Showing 393001 words to 395027 words out of 395027 words

Chapter 132 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

Allah ya sanya alheri yace kin kyauta banson nayi niyar alheri a kawo min akasi cikinsa .

Banda wanan rayuwan suka balle akan aure nasan abinda Allah zai mayar dashi nan gaba Allah yasa hakan ya zamo alheri garemu baki daya.

Ya amsa da amin kinsan Abdul ina jinsa kamar uwa daya ta haifemu dashi yaron nada amana duk zamana dashi bai taba min wani abinda raina ya baci ba.

Da alama nagani ai yadda shima yake damuwa dakai kamar dan uwanka na jini yace na barshi wancan gidan da muke amma nace a,a ba yanzu zan barshi ya zauna shi kadai ba su zan gyarawa gidan su zauna a ciki.

Tare nake son a hada aurensu dana yusuf da Na,ima insha Allahu kinsan shi yusuf Abuja zai zauna ya kula da wancan brach namu da aka bude.

Satin mu daya da aure da kwana biyu su inna suka wuce saudiya su saudat suka zauna da yaran a gida don naso in wuce dasu lagos yaya ibrahim ya hana yace meye amfanin shi su aisai aga rashin hankalinmu har yaushe na tare da zamu fara rashin hankali haka.

Yaya ibrahim mutumne mai tsayawa bisa kan gaskiya gashi da addini da sanin yakamata sai ince shiya kwaso mahaifinmu sak ga komai don haka gaskiya mahaifin mu yake shima amma zama da mama yasashi botsewa daga baya.

Akwai kyakyawan fahinta sosai tsakanina da mahaifiyar su Aliyu wanda shi Aliyun ya haddasa hakan a tsakanin mu biyun.

Haka yasa ako yaushe muna waya da juna na fahinta akan rayuwa aurena da wata ukku ranan ya dawo gida da farin ciki .

Ina zaune ya daukeni can yana juyawa ina ganin jiri nake dan dukanshi akan ya saukeni kar na fadi yace badai a hannuna ba .

Sai bayan ya saukeni yake fada min alherin daya samu na nasaran zama shugaban companysu ga baki daya headquarter su dake frances wanda a yanzu can zamu koma tsayom shekara hudu kamar yadda sukeyi kafin a sauka abawa wani kuma.

Nayi murnan hakan sosai amma dai ina duban yadda zanyi nisa da gida kusan yanzu nice na zama kamar babba a gidab namu.

Shawaran komai kowa dani yakeyi daga baba har inna da yan uwana inka debe yaya sahura data fita daban a cikin mu don har yanzu adawanta na nan akaina.

Sai faman shirin tafiyan mu akeyi ta wani bangare kuma yana shirin aurensu saudat a asirce ranan ina kwance ina fama da kaina baba ya kirani a waya.

Bayan mun gaisa ya soma fadin maryam dama magana nake son muyi ta fahinta dake da fatan zaki fahinceni don Allah ?

Nace insha Allahu baba yace ba wani abu bane rigimace tsakanina da innan ku ya taso akan nace zan kara aure tunda ita wacan uwar taku yanzu gata ga kamar ta bata iya komai .

Don in ragewa Ai nauyi nace barin kara aure in auri wata da mijinta ya rasu nan layin mu nasan ba zaki ganeta ba yanzu shine abin ya zama muna rigima da Ai din yanzu kuma.

Aure baba na fada a firgice sai naji yace ku fahinceni mana maryama kece nake gani mai hankali da wayau a cikin ku idan na fada maki zaki shawo min kanta.

Ita wanan yar kan ubar saudatu ita da sahura har da samuna sukayi wai saina fasa ni kuma naga abin nan fa kamar jahafine zanyi idan na aureta.

Tau baba idan dai ka yaba da hankalin matar aiba zamu hanaka aure ba baba tunda kana ra,ayin hakan abinda bamu so dai shine da girmanku kuma tazo ta haddasa muna fitina a gida ta hanaku zaman lafiya shine ba a so ai.

