Showing 36001 words to 39000 words out of 395027 words

Chapter 13 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO*

Inna da kanta ta zaba min tufafin da zan tafi dasu duk da damuwan hakan a fuskanta amma sam bata yarda in fahinci hakan a gareta.

Har inta gannima a cikin damuwa zata soma min fada kan na sake ai hakan ba wai an rabamu bane da ita rokonta Allah yasa wanan abinda akai muna ya zama alheri a garemu baki daya.

Itace tasa naje gidansu daddy na fadawa anty Fati zancen tafiyana yadda hankalinta ya tashi ko yar uwatace ta jini ya tsaya hakan yadda ta nuna damuwa sosai a kan jin zan tafi aikatau kamar yadda mama ta fada.

Mijinsu na dawowa sai gasu tare gidan shi da ita yasa aka sallamo mai baban mu ita kuma tashiga ciki wajen inna fada sosai daddy yayi ya nuna ba zanje ba .

Shine baban mu yace dashi ai bai isa yace hakan ba zasu samu matsala da mahaifiyarshi don ya gane so ake kawai a hadashi da ita .

Shiko yana fatan rabuwa lafiya da mahaifanshi don haka daddy yayi hakkuri kamar yadda sukayi su dai min addu,a Allah yasa in fada hannu na gari hakan kuma ya zamo min alheri a rayuwata.

Anty Fati na kuka tana fadin jerabawanki a kurkusa yake maryam karama dake ubangiji ya kawo maki jarabawaowin ki a shekarun kankamtaki haka .

Number waya da kudi ta ban hardasu sabula da man shafi ta hada min da nasiha shigen wanda innan mu take yawan yi min tun lokacin da zancen nan na tafiyan ya zo mata duk muka kebe da inna nasihace ke biyo baya akan nayi hakkuri na kama kaina na kawar da ido ga abinda ba a banba kuma bai shafeni ba.

Kuka kawai nakeyi har mijinta ya bugo waya ta fito ban iya taka mata ba har ta mike take tambayan yaushene tafiyan nawa inna tace ance a cikin satin nan zamu tafi.

Sai faman girgiza kai takeyi a cikin takaici sukai sallama da innan mu ta tafi ban iya cin komai ba har dare haka na wuni sukuku dani sai faman tunane da nakeyi kasan zuciyata.

Muryan Baban mune ya farko dani yake fadin tashi mairo kisha ruwam shayin nan cikinki ya sake kiyi hakkuri kinji haka ubangiji ya rubuto maki a rayuwanki ba mahalunkin daya isa kankare maki hakan a tarihinki.

Talaucina da rashi baikai in dauki yata in mikawa duniya da sunan aikatau ba amma macuciyar nan Rakiya taje ta zuga kaddaran hakan ya fada maki.

Ki kama mutuncinki tankar kina a gaban mu mairo kada wuya ko wani wahala yasaki sauya rayuwan tarbiyan da muka baki mairo.

Ki rufa min asiri ki rufawa uwarki din girman Allah kada wani abin assha yadda ake maki fatan hakan ya fito daga gareki.

Kisa duk inda kika taka albarkan ki da addu,an mu yana tare dake insha Allahu mutanen nan da zaki zama dasu ki dauka suma iyayyen kine duk da zumuncin namu bawai wani zumuncin kwarai bane din yanzu ko ance na fadi waye cikin yayan hjy zai daukeki ba zan taba cewa gashi ba .

To amma ko waye ina maki addu,an Allah ubangiji ya basu ikon rike munake a cikin amna da mutunci a nan hakkurin inna ya kare don duk dauriyan innan mu a lokacin saida ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.

Baba ya koma bata hakkuri shima dai kwallan yakeyi a lokacin muryan mamace daga waje take fadin ni naga abin arziki nayi ai yanzu inta dan raramo ai,a samu a kara ko ?

Tunda kullun neman nan akeyi ba a karu ba sai kuma kari ya koma suka itama umma inba din taga wurin ci bane aiba zata yarda da hakan ba.

Baba ya zabura zai cin mata inna tace don Allah malam ka kyaleta tunda bakin mu take son ji a zancen nan ka kuma sani duk abinda mutum yayi ai don kansa Allah yasa shari,a hannun sa yake baiba kowa daman hakan ba cikin bayinsa.

