Showing 354001 words to 357000 words out of 395027 words

Chapter 119 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

Saudat yan dakin mu babane wanda ya tsara hakan kan wanan tafiyan da yazowa kowa a bazata dagamu har yan uwanmu zancen yazo muna a bazata cikin family.

Abin kudi cikin sati biyun za a kammala komai na tafiyan mu inda zamu tashi a karshen wata zuwa kasa mai tsaraki.

A lokacin mama kam haukane batayi ba don gaba daya hankalinta ya daga sai lokacin kuma ta tabbatar daba karamin arzikine ga Oga Aliyu ba tunda ya iya kai yan uwana har biyar umurah lokaci guda haka duk da ance umurah ba kamar hajji bane baikai aikin hajji kudi ba ko kadan amma hakan ya daga mata hankali sosai.

Dalilin wanan tafiyan yasa yaya ibrahim zuwa gida tare da iyalinshi dake da yara biyu yanzu wanda kowa yayi mamakin hakan gareshi sosai.

Yaya ibrahim baida hayaniya baida rigima shine dan farin mama data haifa da baban mu amma sai ba jittuwa tsakanin shi da mama din tun yana karami.

A kan hakane ya soma barin gida shida wani makwabcin mu dan kasuwa suna zuwa kasuwanin kauye suna sayo hatsi suna shigowa dashi kano.

Sai mama tasashi gaba kuma kan bai taimaka mata ita bataga amfanin wanan sana,an ba nasu tunda ba karuwa a cikinshi mama irin matan nanne da in idonsu ya rufe zasu iya yiwa dansu baki ba tare da sun sani ba saidai kai dake cikine zaka gane hakan garesu.

Gata tana fifita dan uwansa akanshi wanda ke dan bata canji ba tare data san ainihin sana,anshi ba wanan yaba yaya ibrahim din haushi yayi kaura daga gida tun wani fita da yayi ya jima bai dawo gida ba don har an dauka ya mutune a cikin duniya saiga wani dan unguwarmu yace ya ganshi a ibadan daga baya kuma akace yabar ibadan din aka jima ba motsinshi sai daga baya aka gano yana kuma cikin Niger state a zaune.

Sai mama ta soma fadin wai asiri innan mu da yan uwanta sukai mashi suka tura mata diya cikin duniya don kada ta moresu.

Shi yaya Rabi,u wanda suke kiranshi a unguwa da rabe ya bar gidane ta dalilin kamasu sun fasa shagon wani dan unguwarmu a bakin layi tunda yaji ankama yan uwanshi ya tsare yabar gari zuwa enugu bai dawo garin ba saida ya share shekara biyar cur sannan yake dan zuwa ya kwana biyu ya koma.

Amma a karshe laifin duk mama ta dorawa innan mu akan itace tayi masu bakin asiri suka watse suka bargidan.

Ance a lokacin ko fada yaya Rabe yayi da innan mu sai yace zai bata kashi dole inna zatayi ta zaman daki har yagaji ya fita zancen.

A can gidansu oga Alley kuwa mutum biyar din da yace a dauka kannesane dukka mata hudu na gidan nasu ya zana sai Yusuf dasu yaya Habib sai wani kanin babansu wanan baba sanusi din.

Gidan malam kuma a can ma ya dauka bayan yusuf mata biyu sai namiji guda daya kara wajen mutum goma zasuje tare dashi.

Ya mikawa Sulaiman sunayen a nemo takardun masu tafiyan aiko da hjy Naito ta samu labari ba murnan hakan da yayanta keyi tayi ba ita.

Don haukacewa tayi a ranan gidan tana sababi wai su za a nunawa karya don suna wawaye kuma su har da murna sukeyi ?

Bayan amfani yakeyi da arzikin jikinsu yana cigaba su kuma suna komawa baya sanan don basu da wayau zaice zai kaisu umura su tsaya suna washe baki ?

Kai da abin yaiwa Abba yawa yashigo ya tsaya kofanta yayi mata tijara tare da fadin duk ya kara jin ta tayar da wanan zance a bakin aurenta da zama gidanshi ke nan gareta haka yasa yayan sukai mata magana tayi shiru dole.

Hjy Hanne kodata isa gidansu ta samu malam zaune a inuwa da mutanenshi dake zuwa wajenshi cikin gida ta nufa inda tasa ai mata iso gata tazo tana son ganinshi.

Bai jima da bakin nasa ba ya sallamesu malam hamza shiya shiga ciki yace tazo ga malam din su gaisa dashi bakin nasa sun wuce ai bata so hakan ba amma dole ta taso tasameshi a can din.

