Showing 162001 words to 165000 words out of 395027 words
Chapter 55 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
na kasa ganewa shine me yasa ta aikata hakan bayan tasan ta dalilinki tasan matar nan amma ta iya rufe ido tayi muna hakan zancen nan ba zan iya kyalewa ba gaskiya.
Hakkuri na dinga bata don ganin yadda ta hau sosai a lokacin a ra,ayina banson abinda zai tayar da zancen a yanzu tunda ya wuce.
Don haka nayi saurin fadin inna dama nace ko za a canza wanan fridge din naki hakana ?
Ina da niyar hakan ta fada zan turo da kudi ki sai sabo sai kuma yan wasu laluran daki daya kamata a gyara a sakawasu Abdul sabon tv da fanka kuma ?
A ina zan samu kudi haka inyi wanan sayayyan da kike lissafo min inna ta tambaya cikin mamaki ga umurnina ?
Kudi zan turo maku inna da akwai kudi a wajena da nake tarawa wanda gwaunati ke bamu duk shekarawa dalibai inna.
Abin mamaki zancen da mukeji ana fasin karatu a kudu akwai tsada ashe karyane na amsa da karyane inna komai nan da dan saukin rayuwa ai inna.
Kada kice zaki roki kudi ko kiyi wani abinda ya kaucewa addini ko al,adan malam bahaushe diyar yaya ki tuno da addininki da tushen ki diyar hausawa kuma musulma yar yaya ?
Insha Allahu inna ina kiyayyewa ai yanzu dai zan kiraki zuwa wani sati sai muji yaya za ayi da ko abindake hannuna zai isa ki daiyi a hankali ban son zancen rigima.
Inna insha Allahu ba zanyi abinda bai dace ba ina sana,a anan ina kitso ina siffawa matan aure da amare kuma Allah yai maku albarka ya tsare min rayuwanku ke da yan uwanki a duk inda kuke dake da sauran diyan musulmin Allah na amsa a cikin jin dadin mafi abinda nafi kauna a kullum a furcin innan mu na wanan addu,an da yazo kamar waka a bakinta kanmu a kullum.
Mikawa su Saudat waya tayi mukacigaba da hiran mu na yan uwa suna fada min abubuwan da suke bukata na rayuwa a dakin mu dama gidan banda kurciya kamar suna tunanen wani aiki nazoyi lagos mai nauyi sabanin inna dake worning dina akan na kula su sai demand din da suke kara min suke fada.
A gidan Alh yakubu dai jikin hjy Naito yakiya don anyi dorin asibiti abin baiyi ba an maimaita sai a hankali kafan hannun kuma sai korafi takeyi bai mata amfani don bata iya dagashi a yanzu.
Wanan yasashi zuwa gida don anyi lokacin da kamar zata mutu hankalin yayanta ya tashi shi Habib shiya kira kanin nasa yana fada mai abinda ake ciki.
Akan ance a koma da ita gida ayi na gargajiya mahaifinsu ya hana yace ba afi asibiti ba ai don shine sukai shawaran fadawa dan uwan nasu yasa baki ko mahaifin nasu zai yarda don a yanzu shine komai a gidan kamar babba don kudi.
Duk da hakan yana ciwa yan uwan haihuwansa rai amma yaya suka iya da ikon Allah shi Allah ubangiji yabawa wanan daman a cikinsu daman da mahaifiyarsu taso a garesu nataga ta hana Aliyu dagowa daga doron kasa.
Sai gashi Allah ubangiji bai nufa ba ya nuna mata iko a hannunsa yake ba wani mahalukin daya isa yaiwa bawansa abinda bai tashi yi a garesa ba.
Ko a yanzun da hjy Naito ke kwance duk abin nan da Allah ya nuna mata hakan baisa zuciyarta taushi akan dan kishiyan nata ba don da zaran an ambaci sunan Aliyun a kusa da ita yanayin fuskanta sai ya sauya ko a lokacin da habib ke waya da kanin nasa a gabantane.
Wani irin bacin rai da kiyayyanshine suka ziyarci zuciyanta lokaci guda da taji Habib na fadin ina ganin sai kazo zancen nan don Abba yaki yarda da wanan mai dorin kariyan gargajiyan da akace a gwada nasa.
