Showing 15001 words to 18000 words out of 395027 words

Chapter 6 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

hakan tunda anci moriyan ganga yanzu za ayada kwarenshi ko ?

Lokacin da nake dafawa in baku kaida tarkacen ka ai naga komai yi min akeyi bakace don me ba sai yanzu ko ?

Waini Rakiya da kike fadin kin ciyar dani da matana da yarana ke din ban ciyar dake bane ko me kokuwa lokacin da nake dashi wayaci moriyan abin bake ba ?

Ko injin din nikan da kike fadin kina ciyar damu waya sayo maki injin din ina nine na sayo shi da kudina tun lokacin naso sayowa kowa nashi kikace daya ya isa ?

Nikan kuma ita da yaranta ke nikan ai da kike fadin haka kuma ki koma ki karbe kudin ki lalurar kanki dashi muna kallo .

Na barki da Allahne Rakiya karki dauka kin rufe min baki bansan abinda nakeyi ba na sani ina binki da halinkine kawai a gidan nan.

A,a,a lalai kuwa yau baban baby ni kakewa gori don nace yarka tayi min laifi kake kokarin tare mata harda min gori inka sai min injin ai ladan wahalan danashane Allah ya fitar min gareka ?

Ni din kikasha wahala dani Rakiya wahalan me kikayi dani yau ki fada koda kika aureni ina da rufin asirina tace ohh ashe kasani saida mai farar kafa mai kafan ribas tashigo ka koma haka ko ?

Kaiya baki da kunya kike fadan haka inma kafan ribas ne aiba kamar naki kema kin sani keda ke kwashe min kudin a lokacin.

Mama kingani ko kinga abinda nake fada maki indai don wanke wanken ne ta barshi mana mu, mu tsaya mu wanke kayan kafin mu fita yaya sahura ke fadin haka daga kofan dakinsu tsaye.

Ke ki barni don ya fadi haka shine me ai bansan butulu yake ba sai yau dama ina kallon take take ka a gidan nan baka son abinda ya taba yarinyar nan mairo don tana yar gwal.

Ko talla ta fita haka zaka shura takalmaka zuwa kofan gidan ka faketa da ido kar a saceta ko ai mata wayau a fakaice kaike sayar da sana,a ka dauka duk ban gano ka bane ko ?

Da kika ganoni ki hana ai baki tsaya fadi ai sai ki hanani fita Rakiya wanke wanken kayan sana,anku dai daga yau din nan na hana mairo yinshi yayanki suyi maki idan basuyi ku barshi nan.

Dama nasan makirci aka kulla min wanan ba dabaran mairo bane ke kuma munafuka mu zuba daku a cikin gidan nan aga wanda zai fasa don Allah ?

Tundaga wanan ranan na samu tulin wanke wanken mama ya fita hannuna kuma daga baba har mama ba wanda yayi min maganan don me nayi hakana naki wankewa.

Mondaya na dawo daga tallana na wanke kafa da fuska zuwa hannaye ba zancen wanka bane sai irin hakan don ujila da yai min yawa.

Mai nake shafawa da sauri don in tafi makaranta nan inna ta shigo ta sameni tsofin kayana dana aje a gefe ta kalla tace min ba zaki saka sabon bane neye amfanin baki da akayi ?

Dole nagama na jawo ledan don tun ranan ban bude ledan naga abinda ke ciki ba nan nasha mamaki bayan na bude ledan.

Dinkine mai kyau ga jakka irinta gayu sai litattafai guda goma sha biyu har fensir da biro ga takalma da safan kafa haka na tsaya ina duba kaina a madubin hannu na dakin mu .

Ban san me yan gidanmu zasuce min ba idan na fito don suna waje suna hiransu kodana shigo sungama cin fanken da suka saye wajen inna.

Kodana fito kuwa ihu suka saka min yaya murja na fadin kaga yan boko inda yaya sahura tace dani kanwata da inada babban waya danayi maki photo kinga kanki yau.

