Showing 117001 words to 120000 words out of 395027 words
Chapter 40 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
iya dole in fita neman abinda zan dan saka a cikina don idan ba karya nayi ba rabona da abinci kwarai tun karin safen jiya da nayi da zan fito gida shine a cikina har wanan lokacin.
Tafe yake yana sharan zufa dake tsiyayyu mashi a saman fuska don zafin ranan da akeyi garin mai kuda da dole kadai zaisa mutum fita a lokacin.
Saidai mamakin abinda ya faru ya hanashi jin kaifin ranan dake sukan ilahirin jikin mutum din idan ya shiga ba komai ke mashi yawo a kai ba sai cewa da akayi ba a daukansu aiki a company ko ince shagon uban nasu da tazama dila yanzu.
Duk yadda akeyi yayi ya zubar da girmansa da kimarsa na yaya ga Aliyu yabi long process din da duk ake bi mutum ya samu shiga amma a karshe sai cewa akayi dashi yaje yayi hakkuri gaskiya sunanshi bai fito cikin list din daukan ba.
Habib ke nan dan gidan hjy Naito daya nace ya kayar da girmanshi da kimarshi kada dama ya wuceshi yaje nin dongon zangon daukan ma,aikatan shagon mahaifinsu da kullum sukeyi saboda cika da kasuwa dake ci yanzu wajensu.
Saman kujera dakin mahaifiyar nasa ya zube yayi shiru yana mai tunane a kasan zuciyarsa watau da akace dan uba ba karya bane wanan kalman ta dan uba da bahaushe ke fadi.
Lokacin mahaifiyarsu dake uwar daka kwance ta samu ta fitodon jin motsin dan nata da yayi sallama kafin ya shigo ya zauna din.
Ja tayi ta tsaya tana kallon yanayinsa kafinta furta a,a yaya kuma na ganka haka a hautsane kamar wanda aka biyo ?
Ya dago ya dan dubeta yana fadin ai dole mama daga kasuwa nake talaucin nan ya isheni mama naira goma yan neman gagarata saidai in gani a hannun mutane.
Fuska hjyn ta daure lokaci guda ta zauna tana fadin ni yanzu me zance daku yanzu lokacin da nazo ma da zancen na baka sharawa aiki kayi.
Mama waini Aliyu zaice kada a dauka aiki a wajen baba kuma baba yaji komai amma yace shi ba abinda zaiyi tunda Aliyun yace haka.
Kiji babafa mama wai mune abin gudunsa mune muka koma abin kyamarshi a gidan nan wai Abba yace naje nayi hakkuri tunda ba a daukeni ba.
Saidana fadama kada kaje kace ina nafito yanzu gashi ai na fadama wa yan nan mutane ko yuka aka basu su kashemu zasu iya kashemu tunda ba kaunarmu sukeyi ba.
Yau nasheda hakan mama zamu zuba dasu a gidan nan sai na bankado duk wani sirin da suke boyewa na fadawa duniya inyaso duk a taru a mutu.
Kada ka soma koma meye mu mukajawa kan mu ai ni banga laifinsu ba sam ka manta abubuwan da mukai masu muma a baya ?
Me mukai masu kakan fara zancen ka ke nan ga gaskiya sai kaki ko munyi masu ai munyi daidai tunda suma da sheri suke bin mu.
To koma dai meye ba ruwanka da zancen ina ya samo dukiyarshi kakai Alh bin kwakwafine tunda kaga ya kyale wanan zance ba dukiyan haramun yaron nan ya samo ba.
Koma me akai muna Hashim yaja muna komai da baiyi wanan abin ba ai duk haka bai taso ba son haka ka barsu kada kazo ka kara bata zancen a tsakanin mu kuma.
Ya dade bai baci ba hjy din dake zaune ragwaf cikin takaici ta fada tana hararan dan nata habib dake hana ayi zancen kamar bashi yaje ya kwaso wullakanci ba yanzu wajen kanin nasa ya dawo kuma yana wani tare zancen kada a fada.
