Showing 336001 words to 339000 words out of 395027 words

Chapter 113 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

mamaki lokacin dana shiga yadda salma da kurciyarta haka ta bari ta koma kazama.

Dakin sai zarnin bauli da yakeyi na yara kona bayine ta shiga kurya ta fesa turare ta fito nan muka fara gaisawa nake fadin.

Ashe Bello ya samu lalurane haka kuma ni wallahi banji ba sai jiya da nake cewa mommy ai zan shigo in ganki wanan karon don da niyar haka nazo garin nan shine mommy ke fadin mijiki ma nanan yana fama da karaya a kafa.

Allah sarki wallahi na zata ko kinjine kikazo gaisheshi ai a,a ni ke nazo gani wallahi Allah dai ya bashi lafiya ina yara na tambaya ?

Tace suna can wajen hjy suna kallo sai naji wani ir8n tausayinta ya dira min a zuciya gashi da ganin zaman nasu har yanzu ba dadi a tsakaninsu yadda ake fadi.

Take fadin amma wallahi naji dadi mairo da kikazo gidana yau idan ina tunanen da sai inji kamar lokacin ya dawo baya wani lokaci har kuka nakeyi idan na tuna yadda muke dake kaddara tazo ta rabamu kuma.

Muka dan soma hira dai ina tambayanta sauran kawayen mu da muka taso tare cikin unguwa su ta fada min inda suke wasu kuma tace bata da labarinsu lokacin nace.

Ina son idan aurena ya tashi ai duk na gaiyaci kawayen mu salma a hasu ayi zumunci nan take tambayan kin kusa aurene mairo ?

Na danyi dariya kafin nace insha Allahu bada dadewwanan ba zanyi aure salma saudatce ta katse mu da fadin mujefa rana nayi.

Na juyo ina fadin amma na fada maki idan nazo zan dan jima wajenta muyi zumunci ko in kina saurine na baki kudin mota mu sameki a can.

Haba dai Saudat ki bari don Allah ku dan kara min zama ga abinci can na dorama kuci nace a,a ba zamuci abinci ba don a koshe muke gaskiya.

Ga dai tsarabaki danayo maki ni rigarcema nake ta tunanen ko zai maki a yanzu don ban sani ba ko kin kara girma nace uwale ta mika mata ledan da muka shigo dashi din.

Tayi murna sosai tana budewa ta zaro lace sai kuma ta dakata tana kallona tana fadin mairo tsaraba irin wanan haka mai yawa ?

Idan an kirani ina waya sai tayi ta kallona a cikon mamaki mun kai karfe biyu saura kafin nace zamu tafi daidai lokacin na fahinci tagama girkita muka mike da muka fito ta dago tana fadin badai tafiya zakuyi ba mairo ?

Zamu tafi zan biya na dauki antyna mu tafi can family house din mijinta tana jirana yanzu ta kirani amma banji dadi ba ko yayane ai ku tsaya ku danci.

Handbag dina na bude na ciro kudi na aje gefen bello ina fadin Allah ya sauwaka mu zamu tafi ban yarda wani dogon magana ya hadani dashi ba har muka fito daga gidan yana min godiya.

Saboda yadda na fahinta farkon shigan mu gidan yadda Salma din ta zata don Bello nazo gidan badon ita ba wanan yasa na tsaya na wayar mata da kai saboda ita nazo na kuma nuna mata a zahiri.

Amma kinji kunya yau da kunsan kunya keda uwarki da kunji ta ai ba mu kaidai zamuji kunya ba har da uwar wasu ta fada don yanzu da yake kwance tasan bai iya dukanta tana kokarin rama zagin da duk yai mata daga kwance din.

Gashi mahaofiyarshi tayi mai baki akan inya saki salma bata yafe mashi ba ko bayan ranta kuwa yayi hakkuri don itace matar kaddaransa na rayuwan duniya.

Yakance banda iskamci ba,a koya maki komai ba kuka hada kai aka cuceni ki duba Mairo don Allah kinga mace tagari ir8n ajiya a gida ta haifa maka alheru a cikin gida kana farin ciki da jin dadin nunawa duniya.

Badai a gidan nan ba kaima ka gani a zahiri ai yanzu ko a kafa aka daurawa mairo kai ba zata ja kafan ba balle ta nuna don motan data shigo wallahi ko garin nan ban taba ganin irin bani mahaukaci kawai .

