Showing 213001 words to 216000 words out of 395027 words
Chapter 72 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
working akan shi tun jiya good amma kinyi kokari sosai har kin duba da kyau akwai abinda aka samu a ciki ba daidai ba ?
Yes sir na duba an samu don almost two and half years ana wanan abin gashi ga date din da aka fara ga fitansu amma ga abinda aka fitar duk nayi fitar dasu a nan.
Kallon juna naga sunyi tsakanin su kafin ya gama ikon shan kamshinsa yace let me see it ya kika gano na soma bayani a jikin computer magic da sai ranan na san akwaishi a office din.
Ina gama a sanyayye nake fadin sune bayanin dana fitar saiku diba idan akwai wani gyara a ciki don da dare nayi working din su out.
Ko hakan you try iya hakan ya ishemu evidences a kansu well done thank you very much ke din abin alfaharine sosai awajen mu.
Yana shiru sai biron dake hannushi daya rike yana dan juyasu kamar me nazari tare da juyawa da kujeran da yake zaune akai a hankali.
Sai bayan ya nisa a hankali kamar wanda kwai ya fashe mai a ciki yace sulaiman zaka kira min taron duk wani director a company nan gobe by nine mu zauna.
Insha Allahu sir sulaiman ya fada idan bom din nan yayi link out kafin goben nan daga cikin kune ku biyun nan don ba wanda yasan da zancen nan a yanzu bayan mu din a nan.
Wani kallon mamaki nayi mai a hankali nace dashi da wa zanyi wanan zance a nan wana sani a wajen nan bayan ku biyun nan ban taba tsayawa nayi magana da kowa ba.
Nasani naji ya fada hakan yasa na dan duboshi yes nasani nasan duk wani movement dinki har gida kar kice na jawoki aikine ban san kowa kike ba ?
Kaje ka duba wancan ma yaudarin joseph koya gama hadawa ya mike tsaye nima nayi kokarin mikewa nayi da niyar fita.
Naji yace daka ina zuwa shi sulaiman din ya fita ya bishi da kallo yana fadin kar kiyi mamakina don kinji na fadi hakan na hada dake shima sulaiman din ina zarginsane ?
Da yardanshi sukai hakan don na kula sai lokacin da nayi tafiya irin haka ke faruwa idan na dawo sai a birkiceni ta baibai suna tunanen ba zan gane ba .
Nasan da wanan abin na nuna masu ban fahincesu ba amma ban dauka zancen har yakai haka ba gaskiya kinsan amana ba kowane ke iya rikonshi ba.
Laifin Sulaiman a nan shine sun gwadashi sunsan baya ganewa shine yanzu suka dauka nima ban fahinta wanan yasa nayi dabaran dauki don ki taimaka min da hakan gashi kuma Allah ya nufa kinsan kanki kin iya aikinki kin fitar min da komai yadda nake so.
Nagode naji fatar bakina ya fada don bansan ma zan fadi hakan ba a lokacin sai na danyi kasa da kaina.
Miko min wayan nan naki naji yana fada na dago kai da sauri na dan dubeshi hannunshi yana mike da alaman in mika mai wayan tawa.
Banji komai ba na mika mashi ya karba ya dan juyata yana fadin na zata aiba zaki ban ba ya duka yana dauko waya daga cikin drower din shi yace wanan zai fi maki sauki na sayone wanan tafiyan da nayi chaina kuma ban samu hadawa ba ashe rabonki ce ?
Na danyi kasa da kai kafin nace aida ka barshi kayi amfani da abinka tunda kana bukata wanan din ma zan iya manage dashi ai.
Ai baki rokeni ba ni nayi ra,ayin hakan na baki don kaina don naga dacewan hakan a gareki so ki karba inma baki so saiki kiyi kyauta dashi at last ?
Ya miko min na karba ina godiya yayi shiru baice uffan ba na daga yake fadin kin koma jiya sun saka maki gashin dokin a kai ko ?
Ke meyasa kike da taurin kaine wai maryam ina ga saina kai karanki kano zaki natsu ki daina wanan abin ?