Aliyun yace to amma habib sai nake ganin kamar Abba ya fimu sanin abinda ya dace tunda asibitin yaga yafi amincewa dashi a barta asibitin mana a kara gwadawa a gani.
Kunji dan banza ko mena fada maku tun farko da ace uwarshice ni da tuni aiya daukeni daga nan din zuwa na gargajiyan wanan yaron sam baida mutunci a rayuwansa sai gadara da jin kai da yakewa mutane.
Naito ina mamakinki yaron nan fa duk wani kudin da ake kashewa da wanda mukeci da sha asibitin nan duk shi ke daukan nauyin hakan a aljihunshi kuma kin sani.
Ai ba don ni yayi ba yaya ubansa ya taimakawa don a yabeshi amma ai kinsan inda ba ubansa a raye bai min hakan da yakeyi ai don ubanshi kawai yake hakan ?
Abin mamaki Naito haka kika koma kamar kafiran farko da riko meye kaifin yaron nan don Allah ?
Da kece uwarshi haka ya faru da hjy hauwa baki taba yarda danki ya zure haka hanawa zakiyi naito yaran ma ba zasuyi ba tunda baki masu tarbiyan haka ba a rayuwan su dagake sai su kuke cin abinku.
Yaya sherin da zaki min ke nan ba sheri bane Naito maganan gaskiya na fada intazo a yita wallahi da kece kwandalanku bai ciwon kai a kan matsalan hauwa ko wanin daga cikinmu a nan.
Abin ke nan ai dole kice haka yaya banga laifinki ba son kince yaron da tun yana ciki a shayar dashi ayar Allah ya fito duniya an bishi da wanka dasha ba dole yai farin jini kamar furen tunfafiya tsakiyan gonan kada ba .
Kunji irin shirmen nata ko ni shiyasa nace daku ba zafin ciwo bane zalla muguntan da kika shukane Allah ya biki da abinki Naito.
Ai in kince baki barin yaya Hanne kina da babban aikin wahala a gaban ki don yaya Naito bata san Annabi ya faku ba har yau din nan ita da ko tuntube tayi tace aikene kowa ke jiranta yai mata aike oho ?
Mama na sameshi yace zai shigo yaga Abba a san abinda za ayi in za a gwada na gargajiyane sai a gwada din amma kafin yazo yace zai turo kudi a kara sai mata kaji irin na hausa ya zamo shine abincinta ko yaushe.
Kaji dan albarka wanan da Allah ubangiji yai mashi albarka yaro ba kyashi ba hassada ko uwarshice ke ai ya tsaya haka .
wani irin gyatsire fuska Hjy Naito tayi tana juya cikin jin zafin yadda yar uwarta din ta zage tana zukawa dan kishiyanta albarka alhalin bata taba jin maka,mancin kalman ya fito dag bakin ita yayan nata ba zuwaga yayan cikin kanta.
Ni mama yaron yana burgeni yana da saukin kai sosai a rayuwansa gashi da hangen nisa da sanin ya kamata ga kowa jifa dayaji cewa,,,,,, .
Kai ya isheni don Allah kaiko baka san ciwon kanka bako ka zauna sai zuba kayi kamar sakarai kai wanan abu har burgeka yayi ?
Arzikin ku dana ubanku duka sun tattara sunyi tsafi sun tura ya koma gareshi shine kai don rashin wayau kake faman damun mutane da sarutu haka.
Kallon juna sukayi cikin mamaki sai Saratu ta iya fadin haba mama zaki fara irin naki maganan kuma ko kibar mutane da kunya don Allah dai mama N kibar irin hakan da kikeyi.
Shiru dakin yayi na dan lokaci kafin shi habib yace shi zai koma kasuwa dama daga can yake ya lekosu a daidai lokacin ne kuma su Na,ima suka shigo da abincin rana dana dare kamar yadda sukeyi kullum su kawo daga wajensu.
A,a Na,ima kune tafe yanzu nake fadin ko lafiya baku kawo abinci ba yau sai Amira tace yaya yusuf yakai mota gyara wai motar sabuwace sai anyi mata service shine muka tsaya jira.
Saratu tace au injin ance Aley ya aikowa mama H da motan shiga shekaran jiya suka amsa da ehh da ita muka zo ai tana waje.
Zakice hjy Naito barci takeyi a lokaci don yadda ko juyowa bata yi ba balle ta tofa bakin albarka yadda kowa ya kokarta ya fadi.
