Showing 258001 words to 261000 words out of 395027 words
Chapter 87 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
bai hana ta halinta ba shine masifa sa ido da jinini tun safe ko ince abinda yafi sati take wanan korafin .
Na ita bata yarda cewa ba maigidan bane ya gyarawa hjy hauwa daki haka don shirin haihuwan da zatayi wanda take ganin kaf gidan bai taba zumudi da rawan kafa kan za a haifa mashi da a gidansa ba.
A cewanta ko wani numfashi Alh ya sauke a yanzu naga tunanen hjy hauwa da abinda ke cikinta wanda fatanta a kull taji cikin ya bare kamar yadda hjy Asabe amiyanta ta fada mata ance cikin ai honkone don ansa iska sun tausheshi saidai ta mutu dashi a jikinta.
Cikin ba zai taba tashi ba illa ayita sa idon haihuwa aji shiru ma,ana an taushe cikin suyi ta bakar wahala kamar yadda itama suka aiko mata da wahala take zaune haka ?
Don acewansu hannu akasa mata taki warkewa daga wanan ciwon tsawon lokaci tana zaune a waje daya tana wahala da kafan garama hannun shi a yanzu ya fara amfani tana dan iya daukan abu dashi wani lokaci saidai ba mai nauyi ba.
Wahalan duniya da takaici ta ganshi ta dalilin wanan kariyan kafan data samu gashi sai faman narkawa kafan kudi akeyi kamar ba,ayi.
Yanzu kuma gashi ta zage wanda ke taimaka mata din tayi mai cin mutuncin ido da ido kan aiba shi ya fara arziki ba balle ya kawo mata karkadin cewa a daina na gargajiyan nan a bari ayi na asibiti kawai tunda abin ya zama haka kowa yayi ta jagula kafan shiyasa ba a gane komai ba.
Aiko baikai ayaba tace kai munafukin Allah anki ayi na asibitin kadai mafarin kuji dadin kara kaimi jifana da kukeyi kaida munafukan iyayenka ko karka dauka bansan komai ba ?
Barganin duk suna wani rawan kafa akanka a yanzu ni banga wani abinda ka zama balle hakan ya rudeni dukiyan da ba,asan asalinsa ba har zaka tsaya kana hurawa mutane hanci sabo dashi ?
Ayi hakkuri mama don Allah naga kina shan wahalane sosai mama da an yi na gargajiyan nan sai kafan ya sake dambalewa yasa nayi wanan magana ?
Kai Aliyu kada ka dauka bansan komai kuka aikata min kaida uwarka ba kana tunanen zakai kudi danine ko mai ?
Haba haba mum wanan maganan kuma fa don Allah idan ance kina danbala sai kicewa mutanen hankalinki daya ina aikin hankali wajen nan din Allah ?
Kai tafi can sakarai sallamame wa yanda basu san ciwon kansu ba yana amfani daku yana habbaka kansa .
Ya mike tsam tare da fadin Allah ya huci zuciyarki mama ya baki mu lafiya fada takeyi sosai a lokacin da yayan nata da suka nuna mata rashin dacewan hakan da tayi.
Shi kadai take shakku saiko hashim da yanzu ya bar gida Auwal din shiyace yanzu wanan abinda kikayi kin kyauta ke nan mama ?
Kema kin sani kin dai take saninkine mama hjy hauwa da yaron nan ba abinda suke binmu dashi na sheri a rayuwan mu.
Ni nan wallahi nasha zuwa wajen malamai da tambayan wanan abinda kike fadi a kansu tun muna yara magana daya ake fada min shine kyakyawan aniyansu da kowa.
Inma sherine mu daina yanzu hanyar da kika jefamu yake tambayan mu ai komai muka rika ya zamo toka tunda bamu tsayawa mu kiyayye dokokin Allah .
Kince hjy hauwa tana jifan mu da asiri mu tashi tsaye naje nayi tambaya ance ba hakana bane kince kudin danta akwai hanyar da yabi ya samu kudin nan shima wallahi har maiduguri nake akan wanan zance abinda aka fada min a can yau shi nake gani sabanin wanda kika fada muna a baya.
Bandashi da irin zuciyarshi wa zai dubemu a matsayin dan uwa inda shi wanine wallahi ko abinda ya shafe mu bai kallo balle mu din har ke mama ?
