Showing 324001 words to 327000 words out of 395027 words
Chapter 109 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
a air port muka rabu da Paapa da sukazo daukan mu da mota biyu yace saida safe yabi wancan motar dayan zuwa nasu unguwan .
Wanan wanda ya dauko mu din ina jin shine Yusuf din da nake jin yana yawan zancensa lokaci lokaci kuma ya fada min a tare suka taso dashi dama kuma har yanzu dai ana taren .
Inda na sheda shine yusuf saida yake ce min lalai Aliyu mugune a takaice dai saidaya gano ki a lagos bayan kin gama zane mai mota ko ?
Murmushi nayi kawai don a gajiye nake ranan ko magana banson yi a lokacin ina jin kaina kamar bani bace a lokacin don irin yadda nake ji din.
Banyi mamaki ba don naga ya tsaya a kofan gidan mu a lokacin muna fitowane yan gidan mu da basu sanda zuwan mu ba suka ganmu ana fitowa mota a lokacin.
Uwale ce ta tsaya tana bin mu da kallo a cikin mamaki sam bata gane ko suwaye ba ni dai na shedata duk da akwai dan duhu a lokacin amma hasken kofan gidanmu zai iyasa in shedata nace.
Ba Uwale bace kin tsaya kina kallon mu kuma acewansu hausana a lokacin yana kama da harshen yare wanda ni sam banjin hakan idan inayinsa amma ko a waya haka suke ce min .
Idan bada su ba ban hausa a can sai mutum ya wuni bai fadi kalman hausa ba turancinsu ba can ne sai kuma yarbanci dashine harshen da muke magana da antyna dashi.
Ta matso kusa tana duban mu sai can tace wallahi yaya mairoce ta zura a guje zuwa cikin gida tana fadin wallahi ga yaya mairo .
Yaya mairo fa kikace saudat ta fada ta juya kuma ita dasu Abdul zuwa waje ihunsune ya jawo hankalin yan unguwa garemu .
Murna sosai yan uwana sukayi da ganina suna bina da kallon da bansan kona meye ba a lokacin duk da darene amma mun samu wa yanda suka shiga muna da kayan mu gida akwai karamci da hadin kai dama yan kano.
Muka shigo da sallama sai lokacin na kara jin dadi sosai da zuwan anty don dani kadaice zan shigo a lokacin ba tare da kowa ba idan da dagani sai paapa muka shigo garin ke nan.
Yaya sahura tazo muka rugume juna ta kara dagowa tana fadin wai mairo kece haka don Allah kamar wata hjyn dubai can Allah mairo ba za ace kece ba ?
Ko yaya llaah,ke mairo ashe har hausanki gaba daya ya juye a yanzu nayi dan murmushi kawai muna gaisawa na tambaya ina mama tana ciki ta fada.
Innan mu na hango tana fitowa daga daki nayi kanta nai hugging dinta ina sauke numfashi nayi mamakin jin bata tureni ba yadda ta saba min a baya.
Don da ko unguwa taje ta dawo ina murna zan rugumeta saita tureni tana fadin bata son shashanci fa wai tana irin kunyar nan na diyan fari dani .
Amma sai naga sabanin hakan wajenta sai cewa da tayi dani cikin yarensu wanda ni kadai sai saudat da tana ji ammw bata iya mayarwa.
Kuna hanya amma baki sanar damu zuwanku ba nace tafiyan ce tamu bashiri inna muma saida dare jiya muka san da zuwan mu.
Inna ta kauce min tana fadin ban waje in tari hjy nidai ta nufi inda yara suka rufawa antyna da murnan ganinta din yaya kin zama balarabiya wallahi .
Saudat ce take fadan hakan a bayana nace haba dai gani kuma jikan Badawace ni muka dubi inna tace mune sarakan fulani ai Badawa .
Saidai al,adunmu sunzo kusan guda da juna amma muna gaba da fulani mu akai dariya a wajen wanda hakan ya kara jawo hankalin mama dake kwance bata jin dadi a lokaci.