Hakan yasa baba din bai biyewa mama din ba a lokacin ya tsaya ya tsureni saida nasha ruwan shayin sai kadan na rage a kofi na mikawa kannena da suma suke zaune a cikin damuwa da zancen daya samemu din.

Washegari har na saka uniform a jikina muna zaune muna karyawa sai sallaman kakarmu mukaji misalin bakwai da rabi na safe.

Gabana ya fadi dam har inna don yadda naga ta rude tana addu,a a bakinta muka fita muna gaida ita da shigo idonta a kaina tana fadin to dake fita zakiyi boko yanzu ?

Ai saiki kwabe kayan nan gasu Usman nan a kofar gida zasu daukeki kai kaje ku gaisa sunce basu son yamma yai masu a hanya don haka sai tayi sauri ta fito tunda kundai san da zancen tafiyan nan.

Amma ai bamu san yau bane don gashi ko gidan kakaninta bataje ta sallamosu ba baba ya fada nan umma din ta juyo tana mashi wani kallo tace dashi.

Wai Ibrahim meke damun kankane wai gidan kakaninta sunfimu ne to idan tsoronsu kakeji idan sun tambaya kace dasu ni kakarta nina turata ina shike nan ko ?

Ni banson abinda baida marmari don Allah baice komai ba ya kama hanyan fita daga gidan a waje muka sameshi yan uwana yaya Saudi itace ta dauko min vaccon kayana suna tafe suna min shakiyanci irin na zolaya.

Dirkrkiyar motar da muka ganine a wajen gidan ga wani a cikin shigan kananan kaya ya fito suna magana da baban mu.

Yasa suka zubo muna ido muma din su muke kallo muka karasa gaban motan yana fadin wallahi gaskiya ba ,a zumunci fa kowa ya kama gabanshi yanzu.

Kome yace naji baban mu na fadin gata nan itace za a da ita masha Allah wa naji sunanki baba yace mairo yace to maryam ki sake rai kin kada kiji komai kinji a zama damu.

Ashe kunsan juna ke nan umma ta fada yace kwarai kuwa suna gaban mu sosai a makaranta shinema muke danjin sanyi a wurunshi lokacin.

Bani number wayanka ya fada baba yayi dan murmushi yana fadin banda waya a yanzu amma ke Ai bada layinki din nan don ya bugo muna ta nan ta mika min na fara kira mashi layin innan mu din .

Ya juya zuwa wajen mota ya zauna yana fadin to muje ko yaya saudi ce tace kayanta fa ya juyo yana fadin kaya anya zamuje da kayan nan kuwa da an barsu a nan idan muje sai a saya mata wani yana magana yana dauko kudi a motarshi ya mikawa baban mu kudi masu yawa hakama innata kafin ya mikawa yaya saudi yana ungo wanan ku raba da yan uwanki .

Ya kara mikawa baba hannu yana fadin to senior mu zamu kama hanya saidai idan munyi waya amma bai kamata ace baka da waya ba a yanzu zan dai kiraka idan mun isa insha Allahu.

To shiga mana umma ta daka min tsawa tare da hararana baba dai yaja gefe suna kallon mu sai cewa da yan dakin mama keyi Allah sarki mairo za a tafi a barmu ke nan kuma ?

Sau daya na daga kai na dubi inda innan mu take na fashe da kuka na juya na shiga motan cike da tausayin kan mu nida mahaifana don da za a bude zuciyarsu a wajen nan Allah kadai yasan halin da suke ciki a lokacin.

Haka motan ta daga dani muka bar kofan gidan mu dagani sai ni Allah yasa kayan undies dina da sauran tarkacen da nake matukarso na hadasu a ledan hannuna da zan shiga mota sariya kaunata ta miko min har takarduna na school duk suna cikin .

Sautin kukana da suke ji a bayan motar ga wani sanyi ga kamshin dadi duk hakan bai burgeni ba don nafi bukatan a barni da iyayyena in rayu dasu da shiga wanan bakar motar a lokacin.

Haba haba keko meyema sunan kuka kuma don Allah ki daina kada ace ko mun satokine zamu gudu dake mana hakan dana gabab motan ya fada yasa na dan tsagaita kukan nawa a lokacin.

Duk da dau ban tsamanin shine uban rikon nawa amma nayi biyayya na tsagaita sai sharan gudu da sukeyi a saman hanya .

Ban taba tafiya a mota haka ba mai nisa yasa na kama jin hajijiya tare da amai taso min amma na daure a takure ga sautin kidan da suka saka a motar wanda baima bari suji halin da nake ciki a lokacin.