Allah ya isa wallahi da kuka hana min arzikina zuwa kusa dani munafukai yan sheri masu mugun nufi da kowa gari ya san hakan akanku dake dasu haka zaku tabbata yar iska tace mu tabbata dai ni dakai dasu a hakan.

Kana baki ciki da ganin mairo da Allah ya kareta daga kaidinka na sheri don da yanzu ka gama cutanta ita ma yadda kai min.

Au ke har yanzu baki gane bane aini sam ban kaunaki salma don baki da abinda namiji zaisa yaso ki a jikinki sam salma.

Ba daya kuke da mairo ba tun farko mairo ta tara komai da akeso ke banda wauta da shashanci sai kazanra da kike fama dashi don kiuya.

Ai yanzu komai ace ina dashi tunda na koma haka koda yaya kike haka kike dip dinki kamar tarin kayan wanki ba wani ma,ana a tare dake yaja tsuki don takaici ba zai barshi ya karasa ba a lokacin .

Haushi da bakin ciki suka cikata ta fara sharara mai zagi itama wanda hakan ya jawo hankalin mutanen cikin gida garesu.

Mahaifiyarshi ta shigo tana fadin wai meye hakane kuma har bakin naku sun tafine kuka soma fada kome ?

Baki ai sun tafi nice nan zai saukewa kwandon bala,i daya saba akan mairo dama nasan zuwan yarinyar nan gidan nan yau sai yajawo firina to gashi kuwa daga fitanta har kun fara hakan.

Dama shiya kawota ai don tazo ta saka fitina a tsakaninku ta tayarwa mutane da hankali a banza yarinya da idonta ya bude haka yanzu aikama kasan tafi karfinka yanzu kam yadda idonta ya bude din nan bariki takeyi a can naji labari.

Wallahi karyane hjy ba gaskiya bane karatu take a can yanzu haka tazo fada min zancen aurenta shiya kawota garin nan tare da wa yanda ke rikonta shine tazo fada min.

Shikuma ya zata ko donshi tazo yake sakin wani magana can wai mairo tafini an cuceshi ta acuceka din mana ai kaima ka cucemu tunda ba,a san haka halinka yake ba ?

Baiji kunyar idon mahaifiyarshi ba ya kara fadin karyane ba a cuceni ba kema kinsan badon kun hada da hjy ba ni ko kallo baki isheni ba salma don banga abinda zanyi da mace haka busassa irin ki ba mara fasali.

Ai baka nuna an cuceka tun farko haka ba tunda ka iya haiwa ukku da ita a hakan yanzu meya saura in kaji da kanka kaji ka zauna da matarka lafiya shine saukinka kaji.

Mahaifiyarshi ke fadin hakan ta juya ta barsu nan saida suka gaji suka kyale don kansu lokacin muna can mun ziyarci family house din mu munje gaidasu.

Da yake bawai na saba bane da kakan mu dama bamu jima ba nace zamu tafi ta soma fadin daga zuwa kice zaku tafi ?

Ni bansan dalilin da yasa yaran dakin Ai baku son ku zo gidan nan ba sai ku kama abu kamar baki baku sakin jiki da mutane kamar yan uwanku.

Kodai me aka kitsa maku nice dai kakanku dana haifi ubanku da cikina ku guda har bayan duniya ko ina kukaje dole ku dawo nan din a kirani da kakan ku kuma ?

Maganan baiyi min dadi ba duk da mun saba da hakan da ita bamu zuwa saita soki inna a gaban mu ta fadi abinda ranmu zai baci kan mahaifiyar mu.

Don haka ba sabon abu bane wanan a waje nace dasu su tashi mu tafi suka fito mukai mai masu sallama muka bar gidan.

Gidan muka dawo kai tsaye saboda nagaji ina son in huta haka kawai nake jin raina yana baci ko don abubuwan cakwalin da naganone a waje wanan fitan ya bata min rai oho ?

Mun dawo bamu jima ba bayan la,asar aka dinga shigo da drinks da wasu manyan kula guda ukku ina daki ina jin suna zance kan abinda ake shigowa dashi.

Paapane ya kirani a waya yana tambayan anty nace sun fita unguwane dazun wai meyasa Sariya bata da hankali tana nufin tazo garin nan kuma hjy tasani taki zuwa gidanmu ?