Murmushi nayi ina dukar da kaina muryan mama naji tana fadin da kayan mlula akai kyau inda kwadayi dai da wullakanci .

Ballema ba kwadayin don duk talaucina banje wajen kowa roko ko yar murya ba wanda ya zargeni kuma Allah na kallonshi nidai nasa kai na fita daga gidan

Ko a makaranta ranan nasha sheri baga yan uwana dalibai ba haka baga malamai ba abin kunya da zan dawo su mamman bello suna zaune a canbansu waje hira dole nakama rabe rabe har na bar wajen .

Inda nagodewa Allah sunyi kamar basu ganni ba dagashi har salis din abokinshi basu ma juyo sun dubi inda nake ba.

Wanan aherin da yayi min shine mafarin shirun mu sosai na kama jin nauyin shi da kunya idan nagansu sai in kama gudu har dai shakuwa sosai yazo ya shiga tsakanin mu dashi.

Haka da sallah ya kawo min kayam sallah masu kyau da tsada dinkakku kuma wanan abun ya daga hankalin mama sosai a cewanta.

Yayyuna gida basu da kowa ni za ace ana min toshi tun yanzu lalai uwata ta iya fice da shiga a wajen malamai kamata za a dinga kawowa kaya haka ba a kawowa yayyuna ba ?

Shiko a lokacin ma da wasa yake min hakan ina karama tunda ban isa aure ba kawai dai yana min ne don yasan banda shi .

Yayinda su salma kawata sune yan aike akai gwauro akai mari akan zancen ko yaushe muna leke da juna da ita duk da mamansu har lokacin tana cewa zan bata mata yarta donni din yar tallace.

Yar talla ba irin shakiyancin da bamu sani ba don da maza muke hurda a cewan mahaifiyarsu salma din saidai kwana biyu kamar zamu rabu sai kuma mu koma mu dinke da juna mun kasa rabuwa har lokacin.

Itace kuma zata biyoni har gida mamansu tayi ta aike sai taga dama zata koma gida bai hana kuma gobe ta dawo dole tasa muna ido ta barmu na kwana biyu.

Shekaru sun dan kora ga hakan don a kullum mairai kara girma yakeyi inga rai ga lafiya haka muma din balle da yake matane mu ga kuma gyara da muke samu wajen mahaifiyar mu don bata yarda mun biyewa yan uwan mu ba na gidan .

Duk aikin wahakan mu kitso da kumshi bai rabuwa damu ko yaushe tsab muke haka tufafin mu tun wajen saka ruwan dama kunu zata bamu ruwan wanka tunda asuba muke wanka a dakin mu don haka ba laifi a wajen tsabta gaskiya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[6/21, 10:19 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Tsaye yayi yana bin matar nashi dake duke tana wanki da kallon mamaki kafin yayi gyaran murya don tasan yana bayanta tsaye.

Aiko cikin zabura ta juyo tana dagowa tare da jefa mai gaisuwa lokaci guda akwai wani siri sai iyalai ko shakikai suke haddaceshi ga mutum yanzu.

Na farko sauti muryan maigida duk inda yai magana ko wani motsi iyali kaidai zasufi kowa sanin shine a lokacin hakama sautin motarshi ko babur dinsa ko wayanshi sudin dai mata da yaranka sune ke saurin fahintar kana waje.

Hakan ne ya faru a lokacin da hjy hauwa dake duke tana wankin tufafinsu dana yaranta Alh daya jima da fita kasuwa ashe yayi mantuwa ya dawo daukan abin a motar abokinsa yasa basu sheda shi dinne ya dawo a lokacin.

Ya haka kuma kike wanki da hannu ga wuta amsan daya bata ke nan a lokacin ba tare da amsa gaisuwan datayi mashi ba.

Murmushi tayi tace ko akwai wuta dame zanyi Alh tunda banda na,uran wanki na wuta da hanju muke wanki ai a gidan nan haba dai kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya nufi dakinsa ya dauko abinda yazo dauka ya fita saidai yanayinsa ta fahinci ya sauya a lokacin ba kamar yadda ya shigo ba .

