Showing 327001 words to 330000 words out of 395027 words
Chapter 110 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
nine ?
Ba yau ba na kula hannatu tana canza maki halaiyanki a yanzu wanda ban sanki ba dashi a baya ke yanzu har kin manta da waye hanne ko ?
Malam don Allah kayi hakkuri baku fahinceni bane a yafe min don Allah haba hauwa nifa ba yaro bane da zaki juya zancen yanzu.
Kin nuna dankine Aliyu na shige maki gabako ni kuma isata gareki balle danki yasa nayi bugun gaba na ari bakinki naci maki albasa dashi bansan kin canza ba a yanzu.
Ya kashe wayan ya barta tana tana sharan jawaye ta mike tare da saba danta da yayi barci a lokacin kafin tace yanzu Alh ka kyauta ke nan kana kokarin hadani fada da malam da yake matsayin uba a wajena balle gadanga.
Yanzu dai an barki da danki ai nima kaina indai malam bai cikin zancen nan to nima bani ciki watau dai hauwa a yanzu nagane kamar kina takama da kudin danki ke nan ko ?
Koda ta kalloshi cikin mamaki yasha mur sosai a fuskanshi alaman abinda ya fada gaskiyane kuma ba wasa a zancenshi.
Kasa wucewa tayi takai zaune tana fadin amma inkayi min wanan fahintar Alh baka kyauta min ba ka barni inji da zancen hadani da malam da kayi yanzu don Allah ?
Tasa kai tafita a cikin kuka ranta a bace zuwa dakinta inda ta hadu da yar gidan hjy Naito tafito zata gida ganinta a hakan yasa ta juya ta koma tana fadawa uwarta taga hjy hauwa ta fito dakin Abba da kuka yanzun nan.
Wani shu,umin dariya tayi kafinta soma fadin aiki yayi daidai ke nan sun fara gani ita da mijin nata saura shi dan nasu kuma inji me zai sameshi yanzu kuma ?
Taja gindi yadda takeyi don dole a yanzu haka take kokarin jangidi tana wasu abinda kanta donta koma ita kadai a dakin nata ga yaran nata a yanzu sun daina shigowa sosai irin da dasukeyi.
Sai ta wuni a dakin ita kadai ba mai shigowa wurinta hakan yasa duk ta kara lalacewa ta rame dakin ya soma wari don rashin kula.
Waya ta dauko ta kira wani layi aka daga ta soma fadin Larai kiyi min murna aiki ya fara kyau yanzu haka ance angata ta fito dakin da kuka.
Guda larai din tayi tana fadin mena fada maki dama aikin mutumin nan kamar yankar yukane ai ki saurara kiji yadda zasu karasa a karshe.
Sundan jima suna magana kafin ta kashe wayab tana ajiyan zuciya ita kadai a daki saida danta ya shigo suka dan taba hira kafin yai mata saida safe ya rufo mata kofan ta baya yadda suke mata yanzu.
Don yan uwa duk sin dare sunki zuwa jinyata din an daukar mata masu aiki har biyu fitina yasa sun gudu sunki zama.
Yana ganin fitanta ya sake kiran malam yace dashi malam kayi hakkuri tarko na hada mata don Allah idan ba haka nayi mata ba bazata fita zancen hjy hanne ba da yarta.
Na fahinceka ai Alh nima ina sane da abinda kake nufi yasa na fada mata wa yan nan maganganun.
Sunyi magana yadda ya dace da juna irin ta maza kafin sukai sallama ya kashe wayan ashe wanan zancen da malam ya kirashi ya sanar dashi shine yasa najishi ranshi ba dadi a lokacin har bai tsaya munyi dogon waya dashi ba a lokacin.
Mukan a ranan saida muka makara don baba daya dawo da dare ya zata ma munyi barcine yasa bai shigo mun gaisa ba da safe kuma mun makara don bamu samu sallah asuba ba a ranan saboda kwana dake idon mu.
Bayan nayi sallahne nafito na gaida inna daje wajen murhu tana kokarin dora ruwan zafi na wuce sashen baba mu gaisa.
Inda na sameshi kishingide yana jan tasbaha redio a gefenshi yana sauraren bbc dake watso labaran safe nayi sallama nashigo bayan ya amsa min da fadin.
Ikon Allah mairo yau kece a gidan namu sai naji ance min wai gasu mairo sunzo nace a,a wata mairo kuma ?
Murmushi nayi ina samun waje nakai zaune na soma gaidashi tare da tambayan yaya bayan rabo sai bayan ankirani shi officer ya kirani yana sheda min cewa wai tare kukazo kuna gida.