Ya dan tausa murya yana fadin ba hakana bane mama aishi ya sani ya nuna dan uwan nasa yace neye bamuyi mashi ba a baya muyi mai kuma musa yaran shago suyi nai har yai fushi ya daina zuwa shagon ga baki daya don yanzu yai muna ai ramawa yayi nake gani.
Shiru hjy din take hankalinta nacen tana tunane ta inda zata bulloea zancen wanan yaron don ba zata zauna suna hadiyan takaici ita da diyanta ba su zamo yan kallo a gidan alhalin sune a matsayin manyan gidan suya kamata ace sun kai wanan matsayin ba Aliyu da uwarshi ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI KEBBI STATE
[8/10, 10:19 AM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
3️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15- HAWAYEN KADA🐊 1000.
_Account No._
_*ZAINAB IDRIS MAKAWA*_
2254380105
ZENETH BANK
PHONE NO.
08036959257
Sai daga baya na kula wajen da nake fitowa insha iska wani lokacin nane wajen zaman wa yan nan masu kitso a kai da nake gani gungun samarin makarantar mu da bajin yarensu nakeyi ba.
Bandani da suke bari in zauna na kula ba wani mahalukin dake zama bayan ire irensu a wajen nima dai zan zauna ina karatuna suna tsabgansu na shedanci wani bi kuma karatu zaki samu sunayi a tsakaninsu.
Ance yau da gobe bai bar komai ba cikin irin haka har sabo ya dan fara shiga tsakanina dasu na gaisuwa sukan min tayin abinda suke ci kosuke sha saidai inyi murmushi ince nagode ban taba karba daga garesu ba.
Duk ko da matsun da nake fuskanta na rayuwa da zai iya sa ingudu ko in fada wani hali marakyau Allah bai nufeni da tunanen hakan ba a zuciyana.
Nasan komai na dan lokacine watarana haka zai wuce zai zama labari a wajena idan nayi hakkuri burina bai wuce inga na samu ilimi ba a wanan wajen mai tsadan rayuwa tankar ba a Nageria kake ba.
Dan kudi mota taxi da Paapa ke ban a yanzu ya daina ya kuma daina rage min hanya ina nake ganinshi nida zanyi kwanaki ban sakashi a ido ba tunda matarshi ta nuna ko gaisuwa bata kauna yanzu tsakanin mu.
A cikin irin hakane wata rana muna zaune a wajen da nake hutawa din a cikin garden din makaranta babu kowa cikin abokan zaman nawa hakan ya ban daman sakewa inyi bitan karatuna da kwana Daga inda nake zaune na hangosu tafe su ukku bayan sun iso mun gaisa suka zauna dayan ke tambaya ina Oke bai shigo bane naji yarinyar dake cikinsu na fadin yaje wajen kitson kanshi.
Mamaki naji dama zuwa sukeyi ana masu wanan abin wai kitso wani dambala ake zana masu akai kuma su biya hakan yasa bansan lokacin dana tsoma masu baki a zancensu ba.
Ina fadin in dai wanan da nake gani akankune ai zan iya wanda yafishi kyau suka kalloni ita macen take fadin da zaki iya aida mun huta da yawon sallon muna jiran layi.
Kizo in gwada a kanki a gani na fada ta dan make kafada tana fadin saidai ki gwada akan bisi shine zai jure jagwalgwale niba kowa bane ke rike min kai da sunan kitso.
Zakiyi missing yan mata don ba karamin kitso na iya ba kuwa da kinsha ruwan kudi don wanan da kike kira da shiririta kinsan nawa mukeyinsa kuwa ?
Almost ten k muke zubewa koma fiye da hakan na kwebe baki cikin mamaki kudi sunyi banza ga yaran nan duk da alama ya nuna sudin akwai hali ga iyayyensu don alama ya nuna hakan a tare dasu.
Don irin jiji da budawan da sukeyi a school din wa sauran dalibai ni nakanyi mamaki don akwai ranan da wata classmate dina take tambayana banjin tsoron zama kusa dasune zasu iya komai fa a cikin school din nan sai ban damu da abinda take fadi ba tunda banga sunyi daban da sauran dalibai ba.