Kano wajenwa ya dan duboni cikin mamaki yace hello watau har kin manta da mutanen gida ke nan niko kinga duk month end saina tafi kano na dubosu.
Wani iri naji sukan maza sunji dadi basu da shamaki akan abubuwa da dama idan sun tashi yin ko menene sabanin ni mace dasai aban izinin hakan kafin naje .
Ok sir nagode ai ban sallameki ba muga kitson nan idan attach ne Allah yau sai kin banyeshi yanzun nan kuwa ?
Sama nake kasa nake nayi mutuwan zaune ina kallonshi cikin karfin hali na soma fadin wanan ra,ayin kainane ai .
Don da banyi kitso ba danayi banda alhakin wani akan hakan don haka ra,ayin kaine saka attach ko wani abin kawa a jikina.
Mikewa yayi tsaye yana fadin iam telling you idan attach ne saina yankesu a nan din nan shiyasa jiyan ban hanaki ba ai ?
Ganin ya yunkura ya nufoni gadan gadan yasa da sauri na fice daga office din na nufi office dina na rufo ina saka key
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/10, 9:21 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊6️⃣6️⃣🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Tuni yaya Aminan hjy Naito ta tattara ta koma kauyesu dake karamar hukumar zaria a kaduna state don ba zata jure ganin wanan takaicin da yar uwar ke zubawa daga zaunen da take.
Tana zaune kullum ace dauri baiyi ba ya samu matsala amma kuma haka take masifa da miji da kishiya a zaunen.
Tafiyanta ya samo asaline a wani yammaci da yar uwar ta soma masifa da miji wai don yaga Allah ya mayar da ita haka yasa ya soma kyamarta yana wullakantata.
Naito wullakancin me nayi maki gidan ki fada min abinda nayiwa wani cikin gidan nan da ban maki ba don kina kwance ?
Naito ina wanan zancen ya fito haka don Allah na kula kebata lafiyanki kikeyi ba Naito bakin hali ne a gabanki wanda aka sai an gyara daurin nan karo na ukku shine har yaji dadin zancen duniya a yanzu ?
Ya kama ace ki koma ga Allah kina istigifar kina tuba ga aiyukan da kika aikata na kuskure a baya ko zaki samu rangwame a wurin ubangiji amma zaki tsaya kina wanan haukan haka kan duniya har me kikaga anyi a nan Naito ?
Mutumin da inya fita tun safe sai daren kwana kuma zai dawo gida inya dawo ya biku kaf dinku ya duba lafiyan ku shine kuma abin zargi wajen ki yanzu Naito ?
Zakice haka mana yaya tunda bake ake ha,inta ba duk abinda akeyi gidan nan duk da ina zaune na sani jiya da yace zasu asibiti ina kin daiga lokacin daya dawo gidan nan da ita ai ?
Akanta aka fara ciki ko itace autar mata mai haihuwan siti,alharini damu bamu haifa ba a gidan nan yanzune kake wani rawan kafa don bakasan kunya ba ko me ?
Kunya Naito kunya akan me akan na aikata zani ko na dauko ta nazo gidan nan muna bushasha a gaban idon ki zakice ina aikata abin kunya da tsufana ?
Alh ya isheni wallahi na kula so kake ka kasheni a zaune so kake kaga na halaka tunda hakan ba hasaranka bane in baka sona yayana suna so na da yan uwana ?
To ban sonki Naito na fada ban sonki kinji in duk abin nan da nake maki baki ganishi sai wanda na danyi wa yar uwarki jiya kije ki mutu din Naito ?
Sau nawa muna fita asibiti dake hauwa na gidan nan cikin lalura ban fita da ita itama zata sakani gaba tana tuna min cewa na kokarta mu koma dake kada a manta amma wai ke hakan duk bai maki ba Naito ?
Idan kin gaji nima nagaji ban iya jidalin nan a yanzu bayan kunya da nauyi da kika jefani ciki a idon iyalina da duniya kinsa na wofintar da matar nan da danta a baya.