Hanne kune tafe ashe mune malam yake fadin inji dai lafiya ko don yasan ta tsamesu a yanzu cikin sha,aninta bata zuwa gida sai can ba a rasa ba idan wani abin ya kawota irin haka.

Eeh to lafiya ke nan ta fada tana satan kallon malam hamza dakw can gefe daya yana rubutu ga allo tace.

Dama akan zancen yaran nan nazo yace na,am wasu yaran ke nan daga cikin diyan namu tace yar wajena Fadila da nake son a hada da dan wajen hauwa Aliyu ?

Sai naji ance kuma kunje kun daura mai aure da wata daban bayan nazo nan da kaina na sameka malam na fadama sai kuma inji hakan ?

Kun kyauta min ke nan ko wani abu ake nufi dayin hakan donni nasan duk abinda nayi sai kuce min nakawo maku sabon akida a gida ?

Bamu muka daura badai hanne Allah ya nufa yarinyarce matarshi ai daga tambayane abin ya juye ya zamo aure a tsakaninsu yanzu.

Shiyaron da kansa ya gabatar muna da ita mukaje nema mashi ita bayin mu bane hakan ko ra,ayin mu yadda kike tsammani ?

Amma malam kasan baku kyauta min ba da kukai hakan nasan daga yaron har uwarshi da ubansa a karkashinku suke garin nan ba wuce ka tankwasa shiba ke nan idan kaso ashe ?

To ni yanzu nazone in kara fadama tunda nayi niyyan hakan ba fashi a gareni sai an daura wanan auren nasu kafin tarewan ita wanan yar matsiyata da kuka daura mai da ita yanzu.

Nina rasa gane meyasa kuke min hakane ance banda zumunci da yan uwana yanzu kuma na nuna ina son ayi zumuncin kun nuna min ba haka ba ?

Hanne idan yaron nan ya amince ina maki albishir din ko yau din nan ke yanzuma din nan mu shirye muke damu daura masu aure a wuce wurin.

Ina na fada maki yadda mukayi dashi a baya yaron nan yace bai amince da hakan ba harma in auren gida yake so ba kuwa yarki ba .

Nasan ko saboda halinkin nan ne yasa yake tsoron hakan ya kasance din a tsakanin ku ban dauka tunda mukai haka dake ba zancen nan ya saura ashe a wajenki.

Don yace hakan shi zaisa a yarda da maganan shi kodon yana da kudine shi ba,a iya tankwasashi kamar ko wani yaro da muka haifa ?

A,a ikon Allah kikan fara zancenki ke nan hanne shi din yafi karfin mune don yana da kudi ai barin maki na mahaukaci a yaran mu kaf dai jikokin malam da kika sani shi Aliyu yafi kowa saukin kai a cikinsu.

Don bai taba ketare zancen mu ba gidan nan halin uwarshi sak ya kwaso harma ince ya darata wajen yi muna biyayya a gidan nan.

Kudi kuma ai bamu maka bashi ba Allahne ya bashi abinsa inya bamu mu karba in bai bamu ba Allah yasa ya mori abinsa a zauna lafiya .

To nidai abinda ya kawoni ke nan yanzu in fada maku zan saka ranan nasu bukin don ku sani tunda nayi niyar hakan kuma kowa yasan da hakan a yan uwanta .

Dako kinyi kunya hanne yau ko diya mace aiba ayiwa hakan balle da namiji dake cikin lokacinshi aure ai saida yarda akeyisa ko ?

Bari haukanki yakai aikata hakan hanne dan kina ganin ke kina iya taka kowa a zauna lafiya a yanzu ko?

Allah ya kai,ki zuwa aikata hakan kunyace rabonki a karshe akan zancen nan don wanan yarin yafi karfin kiyi mai hakan malam hamza ya saka masu baki jin yadda take sa,insa da yayan nasu daga inda yake zaune kan zancen.

Idan anyi magana takaman ki kudi wai in tambayeki hanne mijin naki yafi kowa kudine a garin nan ?

Shi mijin naki dake da kudinsa baiwa mutane irin wanan iya shege kowa a banza kike kallonsa hanne ?

Sai yanzu nagane tabbas kina da manufa ga wanan auren da kike son hadawa baiwa don zumuci ko wani abu bane kikeson hakan.

Akwai wata manufa da kike bin yaron nan dashi yasa kika matsa saiya auri yarki duk da yace ba zai aureta ba yanzu kinji yayi aure kin kwaso kafa zuwa wajen malam ya tillasatawa yaron kike so kome ?

