Showing 186001 words to 189000 words out of 395027 words
Chapter 63 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
goron albishir yasa hannu ya aje mata goron albishi na yan dari biyar wrafer guda a gabata ya fita.
Ai ki gani dan yau zaki gwadawa ke tsohuwar tashace in iyayyensa sun boye ke kin fada nikan ba zan iya abin kunyan nan naki ba Naito ?
Bari mijinku ya dawo in fada mashi gida nayi gobe ban zama nayi ta hadiya takaici da bakin ciki a gidan nan akanki ?
Don baki da kunya danki ya mika maki goron albishir din uwarcikin shi a cikin gatse kuma ki karbe daki rangada guda da kika karba mu tabbatar da kin zama tababa ?
Duk abinda yakeyi zuciyarsa sai maimaita mashi tambayan ciki ciki kega umma har mama na mashi gatse wai tana fada mai halinda uwarshi ke ciki haka kai tsaye ?
Wanan wani irin dane da bai tashi zuwa duniya ba saida girman da tsufa haka ga iyayyensu sun fara gajiya zaice wanan shine tsananin rabo idan ya rantse.
ZAINAB ISRIS MAKAWA
[9/2, 10:05 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
5️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Ina fita daga aji na hango Ozil zaune saman motanshi yana waya wurin shi na dosa kai tsaye abune mai wuya yakai wanab lokacin a cikin makaranta bai fita ba.
Don shi ba sai ya fada ba kwalin shedan karatu kawai yake son mallaka a hannunshi shike kawoshi school din kuma if not ba abin da zai zaunar dashi lokacin.
Don business dinsu yafi mai komai a cikinsa ya taso ya girma yayi wayau yace min yana karatune shi don ya tallafawa mahaifinsa nam gaba.
Haka dinne kuma don indai don duniya ake karatu Allah ya basu abin cin duniya din dama ance duniya ta kafiraine lahira ta mumunin daya dace da rahamar Allah.
Ina isowa gefenshi naja na tsaya duk da a cikin yarensu na ibo yake magana sai kalman karshe da naji ya fada i will call you back.
Jin hakan nasan zai aje wayan a lokacin ya juyo gareni yana fadin mama girl how far now it look like you are not in good mood now ?
Ajiyan zuciya na sauke ina fadin not bad woo banda wani damuwa saina tunanen gida da iyayyena dake arewa bayan haka banda damuwa komai a tare dani.
When last kika je gida na dan rausaya ido ina fadin almost four and half years now yayi dan wani ihu tare da fadin chineke god wooo .
You mean duk tsawon wanan lokacin bakije ba baki gansu ba kuma kuna a kasa daya tare dasu haba haba dole gaskiya ki damu .
Na hada hannayena waje daya ta hanyar dan lankwasasu sukai dan kara nace damuwata shine in sakasu farin ciki koda banje ba amma na rasa way da zan yi hakan garesu yanzu ?
You know what ina da idea idan wanan guy din ya saka hannu ya bada kudi kika karbi share dinki zamu san abinda zamuyi masu wanda zaisa su san sun haifeki a yanzu.
Tare mukaje gida saidai duk dabaran mutum ban taba yarda ya san ainihin gidan mu don ko lokacin shagon maman Bumi na sauka da sunan nanne gidan mu.
Tana bakin shagonta tana auna gari taso tona min asiri don fadin da takeyi yau ma zanyi yaudara ko yasa na kawo wanan mutum nan don ko ita ba zatace ga ainihin gidan mu ba a area din nan.
Bayan tafiya Ozil na dan zauna da ita mun taba hira sabon tun ina secondary idan na dawo da gajiya lokacin a wajenta nake zama in huta kasancewar makarantar mu daya da yarta a lokacin kuma muna shiri sosai da ita.
Anan sabo ya shiga tsakanin har yanzu idan na dan rika kudi nakan dan mata ihisani in bata wani abu daga ciki.