Dakin mu gaba daya tsarinshi ya sauya min yadda aka gyarashi saidai har yanzu banga yaji abubuwan zamani na more rayuwa daya dace ace akwai a waje ba .
Akwai wanan tv din da suka matsa min in sayo masu a lokacin don kallon arewa24 da gidan kowa ake kallon shirin zaira tarkon kauna da aka soma shirin sabo sabo a lokacin shine saudat take tamin mita suna son tv na sayo masu a lokacin.
Dakin mai yara tv har ya samu matsala amma haka suke amfani dashi tunda yana kawo hoto clean ana gani saidai a gareni hakan kamar kasawane wajena.
An gyara dakin hakan yasa saida naga anty ta zauna nace bari naje na duba mama na duk sukai shiru anty tace a cikin yarbanci bata zuwa ko ina itace ya kamata tazo ta taremu ai da zuwa.
Tare da uwale da saudat mukaje dakin na mama da muka samu kwance yaya sahura na tsaye a kanta tana magana da ita ta tashi gani can nazo taje mu gaisa sai gamu.
Ai ga yaya din tazo ki barta duk yinin yau a kwance ta wuni inji uwale ke fadin hakan nace subbahanallah tasha magani ko ?
Maganin ya karema shine kikaga na fita nake son inje in samo mata ai don kudin bai kaiba yasa ban fita tun dazun ba .
Ba,a fadawa baba bane bata da lafiya na juyo ina kallon yaya sahura din cikin mamaki tayi murmushi tana fadin ko an fada mai me zai mata mairo bari dai in fita din in duba kemis din idan anrage in karbo hannun Salis.
Ke dauki min handbag dina a daki na fadawa uwale ta juya zuwa dakin da sauri na fara gaida mama din da jiki ta dago tana fadin mairo kuna hanya ashe ?
Sannuku da zuwa yadda ta fada yasa tausayinta ya kara shigana sosai a lokacin uwale ta iso da bag din take miko min na karba na bude kudi na zaro bansan nawa bane nace yaya a karbo maganin inson samune yazo nan ya dubata yayi treating dinta don Allah sai a kara mai kudin tace barin je ai zaizo idan yaji ance kecema kikace hakan don ko yaushe yana tambayanki dama ?
Wayene na tambaya tace min salis mana salis dai abokin tsohon saurayinki bello da suke zuwa wajenki tare yanzu sana,an da yakeyi ke nan ai kisan karatun asibiti ya koya ai.
Bayan ta fita nima na daga ina fadin bari na dubo anty wanda a daidai lokacin kuma yaya sahura ta dawo tana fadin ke saudat wani yace a kiraki waje ki karbowa Mairo sako.
Waye kuma ta fada ta mike nace yaya don Allah daga nan ki samowa mama fresh milk da wani abu ko nama haka mai zafi da zata iya ci ta amsa tana dariya ta fita.
Leda niki niki muka hadu da Saudat tana shigowa dashi gidan wai ance ta shigo muna dashi lokacin ma inna tana kokari ashe ta hura wuta a kitchen .
Don naji saudat na fadin inna saiki huta don ga abinci an biyosu dashi nace me zatayi dama wai girki zatayi maku a cikin daren nan.
Haba dai inna gamu yanzu sai kin shiga kitchen kuma ballema ai basai an girka ba inna sai a sayo mana zaifi sauki.
Zata shiga daki dashi nace takaiwa inna a kitchen ta duba sai a diba a kawo muna namu daki na shiga dakin don in rage kayan jikina a lokacin.
Na soma rage kayan don na samu antyna tana kwance tana waya tana fadin bata jin dadin jikinta a lokacin dama daurewa tayi ga wanan tafiyan tun gida bata jin dadin jikinta kuma ina tuhumar kamar ciki ta samu a lokacin.
Naji dadin ganin harda bandaki a dakin nasu inna na shiga na kewa tare da watsawa jikina ruwa na dauro alwala na fito na fara shirin rama sallah magariba da isha,i dake kaina.