Gashi cikin ikon Allah ubangiji ya duba hakkurunsu a kan mu ya duba masu yanzu sune suka koma tallafe damu ko yanzun nan kafin in shigo gida wallahi yaya saida yaron nan ya kirani ?
Yana rokona in bari a fita da Naito zuwa indiya da akace ana gyaran kashi haka kuma ya turo min da kudi yace a sauya mata shimfidan nan a sai mai laushi don zama waje daya ba dadi ga mutum amma duk hakan wai baiwa Naito ba yaya ?
Ai ban saka hauwa ko danta kulani ba ni za a kawowa makircin banza meye ban sani ba balle su boye fuskansu ta gaskiya gareni don duniya tace babu hannunsu ciki ?
Me kika sani aisai ki fada muna muji Abba ya fada yayin da yaya Amina ke gefe daya tana rafka salati tana taba hannayenta cikin mamaki a garesu.
Ki fada mana muji ya kara fada mata tace ko ban fada ba aikowa ya sani ba sai na bude baki nacewa wani aiko min da hakan akayi don in nakasa ba ?
Tunda kafan nan kowa ya fadi kamar ansa min hannune a cikinsa towa zaisa min hannu bayan hauwa da danta da suke ji kamar su dafani da raina a gidan nan ?
Salati yaya Amina ta sake sakewa ciki mamaki tana dafe kai tace yanzu naito shirkan dake ranki ke nan dama baki yarda ubangijine ya jarrabeki da wanan laluran ba ?
Yaya ai kinsan me hali ta dauka kowa irintane haka da zuciyar mugun nufi ga dan uwanshi ta dauka yadda bata da imani haka kowa yake shima ?
Tona gaji kuma wallahi tunda haka kike zato indai ni zance mutanen nan yaron nan ya fita dake waje yaje ya kashe kudinsa a banza kanki babu godiya sai mugun nufi wallahi yaya ba zan taba hurta hakan garesu ba .
Mata kuma tawace ko ciki goma na bata a rana ba abinda ya shafeki kema idan kina iyawa kwanta in baki yanzun nan ki dauka kamar yadda itama ta kwasa a wajena kaji min zancen banza zancen wofi.
Mata ana kokari dake amma son kai ya hanaki ganin hakan saboda jin dadi wa kika haifane wai saiki tsaya akan shashashun diyanki da basu san ciwon kansu ba kiyi masu wanan dokan bani ba.
Cin mutunci ta fara a zaunen itama yace zaki san kiyi min haka nasan matakin dauka a kanki wallahi ke in badon albarkaci ba Naito har me zai zaunar dake dakin nan a yanzu ?
Amma zaki san kiyi wanan abin yasa kai ya fita duk wanda ke gidan yaji wanan draman tasu a ranan a lokacin ne yaya Amina tace goben nan zan tafi gida Naito tunda zaman banza nake a garun nan ban sani ba saiki zauna duk wanda zaizo bayana ya dubaki.
Hakan ya faru kuwa don washegari da safe daga kofa Abba ya tsaya yana gaida yaya Amina din don baishigo dakin ba kamar yadda ya saba bayan sun gaisa take fadin Alh yau din nan nake son in koma gida insha Allahu.
Yau yaya to zan turo habib yanzu idan na fita iya hakan yace bai tsaya wani tambayan dalili ba a wajenta yasan don abinda ya farune jiyan itama ta yanke wanan hukuncin don bayan tafiyanshi yana jin muryansu sunawa juna cin mutunci a lokacin.
Itama dai umma Hauwa tazo gaidasu a kofan kamar yadda maigidan ya tsaya ta tsaya saidai ita jam,i tayi tana fadin kuntashi lafiya yaya yaya dare kuma ?
Lafiya hjy hauwa yaya karfin jikin naki kuma ya kwanan yan matan dakinki kuma ta amsa da lafiya kalau yaya Alhamdullahi.
Tace yau na dan makara ba a kawo abin karyawa da wuri ba yau don Allah ayi hakkuri yaya amina ta murmusa tana fadin.