Shine karkon shirin namu sosai har yanzu don ko wanan zaman da nayi a wajen lokacin da zan tafi na bata dubu biyar daga wanan kudin dana samu a hannun Ozil da wanan mutumin da nake dauka yana da manufa a kaina saidai bansan tashi manufar ba a lokacin.
Gida na nufa kofa a bude na hangoshi da mamaki na karasa gidan nashi da yar siririyar sallamata ba kowa a falon lokacin sai tv daketa aiki shi kadai a falon.
Dakina na nufa ina kokarin budewa naji motsi a bayana Amirace da gani a galabaice yarinyar take tana ganina ta sheko gareni ta rugumeni tana fadin.
Ta dawo gida mum dinta suna fada har anty ta jin mata ciwo ankaita asibiti har yanzu basu dawo ba.
Gabana ya bada ras na mike na riko yarinyar ina tambaya nace dawa tayi fada take nuna min kofan hajja yabi da hannu nan gabana ya kara harbawa.
Irinsu hajja yabi dake fakewa da gudun hijara yawancinsu yan dabane yan iska sai kadan ne zaka samu da halin kwarai daga cikinsu.
Kama hannun yarinyar nayi muka shiga daki da ita jakata na aje na fara cire mata kaya nashiga da ita bayi nayi mata wanka tea mai kauri na hada mata na bata ta tashi dashi dama shine abincinta.
Wankan nayi na sauya kayan jikina zuwa wando da riga muka fito falon sai a lokacin na kula da yadda aka zubar da abubuwa a falon na fara gyaran wajen tare da dora abinci.
Ana gab da magaribane suka shigo gidan hannunta da gefen idonta ansa plaster da auduga a manne nafito ina mata sannu ta amsa min tana zama lokacin uncle shima ya shigo ransa a bace yake lokacin.
Gaidashi munayi ya amsa yana kai dubashi ga matar nasa da yarsu dake tambayan mamanta meye wanan tana kai hannuta sama.
Okey kin dawo kin sameta ko muna can ai hankalin mu yana nan don bamu barta da kowa ba na dan jima tsaye a wajen kafin in juya jiki ba kwari zuwa kitchen din don jin uncle zai dauki waya.
Wallahi na zata tun shigowana hajja yabi bata gidan ashe wai matar nan tana dakinta kulle saida taji dawowansu ne tafito a lokacin.
Ina tsaka da aiki naji hayaniya ya kaure a tsakaninsu kuma again da sauri na kashe gas din na fito zuwa falon.
A tsaye na hango antyna tana fadin sai ta rama yadda ta zubar mata da jini sai tayi mata hakan itama tana hadawa da hausa da yarbanci da turanci a cikin fadan.
Yar iska ko yanzu na daki banza kuma ba abinda zaki iya min ba kina takamar ke ga yar bariki ba shegiya karuwa kawai mara asali.
Haba haba wanan abin ai baiyi ba wallahi ka zauna kana zagin yar uwarka musulma da sunan karuwa kuma kasan ba haka bane abin.
Ke karamar shegiya ko zaki sayane a sayar maki dama na dade ina haushin ki a gidan nan wallahi kika tanka kika fara saka kanki a cikin fadan nan yau sai an kwasheki a wajena gidan nan.
Cikin mamaki nace ni din nan hajja yabi me kuma nayi daga rabaku fada zaki zageni an zageki din yar iska ba sai ki rama ba insan kinji haushi ?
To Allah ya baki hakkuri amma ki daina zagina wallahi don ni ba yar iska bace na juya da zuman komawa kitchen don idan na tsaya a wurin abin zai iya dawowa kaina a lokacin.
Ji nayi ta shako min wuyan rigana ta baya ina juyowa ban tsaya jiran komai ba na samu gefen fuskanta na sauke mata mari a iya karfina
Wai wai wai kika mareni ke kamarki zaki mareni ta sake min hannun da niyar kamani da kokawa na daga kwarin kafana na daki cikin ta sai da tayi fadawan baya cikin wani kara mai karfi .