Motace tsaye a kofan dakin da muka gama shiryawa don ban yarda na shiryo daga gida ba haka kuma bayan antyna ba wanda yasan da zancen abinda zanyi din na sayen kaddaran da zan sake afkawa din a karo na barkatai.
Tunda muka shiga motan da aka kawo don fitan namu ban iya furta komai ba a lokacin duk wani addu,an kariya dana sani shine bakina sadakan da nake nayi tinda safe dana fito haka na kwana ina neman sa,a da wanyewa lafiya a gurin Allah.
Meram why are you sellent ?
Are you thinking of something muryan Linda dake zuba surutu a gefena taji ban amsa ba take tambayan na dan gyara zama tare da nisa a hankalin na furta nothing.
Ina kara gyara rigan jikina ta hanyan janshi zuwa kasa ya rufe min kafa duk da zaune nake a lokacin take fadin you know what ?
Nope na fada har lokacin muryana a cikin taushe saboda yadda nake ji ba dadi a jikina tace ina jin dadin idan mun kasance a haka.
Saidai na kula wurin da zamu yau yana da muhinmanci sosai a wajen oganan mu don yadda naga Ozil ya daukaka abin nan musanman a kanki.
Na kanyi tunane who i wish muma mun kasance cikin yaran daula yaran da suka fito wani babban gida haka kin san da bamu tsayawa yin wanan sbirmen saidai muje don kanmu mu shana kamar kowa a wajen .
Amma yanzu a matsayin egent din company fa zamu dole girman mu ya dan rage a nan ina matukar son lamari na rons da za aje waje a baza capacity na jan aji.
Ki godewa matsayin da Allah yayi maki ko a hakan da badon Allah ba daba zakije wajen ba hakan ma wani baiwane gare mu tunda masu kudin sai sun laba damu su samu abinda suke nema.
Hango wajen da ake taron da driver namu ke kokarin shiga wanda ba komai sai manyan motoci na alfarma da jan aji bakake da farare da jajjaye sai ashe da blue sune kawai ke walkiya a gaban wajen a fafakasu a waje hakan ya nuna muna taron ya soma ke nan a lokacin.
Ya samu waje ya faka namu motar an dan dauki lokaci muna zaune yana waya da Ozil kafin muka fito daga motan zuwa inda ake taron .
Wajene haka babba kidan taushi a cikin harshen turanci yana tashi ga mutane maza da mata wasu a zaune wasu a tsaye suna shan abubuwa a kofuna.
Kallo daya nayiwa wajen nagono waje daine mai kama da dan get to gether akeyi a wajen don wani dana hango yana jawa bi.
Daga can nesa na hango sit din da babu kowa na dan ja Linda muka nufi wajen ban tsaya jiran komai ba na kai zaune.
A cikin bayanan nagano taro akeyi na matasa duk da akwai wa yanda sukafi karfin shekara sittin a wajen amma sun gwangwaje sun murje a cikin matasa su adole suma matasane dai.
Abin sha aka kawo muna na girgiza kai ban karba ba sai linda data mika hannu ta dauki cup guda wayana ya danyi kara na duba Ozil ne ya kira donshi na dan kara a kunnena yadda zanjishi yake fada min yaga shigowan mu.
Nan ya soma min bayanin mutum da zan gana dashi din daya kira da dan Northerm Nageria dan arewa ke nan amma mazauni kasan waje.
Duk kasuwancinshi a can yake yana turowa nan gida Nageri yayi min bayani tun kan mu zo wajen na hango guy din wani bakine dogo ya aje dan guntun gemu a fuskanshi kadan haka.
Hankalina yana ga wayan da nakeyi har Linda ta tashi ban kula ba ina wayan daidai nagama nake jin a zauna kusa dani.
Kamshin da najine yasa nagane ba Linda bace muryan namiji ke min magana a cikin hausa yana fadin yan mata adon gari.
Da sauri na dago ido mukai arba dashi wani shu,umin murmushi ya sakarmin cikin basarwa yacigaba da fadin ai ban zata kina shigowa irin wajen nan ba ?
Baka fadi karya ba da akwai abinda ya kawoni nan din Okey ya fada tare da cigaba da fadin naga alaman hakan kamar a tsorace kike ko yanzu.