Gashi din kuma basuyi min komai ba duk daba wani kula juna mukeyi dasu ba amma akwai mutunci sosai tunda muna gaisuwa a sanadin zaman kusan waje daya yasa an fara dauka ko tare muke dasu.
Yau kusan sati ke nan banji duriyan Paapa a gidan ba gashi kuma ina tsoron tambaya kada tambayan ya zama laifi gun uwar dakina da a yanzu muke yau dadi gobe daci da ita .
Don wata rana sai kice ba wani matsala a tsakanin mu muna nan a yadda muke da farko da ita wani lokacin kuma ina dawowa zan fahinci yan kai na kai don yadda zata sha min toka gaisuwama da kyar take amsa min shi a ranan.
Da ganin hakan gareta nakan kiyayyi kaina da ita in koma kamar bani gidan kowa zan zauna dashi tso daga ita har yarta da yanzu tayi wayau sosai ta iya magana sosai suna zancen sakata makarantane ma.
Hakana cikin karfin hali na daure na sameta da zancen kudin school dina da yanzu muna shan matsi muda bamu biya ba ana batun fara tozarci kamar yadda sukewa mutane.
Hankalina ya daga sosai da zancen kudin dole yasa na samu anty da daddare a falo tana zaune ta kunna tv ga waya kuma a hannunta ganin hakan yasa na juya zan koma harta gama wayan.
Lafiya kinzo kuma kin tafi kin koma da baya ba magana kikazo dashi ba dama na juyo tare da fadin dama zan bari ki gama wayane ai na fada cikin inda inda nake maganan don yadda take min magana a tsatsaye lokacin cikin tsana a fuskanta.
Kasa magana nayi na juya kawai na koma dakina muma dakin kwance ta kwala min kira na ansa nazo na sameni ta azaune tajuyo tana fadin wai meye kinzo dazun na dan kai zaune ina fadin dama akan zancen school fees dinane nazo in tuna maki.
Tankar bata san dani a wajen ba tun bayan data dago fuska ta dubeni ta mayar da kanta ga tv tana kallo
Bata kara bita kaina ba balle tayi min magana kuma akan zancen shiru nayi tare da tunanen abubuwa da dama a zuciyana.
Na mike da kyat don zuwa dakina lokacin naji muryanta tana fadin Maryam ke nan aini na dauka abin girma da arzikine bansan da biyu iyayyenki suka turo muna ke ba.
Da sai nagama wahala dake a sakama min da tsiya a kwasoki kamar tarkace wai an daura maki aure da mijina to abin Allah gari da yawa maye baicin kansa ai.
Naji naji plan din ku kedasu wallahi maryam kin ban mamaki sosai a rayuwana musanman ma iyayyenki yadda nasoki naso su don kawai yanayin dana gamsu a ciki amma waini za aiwa sakaiyan sheri irin na dan adam.
Haba anty zargin ya isa haka don Allah dani da iyayyena bamu san wanan maganan dakikeyi ba a yanzu komun sani ma mu ba butulai bane da zamu manta da alherinki mu saka maki da sheri.
Nima ina fatan in zamo kamar kowa ingina ramin kaina ba sai wata tagina inshaga ba don ba macijiya nake ba da ban gina ramin kaina saidai inyi mamaya.
Wallahi ko maza sun kare a duniya ba zan taba auren mijinki ba yarda da amana nake zaune dake kamar yadda kika nuna min tun farkon zuwana garin nan .
Inma wani ya fada maki hakan kika yarda maishi ya fada makine don ranki ya baci dani dama ban taba zaton zaki yarda wani mahaluki ya hadani dake ba anty don daukar uwa yaya nake maki har kasan zuciyana.
Maryam ashe da gaskene tunda har kin samu courage din tsayawa gabana yau kina fada min magana haka yada kikaga dama lalai biri yayi kama da mutum.
To bari kiji indai Paapa koni zamu biya kudin don kiyi karatu mun daina a gidan nan sai kisan dabaran da zakiyi yanzu matukar kina son karatun ki yacigaba.
Sai kisan dabara yanzu kuma na zata abin arzikine zaki zamo min yasa na bada goyon bayan zuwanki karatun tunda da wani manufa kikazo min ai shike nan yanzu kuma.