Barci sosai na samu nayi har bansan inda nake ba a lokacin ga tafiya tayi nisa har mun fara barin arewa sai wani gari da suka tsaya don suyi sallah na falka babu kowa a motan can na hangosu suna alwala.

Naso fita daga motar amma kauyanci bai barni ba don kuwa ban san yaya zan bude motar ba iyakata da mota idan ba karya zanyi ba tun na gidan su salma da bake shiga idan zan bisu unguwa.

Wata mace mai abinci tazo ta sameni take fada min ance in sauko inci abinci itace na samu ta bude min motar na fito ban zauna cin abuncin ba sai wurin kewayawa dana nema don a matse marata yake lokacin da fitsari.

Daga nan kuma nayi alwala naje inda naga matan da suma motarsu ya tsaya nayi sallah a lokacin ne suka shiga nemana.

Matar nan mai abinci ta nuna masuni ina sallah ta a natse sai bayan na idar wanan mutumin dai na dazun yake fadin ke baki tashi yin sallah ba sai yanzu don Allah hanzarta mu kama hanya kada mu makara.

Naji dayan yace ka barta tayi sallah ta a natse mana abincin sai a takeway aka zuba min min muka kama hanya kasa ci nayi don sai naga kamar zasu ganni a lokacin ina cin abincin har muka fara fita arewa muka nausa wani nahiyar da nake ganin dabi,unsu daban da tamu dana baro a gida.

Bayan barin mu kofan gidan innan mu ta juya ciki tana sharan kwalla tunkafin wani ya ganeta a lokacin.

Saida suka koma cikine umma ke fadin ke Rakiya ai sai yau na sheda son da yaran nan sukeyiwa yarinyar nan wai ace danka na fari zaiyi tafiya don rashin kunya har da uwar wajen rakiya ?

Umma ai Allah dai ya kyauta gidan nan meye ba zaki gani ba yanzu kuma ai a lafa dama itace duk hatsabibiyar gidan nan.

Daidai lokacin baba ke shigowa gidan nan fada ya kaure a tsakaninshi da mama din fada sosai sukayi a gaban umma din wanda hakan yasa tayi fushi tabar gidan cikin bacin rai innan mu na daki bata fito ba har suka gaji suka bari don kansu.

A nan umma ta fahinci manufar mama na turani gaba ta rabani da iyayyena wanda tayi hakan akan kishin dake tsakaninsu da innane da kuma son da tace maihaifina yana nuna min bambamci tsakanina da kowa a gidan.

Inda har take fadin da baiso hakan meyasa da aka bashi biyan aikatauna ya karba da cewa kudin da mutumin daya daukeni yabashi har kuma ta kara da cewa saidai yayi hakkuri don ta gama dani dasu duka wanan ya bata ran kakan mu din a lokacin .

Kinsan yadda jininka ko yaya kake dashi aka aibantashi dole ranka ya baci da hakan amma ita mama idonta ya rufe sai magana take zarowa a lokacin daga bakinta ga yaranta nata bada hakkuri akan tayi shiru don Allah tunda dai na tafi din .

Rakiya ashe rashin mutuncin naki yakai haka a gabana kike fadin wanan maganan haka har kira kirawa yarinyar nan lakacewa a gabana ?

Dama kinyi hakan ne son ki cutawa yar mutane ashe lalai Rakiya sai a barki abarki da halinki tunda har kika iya fadan hakan yanzu ?

Umma nida ake fadawa diyana fa don na fada ga yar sonsu shine laifina indai shine laifi na kara fada uwarta batayi kuka ba yanzu ta fara ba miji da ake muna sallo dashi kuma karshe bata ga yar nata .

Shine tsohuwar ta fita a gidan ta barsu don babu abinda ya saura kuma mai muni da mama zata fada a yanzu bayan wanan .

Yadda hjy ta dauki zancen da wasa ashe abin ya wuce hakan don kuwa anyi juyin duniya danta Hashim yaki fadan inda kudi suke.

Hakan ya fara dagawa hjy Naito hankali don duk yadda zasuyi sunyi tare da yan uwanta da nashi sun kasa gane kan yaron don yaki fadan gaskiya ga Alh ya tayar masu da kayan baya yayi rantsuwa sai ya daureshi idan bai fito mai da kudinshi ba.

