Showing 75001 words to 78000 words out of 395027 words

Chapter 26 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

goyo ba ba kuma da mugun kama ba Rakiya hakan yasa na gane har yanzu abin na nan daram a gidan mu baije ko ina ba.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

YAURI KEBBI STATE

INA MIKA TA,AZIYANA NA RASHIN SHUGABA ADALI DA MUKAYI GA YAN UWA MUSULMAI DA KUMA UWAR DAKINA ANTY ZALIHA UBANGIJI ALLAH YA JIKINSA YASA MUTUWA HUTUNE GARESHI DASHI DA AL,UMMAN MUSULMI BAKI DAYA ALLAHUMA AMIN YA ALLAH MU KUMA IDAN TAMU TAZO MU CIKA DA KYAU DA IMANI MUTUWAR BABA TA KOWACE DUK WANI MUSULMI MAI IMANI WANAN MUTUWAR DOLE TA BAR MAKA AYYA A RAYUWANKA ALLAH YA GAFARTA MASU ALLAHUMA AMIN.

[7/17, 10:04 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

2️⃣5️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15- HAWAYEN KADA🐊 1000.

_Account No._

_*ZAINAB IDRIS MAKAWA*_

2254380105

ZENETH BANK

PHONE NO.

08036959257

Tirkashi wai mairoce ta koma haka yaya sahura ta fada tana kare min wani irin kallo dan harrr nayi da idona da zaki zata an laka min eyeslash a saman giran idonane.

Nace yaya hajara kece a nan mun sameku lafiya kinzone ina baby din mu don na zata tayi aure a lokacin banda labarinta ga zancen baba da baji ta baibai da yace na dawo ba goyo ba ciki a tare dani.

Hango innan mu da nayi ta soro tana leke don ta kasa hakkura da inshigo hakama kuma takasa fitowa kuma daga wajen ta tareni yasa nayi wajenta da sauri ban tsaya sauraron amsan da zasu ban ba.

Innan mu na fada na sake hannun yaya sahura din nashiga ciki da murnata wajen innan mu na rugumeta cikin danjin nauyi da murna take fadin ke tsaya ni kada ki kayar dani don Allah.

Innan mu baki kewana ba ke nan yaufa kusan shekara hudu bani tare daku to ko nayi kewarki yaya zanyi tunda ba zanje in ganki ba can.

Shigo da buhun shimkafa da akeyi yasa muka shige gida kannena suka shiga kwaso tulin kayan da aka shake bayan mota dashi zuwa cikin gida.

Duk da akwai sauyi a gidan namu amma sai naga gidan namu ya canza mi kamar a hargitse yake nace Allah sarki bayin Allah suna nan dai a yadda na barsu ke nan.

Babane ya shigo yana fadin ke Uwale zo kije ki sayo lemun kwalba a wajen mai shago ki kawowa yar uwarku ina fadin lah baba ka barshi don Allah daga gida nake yanzu ai.

Wawawa ina ruwan yau ga baturiya a gidan namu wayagasu jajaye harda lemon kwalba za a aika a sayowa yar so lalai yar birni tazo gida ke nan yau ?

Keko kikan fara tsiyarki daga zuwan yarinya baki bari ta huta zaki shiga baza mata halinki data barki dashi a baya don Allah ?

Meye ciki don na saya mata lemon kwalba kuma ai karrama bakon ka wajibine ko ?

Baba a barshi bama zansha ba wallahi a koshe nake saida naci abinci na fito ai kaji dai tun ba,aje ko ina ba an fara nuna kyamar gida tsiyan dan kauye ya waye ke nan ai dama .

Na fahinci duk jan iyayyena takeyi amma saina kula baba daine bai kuma kulata ba ita inna data soma dama amsa daya take bata nai cin rai taja bakinta tayi shiru.

Ina Ubaida nake tambayansu kowa yayi shiru ban samu amsa ba yasa na fahinci da magana ke nan shiga mi da kayana daki na fadawa kanwata dake bina don kama yaya hajara danayi tana satan kallo troler dina da ido.

Murnan dana gani a fuskokin yan gidan mu yasani jin dadi har kasan raina don sun nuna min yadda nayi fama da dakon kewansu acan suma haka sukai fama da nawa ke nan don har mama datayi sanadin zuwana ido ta kafeni dashi tana mamaki.