Yace tama isa ai saboda na auna naga natsuwanta naga ita zata dace da gidana ita kuma Ai bata fahinci hakan ba duk nayi mata bayani ta kasa fahintata .

Zata yarda insha Allahu baba saidai don Allah baba asa adalci a ciki don gudun abinda zai haifar da fitina yace insha Allahu mairo yanzu ita Ai ta kafe wai sai in saketa ko in san inda zankai ita matar badai nan gidan ba.

Zamuyi magana baba na fada sai naji duk yaban tausayi duk da farko naji zafin hakan amma zancen abin a duba mashine tunda yana son auren Allah kuma bai hana ba.

Muna gama waya dashi nakira innan mu din tana dauka naji ta soma fadin yakai karana wajen ki ko ?

Nace haba inna kara kuma wa zaikai karanki wajena tace malam mana tunda ya koma kamar karamin yaro yanzu ?

In banda motsin naira dake diban malam ya rasa abinyi yanzu wai sai aure saboda mijinki na narka mai kudi sakaiyan da zai muna ke nan yanzu ko ?

Haba inna ki kwantar da hankalinki don Allah yau ko baba yayi aure duk wace zai auro ba zata taba kai mama ba kika iya zama da mama a duniyan nan dawaye baki iya zama yanzu ?

Wai haka kikace ke nan naji muryan saudat na fadin wallahi bai auren nan don zamuje mu samu yar,,,,,

Ke saudat ki shiga hankalinki wallahi kada in saba maki kinsan abinda kike fada kuwa ina ruwanki da zancen aurenshi tunda ba akan innan mu zai dorata ba ?

Shidaya dauko aure ya karata da ita can illa iyaka ba zan yarda abinda yaiwa inna ba kan mama ya maimaita hakan yanzu zan sa a kara gyara maki wajenki a fitar maki da plan dinki daban dasu duk abinda akeyima baki gani.

Harsu Abdul zansa a yi masu dakinsu na samari a can gefenki ta baya bashi ke nan ba in akwai wani abinda kikeso kuma bayan haka ki fada min komeye insha Allahu inna zanyi maki shi matukar baifi karfina ba.

Amma don Allah ki barshi yayi aurenshi baki san abinda yin hakan ya kumsa ba aida bai taba cewa zai kara aure ba sai yanzu kada rabo yazo ya kashe muna ke inna ?

To shike nan tunda haka kikace ba zan kara daga kaina akan lamarin ba insha Allahu ni dama dai don baka sanda wace mutum zai shigo maka bane.

Nagode inna da kika fahinceni na koma kan saudat nayi mata tas akan iyayye tayi sanyi naji inna na fadin aiba wanda zai kara zancen na fahinceki yanzu.

Baba yai aure da wata biyu zancen bukin su saudat ya taso rigiri don saida ya shirya komai ya samu baba da zancen har zancen tafiyan mu francer a lokacin ya fadawa baba.

Ina wuta ranan da mama taji ta saka mu ciki akan sahura ta sauke haushinta tasha tsina da shagube a wajensu mama da yaya murja anyi haka da sati biyu shagon yaya murja din ya kone tas bata tsira da komai ba dole ta dawo gida ta zauna kuma.

Mun shigo bukin su saudat din dayazowa kowa a bazata amma duk da hakan ba karamin shiri akaiwa bukin ba irin nawane ba komai zamuyi ba sai wanda muka ga dama abangaren mu din don ko nawa duk da yace ba son komai sai mata iyayyena sunyi min gara na fita kunya daya kashe bakin kowa a lokacin.

Hakan kuma mukaiwa saudat itama don gara na gani na fada muka shirya da za akai din Allah da ikonsa wajen wanan bukin yaya sahura ta hadu da Alh musa dan kanone abokin kasuwancin maigidana.

Matarshi ta rasu wajen haihuwa ta barshi da yara hudu yana neman mace data manyata ya aura saiga yaya sahura yagani a gidan mu yake tambaya aka fada mashi yayatace bata taba aure ba.