Dama nasani nasan ana min bakin ciki a gidan nan don anga kawai Allah ya rufa min asiri bansan abin yakai har da yayana ake bakin ciki ba ashe ?

Ba wanda ke bakin ciki dake hanne don baki tarewa kowa a gidan nan komai ba tunda ba cinki bashanki ga kowa kije din kiyi abinda kikai niyar karshen ki bakin ciki .

Maganganu masu zafi ta soma fadawa yan uwan nata kamar yadda tafadawa hjy hauwa kafin tazo nan din ta mike ta tafi tana sharan kwalla wai an nuna ba,a kaunarta a cikin dangi.

Wanka na fito ina shirin tafiya school wayana yayi kara cikin mamaki nake fadin waye haka da safen nan don kiran safe wani lokacin yana dagawa mutum hankalinshi.

Sunan saudat dana gani yasa da sauri nakai hannuna a wayan don bata faye kirana haka da safe ba saidai zuwa rana ko yamma ko kafin Aliyu ya kirani da dare.

Saudat lafiya na fada ina daukan wayan naji tace yayan ba lafiya wallahi mun tashi yau gidan mama ta rikice muna fa.

Innalillahi na ambata meya sameta na tambaya tace wallahi ba wanda ya sani ihun yaya sahura daine ya tayar damu da safen wai mama ta fadin a hanyar bayi .

Hanyar bayi kuma tace wallahi bama wanda yasan ko yaushe ta fadi fa da yaya taji shirune ta biyota shine ta sameta kwance a tsakar gida kace kace gata can dai an kwasheta zuwa asibiti har da inna.

Barin kira baba ko inna na fada tace to muma gamu nan cikin zullumi tunda suka tafi ba wanda ya kira gida cikinsu tundazun.

Bara na kirasu na fada ina kashe wayan hankalina duk a tashe kardai ace min mama ta mutune da gaskiya banji dadin hakan ba wallahi.

Duk yadda kake da mutum indai kai musulmin kwaraine ba zaka tabawa mutum dan uwanka fatan mutuwa ba koyaya kuke dashi ?

Hakan ne naji akan wanan labarin don sai nashiga damuwa sosai a lokacin haka nafita gida ranan ban sanarwa kowa fitana ba.

Nakirasu sunce kamar shanyewan bari jikine ta samu amma zasu jira bayanan likita dai idan ya fito wanan yasa hankali kara tashi sosai saida nakai school har mun shiga lectures na tuna bamuyi waya dashi ba ranan.

Gashi kuma har mun zauna lectures dole na hakkura saida muka fitone na kunna waya da niyar kiranshi duk da nasan yana tsaka da aiki a lokacin amma dole in gwada kiranshi din ai.

Ina kunna wayan kirashin na shigo min a lokacin na dauka da sallama tare da fara gaidashi da kwana ya amsa yana fadin ya kika fito gida haka kowa bai sani ba kuma kin kashe wayanki ba a samunki gabadaya.

Ina lecture nafada naji yace kin samu babane a waya nace ban sameshi ba yanzun muka fito na kunna wayan zan kiraka sai gashi ka kira.

Ok yana nemanki yace a fada maki an basu gado asibiti ta samu struk a hannu da kafa amma likita yace bai kamata sosai ba dai.

Innalillahi Allah ya bata lafiya yace amin naji yana fadin nasa a kaita Aminu kano yanzu haka munyi waya dasu harsun isa din a can ma gadon suka bata.

Nayi mata addu,an samun sauki muka dan taba hira akan laluran kafin mukai sallama don zamu koma lectures din a lokacin don breakfast muka fito yi da shabiyu shine na kirashi.

Shigana da yanayina a ranan da a arewa nake zasu fahinci na sauya sosai a lokacin ga dabiun da suka sanni dashi a baya nashigana.

Amma nan da yake yan nocase ne su ba wanda ya damu da hakan gareni saima kokarin suke muyi shaking din hannu dasu yadda aka sabayi din da juna.

Har muka tashi nafito na nufi wajen motana dake fake don tafiya gida duk dana hango Ozil a lokacin hakan baisa na tsaya ba mu gaisa yadda aka saba dama sama sama muke dasu tun faruwan wancan matsalan yanzu kuma ina son avoiding dinsu gaba dayane a rayuwana saboda tsaro na addini a kaina.