Mun shiga dakin mu da yan uwana da ranan sabodani sukai fashin zuwa islamiya dana sama zasu tafi da farko muka zauna suke nuna min wanan dan innane kannin mu ke nan haihuwar innan mu biyu yanzu a bayana dukka kuma maza.

Na kafe yaran da kallo ina mamaki suma dai kamarmune suke sun dauko hasken fatan iyayyen mu saidai kamar basu kai mu mata daukowa ba.

Baba ya dawo da ledoji a hannunsa yana fadin ku mika mata tasha abincin dai kince sai zuwa anjima ko toki fara da wanan kafin anjima din ke Ai meye za a karo zan shiga kasuwa in dawo ?

Inna ta mike zuwa kofa inda yake take fadin saidai man miya da dan maggi sune suka kusa karewa dama to bari dai inje din tunda Allah ya rufa wanan asirin abinci dai gashi da alama mun samu don da gani wanan din namune aiko ya nuna buhu ukku dake jingine a kofan inna din wanda nazo dasu.

Ai tunda ya shigo kasan namune mutanen nan akwai alheri a garesu toke Ai ai ina jin wacan abin man da kike zancene a ciki wata kila harma maggi din an hado muna ai jeki duba kayan muga amma sakasu a daki don ban son saka ido.

Aikuwa baikai ga rufe baki ba nake jin muryan mama na fadin ina ruwan yar gwal yau ta dawo ai dada sai abinda idon mu ya iya gani a gidan nan yanzu.

Balle anga bariki yayi kyau haka yarinya ta goge tayi clean kamar wace aka saka a cikin injin ai dole jiki ya fara rawa haka a koma ana hada kai ana shawara anga banza.

Mairo kedawa kuka zone baba ya jefo min tambaya jin hakan yasa na dago na fito babu dan kwali a kaina gashina daya sha kitson zamani ghana weaving yana sheki nace baba dukkan mune mukazo ai da Antyna da Paapa sai yarsu Amirah.

A,a kice tafiyan tafi da gidanka kukayi wanan karon ya fada fuska a sake yana nuna jin dadin hakan da yaji yayin da inna tasawasu Uwale kira dasuzo su kwashi kayan su shiga dashi daki .

Dan satan kallonta nayi don jin abinda ta fada din tunda nasan hakan ba dabi,an gidan bane abin daya shafi dangin abinci akan ajene ko a raba kamar yadda mama ta sabayi ko kuma akai dakin shi baba din .

Amma yanzu naji tace a kai mata daki na juya na barsu a wajen zuwa cikin daki tun kafin mama ta fara sakin layi akan innan mu daga zuwana a tura min takaici da bakin ciki tun ban huta ba.

Amma sai naji shiru batace komai ba a lokacin yaran nata murna suna jidan kayan zuwa dakin inna din hankali kwance.

Kayane fa masu yawa wanda nudai bansan lokacin da aka sayesu ba haka kuma itama anty muda mukazo da jirgi ina zamu kwaso kaya haka masu yawa muzo dashi.

Yaya mairo kinsan kawarki tayi aure kuwa muryan saudat ke fadin hakan gareni na juyo ina fadin wata kawata kuma saudatu ?

Salma mana salma dai kina da wata kawa data wuce salmace a garin nan ai kuwa tayi aure ta auri wanan yaya Bello din dai da kikabar ana zancen shi zata aure harta haihu .

Kai ashe anyi auren na fada cikin mamaki tace tuni kuwa aikuwa dukkansu yan gidan da kika sani sunyi aure amma dai tau ?

Saudatu ni banson yawan magana din Allah daga zuwanta zaki fara da labarin haushi meye hadinta da zancen yanzu tunda tasan za,ayi tunkan ta tafi ?

Inna naga kawartane yasa na fada mata balle wanan aure ai sunanshi sorry auren da mace ta koma wani iri abinda ake son aga kaci gaba itako sai figewa da tayi duk ta koma kamar ba salma ba a yanzu.