Paapa kuma dai ba a garin nan yake yanzu ba yana inda aka mayar dashi ko kafin yazo nan yanzu sai ya dauki lokaci mai tsawo bamu ganshi ba so yanzu dabara ya saura gareki.
Da baya baya na bar falon a cikin kuka don nasan karshen karatuna yazo ke nan kamar yadda ta fada da bakinta wani dabara nake dashi a bayan Allah da Annabinsa bansan kowa a garin nan bayan Allah dasu din.
Ooh kuji kema inda dadi don nice kuka so jefawa a cijin bakin ciki haka ai saida aka fada min naki yarda da zancen mutane gashi abin nason zama gaskiya.
Banda wauta irin naku me Paapa zaiyi da mace irinki haka mara ma,ana ni tausayima kike ban shiyasa ba zan koreki gidan nan ba a yanzu.
Daki na koma nacigaba da kuka don kunnena ban iya jure sauraren kalamin dakw fita bakinta a lokaci kamar wace tasha wani abin maye a ranan.
Nayi kuka kamar raina zai fita wanda yasa washegari na kasa fita duk da nasan konaje school din yana da wuya su barni in shiga aji in zauna.
Hakan yasa na share kwana uku cur tare da weekend ban leka school din ba ban kuma fasa aikin da nake mata ba illa iyaka ba wani dogon sakewa a tsakanin mu yanzu sosai.
Ranan monday haka na shirya da fargaba zuwa school din duk da nasan abinda zan sama amma nayi addu,a Allah yasa su barni in samu attending class a ranan.
Saidai zance kamar addu,an bai karbu ba don kuwa da kazo dole saika nuna resit dinka zaka shiga class din koka zauna awaje inda muke zama dole na nufa na zauna cikin wani yanayi mara dadi .
Ina zaune nakai kusan awa daya da rabi a wajen zaune duk daba lale bane ka fahinci abinda ya fito dani lokacin.
Omo,ge waitin you de do there by dis time muryan Ozil ne abokin su Oke da suke zama tare duk da ba sosai yake zama a wajen bashi sai jefi jefi yakan zauna.
Amma duk da hakan saboda kula na shedashi duk ya zauna su kansu suna jin dadi duk ranan daya shigo school din don a ranan akwai bushasha da suke kira da hoszily .
Me i no want dis kind of wahala dem de send people out of d class becouse of school fees ?
How many people de go send away today na d hol school go go out abi na ,,,,,,
wait woow na bcous of d school fes you too stop coming to school last week abi ?
Cikin haushi na bashi amsa da fadin inshine bani kadai bace ai ban biya ba don haka meye damu wanka dani sorry miss nayi shishigi da yawa ko ?
Nasan baki zama wurin nan ana aji baida matsala idan ba damuwa zakiyi iya tashi muje in biya maki tunka saura su fito koda yake no need sai mun tafi tare ban account dinki na tura maki kije ki biyasu.
Yadda yake magana kamar da wasa yasa ko kallonshi banyi ba lokacin saida naji ya maimaita fadin ban number account dinki.
Yasa na dako kai na dan dubeshi yana tsaye da wayanshi sabuwa fil kamar yanzu ya cire a kwalinta.
Cikin gatse na karanto mashi number kamar a mafalki ba afi second uku ba naji alert na sauka min a waya na dubu saida na mike tsaye ina nuna shi fuska a dake ya mike da niyar barin wajen.
Wait please hannu kawai ya daga min ya nufi inda ya aje motanshi nan ya barni tsaye cikin mamaki da ikon Allah.
Kakakarakaka inji yan magana don ga koshi ga kwanan yunwa ban taba zato ko tsamanin da gaake guy din nan yakeyi ba sai gashi yai min bazata lokaci guda haka.
Biya zanyi ko neman shawara zan tsaya zancen uwar dakinane ya dawo min a raina inda take fasin mijinta a yanzu ina tsaya jiransa yai min nisa tun wuri insan mafita akan karatuna.
Me hakan ke nufi ysnzu