Saida zan wucene nayi masu horn kallon mamaki suke min ina kallonsu ta mirrow din motan ban dai tsaya ba na halba motana na fice 8828waaaa2wa8adagaaaa8a8wa8aa school dinaowaaaaaaaaaaawawaaaaa8a8a8aaaaaa8waaaa.

Nayi hakane don kare kaina daga shiga hakin aure da kuma tsoron irin azaban da Allah ya tanada akan hakana donshine nake son sabawa kaina kamun kai a yanzu din fiye da8 wanda nakeyi a da.88

Gida na nufa kai tsaye amma saidana tsaya8a na nemi abinda zanci a8 hanya don ba lalai bane ina samu anyi abindaw 8a88a88mutum zaici idan na koma gidan lokacin.

828w Haka dinne kuwa ba kwowa a falo nasan tana can tana barci na nufi dakina na bude nashiga tare da aje kayan dana shigo dashi a hannuna.

Nashiga sauya tufafin jikinane don in rage nauyi da gajiya alokacin Amira ta shigo dakin tana gaidani.

Nace shine rudin shedan sudakeyi sun bada gaskiya akan hakan cewa wani zai iya masu abinda Allah bai tashi yiba a lokacin sai su manta da Allah keyi ba wani ba.

Ai ba zan kara hakan ba gaskiya duk abinda kika fada gaskiyane karshe ba riba ga hakan kai bakai amfani da kudin ka kaba wani kato yacisu a banza dama ace laluran ciwone ko wani abu aida sauki koda anci din.

Gyara da kwato miji a hannu yana gun mace don tafi malami makamin hakan keda kanki zaki gyara duk wasu hali naki anty.

Lokaci yayi daya kamata ace kin bar duk wani abu na kurciya a yanzu don Allah saiki barwa yara kuma suci gaba da hakan ki kama gidan ki kin daiga yadda yabi tazo gidan nan tayi.

Uncle namijin bahaushe nefa koda yabi zai iya karo wata mace don haka kedai ki gyara bangarenki yazamanto kowa ya dauko kece dai a gabansu.

Ba azo ana maki kallon rainin wayau ba a sameki waje ace kuma anfiki iko da sanin yakamata da wajen mun jima muna wanan hiran da take fadi a karshe.

Kuna ban mamaki yaran arewa wai koya maku wanan abin akeyi kome sai inga kowace tasan komai koda batayi aure ba kuwa.

Nayi murmushi ina fadin da hakafa muka taso ba fita talla kana gida da iyayyenka kana ganin komai hakama a isilamiya ana koyar da zamantakewan aure wani lokaci.

Saidai idan diya tasawa kanta shashancine ba zata tsaya ta kula da irin tarbiyan da uwa ke koya mata ba.

Anty kinga dauko min kauda wancan wanke wanab gyara can gun kwashe wanan duk wa yan nan aiki ga diya mace ba wahal da yaro bane gyarane agaresu .

Don yarinya zata taso mara son jiki da tsabta da iya wasu abubuwan amma iyayye a yanzu sun dauka ka dauki yar aiki a gidan ka wayewane wanda basu san suna kashe kansu da kansu bane a hakan.

Donko yaya zasu taso cikin rashin tarbiya da rashin kuzari su kansu basu gane zasu cutawa zuri,ansu wajen son jiki.

Maryam na yarda da zancen ki don ko ni kaina nataso a hakan ga kuma Amira yanzu banda yawace yawacen makwabta ba abinda ta iya yanzu nace babban illa ke nan anty kabar danka yana mu,amula da makwabta baka san irin rayuwan da yaro yake koyaba a can din.

Mijinki kafin ya dawo gida kin gyara gida kin gyara kanki kinyi girki kin gyara yara fada min ta inda zaku samu matsala anan anty.

Dariya ta kwashe dashi tana fadin shame on me maryam nice yakamata na tsaya na lurar dake wanan abubuwan a yanzu amma sai gashi nice kikewa huduban hakan a takaici.

Nan nake mata hiran zancen zuwa umurah din da zamuyi amma naso aje da ita yace zaiwa paapa magana yaji take fadin nasan ba zai yarda ba din cikin nan dake gareni maryam.

Sai lokacin ta iya sanar dani zancen cikin dake jinkita nake fadin aina sani tayi mamakin hakan take fadin to tana tsorona sosai gaskiya.

Sai gashi mun shiga kitchen a tare ranan munyi girkin abincin dare har lokacin hiran namu bai kare ba don tana min hiran inda sukajene wai duk akan hajja yabi.

Anty da ki cuci kishiya gara ki bari ta cuta maki don zakiga sakamakon


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login