Tacigaba da aikinta a tsanake lokacin hjy babba tana dakinta tana barci bata ma sanda dawowanshi ba har ta gama yan aiyukanta sai azahar ta tashi ta samu danta munir yayi mata kira ukku a waya.

Ta kirashi kuma bai dauki waya ba don cewa akayi wayan nasa yana rufe a lokacin abinda computer ya sanar mata ke nan a lokacin.

Abubuwa suke faruwa a gidan amma hauwa bata kallon hakan tana kokarin kawar da idonta akan hakan ko wani lokaci .

Shi kawar da idon badon tsoro ko wani abu mata da yawa keyinsa ba don kawai ka hutar da zuciyarka dana abokin zamanka a zauna lafiyane.

Ba,a son mace tace komai tagani ba daidai ba da wanda yake daidai sai tayi korafi a kansa irin hakan yakan dushe gaskiyar mutu koda ancuceshi kuma yasawa natare dashi kiyayarshi a zukatansu.

Da yamma da Alh ya dawo gida bayan sallah isha,ine yaci abinci ya dauki waya yana kiran iyalinsa daya bayan daya har yaransa maza da suke zuwa kasuwa tare .

Kusan Hashim nema ya bata masu lokaci don dama yacewa mahaifin nasu bai kusa amma gashi nan zuwa a lokacin yasa suka dan tsaya jiranshi har yazo.

Ya shigo yana mamakin irin haduwan da yaga anyi a yau din dole akwai wani abu daya faru yasa mahaifin nasu hadasu haka a falonshi da yamman nan.

Sai bayan ya zaune Alh ya soma magana yana fadin kai Hashim kwanaki da aka kawo kayan wuta nace ka cirewasu hjy guda guda ka kawo masu a samu na amfani anyi haka ko ba ayi ba ?

Hashim din ya dago kai ya dubi uwarsu kafin yacewa mahaifin nasu eeh anyi haka Abba sai mahaifin yace ka kawo masu din ?

Kwarai kuwa na kawo mana mama ba na shigo dasu ba nan nace baba yace in kawo hjy ya sake kallo mahaifiyar tasu yana fadin hakan.

Ankawo mana baba Munir ya amsa daga gefensu yayin da hajiya ta gyara zamanta tana cin magani na daure fuskanta tamau.

Tace ankawo mana wani abu akace kuma ?

Alh ya gyara zama yace Hashim ina ganin in ban manta ba nace ka dauko masu blander da dutsin guga da ijimin wanki da gas ka kawowa kowa ko kuma a lissafi ka fito dasu daga shago zuwa nan gida.

Kwarai Abba amma nida na kawo nan wajen mama na kawo duka ai to wai meya kawo zancen nan kuma tunda yace ya kawo ?

Yaya akayi yau na dawo gidan nan da rana na samu hjy hauwa tana wanki da hannu dana tambayeta kuma sai naga kamar bata sanda zancen wa yan nan kayan dana turo masu ba ?

Wanan ai makircine ai tasan akwai anjin din wanki wajens bata zuwa ta wanke a can dama don kayi maganane ai tayi hakan ba komai ba.

Akan me sai taje wajenki ina nabawa kowa nasa injimin don me za ace sai tabar wajenta zuwa wajenki meye amfanin bawa kowa nasa din hakan baiyi amfani ba ke nan ai ?

Baiyi ba gaskiya Abba Hashim ya fada sai Alh yace yanzu ina nata yake don ga alama bama injin din wanki ba kadai komao ita kamar ba a bata bama nake gani a lokacin ?

Shiru hjy tayi bata magana ba hakama yayan nata saida ya kara tambaya habib karaminsu yace suna wajen mardiya shi injin din wankin gas kuma Amira nakaiwa da dutsin guga.

A cikin wani yanayi na nuna rashin jin dadi Alh ya dubi hjy Naito yace akan me Naito akan me zakiyi kyauta da kayan yar uwarki idan gaskiyane kina son yayanki su huta ki basu naki mana ni matana na bawa basu ba ?