A lokacin Saudat tashigo da tire da plates har da ruwa ta aje a gaban antyna tana fadin mommy ance ki tashi kici abinci ta zata irin abincin mune na tuwo ko shinkafa tana yanutsuna ta dago tana kallon abincin.
Abincine lafiyayye irin na hotel din nan sai kayan su shawarma da pizza sai kaji guda biyu da kamshinsu kawai ya ishi hanci a lokacin.
Kice min abinci na manya muka samu ai ta fada tana tayar da Amira da tayi barci don ita dama bata jimawa ido biyu da dare.
Sallah na tayar na barsu har innan mu ta shigo dakin ta samesu sun somaci ta zauna donsu kara gaisawa da anty din sai bayan na idar na juyo nake tambayan inna cikin yaresu na Badawa nace ankaiwasu mama kuwa abin nan ?
Ankai mana ai kinsan ni ban taba hanawa wani abinci shiru nayi don kada mu soma kwasa da inna din da zuwan mu dama bamu shan inwa daya da ita mu kwashe lafiya sai nayi laifi a wajenta.
Jakkata na tafiya na bude na ciro rigan barcina na saka tare da feshe jikina da kamshi na dauki wayana da sauran abinda zan dauka na nufi hanyar fita daga dakin dakinsu Saudat dake kusa da nata can na nufa a lokacin tana fasin abinci fa ba zan zauna inci bane ?
Antyna ta karba da fadin indai maryam ce ba zataci ba haka take abinci bai dameta meta ba tun ina fada har nagaji na kyaleta yanzu.
Jam aiko bata samu dabi,a ba ina ruwan wani ai cikinta inna ta fada nikan tun kafin na fita na kunna wayana dana kashe a jirgi sai lokacin na kunnashi don nasan zai nemi da daren nan.
Dakin ba laifi sun gyara abinsu tsab ina shiga saudat ke fadin anan zaki kwana ke nan nace eeh dauko min hand bag dina don Allah da ruwa .
Sai gata da hand bag din da zanin gado da goran ruwa tana fadin yaya mike in kara shimfida muna wanan a sama dole na mike ta shimfida ina zama kiran wayanshi nashigo min a wayata daidai lokacin na dauka ina bude ruwan tare da sallama.
Kin samu gida kin mance da kowa koda yake nasan saudatce tasa kika manta dani yau har wanan lokaci baki nemeni ba.
Saudat din na mikawa wayan don insha ruwan data kawo min din ta dauka murya zakwai tana mashi sallama yace yau dai ga yayansu gabansu korafi ya kare ?
Tayi dariya tana fadin wallahi yaya Aliyu kun shanmacemu sai ganinsu mukayi daga sama kamar a mafarki waiga yayan mu tazo.
Naga ta tsaya tana saurarenshi har na kwankwade dan roban ruwan na cilla goran gefe na juyo ina fadin ban wayan na karba ina karawa akunne nace Oga wanan duk dawainiyar tameye haka don Allah kamar ba gida nazo ba kuma ?
Dawainiya tame kuma ya tambaya kamar bai gane me nake nufi ba a lokacin nace haba dai daddy na sai naga su saudat dake dakin sun kalloni hakan yasa na wayance da fadin.
Amma kasan ai mai sunnanka ba zai kasa dawauniya damu ba nan tunda munzo yace no ba sobodashi kukazo ba ai.
Wanan tafiyatace ba zan bari kowa ya wahalal da kudinsa ba daga ku har uncle duk bakina kuke a yanzun banson inna tace zata wahala akan zuwanku please.
Yusuf yana waje yace a tambayeki ina zai aje mota ko yakai maki nan gidan malam da safe ya dawo maku dashi nan kofan gida ?
Daddy kaima kasan bamu da inda zamu aje mota a nan ya tafi dashi can din ni dama kabar zancen motan nan don Allah tunda ba fita zamuyi b ai.
Haka dai kilace haka zaku zo har da anty bataje can family house din su uncle ba ko haka zakiwa Ummah idan kinzo saidai taji kinzo kina gidan inna ko ?
