Showing 285001 words to 288000 words out of 395027 words
Chapter 96 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
nan na sauka kasan nan da safe yau dana dan shiga office kafin lokacin tashin jirgin mu sai nayi shawaran inzo in ganku kawai kafin abubuwa suyi min yawa .
Yarinyar ce ke gaidashi yake amsawa tare da kallonta lafiyanki kalau kuwa Amira kafin diyan tayi magana uwarce ta soma bashi labarin dalilin kwamciyanta a lokacin.
Ummah meye a ciki aida kin barta taje ta zauna da ita din shima Abba ai yasan tunda a na waje daya dole a taimaka maya irin hakan .
Wanan haukan kuma zafin ciwone yake sa tana abubuwan nan da takeyi din tana cikin wani haline babba abinda take gani tafi karfi a yau shine yafi karfinta sai an taimaka matayi hakan.
Ko gaida ita ba zasu koma zuwa ba a halin yanzu tunda abinta ita bana marmari bane tana ciwo amma sheri yana cinta a zaune.
Balle Abban ku yayi masu iyaka da part dinta yanzu idan na barta taje duk abinda ya faru karshe laifina zai gani.
Shiru yayi ya dafe kai bai sake magana ba sai can uwar ke fadin zaka kwana biyu ke nan garin nan ko ?
Hannu ya sauke yana fadin ina ganin goben nam ma zan koma da safe saidai naje naga malam da jikinshi yanzu nasan suna wajen karatu.
Anya malam din nan ya fara fita kuwa to ban dai sanarwa karfin halinsa ba amma yaji jikine sosai wanan karon don har ana zancen kaishi na gargajiya yace ba zai tafi ba.
Allah ya bashi lafiya shi nazo inga yaya yanayin jikin nasa dazun ko munyi waya da hjy Hanne take tambayana wai baka zo ba har yanzu ?
Ba kunya ya dubi uwar yana fadin idan nazo me zan mata ummah don Allah kibar danganta mu da wanan matar a duniyan nan tana cikin mutanen da ba zan iya mantawa da abinda sukai min ba.
Koma meye dai tayi yar uwatace baba bayan haka kamar uwa take a wajena don kasa itace ta fara tayar dani lokacin yanzu kuma ba komai bane zancen ka da Fadilane take tambayana akai.
Don na kula so take ta gabatar da zancen a wajensu malam don taga bata gane komai gare mu ba har yanzu.
Ba zata gane ba koda kuwa banda wace nake so ba zan taba hada wani hakaba da ita don shine zaman lafiyan kowa har su malam.
Kana da wace kakeso shine gida ba,a sani ba ga Alh yana mitan zaman ka haka a can bai mashi dadi bawai don yana zarginka ba a,a yace cikar kamalam namiji ko mace shine aure ?
Bai sake magana ba shiru yayi don bai shiryawa wanan zancen ba a yanzu donshi ya kyale zancen bai bata amsa ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[10/4, 9:49 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊 8️⃣6️⃣ 🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Bayan sun gaisa da malam din ya tambayi karfin jikinshi yace yaji sauki sosai Alhamdullahi yanzu bai jin komai kuma.
Ya tambayi sauran al,amura suka dan taba hira da kawun nasa nadan lokaci lafin yayi mai sallama zuwa masaukinshi inda ya saye don saukanshi a garin idan yazo.
Wanka yayi ya fito yayi shirin barci har lokacin baici komai a cikinshi ba yana jin jikinsa tankar an masa duka don gajiya ga idonsa sun kada sunyi ja a lokacin don tun zancensa da ummah yake jin wani yanayi na bacin rai a tare dashi.
Har yaushe ummah zata amincewa bukatan yar uwarta a kanshi alhalin tasan badon Allah da Annabi take son hakan ya kasance a tsakaninsu ba yanzu.
Irin maganganun da take fada akan yar uwar nata a baya da yadda ake labarin irin rikon da tayiwa mahaifiyar tasu yau kuma don ubangiji ya rufa masu asiri zata nemi wai a hada zumunci ayi yar gida tsakaninshi da yarta don manufarta ko ?