Hakan ya jawo hankalin uncle dake waje yana waya ko kafin yazo na aza mata naushi da yakusa duk na karceta da yatsun hannu a fuska.
Innalillahi meye hakane wai me zangani kuma a gidan nan wai tana kokarin tashi na tausheta a kasa sai lahani nake mata a jiki ta kasa tashi dagoni yayi da karfi samanta ya yarfar dani gefe daya.
Cikin fada yake sababi yana fadin meye hakan ya akayi har haka ya kara faruwa kuma tazone tashigarwa mutumiyarta mana.
Maryam ya haka kuma har kika zo fada da yabi kuma uncle na juya kawai zanje kitchen don nace tabar kiranta mana da karuwa shine naji ta makure min wuya ta baya ni kuma najuyo na mareta ina fadin hakan nayi kasa da kaina.
Zaki san kin taba lafiyata wallahi gobe ba zaki kara karanbanin kai hannunki a jikin wani ba Allah ya fiki yafi nufinki wallahi ko yanzu kika kara tabani wallahi saina rama tunda baki rike girmanki ba gareni.
Fada sosai a ranan mukayi don haka bamu samu natsuwa ba a gidan sai wajajen sha biyu kuma duk da hakan munci abincin mu ita daine ban sani ba ko taci.
Saidai duk barazanan nikan ko a jikina don nasan bata iya komai dani insha Allahu sai idan Allah ya nufa zata sameni da sherinta a kaina.
Wanan fadan yasa komai kara lalacewa a gidan donni ban,ma san dalilin fadan nasu ba lokacin amma kuma abin ua shafeni tunda harni tana jin haushin zamana a gidan lokacin.
Ko danta nabar kulawa na daina daukanshi yaron idan ya ganni yayi ta zillo yana bina da kallo da a bayane zan daukeshi in mashi wasa in bashi chaculet tana fada yayi ta tsotsa sai ya dansha in karbe ina mashi wasa amma yanzu a kwanakin duk na daina hakan da nakeyi din.
Hakama tsakaninta da sariyan bako ga maciji kowa harkan gabanshi yakeyi itace dai zance tana takure a cikin mu don itace bata da abokin magana.
Ba ruwana fa nafito fili a ranan na nuna mata dabanci da iya shegen yan lagos da kosu uwayen dakin sai a ranan suka san na hurhura daga sanin da sukai min.
Sabon kitso nayi na attach brown mai yawa da nake nade abina a cikin hula da nake dorawa a kaina wani lokaci kuma iya gyale kawai zan dora akan nawa .
Wando da riga na saka pink irin da ake daure dan kasan rigan gefe da gefe baiko rufe min mazaune naba rigan saboda karantan shi.
Nafito da niyar in shiga gidan maman Teema na karbo abu kawai naga motarshi tsaye kofan mu yana laluban wayarshi sai gani.
Kallo daya yayi min tundaga samana har kasa ya kauda kanshi gefe daya naji kunya gaskiya a lokacin amma na share kamar ba komai na nufi wajenshi.
Sannu da zuwa nayi mai ya amsa ba tare daya kalloni ba yake fadin maigidan yana ciki don Allah baya nan ya fita na bashi amsa.
Yace Ok yana kokarin yiwa motarshi key gani hakan yasa na juya abina don barin wajen bakiji ba mana ya fada a ciki motar na dan juyo yake fadin ko zan samu number wayanshi don Allah ?
Wayata yana ciki na bari na fada okey no need ki barshi amma don Allah ki fada mashi nazo nemanshi ban sameshi ba.
Ya tayar da motanshi ya tafi na juya nabar waje ban shiga gida maman teema din ba don wata makwaciyar mu data tsareni tana yaba shigata.
Ina zaune wayan ozil ya shigo min na dauka yake min albishir da an saka hannu sun bada kudi za a yi deal dasu yake fadin ya karban min kudina da komai suna wajen shi.
Naji dadin jin hakan don ban da matsala ko fargaba a yanzu irin yadda wacan karon na wahal da kaina iya kadai ba zan kara yarda in daure kaina ba kuma again.