Nace aida bai wahala da zuwanku ba yace min ai jirgi kukazo dashi kuma wanan yaron ya dauku dawainiyar hakan ma ?
Nima jiya uncle paapa ke fada min da yamma cewa zamu shigo kano tare dasu baba din yace ance da matarshi akazo ko nace eeh suna daki basu tashi ba tukun.
Ai akwai gajiya dole a rama barcin ai nayi murmushi kawai a lokacin bance komai ba don baba baisan jirgi ba irin wahalan nan ba irinta mota.
Inna tashigo da sallamanta ta samu waje takai zaune baba ya dubeta yace ai kinga Ai tun jiya ta kasa zama tana murnan dawowanki gida a yau ?
Nima dan murmushi nayi ina dukar da kai don zolayan inna din da baba keyi a kaina itako inna sai cewa tayi kadai kasa zama kai kana murnan ganin yarka takoma haka kamar wata kabila da ita ?
Kodai yaya ta koma mu abin yai muna dadi sosai Allah ubangiji ya karbi rokon mu akanta yau har gashi muna shirin ganin mijin mairo da idanun mu akwai abinda yakai haka dadi ga bawa.
Yau ace ka haifa har Allah ubangiji ya nunama irin wanan ranan ai hakan ba karamin godewa Allah bawa ya kamata yayi ba.
Allah ya rayama yakai yaro har yayi ilimi irin haka mai amfani ya kuma kare lafiya yau har zai kai ga dakin aurenshi ai wanan ba karamin baiwa bane ga yaro irin hakan har iyayyenshi.
Malam gata tunkan uwar dakin nata ta tashi ka tambayeta ko akwai wani maganane da sukazo din nan a tare don ni zuwan nasu ya daure min kaina ?
Wani magana dai sunzo da itane don iyayye su tabbatar cewa itace ta amince da wanan baikon da za ayi mata din kinga dai ba halin suce zasu sameta a can din shine shi officer yace zaizo da ita.
Yanzu hankali na ya kwanta malam amma tun jiya sai faman tunane nakeyi a kai zuwan meye wanan sukayi ni a zatona ko sunzo da itane ayi magana kan me zamuyi nan suji.
Kinji tako kinji irin shirmem uwar taku ko haba inna bafa sai kunyi wani wahala ba don shi gidanshi akwai komai zakice gidan matar aurene balle nasan zaiyi maku bayanin hakan nan gaba ai.
To kodai yayane mairo ai dole matsayin mu na iyayyenki muma mu nuna tamu bajintar akai mashi ke haka hannu sakene don munga yana dashi ?
Baba don Allah kada kuce zaku wahal da kanku duk yadda kake tunane Aliyu ya wuce hakan yana da halin yin komai a rayuwanshi.
Shi din dan gidan wayw ance zuri,an nan gidan malam babbane ko inna take tambaya nace toni inna bansan gidansu ba ai shine dai wanda kukaje gidansu ranan kedasu Saudat.
Malam kaji ba irin wanan gidan mu masu karamin karfi me zamu iya kai masu su dubeshi da daraja a idonsu dakin mahaifiyarshi kawai fa abin kallone don tsaruwa.
Tace dake mu kwantar da hankalin mu tunda tace hakan wai me zaisa ki daga hankalinki hakane Ai mun roki Allah ya kare muna su ya basu mazajen aure nagari yan mutunci Allah ya karba muna ashe yanzu ba godiya ya rage muyiwa Allah mu zurawa sarauta Allah kuma ido ba.
Komai kokarin mu irin wanan wajen ba zasu taba gani ba tunda kema kin fada yanzu irin abinda idonki ya gano gidansu ni banga wani abin daga hankali ba anan kuma ?
To shike nan ubangiji Allah ya shige muna gaba a cikin lamarin nan shiya kamata kice tun dazun kin tsaya kina zancen ku na mata nabawa kanku wahala.
Baba ya juya tambayana kan karatuna ina mashi bayani a tsanake har irin matakin da nake ciki ayanzu daya saura min time guda in karasa gaba daya insha Allahu.
Mun dauko maganan Ozil ne lokacin mama ta fito tana nemana wai tazo tagaidani da zuwa nan na fito wajen na sameta muka fara gaisawa ina mata yaya jikin nata kuma ?
Sai wani irin kallo take min har takai ga dafa bango don ta kasa tsayar da abin a zuciyarta har fuskanta saida ya nuna hakan a lokacin.