Ya nuna yanayi Aliyu yace dashi baison wasa a cikin harkanshi har inda gaske yakeyi ya fito tunda ba abinda yafi karfinshi sai a hada jibi a daura da yan uwanta su shirya idan su gamsu da juna ayi a wuce wurin.

Da dan cikina wata shidda nazo bukin don na dan kwana biyu ban samu ciki ba kusan shekara don har sarakuwana ta soma magana sai ga Allah ya kawo cikin a lokaci.

Farin ciki wajen mu rananan bai faduwa jin abin kamar labarin yan litrafi amma inkon duba ikon Allah sai kiga wanan ba komai bane a wajen ubangiji mai tsara hikimarsa yadda yake so.

Kukan da tayine ta bamu tausayi don gwiwa biyu ta zube kasa gaban antyna da anty fati don tare sukazo gidan namu a lokacin tana kuka tana godiya ga Allah tana fadin.

Allah kaga zuciyata ance ina bin maryam don kudi Allah kaine sheda ba don kudi nake bin yar uwata ba don zumuncine da kauna.

Nima kuka nayi a lokacin da take fada muna irin cin mutuncin da sukai mata yanzu haka gidan yaya ibrahim take zaunema din abin yayi yawa tace.

Mundai bata shawara tashiga da zuciya daya ta rike mai yara amana da yan uwanshi tunda ya fada mata bukatanshi akan ta auren mijin marigayiya kuma saika hada da hakkuri da kawar da kai duk anty fati ta lurar da ita.

Da labari yaje gida kowa yayi farin ciki dajin wanan alherin daya samu kuma yaya ibrahim har gida yazo da matarshi sukai ma Aliyu godiya don itama ya dauke komai akan shi zaiyi.

Aka sha buki aka kai amare dakunansu don ni bukin ya zame min biyu lokaci guda haka nayi ta jigila da cikina ban bari an barni baya ba ko wani bangare nayi iya yina a lokacin.

Ban tashi haduwa da hjy hanne ba sai da muka dawo kasan waje wajen rasuwan malam muka hadu da ita da yarana tasha mamaki ganina haka yadda na koma ga yan aiki ga makarabai fadancin da ko ita bata taba samun irinsa ba duk takamata shi taga ana min ba kuma wurin da zata iya cin mun fuska a yanzu don Aliyu ya tare wanan kafar.

Hjy Naito kuma dai ana nan dai ne yan aiki ako yaushe ana canzasu suna guduwa yanzu takai akwance take komai an dauko malami yace saidai ayi hakkuri don abinda ya koma mata yagama bin jikinta yanzu saidai ta Allah kawai a kanta.

Yan magana suna tambaya da a fika uba da kafi miji wanine yafi daraja da kima a wajen mace gareku masu karatu ?

Ni dai kan sai ince nayi sa,an aure Allah yaban miji mai kamar uba a wajena don shekaran mu goma sha biyar a yanzu munyi zaman turai mun dawo Nigeria da yaran mu ukku.

Dukka maza sai wanan cikin dake jikinane bansan abinda Allah zai ban ba naga hassadan kishiyar uwa a filin Allah wanda karshe kukana ya koma min farin ciki .

Ya kan muna da kirari da Mun zama yan hawayen kada ko an tabamu a haka asha wahala

Ina godiya da dama da lokacin da ubangiji Allah ya bamu har muka kai karshen wanan dan labarin nawa izzina gareku mata muyi hattara da hassada akan kishin yayan mazan mu wani lokacin hassadan na zama taki ga yaro .

Karshen labarin maryam da tayi zaman lagos wace kishiyar uwace sanadin hakan da yanzu ya zamo mata alheri taku har kullum zainab idris makawa .

Alhamdullahi yan uwa na gode kwarai da bibiyan wanan labarin kuskuren mu a ciki ubangiji ka gafarta muna abinda muka karu dashi Allah yasa yazamo mai amfani a garemu bissalam mu huta lafiya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

THE END 9/Nov/2025.

ALHAMDULILLAH


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login