Kudi kan babu su ba dalilinsu hakan yasa Hashim din tattara kayanshi cikin dare ya bar gari zuwa inda bai sani ba don kuwa a halin gaskiya babu kudin yan damfara sukai mai damfara .

Akan ya kawo kudin zasu nika mai kudin gida ukku shine ya dauki kudin yakai masu da sunan zasuyi mai kudin da zai tsaya ga kafanshi ba tare daya dogara da mahaifin nasu ba kuma .

Shine dalilin dayasa ya kasa fadawa kowa ya gudu ya bar garin don yasan da gaskiya mahaifin nasu keyi zaisa a daureshi din dayace.

Wanan abin daya faru shiya kashewa kowa jiki don kuwa an wayi gari babu hamshin a gidan haka kuma ya debi wasu kaya nashi ya bar gari ke nan.

Ance mai kishiya bata mutuwar Allah don kuwa hjy Naito cewa tayi ai hjy hauwace tayiwa danta asiri har hakan ya faru dashi itace tasa mata hannu ta don ta lalata mata yaya.

Abu tun ana tsegumi har takai fadawa hjy din garan da garan don bokayan ta sun fada mata karya kan cewa asiri akai mai hakan ya faru dashi.

Duk da hakkurin hjy hauwa a ranan saida ta kaiga magana take fadi wurin bada amsa tace banda gadon hakan kuma bamu gaji sheri ba kona fatan baki balle har na daukarwa kaina alhakin da zai hanani shiga aljanna don duniyan nan .

Saiki fadawa wawa da baisan sherin da yan gidan ku suka iya ba hauwa anyiwa banza balle da dalili yadda dana yabar gidan ubanshi nayi kuka koke sai kinyi kukan naki hakan fiye dani hauwa.

Saukin abin dai ba kece Allah ba yaya haka kuma ni nasan Allah duk abinda ya sameni koya samu dana ubangiji yana sane da hakan .

Kaji makira Allah ga baki fir,auna a zuciya saiki fadawa wanda baisan sherin ku ba niban hana danki zama a nema dashi ba ai daya saka takalmi yabar gari ya bi uwar duniya yana sha shanci.

Shine kika sabauta mini nawa dan don ya gantale yabi duniya a zagesu su biyu hauwa ta Allah ba taki ba wallahi son kinyi da maiyi ko a dawo min da dana gida ko kuma wallahi na kowa ma ya lalace hakan yadda nawa yabi duniya gaba daya diyan ki saina watsa makisu a cikin duniya.

Babba gareki Allah yana jinki yaya shiyasan yadda zaiyi dake matukar ban taba bin danki ko ke ko wanin ki da sheri ba kikace zakiyi min a kanki zai kare matukar kikayi hakan kinji na fada maki kuwa.

Muryan maigidan daya shigo don kasuwa bata zaunuwa mashi saboda matsin da yake ciki na masu bashi yasa ya daina dadewa a kasuwan yanzu.

Ya shigo yana fadin wai yaya haka kuma meya kawo hakan a yanzu mutum yana fama da abindake damunsa zaku tsiro min fitina a gida ?

Gata ai tace nine nasawa danta hannu har haka ya faru dashi to itama sai ta watsa min diya a cikin duniya kaf dinsu kamar yadda nayi mata itama .

Kaji jahilince ko ince abinda ya cuci danki ke nan har ya fada hannun yan dafara suka damfareshi da kudina waye zai tsaya yiwa dakin asiri yaran da kika lalata da kanki ?

To danki kudi yaje ai mashi da kudina ba a sani ba kuma yaki fada sai yaron nan sama,ila abokinshi shine yazo yana fada muna abinda ya faru.

Allah nagode ma daka wankeni daga zargin matan nan kinji wa yanda sukaiwa danki asiri ko kudi yaje yayi aka damfareshi saiki sake min kurwa da diyana .

Mu mun yarda da Allah da Annabinsa yaya kin kasa gane hakan shi kuma wacan da kike magana ya shiga duniya Allah yasa shiga duniyan ya zamo mai alheri.

Ban taba zaton baki san Allah ba nina yadda da kaddara kaddaran mutum bai taba wuceshi nasa kaddaran akan neman na kansa yake bai tsaya fakewa a kasan wani ba.

Sunyi ba dadi a ranan abinda bai taba faruwa ba a gidan ranan shiya faru nasu tsaya suna fada irin haka a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login