu daya dace ayi din yanzu don haka ni zan koma kun daiji ba zancen komawan yarinyar nan kuma ikko.
Ta mike da kyar babama ya mike suka nufi hanyar fita dashi har takai kofa taja ta tsaya ta juyo tana fadin to kada inji ko naga wani rigima ya taso daga bayan hakan.
Ka daiji mena fada yanzu na yake hulunci ba itace zata koma ba kuma daya daga cikin yan uwata zasu kuma suma su dangwalo irin nasu arzikin .
Uwalece ta shiga gidan anty Fati bayan tafiyan umma take bata labarin abinda ya faru cewa da umma tayi ba za a koma dani lagos ba da wata cikin yaran mama za a tafi.
Kam kazan uban nan wai wanan matar meke damun rayuwanta don Allah bar yar iska ko dawanau babu mai zuwa a cikinsu balle har ikko ina Sariya zata iya yan iskan yaran nan fitsararu marasa tarbiya.
Ita dai data bata su ta zauna da abinta ta girbe sherin da take shukawa mutane a rayuwansu ba inda za a dasu kice maryam ta zauna a shiri kawai .
Ta daga waya ta kira anty Sariya din tana sheda mata abinda yarinyar tazo ta fada mata tace hauka mama keyi kawai ba inda zata da wata inba maryam ba don haka su kyale kawai.
Duk wunin ranan haka na wuni kwance a daki kina jin dariyan mama da yaranta suna sakin magana mama harda cewa