Bread da katon din kwai dasu irish da aka shigo dashi gidan ya katse muna gaisawan da inna da na somayi ana ta zubesu nan kofan innan mu tace wanan fa kuma ?
Ai tun jiya ake wanan hidimar haka kinsan tare da uwar rikon nata sukazo tana daki kwamce tana barcine bata tashi ba .
Tana cikin gidan nan ke nan inna tace tana nan kwance a dakina mama tayi wani iri da fuska sai kawai ta juya zuwa dakinta ba,a jima ba ina wankewa Amira baki yaya sahura tafito daga part dinsu.
Na bar yarinyar ina gaida ita nan ta soma ban labarin jiya dana barta taje sayen magani lokacin baba ke fadin Ai zo dacewa inna tazo tana zuwa ya soma fadin.
Yanzu Ai don Allah ki duba ki dubi tarbiyan yarinyar nan yanzu akwai inda take da illa don Allah ?
Dan murmushi kawai inna tayi mai tana fadin narigaka wanan tunanen malam nadai barwa cikina hakanne ai banga wani abin asha tare da yarinyar nan ba gaskiya.
Suna wajen anty Fati tashigo da sallama saidai wanan karon ta dansha jinin jikinta na dago daga Amira ina mata sannu da zuwa ta amsa tana fadin mutanen lagos ashe kunzo ?
Wanan Amirace ta girma haka na shafo kan yarinyar ina fadin itace anty ina su Affan da yan uwanshi muje daki antyna na ciki kwance nace ganin yadda su saudat sukai mata sai banji dadin hakan ba a lokacin.
Koba komai aita ba da hakkuri ga kuskuren da tayi amma su ashe har yanzu zancen na nan sun rike a ransu suna faman dubanta ta dashi.
Don in nuna masu ba komai da ita na fara bawa tsaraban danazo dashi inda tanuna jin dadin hakan sosai faman fadin takeyi ashe baki manta dani ba har yaran nan maryam?
Ance zancen auren ki akazoyi kon gani ba kinga abin Allah ko maryam dama ance wani hani ga Allah baiwane ga bawa hakan jinkiri ana fatan ya zamo alheri ga bawa .
Ashe hakan ba karya bane mukanta gidan mu da Allah ya rabaki da wahala yanzu ba komai sai tarin hakkuri da takaicin da sukw kwasa Alh yayi fada kamar me kuma yaki a raba auren yanzuma haka mijin zaune yake gida tunda yayi accident dole ankwasoshi hakana andawo dashi gida yana jinya duk uwa ta halaka dan abinda ta samu akanshi shiko bai aje komai ba ashe sai duniyansa yakeci can da mata.
Subbahanallahi Bello din yayi accindent kuma na fada cikin damuwa tace a, tanan Allah ya jetabeshi ba gashi yanzu ya zauna masu a gida yadda sukeso ba amma kuma ba moriya ?
Shiyasa karka hada mutum da malamai din ba,asan mugun abinda zai iya samun mutum ba idan sunyi mai kiranye din nan Allah ya bashi lafiya na fada aka amsa da amin.
Ke ita wanan da kike gani fa na rasa irin rayuwanta abu bai damun maryam don kayi mata takaici tace zata rikeka a rai a,a maryam saima ta nuna bata san kayi ba.
Mutum dayane naga hankalin maryam ya kauce a kanta itace kuma hajja yabi ko ita itace tajawa kanta hakkan taki kwantar da hankali ta fahinci maryam.
Wanan kishiyarki din ko dade ranan ba sai gasu gidan mu ba tare da wanan kanwar mijinku din nan wai sunzo unguwar nan ne ta tambaya aka nuna mata gidan mu.
I was shock danaji hakan nace ita hajja yabi din tace wallahi ai kinsan bansanta bani saida sukai min kwatancene nagono itace nake tambaya ko lafiya sukazo gidan mu ?
Aidana murde fuska karshema fita nayi na kama aiki a kitchen sai gasu sun fito wai zasu tafi ko rakasu banyi ba nace angode agaida gida.
Anty dake kwance saida takai zaune don mamaki tace hajja yabi dai ita dawa ke nan tazo wayasan da gidan nace Anty Asmau mana ba ita kika taba turawa ta karbo maki sako ba takai tura maki ?