Ba alfahari ba ko mijinta Alh Chindo a yanzu yace zai daga mashi hannu zaisa a kawar mai dashi cikin second balle ita matarshi hjy hanne din don haka zai mata iyaka face to face dashi.
Haka ya ringa juyi a kan gado yana tunane ya rasa abinyi gida akwai dadin zuwa gako wani mutum amma abinda ya kula shine duk zuwa sai ya samu wani rikicin zumunci da zai daga mashi hankali idan yazo.
Hannu ya mika ya dauki wayanshi dake gefe aje yana budewa ga mamakinshi miscalled din Maryam ya gani ba zaice ga lokacin data kirashi ba .
Ya dannawa kiran waya har na soma barci na fitar da rai ga kiranshi a ranan sai gashi ya kira a cikin dare na dauka murya da dan amon barci ina hamma nayi sallama a gareshi.
Barci kika somane ya fada na sake hamma ina fadin wallahi wai ashe barci ya daukeni ban sani ba ina zaune.
Gaskiya kinji dadinki da nima zan samu hakan aida na more gashi duk gajiyan dake jikina amma ko darr banji a idona yanzu sai juyi nakeyi saman gado.
Tausayi ya ban sosai daya fadi hakan har ina tunanen kamar shi me zai damu zuciyarshi har ya hamashi samun hutu haka ?
Jinayi ina tambayanshi da kaci abinci kayi wanka kuwa yace wallahi banci ba maryam na daiyi wanka dazun nan kafin in kwanta.
To ka tashi kaci abinci mana don Allah ko yunwa zai iya hanaka barci da samun natsuwa gara ka danci wani abin kaji dadin samun barci cikin natsuwa zaifi.
Okey to shike nan tunda kina ganin hakan zaifi amma nina so in bari sai gobe idan Allah ya kaimu in karya gaba daya.
A,a don Allah kaci abinci ko kadanne kada ciwon ka ya tashi kuma ka koma kwance kamar wancan lokacin.
Ai yanzu koya tashi banda farga don gaki ai kinsan kin iya jiyan mara lafiya sosai har ya warke bai sani ba kinga sai in baro kano in dawo lagos in mike a shiga jinyata.
Kano kuma na tambaya cikin mamaki ina fadin yaushe har ka bar nan ka isa kano ina dazun kace min kana office kin manta da hanyar saukine jirgi na hau zuwa kano ai ba mota ba ko rufa ido ina kano tun karfe shidda na yamma muka shigo kano.
Nazo in duba jikin malam ne in kuma ga iyayyena dana kwana biyu ban zo na dubasu ba kinsan komai zakayi idan kana da iyayye a raye duniya ka fara basu kulawa don farin cikinsu shine naka.
Hakane an samesu lafiya ko ya kuma mai jikin shi kakankane ko malam din don naga kai da gatanka kamar kowa naka yana raye ?
Malam kawunane kuma babana haka kuma kakana duk shi daya ya tara wanan matsayin a guna ai zaki san malam Innuwa mana na unguwarku nan bayan ku ?
Wai kana nufin malam babba dai wanda na sani dogo mai farin gemu dama yan uwankune su ashe ?
Su malam Hamza mijin malama duk yan uwanka ke nan nima nayi karatu a baya kofan gidansu da mama tayi fada dasu ta kwashe mu ta kaimu islamiyan dasu saudat ke zuwa har yanzu.
Subbahanallahi mama don tayi fada dasu yasa ta kwasheku nace bafa inna nake nufi ba mama uwargidan baba din nan dana baka labari kwanaki.
Yanzu naji magana har gabana ya fadi tun yanzu kada inzo ace yan gidanmu basu da kitki azo a ja min matsala da naje na shiryasu kafin lokacin.
Haba dai akan me abinda akayi tun muna kanana sosai kila sun manta da hakan ai yace kike gani ai tunda ta kwasheku daga tsangayarsu kinsan fadan babbane.
Na danyi dariya na soma bashi labarin abinda ya faru a lokacin tsakaninsu har yadda muke nika mama na hattaran mu gama ta karbe kudin .