Sorry uncle amma naji sunce daga can zasu tafi su gaidasu bansani ba ko suna can din yanzu tsuki yaja ya kashe wayan nima sai banji dadi ba don abu nafarko ke nan daya kamata ace tayi tun washegarin zuwan mu garin.

Muna gama wayan na fito waje don ganin meye ake shigowa dashi din banyi mamaki irin yadda suka tsaya suna mamaki ba donni nasan waye wanda suke magana akai wai ashe bayan fitar mu da yan uwana yaya murja tana ta sakin magana irin yadda suka saba tana kusheni dashi Aliyu din wai kilama barawone ko dan 419 yazo da kudin damfara yanawa mutane bargan ai .

Sai bayan magariba inna ke fada muna wanan zance ni abinda nace a lokacin shine kawo dan,damfara ma gida haka ai isane ita ko dan fashi tasamu data kawoshi gidan ai.

Ki dai fada mai ya daina haka don Allah wanan abu yayi yawa wallahi ba zai dana ba konayi magana don haka halinsa yake shi.

A can haka kodan buki karamine ake kashe jiki nama za aitaci tare da drinks kila shiyasa yake hakan shima.

Ferfesun kan shanun da suka dafa aka debo muna shi kawai nasha na kwanta don akwai gajiya a jikina har lokacin yaro ya tsaya daga kofa yana fadin wai ance maryam tazo inji Aliyu.

What na fada donni a sanina Aliyuna yana lagos koda yamma da zamu dawo gida munyi waya dashi yace min gashi office yana aiki to wani Aliyune kuma yazo ?

Uwalece tace bari na duba ko waye ta figi hijjab zuwa wajen bata jima ba sai gata tana fadin wallahi shine da wanda yazo jiya.

Tsuki naja ni wanan abin kuma meye da bai sanar dani sai inji kawai gashi kofan gida in yayi hakanne da niyar ban mamaki ya bata min rai bayan wanda anty ta bata min don nayi kiranta tun lokacin in fada mata kiran da uncle yayi min ban sameta a wayan ba sai naji raina ya baci da hakan.

Banyi wani shiri ba nafita na samesu da alama lokacin ya shigo gari haka kuma yanayinsa ya nuna dan damuwa a lokacin.

Gaskiya maryam kin shiga gaban mu idan takaman mu diyan malam jikokin malam kin damamu kin shayemu kinga mutumin yakasa zama saida ya biyoki .

Yanzunan ko gida bamu je ba yace sai na kawoshi nan ya fara ganin ki kafin mu karasa gida dashi don Allah ka gama sherin ka ka bamu waje naganta kada ka cikamu da surutu.

Haka kayi ta damunta nasan da sherin nan naka harka isheta dame ta damamu ta shanye banda tsiyar ka ?

Sai lokacin nayi dan murmushi ina fadin sannu da zuwa a cikin hausa kagani na fadama ai bata iya magana a gabana saita nuna kamar batason magana ?

Lafiya kazo gashi har an fara min sheri sabodani ka shigo kano yau yace kyale dan iska duk yasan abinda ya kawo dan matsala nazo solving kuma ya tsaya yana maki sherin ke kika kirani.

Ba laifi bane inma donni kazo ai baka hanashi zuwa nashi wajen ba in kuma daukoka dayi airport yajewa jinini ya bari in kaika gida da kaina .

Ohh lalai yanzu da kika ganshi bakinki ya bude ko duk zuwan da nake bakanan iyakata da ita gaisuwa.

Me zance ma mijina baya kusa zan tsaya ina magana da mazan mutane yanzu ko yana kusa damu dariya yusuf din yayi yace saukin zancen kin gyara maganan ya fita daga motan shima fitowa yayi ya dan dubeni yace how far now ?

I hope ba matsalan komai dai tunda kuka zo nace bakomai sai godiya korafi gudane inna keyi don ba,a saba da hakan ba aikenka yayi yawa gidan nan tunda ba sayar maka dani zasuyi ba ?

Saida yayi gajere murmushi yace ki fadawa inna nima ai dantane don na aikowa iyayyena da abu wanan ba zai zama laifi gareni ba ai suyi hakkuri dani hakana ?

Kafin nayi magana wayanshi yayi kara ya dauka yana fadin Abba mun sauka na dan biyo inga maryam ne kada dare yayi ban samu ganinta ba.

Sun daiyi magana don banji me yake fadi ba saboda hankina daya dauku kansu anty dake fitowa Napep a lokacin naji yana fadin ganinan karasowa gidan yanzu tare da yusuf muke.