Babu komai hjy hauwa sannu da kokari nima a yau zan maku ta baki don zan koma gida insha Allahu wani kuma sai yazo ya zauna da ita don gida suna bukatana a can suma.
Ayya Allah sarki kawai ta fada ta juya zuwa dakinta bata tsaya ta shiga ta zauna yadda ta sababa ta danyi hira da yaya Amina din wani lokaci hjy din ta saka masu baki tana gwatsale hauwan amma baisa tayi fushi da halin abokiyar zamam nata ba.
Amirace tayi sallama a dakin tana saye cikin tufafin makaranta a jikinta ta gaidasu tacewa yaya Amina gashi Abba yace in kawo maki idan kinje gida ki gaida mutanen gida.
Ido hjy Naito ta sakawa kudin da yarinyar ke mikawa yar uwarya inda wani bacin rai ya ziyarci ziciyarta lokaci guda ina ce kun gani yanzu ai..
Don wullakacin da Alh ya dauko yi min Amirace zai aiko da kudi ta kawo maki shi baya iya zuwa ya baki hannu da hannu kome ?
Wani aiki nayi mai balle kice sai yakawo min kudi hannunshi hannuna ko a hakan nagode donni ban iya butulci ba ?
Au haka zakicema yaya sai ta fashe da kuka tana lalaban wayanta ta fara neman yaranta duk wanda ya daga sai tace yana ina yazo tana nemanshi yanzun nan.
Hankali tashe suka hadu a dakin aka soma magana sai kuka takeyi tana fadin maganganu ga yayan nata wai harda yaya Amina taki fahintar ta tace gida zata tafi.
Keko umman Soba in baki zauna da hjy ba wa zai zauna da ita ai dole ko kowa ya gujeta ku ku zauna da ita haka ?
Waya gujeta me akai mata bafa zan zauna ba tunda a shekarun nan na Naito har ubangiji ya jerabeta da lalura irin haka amma Naito ta kasa imani ta kwashe abinda ya faru ta fada masu kaf.
Haba hjy ina ruwanki da abinda akeyi gidan nan keda ke fama da kanki yanzu ai umma nada gaskiya ko nice gara in koma tunda wanda nazo donshi bai gani ba ?
Zakace haka mana kai tunda baka fahinci bakin cikin da hjy din take gani ba tunda kai ba mace bace amma ta yaya don hjy Hauwa nada ciki Abba zai dinga rawan kafa a kanta ya habib ?
To ni dai bance komai ba ke hjy yanzu sai kiyi hakkuri dole tsoho yai rawan kafa tunda kullum yana jin dumus a aljihunshi bakiga wani irin haske da kiban daya kara bane ?
Ke hjy yanzu saida saidai kiyi hakkuri gaskiya don tsoho yanzu ko kina da lafiya ba zancen ki yakeyi ba don bai yarda ya bata inda ake tallafa mashi.
Sanusi wanan wani iskancine haka wai na kiraku don a san abinyi kazo kuna min shirme yaya Amina ta fito da kayanta daga daki tana fadin .
Nina tashi ke nan wanda ya shirya a cikin ku ya saukeni gareji yau ba zan kara kwana garin nan ba wallahi ba yadda basu bata hakkuri ba amma tace tayi rantsuwa bata kaffara dole suka kyaleta ta wuce sunaji suna gani suka koma zugun musanman matan don sunsan su aiki ya sama yanzu kuma.
Saboda ba karamin taimako yaya Amina tayi masu ba gata da tsabta da hakkuri da sanin ya kamata bata duban komai tsakani da Allah takeyin shi gidan.
Tun wanan lokacin dole suka raba idan wanan tazo ta kwana da ita wanan zata zo ta wuni ita dayan taje gidan mijinta wajen iyalinta haka suka raba abin a tsakaninsu.
Nayi shiru a inda nake zaune na gama gyara wayana dake ban matsala haka yasa na tuno da wanan wayan da yaban na tura a jakkata tun a office din nashi.