Jam saboda me kuma bata da lafiyane tace waya sanar mata wallahi baki ganta bane gwanin ban tausayi ni naji anty Fati na fadin wai ashe mijin dan duniyane na gaske Allah ya rabaki da wahala.

Kai anty Fati kuwa tana nan gidan daddy ashe har yanzu dama ina zata ai tace sai mutuwa ita da fita gidan daddy suna nan suma anata kwamawa da ita da hjy kullum fada ai zakiga danta yau baida lafiyane bai shigo ba.

Allah sarki ashe harta haihu su anty fa da cewa yayyun salma din nan dai suke ban labari babban har aurenta ya mutu ta fito amma ta auri wani yaro kuma yanzu.

Muryan mama ya katse mu da take magana kamar fada tana fadin ai dole a saka kaya a daki yanzu tunda anga banza amma lokacin da nace taje din ba abinda ba a fadaba cewa ina bakin cikine yasa na turata wani irin tijarane ba ai min a gidan nan lokacin.

Allah kuma ya mayar maki da aniyarki ba tunda badon Allah kika turata ba ai kowa yasan sheri kikayi sai Allah ya kare ya bata gidan kwarai.

Yanzu kuma ke nan ko da abubuwa suka koma dadi za a fadi hakan kedai Ai munafukace ke bakiji kunyan an dawo da abin arziki har kina rawan kafan tura kayan zuwa daki ba kega yarki takawo alheri gida ko ?

Wai har yanzu suna abin nan na zata ai sun daina yanzu da girma ya fara kamasu ni mama dince ma naga ta soma tsofe min a idona ko bata da lafiyane wai ?

Lafiyanta kalau fitinace kawai irin nata ai kinsan ita a kullum inba ai masifa ba bata jin dadin rayuwanta.

Burodi fa yaya hajara tabasu Abba amma mama tasa masifa don me ta basu aikowa ya samu abinshi yakai dakinsane yanzu wallahi mama ta kwace bread din nan a hannun yaran nan babu kunya ko tsoron Allah.

Murmushi nayi ina fadin kai mama hoo ita dai halinta ke nan aida inna kada ta biye mata akai mata can din ba shike nan ba don yanzu ta nuna taji haushin hakan da inna din tayi mata kuma ?

Akai mata me anty Mairo halam tsoronta akeji da za akai mata kayan wallahi ko ina ba akaiwa tunda ita ta fara nuna hakan ai.



Waini Alh bangane bafa ya dago a yadda yake kwance rigingine saman dogon kujeran falon shi yana fadin da akai me kuma ?

Alh abin hauwa yana daure min kai idan nayi magana kace kai baka san yaya akayi ba to ita hauwa ajannace ko mai ira,izai da kawai saidai a ganta tana busha,shanta a gidan nan.

Yauma fa wai doya da kwai da ruwan shayi suke karyawa dashi gidan nan ba dole in fara zarginka ba ga hakan ko maza ta soma bi kuma ba a sani ba ?

Wani zabura yayi zaune saida tsoron furta hakan da tayi ya kamata ta juya fadin ina nufin ita dai ba karamar yarinya bace da za ace maza take bi tana samun kudi haka a yanzu ?

Naito fita daga dakin nan kafi ranki ya baci don yanzu zan iya saba maki kan wanan kalami da kika fada a wajen nan .

Ke baki taba sanin cewa in ma zargin hakan aike koda tsufan ku haka ya taso Naito kece zan zarga don kece da zubin hakan amma ba hauwa ba .

Alh ta fada cikin muryan mamaki yace kwarai kuwa ko kina mamakin hakanne in fada maki dalili hauwa bata bi maza ba tana karama balle da girman ta.

Au nufinka ke nan Alh kwarai kuwa ashe kon gane inda zancena ya dosa a yanzu hauwa ba a cewa zatayi haka da girmanta ya kara fada .

Inda hjy din ta amsa da fadin niko zan iya ko yace to lalai dai kan don in mutum ya faye hassada da baki ciki babu abinda zuciyarshi bai saka ya aikata.

Waiko kin mata yan uwan hauwa nada dan halinsu da zasu iya taimakawa yar uwarsu tunda sunsan halin da muke ciki a yanzu gidan nan aika samu yan uwana na kirki hakan ma wani abin godewa Allah ne shi.