Halama wani zakuyiwa aiki a nan da sauri na juyo gareshi ina fadin ban fahince kaba malam don kayi maganan ta yadda ba zan fahinta ba.
Okey na manta dake ba bahausa bace ai na zata wani kukazo duba a nan din ai eeh kasan yanayin aikin yadda yake.
Aiki mai hatsari ko wanan aikin naku da maza wanan aikin naku yafi dacewa ko manyan mata ba irin ku kananan alhaki ba da za a yaudara.
Yadda yake maganan zakice ba dani yake maganan ba a lokacin cikin basarwa da nuna isa bin mutumin da nazo gani da nayi da ido yana magana da wani dan nisa kadan damu.
Da alama A A J kikazo gani a nan da sauri nake fadin waye hakan don ban sanshi ba wanan na tare da wancan mutumin ya ban amsa.
Cikin mamaki na juyo ina kallonshi don yadda ya gane shine taget dina a wajen banda mu waya san da zancen abinda yashigo damu wajen ashe shi wanan dan kwakwafin har ya gano hakan ko.
Sai kibi sannu don shi din shedanine ba na gaske koda zai yarda sai ya bukaci wani abu daga gareki bayan hakan sai yaga dama zai yarda din a karshe yasa a wullakanta mashi ke.
What na fada a dan razane ya kada kai yace gaskiya na fada maki kamar yarona yake don tare mukai rayuwa dashi a germany .
Dan satan kallonshi nayi ya kara daure fuska yace na fada maki tun ranan ki daina wanan harkan bai dace da mace irinki ba gaskiya.
Neman kudi aiba dacewa bane sai neman sa,a banzo nan ba saida na roki Allah ya ban sa,a a kanshi nafito don haka kome ke zuciyarshi na mugunta dashi dako waye Allah bai taba basu sa,an hakan.
Well tunda kince Allah kin gama magana amma still kibi a hankali don bai dora idonsa akan mace mai kyau irin ki balle ya ganki a wajen nan ba zai kyaleki ba.
Nagode da taimakon ka ni zan tafi na fada ina kokarin mikewa tsaye so soon har zaki tafi zancen ganawan dashi fa kin fasa kenan ?
Aina fadama ban fito ba saida na roki ubangiji kariyansa wata kila kaine ubangiji ya jefo a cikin rayuwana a yanzu don ka kareni.
So nagode da fadakarwanka gareni na suri jakata dana aje a gefena zan mike ya kara fasin wait tunda kince hakan zan taimaka maki sai dai in one condition.
Kamar me kenan fa na fada ina mai kallonshi idan kunyi magana zaki bani time dinki akwai maganan da nake so dake na fada maki tun a wacan ranan kika gudu kika ban fake addres da cewa wanan shagon dana sauke ku nan ne gidan ku.
Sorry kasan this is lagos ba kowa bane zaka yarda dashi haka daga sama so in ba matsala ni zan tafi don Allah.
Ba sai kin hadani da Allah amma ki godewa Allah kafin ki ganshi kin fara gani if not gaskiya yau wanan irin kyau da kikayi mai kwatanki wajen nan sai Allah.
Kinga nan duk arnakune ba damuwa da hakan zasuyi ba ban fito gida ba saida addu,an iyayyena na tako lagos don haka ina cikin tsarin ubangijina ko wani lokaci.
Dan abinda ke makale a wuyan riganshi naji yace da wani kira min A A J ina magana dashi a nan iya abinda ya fada ke nan ya juyo gareni muna fuskantar juna dashi.
Kasa nayi da kaina don kunya ban taba daukan magananshi gaakiya bane duk da ban tabbatar wanda nazo nema sin bane zai kira min .
Don a yadda suka nuna min wanan din da zamu gani a yanzu kamar yafi shi wanan da muke tare yanzu powe in monney da komai ma don sunata kwadayin yim halakan na dashi sosai.
Ba,afi mintu biyar ba sai gashi gaban mu kamar mafalki yana fadin ai ina can ina raban ido na zata koka wucene ai nasan kai baka zama irin wajen nan namu.
Ban tafi ba yanzu dai zamu tafi ya fada tare da nuna mashini da hannu yana fadin wanan kamar sister take a wajena kafin yacigaba mutumin yayi wani kashe ido yana fadin kai kai kai.
Yanzu na yarda amma to bandaice komai ba don da badon wani abu ba sai ince ita