Lalai matan nan tana da mugun abu a zuciyar ta nan inna ke fadin ko wasu da sukazo da yaro ai har gidan nan suke tayi bayanin yadda suka kwashe itama tace tazo gidan nan kuwa tace itace amaryam officer yanzun garin nan take da zama tana wani yatsune yatsunen fuska ashe da wani manufa tazo gidan nan ke nan dama !
Nikan fita nayi daga dakin don banda lokacin tsayawa wanan shirmen tunda naji ansoma hiran hajja yabi uwale na tura dakin inna ta kwaso min kayana kaf ta dawo min dashi dakinsu saiga anty din tayi wanka tace zasu fita da anty fati sai hakan yayi min dadi sosai ko banza zan samu na sakata da yan uwana a gidan.
Bayan fitan nasu muka bude kayan danazo dashi din na fara rabawa inda hat makwabta da innan mu ke abin arziki dasu saida na ware nasu na salma da yayantane yabawa kowa mamaki.
Yaya yanzu ita zaki kaiwa wanan na dauko yaddi guda cikin kayan baba nace wanan kuma Bello din wanan turmi mahaifiyarshi.
Cabdi jam in,nice wallahi saidai suji a gari nazo saudat tace min inna ta karba da hakkan yayi daidai sunsone ta ga hakan a wajensu sai gashi ubangiji ya juye lamarin nasa yayi ikonsa a kai ?
Ni kuwa cewa nayi meye laifin Salma Saudat salma fa da uwarta dorasu akayi ga hanya kinsan rai da kwadai salma da bello rabasu akayi dani da karfi da yaji harda asiri a lokacin kuma mamace tayi hakan don can ta hango far8n cikina a lokacin.
Ashe Allah ne ya rabani da shiga tasko ta dalilinta bata sani da tasan hakam zai faru a lokacin aida tayi tsaye a lokacin an aura min bello an kaini gidansa don haka ya faru dani.
Allah kuma na iya juya hakan ya zamo alheri a gareku gaba daya ba ba abinda ubamgiji bai iyawa ga bawansa ai.
Allah sarki ni wallahi har salman taban tausayi amma kuma wallahi ba zan iya hakan ba maganar gaskiya saidai ta tabbata a hakan da take yanzu.
Saudat ba a aon dan adam da riko sai ubangiji ya barka da iyawanka yagani amma kamaida komai ba komai ba sai Allah ta shiga lamarin ka ako yaushe haka rayuwa take inna ke fadin halan ga yar uwartawa.
Saudat ki koyi hakkuri don Allah ki daina biyewa duniya ni gashi naji yayanki na fadin yayi maki miji bandai san kowaye ba yake nufi akanki to wallahi ki gyara halinki tun yanzu don kina wanan rayuwan ba zaku shirya dashi ba ?
Wani yayan nawa yayi min miji kuma nace Oga Aliyu mana Allah ranan cewa yayi yayi maki miji da kanwarsa yaso ba mutumin amma kanwarsa za abawa wani dan uwansane yasa zai badake tunda yana da kanne da yawa yanzu.
Baki ta turo gaba inna tace ke arrr anyi maki gata har kina wani turo baki gaba nace abinda ya fada ke nan yace auren gata zaiwa yan uwanshi ko uwale da Amira shi zai zaba masu maza su aura nan gaba.
Kinsanshi rayuwanshi kamarta manya yake lamarinsa ai kamar wani tsoho dashi can mugun akidane dashi wallaho duk dabi,unsa na malam bahausheni dana addini baiso sam yaga ka kauce ko kadan yanzune zaku samu matsala dashi.
Ikon Allah har naji ya kara kwanta min a raina wallahi inna ta fada mu ance kina can kina sheke ayan ki a garin can hankali ya daga sosai a nan shine dalilin zuwan iyayyen ki ai kwanaki.
Murmushi nayi nace inna Allah ne shadata saina tare dani a can ba zance komai ba Allah ya isar min ga komai wallahi.
Shike nan kuwa bandaiyiwa dan wani wanan fatan don idan nayi kaina nayiwa hakan idan sun lalace kimga ba dadin hakan ke nan haduwata da Aliyu kadai ya ishi bawa nadama don kamar ubamgiji ya turoshi a rayuwana inna haka nake ganin abin idan ina tunane .
Amma shi yace tun ina karama yasanni a unguwar nan har ya dauka ni ko aljannace daya ganni kuma a lagos da irin dabi,ata nan na basu labari munata kwasan dariya saiga yaya sahura data dawo daga school of hygiene da take zuwa itace ta katse muna hiran mu tashigo tana fadin .
Yau kan innan mairo kece haka ke wanan dariyan a cikin farin