Tunda ni dai a sanina bamuyiwa yaron nan da uwanshi daidai ba a rayuwan mu shine kuma Allah ya mayar muna da nufin mu a yanzu.
Nikan Auwal na fita wanan har kan zancen sunyi muna sunyi muna din ina son inga na zama cikakken mutum kamar kowa a duniya nima .
Nasihan Abba a garemu kullum shine muguji wanan halin da kike dora mu a kai mu zama maza don mu haifi abin kwarai mu zama kamar kowa amma muke ganin kamar bai son mune yake fadin hakan.
Wallahi yaya Auwal nima akwai malamin daya fada min hakan har sanadin ciwonki mummy kin sani akan Aliyu kikai wanan tafiyan kamar yadda kika farfado kina fadi asibiti muka rufe maganan a lokacin .
Wallahi an fada min komai cewa matukar baki daina bibiyanshi ba baki taba warkewa a rayuwanki gashi yanzu kin kara jagule zancen gaba daya kin bata komai a yau Rukaiya yarta ke fadin hakan gareta.
Ranan bataji dadin diyan nata ba donko sun nuna basu bayanta ta bari a zauna lafiya kamar yadda suma suke nuna hakan a kansu inma har sunayi ya koma masu kansu din amma tabar hakan don Allah ?
Saukin abin ma yaya habib baya gurin yaje sarin kayan shagin shi wanda wanan haushin na cikin abinda ya bata mata rai tayi hakan ga Aliyu din.
Sai gashi ba afi sati daya ba taga anzo ana rushe part din hjy hauwa an soma gyara bata kara firgita ba saida aka kawo kayan decoration din gida masu tsada daga company aka zuba mata taga an kyale bangareta yadda yake ta koma kamar mahaukaciya a lokacin.
Gashi yanzu yaya nata mazajensu dake jin suraitai game da ciwon mahaifiyar nasu cikin gari sun fara barazan aurensu dasu akan yawin hanyan da sukeyi a kullum zuwa dubanta.
Shi mijin Asmay cewa yayi idan dai zataje ta kwana saidai ta zaba a yanzu kam shikan ya gaji gaskiya ko zaman aure ko gidansu asan inda take wanan yasa dole take dan zuwa ta wuni da anyi la,asar ta koma gida.
Ita kuma Rukaiya din mijinta ba mazaunin gari bane dama yana tafiye tafiyene yasa take kwana a gidan da mahaifitarsu saiga uwar miji kuma tace sai dai miji yayi aure tunda matarshi bata zaunu a gida ba kullum tana yawon hanya.
Dama uwar mijin irin su hjy Naitone wajen masifa dole take dauke ranaku subar hjy ta kwana ita kadai a dakin wasu ranaku sai can ba a rasa ba suke dan kwana da ita din.
A yanzu kam ta sheda bakin cikin zaune yafi na tsaye don da wani zataji da yan uwa da suka gama more mata kowa ya jaye a yanzu aka barta da yayanta ko da fitinan gidan miji da takaicin miji da take kwana tana tashi dashi a kullum yanzu ?
Wanan gyaran dakin na hjy hauwa kuwa ne kawai bata samu iyaba a lokacin tunda Aliyu ya fito fili a lokacin ta nuna mata ita bata haifishi ba ke nan ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/26, 8:50 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊 7️⃣9️⃣ 🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Ya rikita min lissafi na kasa kwana na kasa sukuni na kasa shakat a cikin rayuwana a yan kwana biyun nan daya manna min sabo dashi a zuciyana.
Tayaya zan iya gaskanta cewa wai ashe sir A A Y sone yake nufin yanayi wai so kuma mai tsanani da a yanzu na kula da duk irin abinda yakeyi a baya wanan yana nufin shine alaman so ?
Ashe so abune da baka iya fassara kalansa kowa da yadda so ke samo mafari a gareshi wasu yazo masu ta baki wasu kuma daga alamomi irin haka wasu ta hanyar kyautatawa ga juna sai abin ya rukide ya zama So ?
Irin nawa din nan yazo min da ban mamaki mutumin da a farko nake zargin wani amfani yake sonyi da damanshi a kaina ya cinwa manufarshi lagos ce fa abinda mutum zai maka wani dabban ba zai taba cutan dan uwasan dabba haka ba.