Sai ikon Allah naji yana fada a karshe yace wai kinsan wani abu maryam nace a,a yace kibar ubanfgiji da bawansa kawai .
Allah yakanyiwa bawa wani hikima wanda ba kowane zai iya fahintar hakan ba sai lokacin da ubangiji ya tashi ikonsa ga mutum .
Labarin nan da kike ban yasa na tuna da abubuwa da dama na rayuwa abu mafi a,ala ga bawa duk lokacin daya tsunci kanshi a wani kuncin rayuwa kada ya yarda hakan ya zama silan kaucewanshi ga ubamgiji .
Daddyna dare nayi ka tashi kaci wani abu kafin barci ya daukeka na kara fada naji yana fadin yanzun nan aka shigo min da abincin ai.
To barin barka kaci abincin kada in dameka da surutu kazo bakaci da yawa ba sai naji alaman yunkurawa yana tashi tare da fadin ina zaki ko har kin soma jin barcine dai ?
A,a barcin ya tafi ai karatu zan dan taba a yanzu Okey na zata don kinji mummy ki kusa kada matar nawa tayi fushi kin hanata hutawa da mijinta tun dazun.
Ina jin hakan na kashe wayan da sauri ina lumshe ido don kuwa na manta kano yace yaje wajen iyali ke nan ya tafi ni kuma lokacin da take bukatan mijinta na tsare mata shi da surutu.
Har ta dauka nayi hakanne don kawai inshaga hakkinta yadda wasu mata marasa hankali sukewa matan aure lokacin hutawa da mazansu.
Agaskiya wanan matar ma tayi hakkuri sosai don yanzu kam nasan ta sanda ina tare da mijinta zuwa lokacin nan don yadda muka shakun nan dashi haka dole ta gano yana tare da wata mace .
Ido na lumshe ina gyara kwamciya sanan na jawo bargo har kai ga mamakina sai barci mai nauyi ya daukeni ga hakan da nake.
Sai washegari na falka ina daki don ban fita da wuri ranan sai da rana ya dan fito ina fita mukayi kicibis da hajja yabi tana fitar da kaya falo.
Ban kulata ba nayi niyar fita na jiyo muryanta tana fadin idan mutum ma yana farin ciki da tafiyanane sai yayi bakin cikin hakan daga baya shima don komai nacin mutum sai yabar gidan nan wallahi.
Kallon tababba nayi mata tukun na sa kaina soma tafiya don fitan da zanyi sai wata zuciya ta izani da in fada mata magana nima.
Ban jiyo ba nake fadin da sauki ai tunda ba duniya mutum zai bari ba ba kuma gidan ubansa ko namijinsa bane ai hakan dama yana tafe.
Zata fara kwaran bakin nan nata nayi saurin fita daga falon ina murmushin ciki mukayi kicibis da Paapa tsaye gaban motarshi yana waya.
Da sauri na saita kaina ina gaidashi ya amsa da kai har na juya naji ya soma fadin maryam yau zan shiga arewa insha Allahu zan kuma tafi da yabi da zata zauna a can ko da sako wajen su senior ?
Baba uncle ina gaidasu da kowa Allah ya tsare sai gata har wajen tana masifa tana fadin wallahi zaki san kin shiga gonata ki jira kawai ki gani.
Meye haka kuma yanzu kin fito ki nunawa makwabta dalilin da yasa zaki koma gida da zama ke nan ko ?
Uncle Allah ya tsare hanya muna gaidasu Al Amin sai munzo ina dagawa yaron daya tako zuwa wajen ubashi hannu.
Kamar babba yaron yayi min hannu shima yadda nayi mai din shima ko da cewan yaron nata hakan nake sallamanshi.
Saidai a fakaice kuma da ita da tace sai na bar gidan nake ba amsa a lokacin ta kuma gane hakan dana fada gatsene gareta don naji tace fadi da guda kara da kuwa sai kin bar gidan nan kema.
Ban tsaya naga wucewansu ba na wuce zuwa get in fita na barsu nan suna rigima yabi oho na fada sai naji taban tausayi sosai akasan raina.