Suka san soma musayan zance a wurin yake fadin sai kije kema naki yan uwan ko diyanki su taimaka maki yadda ake taimakota itama.

Amma banga dalilin mata na iya kokarinta damu a gidan nan ba yanzu kice kuma zaki kalli idona don tsaban raini ki aibanta yar mutane don bakin hassada irin naki ?

Ke na kula komai kinfi bukatan a gani daga wajen ki ko yayan ki na rabaki da wanan halin hjy kinki bari yanzu idan matar taji ko yan uwata yaya zaki da wanan kazafin da kikai mata yanzu ?

Dama ai ba a taba kawo zancen hauwa baka juyashi kamai dashi wani kala ba kai a wajenka daga magana zaka tsaya kana dogon sharfin nan don Allah ?

Anyi ba dadi don ya nuna mata baiji dadin hakan ba sosai tare da kwakwaran kashedi a kanta taja kafa ta fita a cikin kunya.

Ko ita kanta taga wautarta na furta wanan bakin kalman a gaban mijin nasu duk da tasan hauwa bata taba aikata ko abu makamancin hakan balle takai ga aikatawa.

Kantane ya kulle ta rasa ina kishiyar nata take samun kudi take facaka yanzu a gefenta wanda taso ta kara da ita amma ta kasa don ba karami abin takaici take gani ba a yanzu da talauci ya hausu sai taga kamar saboda hauwa din ma abi hannun miji nasu ya gudu.

Wai abin mamaki tana komawa daki Amira na sallama da kayan abinci niki niki ta girke inda suke ajewa tace Hjy ga abinci angode kawai ta iya fada a lokacin saboda bakin ciki.

Inda sabo zuwa yanzu aisun saba da halin hjy din don intaga dama kala batacewa,yaran sai dai su fita don haka sun saba da irin wanan halin na mamaN din.

Haka Alh ya wuni a cikin bacin rai da wanan zancen da Naito din tazo mashi dashi kan bata abokiyar zaman nata a wajenshi .

Shiya san duk abinda hjy hauwa keyi taimakone daga yan uwanta tunda harshi din tunda ya shiga wanan halin ba ,a sati daya cur basu taimaka mashi da dan abinda zai saka a aljihunshi ba.

Tun yana jin nauyin hakan har yakai ga dauke kafanshi zuwa sauraren wa,azin malam sai gashi ana biyoshi har gida da alherin.

Amma don Naito bata da tunane ko mutunci shine take shirin kullawa hauwa din sheri duk da tasan hakan sai kuma idonta ya rufe tazo gabanshi da wanan maganan.

Ire iren tunanen da yakeyi ke nan a wunin ranan don haushin wanan maganan fita yayi ko zai samu saukin hakan a zuciyarshi.

Yana fita kofan gida ya hadu da danshi habib suka tsaya habib din na fada mai sakon abokinsa na kasuwa daya fada mai game da shagonshi din .

Don yaki sakewa ya kuma ki bawa kowa shagon ya kama don haka shagon a rufe yake na tsawon lokacin nan duk da wajen idon kasuwane mutane da yawa suna kaunan wajen .

Dakyat ya iya bude bakinshi yana fadin habib na fadama ka fita zancen Alh sanusi baida buri a rayuwa sai ya bude ido yaga ban mallaki komai a duniyan ba shine burinsa .

Duk ya kara maka magana kai tsaye ka fada mai nace ba zan sayar ba kuma ban bada haya yaje gaba ya nema.

Alh Sanusi itin mutanen nan ne masu kudi wa yanda kudinsu amfaninsa yafi tasiri a wajen mugunta abinda yasa nace mugunta shine.

Duk wani dan kasuwa da ya kasa shine zai saye duk wani abinda ya mallaka haka kuma ko rasuwa Allah yaiwa wani mai hali zai lalaba ya sayi kaddaransa a raha a wajen iyalinsa.

Kana kuma kusan duk matansa matan mamatane abokan kasuwancinsa yake samu ya aure idan yaji labarin mace mai shanawace sai yabi baya ya aureta .

Gashi kowa ya sani yana bada bashi da ruwa bashin da zaikai mutum kasa warwars


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login