Amma sai kaga mutum a lokaci guda ya ha,inci dan uwansa mutum ya jefashi a masifa wani lokacin har rasa rai sai ayi kan yaudara.
Don haka a yanzu ba zan iya tantance wani irin so yazo min dashi ba ta gaakiyace tsakani da Allah kona yaudara da mafi yawan maza sukewa mata yanzu don rage sha,awansu ga mace ?
Zancena abin dubawane a yanzu duba ga yadda duniya ya koma a yanzu na shirmen auren kwarya tabi kwarya da aka dauko yi wanda iyayye da kakanni basuyi ba a baya.
Don yanzu aurene da akeyi yar wani da dan wani ko yar wance da yar gidan wani suko diyan talaka masu kwadai sai a zauna ace ana jiran mijina nagari .
Koda ubangiji ya turo nagari din ba za a soshi ba don baida jagoran duniya (kudi) sai yarinya ta bari damarta ya subuce mata tana kallo wata zatayi wuf dashi idan da rabo kwana biyune zakiji Allah ya daukakashi ya zama wani abu a cikin duniya .
Kudi a yanzu ba sai ka gaji yinsa ba daga sama zakiga dan talaka litis yayi arzkin da sai gari ya amsa lokaci muke da ba,a tambayan asalin kudin mutum da zaran ya fake ga wata yar sana,a yanawa mutane rufa ido dashi.
Sabanin baya dasu masu kudin na yanzu dake kurin basu hada jiki da tallaka a yanzu saidai aje gidan wani a nemawa da aure ko gidan matan sukai tayin yarsu gidan wani da suke ganin ya dace da yarsu.
Sun manta cewa su ba irin auren da akai masu ke nan ba a baya aurene na tsakani da Allah wanda bahaushe ya taso a cikinsa na nagani ina so ko na hadin iyayya don karamci a tsakani badon kudi ba ko wani dalili.
Allah sarki tallaka bawan Allah shida iyalinsa da yake ji dasu a rayuwansa sune gatanshi yake masu fatan alheri a kullum a yanzu wani zuri,an banza suke kallonsu a wajensu har suna kyamarsu kamar su sukayiwa kansu talauci.
Karya yayi yawa a duniya wata uwar mafarinta daga gidan tallakawane ko wani uban asalinsa daga gidan tallakane .
Ansamu budi a wajen Allah a yanzu wai kuma talaucin ake kyama kowa ya samu bai fatan cigaba ga dan uwansa a yanzu saidai ya taushe ns bayanshi duk akoma mashi maula yana taka kowa yadda yaga dama.
Irin wanan rayuwan shi yafi yawa a yanzu cikin alumma don me ba zamu dinga ganin masifi rashin imani suna bibiyan mu ba ?
Ire iren tunanen dake addabana a yan kwanakin nan sune wanan nasan hakan yana da nasaba da irin abinda akai min a baya wanda har yasa soyayya ya fice min a raina har abada.
Yana kano duk wanan abinda akeyi a yanzu ta wayace yake kasheni da dadin bakin maza da nake jin suna daure min gangan jikina.
Nasan abune mai wuyan yuyuwa a garenu mu fada tarkon soyayya mukai ga cin riban abin a rayuwan mu iyayyen Bello da basu kokai rabin wanan ba sun nuna min kyama sunce shi ba sa,an aurena bane .
To balle wanan din da nake gani ya nuka Bello dubu da komai ina haka zai yuyu wanan mafarkine kawai gami da burin rayuwa ga dan adam .
Haka yake sa jikina sanyi idan na tuna abinda hakan zai iya jawo min kuma a rayuwana nan gaba donshine zuciyata ta kasa tsayuwa a waje daya in bashi amsan da yake nema a gareni.
Nayi tunanen hakan kamar yadda nayi gangancin sakawa aka nemo min gidansu a kano shima hakan zai iya wanan din a gareni wata rana.
Yako nemo din inda ya gane muna cikin makwabtan gidan kawunnansa layin gidajen mune a gaba nasu yana bayan namu saidai da yake su har yanzu suna gargajiya a gidan nasu duk da cigaban zamani da suke dan surkawa dashi har wanan lokacin.