Don da alama ba don taso zatayi wanan tafiyan ba a yanzu don kawai miji ya takura da sai ta koma canne din zata bishi don dole tunda bata bari a zauna lafiya har makwabta ta soma fitina dasu a estate din namu.
Ji nayi kamar in fasa fitan a lokacin in zauna ayi komai a gaban idona har wucewansu saidai na kwabi kaina da ina ruwanki maryam kema mace ce fa.
Sai gashi kodana fita din ma lectural bai shigo ba ya aiko muna ayi hakkuri da bitan da zai muna din sai mun hadu a exam hole .
Ban jima a wajen ba na juyo zuwa gida don nasan yanzu gidan iya mune mu kadai zan sarara iya son raina babu wani fitina kuma sai dai abinda ba a rasa ba tsakanin zama.
Koda na dawo gidan shiru anty na daki na shiga na kwabe kaya na soma gyaran gida daga dakina zuwa falo nayiwa ko ina kwal na koma kitchen don in gyaro gaskiya bansan wacece gwaunan kazanta ba a cikinsu gaskiya.
Sai ince yabi ko badon bamu shiri ba sai don ganin ko yaushe ita tana kitchen tana dahuwa mace ce da bata wasa da tumbinta ita koba dadi zata dafa taciwa cikinta ta koshi ita da danta.
Amira ta shigo gidan tana cire takalma a kofa mukai arba da ita da ban gida a lokacin haka zata dawo ba tare data samu abincin da zataci ba.
Uwarta nace na tanbele a daki ko barci ko tana kallo inba yabi bace taji tausaya ta bata ba abincin a lokaci uwarta na daki kwance abinta bata damu ba
Saidai idan ta dameta ta hadata da buscuit ko snack shi zataci ko garin kwaki da gyada har yarinyar ta saba da hakan da uwar ke mata yanzu.
Tunda ta dawo ta manne min duk inda na saka kafa muna tare tana min surutu na rasawa Amira ta biyo da yawan magana haka yanzu.
Daki muka koma tayi kwace rub da ciki tana jawo wayana don tashiga danna na amshe da sauri ina mika mata tsohon wayar tawa dake gefe ajiye nace karbi wanan dai na fada maki wanan banson ana taba min shi ai.
Antyna tace min naje na dawo yau su Al,amin zasu koma kano dazun da zan fita nace zanje tace sai in zasu tafi dake zamu manyan idanuna na zaro da sauri na dubeta ina gyada kai sai tace kuma antyna tace ai ba zasu dawo ba sun tafi ke nan mama Al,amin akwai fada ko jiya kafin ki dawo tayi fada dasu maman,,,,,,
Katseta nayi ban bari takai ga zancen da zata fada ba nace ai badake take fada ba dai ko ina ruwanki da fadanta ke ?
Sai tayi wani irin murmushi kamar taji kunya tana gyara kwanciya kamar wata babba yadda tayi lokacin tace amma ai tanayi dake da antyna da kuma paapa.
Maryam wai kin dawone dama sai yanzu da naji wanan shiru bata shigo ba na fito naga har kinyi aiyuka a gidan ashe tana nan tana maki surutun data iya ko ?
Takai zaune tare da dafa yar nata tana kai hannunta a saman bakinta tace kinga wanan akwai gulsi a cikinsa gulman tsiya na rasa ina ta koyo surutu wallahi.
Dariya nayi nace haba dai surutun yarintane ai anty duk yaro kuma haka yake da surutu koda shi kadaine kuwa gyara zama tayi tana fadin umm,ummm maryam banso wallahi ta faye zuba ki tayani kwabanta don Allah ?
Nace inayi zan kula amma zata daina ai idan kinga haka kila koya mata akayi ana yawan tambayanta abubuwa yasa taga komai take fada .
Nima nayi tunanen hakan a raina don hatta babata idan yai magana dani saina jishi a bakin Yabi haka komai ya aje a dakinmu zanji tana fada.
Kirji na dafe a tsorace ina fadin amma matar nan makirace ta lalata maki yarinya a banza ba a sani ba wallahi maryam shima yana