Na soma tunanen yadda zanyi da kudin me zan sayawa iyayyena na more rayuwa suji dadi kamar yadda Ozil ya ban shawaran yi a baya.
Baba dai yadda naji a baya shidan fasakwarin motocine da suke shigowa dashi ta haramtaciyar haya wanda gwaunati ya hana hakan a garesu amma mutane sukeyi.
Wanda rana ta baciwa irin nasu baba shike nan in ba Allah ya gyara ba shike nan mutum ya durkeshe kenan a rayuwansa irin nasu baba din.
Amma kuma har gobe haka mutane da dama suke wanan sana,an na kasada su saka kudinsu su sayi kaddara da hannunsu Allah ya gyara amin .
Wanda sai kaga a karshe saboda damuwa mutum ya koma kamar tababe don irin hasaran daya tabka yana duban abin a ranshi don abune dake cin zuciya irin hakan.
Wanan yabawa mama daman samun mulkan baban mu a lokaci harta koma kamar tafi karfinshi in badon Allah ya gyara ba da duk kannena ba a samesu a gidan mu ba don ko mama tasawa inna kahon zukan cewa itace me farar kafa datazo da tsiya gidan ta goga masu tsiyarta har hakan ya faru dashi.
Kuma wanda da yawa a cikjn dangi sun dauki wanan zancen da gaskiya saboda yadda bamu da farin jini a cikin dangin namu duk tabi ta batamu a wajen yan uwa.
Ko wanan mugunta da take ganin tayi min aida goyon bayan yan uwa da kakanin mu akaci galaban iyayyena suka turoni gidan Uncle da sunan aikatau a gidan har na koma hakan.
Yanzuma din duk da ban gaban iyayyena inna bata tsira a wajen mama ba don duk magana ya tashi takanyi hausa tace ai gara kazantar da kagani sunan shi tsabata.
Ita yaranta suna gabanta ai basu ko inaba da wanda aka turashi wajen wasu ba dangin iya babu na baba fa ?
To duk naji innan mu takirani tana min nasiha a cikin tausa murya akan don Allah inkula da kaina kada in basu kunya a rayuwa nasan wani abu mai muni ya faru a ranan tsakaninsu da mama ke nan.
Kuma idan na bibiya sai in samu haka dinne ta jefeni da wani mugun kalmane dake dagawa inna din hankali yasa ta kirani.
To yanzu ina ga taga na turawa iyayyena abinda bata taba zato ba ko tsamanishi a wajena gashi kuma banda aure ba aiki kuma taji nake yi ba.
Nashiga dan tunane har na manta da komai a lokacin ihun hajja Yabine da naji a razane yasani dawowa daga duniyan tunanen dana lula.
Falon ta nufo mu da danta a sandare dayake wani irin abu a cikj tashin hankali ba riga ba dan kwali tana fadin ku taimakeni don Allah Al,amin zai mutu ?
Kafin ta iso na isa gareta ina fadin meya faru dashi bata iya ban amsa ba sai miko minshi da tayi kawai tana fadin ku taimaka min don Allah kada ya mutu.
Daga inda anty ke zaune take min yare da in bashi manja a bakinshi saidai bata ko motsa ba ita balle tazo ta karbi dan ta gani.
Dauko manja nace ta juya zuwa kitchen ta dauko galan din manjan zuwa falo itace ta bude ta debo a marfi muka durawa dan.
Gushiri tace a dauko a shafa mai ko ina a jikinshi da sauri mukayi yadda tace din sai gashi yana kakari ya fara yi kamar amai lokaci guda ya sako zawo da amai mai wari duk ya bata muna jikj mu nida ita.
Tace in kara mai dan manja din nace ta dan kara zuba kadan muka sake ba yaron zawo ya kara sakewa ya dan bude idonshi sai kuma ya fashe da kuka cikin tausayi.
Ba tare da tayi muna magana ba tamike zuwa kitchen ruwan zafi tasa ya danyi dumi tace ai mashi wanka dashi