Don gaba daya kamar layin nasune su kadai da almajiransu dake tasowa suna gidaje manne da malaman nasu wanan yasa ake kiransu da layin malamai.
Suna da almajirai masu yawa a gidajensu kananu da manya har da yan gari masu daukan karatu a wajensu mu dai kam bamuyi karatun tsangaya ba a wani islamiya mama tasa yaran gidanmu don kawai dan hatsaniyan data tabayi da daya daga cikin matan malam din akan nika lokacin tana da injin din nika a gidan mu ta saba sosai da mutane da dama ta wanan dalilin na nika a lokacin .
Baisha wani wahala ba wurin gano gidan mu da mahaifina don Bashar yaron malamai ya dauka a motanshi don wanan sirin yake tambayanshi da malam bashar .
Wani aiki nake so kai min kasan dai ba yau na fara siri da kai ba bashar din yace nasani kuma ba mai ji sai Allah insha Allahu.
Na sani ya fada yana gyara zama ya soma fadin akwai wata yarinya unguwar nan dake zaune a lagos a can take zaune hannun dan uwan babanta shike rikonta kuma can take karatu ance mahaifinta yana sayar da mashin mashin dasu keken dinki da frezer ina son jin ainihin labarinsu zuwa gobe daidai wanan lokacin.
Tunda suka rabu malam bashar bai zauna ba ya shiga biincike inda yaro karami ya fada mai cewa ina ganin mairoce fa mairon gidan Ali mai mota don ance Lagos take zaune.
Kaga babanta kuma ai yanzu sana,an mashin yakeyi a kofan wambai ko malam sani wurinshi ya sayo wanan mashin din nasa yana kawo sabo da toris toris masu saukin kudi.
Mairo niko ban sheda yarinyar nan ba a,a mairo dai mairo mai shinkafa a lokacin gata nan tana fanke da koko da safe a kofan shangon isah.
Ya dan tsaya tunane kafin ya tuno yana fadin kai kai kai mairo nagane aina zata tayi aurene dana daina ganin ta banjin tayi aure gaskiya wani abu ya farune da ita ?
A,a nima a can cikin gari wani ke min kwatance da ita ya ganta ikko din tace mai ita yar nan unguwarce ai nace ban ganeta ba kuwa shine nake tambaya ai.
Itace ina gani ita dince ma don gaskiya ta jima bata zo garin nan ba sundan taba hira sukai sallama yaji dadin wanan abin sosai don ko lokacin ba akai ba gashi ya gano komai a kaina haka .
Gefe ya samu ya kira layinshi suna tare da Yusuf a lokacin ya dauka yana amsawa yake fadin na gano ko wacece ai ga gi,,,,,,
Ka bari zanzo muyi maganan anjima ya fada ya kashe wayan yana murmushin keta a kasan zuciyarshi don sai ya ban mamaki fiye da wanda nabashi a kansa nima.
Gidansu suka nufa don yasan duk wani bako a ranan baya gidan sun koma gidajensu irin nasu cewa saboda nisa a nan zasu kwana wajen hjy din don aiki yan uwa na kusa ke nan a gareta sune suka cika gidan da safene ya shigo a ranan sunan amma sai kace a lokacin ake taron sunan gidan.
Sai dai kuma zuwa a lokacin bai mai dadi ba don ya samu hjy mama nacin mutunci wai an yanka nama a gidan a rasa abinda za a bata sai kasusuwa da tarkace za ace shine rabonta.
Duk da kasancewar matan malam da kamun kai da rashin son magana irin dabi,un matan malaman zaure din nan mai kama dana matan sarakuna shine dabi,un matan gidan kawunan nashi amma ya samu mama tana bawa hjy Naito din amsa a lokacin.
Tana fadin ai dole kice haka Naito tunda kin saba da taushe hakki har na mai haihuwa ayanzu ko kinga sauyi ba dole kice an baki kasusuwa ba tunda shi kika saba bawa mai haihuwan ke kin dauka kowa baida imanine irinki Naito ?
Ke ba afa tsorin ko dubaiya da halarci ake maki kan wani abu don mijinki da diyanki amma ba mai tsoronki gidan nan Naito