Please kada ka daureni don Allah ni bance ba zamu gaida hjy ba dolema muje nasan paapa zaizo ya kwashe mu ya kaimu ai.
Kin manta da zancen yabar motarshi a can ko shima nasa akai mai motan da zaiyi amfani dashi so kibar wanan zance don Allah.
Haka nake so haka kuma na tsara za ayi so ki barni da dabarana duk da hakan yayi min dadi amma sai da naji wani iri a kasan raina don ya maishemu dai masu karamin karfi ke nan ko ?
Mun dai dan taba hira amma bamu jima ba yayi min sallama sai lokacin na samu lokacin hira da kannena suna ban labari hakan yasa muka raba dare muna hira a ranan dasu.
Wanda karfin hiran akan yaya murjace suke fada min irin yadda ta koma a yanzu na rashin jin tsoron kowa a gidan sai tayi kwanaki bata gidan sai taga dama ta dawo gida.
Kuma haka mahaifinmu dole yasa mata ido tana rayuwanta tunda yan uwa sunce yayi hakkuri da ita don Allah gara ana ganinta a gidan da yace ya koreta gidan gaba daya ai.
Allah ke nan duk yadda yaso da bawa ba wanda ya isa hana hakan sai na tuna da farkon zuwana da mama ta fito tana tambayan ina dan dana haifa a bariki a cikin gatse yau sai ga bariki Allah ya aje mata a dakinta tana kallo ba yadda ta iya.
Abinda taso gani innan mu a cikinsa Allah bai nufi hakan a kanta ba sai gata itace taga abinta da idanunta biyu wanan hukuncin sai ubangiji mai juya lamari yadda yaso.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊9️⃣6️⃣🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Abba din yana zaune ya mike kafa saman table sai kada kafafuwanshi yakeyi yana waya da dan uwan nashi daya kirashi a lokacin.
Hjy tana gefe daya zaune tare da danta tana saurarensu idan ta kula zance akeyi kan zuwa neman aure to nawa take tambayan kanta a lokacin.
Da kyat ta samu ta taushi zuciyarta har mijin nasu ya gama waya ta dago tana kallonshi bayan ya gama tsara komai da zai kasace a lokacin.
Waye kuma za a nemawa mata abinda ta tambaya ke nan a lokacin kamar ya waye kuma ?
Shi Aliyu bai kiraki ya sanar dake gidan yarinyar da yake nema sunce a tura iyayye ba ni malam yazo ya sameni ai da zancen shago ya fada min ashe nan unguwarkune nema ta gaban layinku .
Unguwar mu kuma wani gida ke nan a unguwar tamu idan kinsan gidan sai me tunda malam ya sani dashi yaro maiyi ke naki ai addu,ane a yanzu kawai ?
Amma Alh ina da hakkin sanin ko yar wayw zai aura ko to malam bai isa dake dani ba ke nan kome ?
Don ban fahinci zancenki ba hauwa ko ince kina da wani manufa akan zancen nan ke nan ?
Manufar me tunda baiji maganata ba sai inje idan mutuwa zanyi ma in mutu ke nan ko to wanan ba maganata bane gaskiya hauwa amma barin kira malam saiki fada mai da bakinki cewa bai isa damu ba ?
Ni kada ka hadani da malam haka bai taba faruwa a tsakanin mu ba dashi yanzu ko ba zai faruwa ba din.
Mika mata wayan yayi yana gashi kiyi magana don tun dazun da kika soma yana jin komai da kike fada.
Kara ya saka wayan inda taji muryan malam d8n yana fadin hauwa aina dauka a duniyan nan ko kina raye ko baki raye nina isa da kayan ki ashe abin ba hakaba a wajen ki to kiyi min gafara daga yau ba zan kara hakan ba ga gayanki .
Aliyu dai dankine ke kika haifi abinki keda Alh yakubu don haka na fitar da bakina a zancen danki .
Wallaho malam ba nufina ke nan ba maganan muce nan dashi kawai mukeyi ashe ya kiraka ban sani ba hauwa naji komai a kunnuwata bandai isa ba ko to ya kare idan