Su antyne suka karaso take fadin wai Oga Aliyune nake gani cikin turanci yayi dariya suka gaisa dashi nayi masu sannu da zuwa suka nufi hanyar cikin gida.

Shima hakkuri yaban zai tafi Abbansa yana nemanshi zasu zauna dashi kan wani magana mukai sallama suka tafi nashiga gida da dan ledan daya miko min daga hannunshi.

Ba sai anfada min ba nafahinci hankalinsa ba a kwance yake ba lokacin don irin yadda naganshi magana ma a cikin daurewa yakeyinsa lokacin.

Daga kofa na tsaya ina kara gaida anty tare da fada mata Paapa ya bugo yana tambayanta tace ai daga can suke sun biya sun gaida hjyn.

Ban shiga dakin ba na koma dakinsu saudat na kwanta nayi zaton zai kirani amma a ranan har barci ya daukeni banji kiranshi a wayana ba.

Washegari daine da safe na koma barci ya kirani yana tambayana ya dare yaso ya kirani bai samu fitowa wajen Abba da wuri ba.

Sama sama muka taba hira dashi mukai sallama yace min zai shigo nan unguwarmu wajen iyayyensa kila yazo nan gidan mu din.

Ashe abinda ya faru shine Abbansa ya kirashi kan yazo mahaifiyarsa ta nuna bata yarda da zabinshi ba koda zaiyi sai ya fara na yar uwarsa ita bata hanashi aurena ba amma ya fara na Fadila din kafin nawa.

Shine dalilin zuwanshi inda ya nuna shi a rayuwansa baida ra,ayin yin mata biyu balle kuma ba zai taba auren yar wajen hjy Hanne ba koda auren gida yake da niyar yima .

Don haka nice zabinshi idan uwar tace bata so ya fasa auren ga baki daya shike nan dama auren ba damunshi yayi ba.

Inda uwar ta nuna cewa batace bata sona ba tarbiyanace dai bata yarda dashi tunda ance ba a gaban iyayyena na girma ba don haka ba zata yarda ya dauko ya kada cikinsu ba.

Anya hauwa kanki daya kuwa Alh nifa baku fahincini bane ba cewa nayi kada ya auri yarinyar nan ba ya fara auren zabina abinda na fada ke nan ?

Baida matsala Abba zan samu su malam da safe in fada masu a fasa kawai a basu hakkuri daga baya zanbawa maryam din hakuri tunda dama nina matsa itama ba sona takeyi ba.

So su malam suje su basu hakkurin kan bata masu lokaci da akayi sai ummah ki gafarce wallahi ba zan taba auren Fadila ba gaskiya.

Fakat tunda hakan yafi maki sai kaje din ka samu su malam din da safe nidai ba zan iya tunkaransu da wanan zance ba sai kaida ita ku samesu kuyi masu bayani.

Zan kira yan uwana da safe in fada masu anfasa suyi hakkuri tace Alh waiba zaku fahinceni bane don Allah nifa so nake ya fara auren yar uwasa kafin ya auro wanan yarinyar da ake zance.

Wacece yar uwana ummah kice diyar hjy hanne zaifi sauki matar da naje don ta taimaka min ummah tace naje matsiyatan iyayyena dake takaman sunada kudi su taimakeni .

Takara nake son yi dasu watau to naje tunda muna ganin zamuyi ja dasu naje din kukaini nayo karatun waje.

Itace kuma da naje din yanzu zata saki gaba tace ga yarta in aura wallahi ko mata sun kare a kano ba zan taba auren ko wanda ya hada hanya da wanan matar ba .

Wanance dama nake ganin namu zaizo daidai da ita kince baki sonta to nafasa suyi hakkurin bata masu lokacin da nayi din nasu ita kuma zan bata hakkuri tunda dama nine nasa ai wanan abin bada son ranta bane za ayi a yanzu.

Wai meyasa ba zaka fahinceni bane ummah nafahinceki ai tunda batayi maki ba me zaisa in dauko matar da baki ra,ayina da ita ?

Kaje Allah ya bada sa,a shike nan ko ni tun farko bance ban sonta ba me tayi min da zan ki kaunarta wai ?

Na dai gane kaida Alh kuna son hada fitina tsakanina dasu malam zumuncin mu ya lalace dasu ummah ban fatan hakan auren yarinyarce dai na fasa ai baka isa ba ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login