Alh don nabasu Amira kayan shine kake fada idan tana son aiki dashi tazo wajena mana tunda akwai tayi amma baka zaunar dani gabansu kana tambayana ba don na basu kayanka ?

To ban basu ba matana naba don haka a amso min kayana kinji na fada maki tace nikan ba zan amso ba ai bansan kaji haushin daukan da nayi na basu ba saida ka nuna hakan.

Ni makircin mutum wallahi bai taba daga min hankali a gidan nan bansan taji haushi har taje fada maka ban bata ba sai yanzu data turoka kaci min mutunci ai.

Allah dai ya sauwaka yaya ajan me zan fadawa Alh wanan karamin zance sau nawa ake zuwa da abu gidan nan ina gani ba a ban ba kuma insa ido a zauna lafiya tunda bani na nema maku ba kuma babu dana a cikin neman ?

Kwarai kuwa don ko gasu nan suke wahala a dukiyan don haka ba ai muna yadda akaga dama kaya nabawa diyana don na ubansune kuma da yan uwansu ake nema.

Allah yasa su morewa abinsu hjy hauwa ta fada tana mikewa tsaye Alh yace ta koma ta zauna takai zaune tana fadin Alh daka barni na wuce.

Don yaya tana ganin nice nakai karanta wajenka din i tozarta tako wani abu niko wanan ba halina bane ko ita tasani don me zance maka duk abinda nagani wajenta sai anbani irinsa nima ba a koya min hakan bani.

Kaya daine kokin fada nabawa yaransa donsu suka dace dashi bake ba ta dube tace aiba sai kin fada ba Allah ya kawo min nawa rabon bashi ke nan ba ?

Ooh dai maki da makircinki kaya daine na kuma bayar eeh,hee ba kuma yadda za ayi dani gidan nan aida tunda kinji inda kayanki suke sai kije gidan ki karbo abinki ko ?

Allah ya sauwake yaya ko a wuri suka ganshi suka nuna suna so nimai dauka inbasune ai ba sai kowa yaji ba balle in tafi nace zan karbo don kin basu ?

Don Allah ya isa haka aiba hauwa kuka zalunta ba nine meye na hauwa a cikin zancen nan kuma kaya daine kince kinkai kiga abinda za ayi ko to zaki gani dake dasu ai a tafin hannuna kuke gaba dayanku ko ?

Kai hashimu gobe ka daukowa hauwa komai irin wancan ka kawo mata kada ka bari saina tuna maka yayi Abba yaron ya fada yace su tafi.

Suna fita hjy hauwa din itama ta mike tabar hjy na sakin maganganun a cikin borin kunya shima mijin yana bata amsa haka ta koma dakinta cikin bacin rai.

Ta rasa me tayiwa wanan matar haka ta tsaneta koda yake tace auren cin amana akai mata don tare take da matan yayyun hauwa amma mazansu suka dauki kanwarsu suka bashi ya aura don haka anci amananta ita.

Inda sabo ta saba da halin hjy Naito ai don mace ita mai izza da takama da kuma kafa dokan da dole a bita koda ba dadi a gidan.

Haka suka kwana kowa ransa a bace washegarine saiga Hashim din yayi sallama da wasu maza kofan dakin nata sun kawo mata komai harma wa yan nan daukowa sunfi kwaliti tafi hjy din dace da kayan kwarai.

Hakan kuma sai kara batawa hjy rai take ganin ai yanzu kuma ita aka kwara tunda danta hamshin yace wa yannan daukan sunfi quality da kudi ba zata yarda hauwa ta kwareta ba.

Wanan ya kawo fitina saida Alh ya fito yayi mata kwakwaran worning a gidan kafin ta shiga hankalinta ta kama bakinta.

Anyi haka da kwana ukku saiga yaranta mata dake auren su Amira agidan gaba dayansu su biyun sun shigo itace ta kirasu a waya sukazo gidan ta labarta masu karya da gaskiya akan abinda ya faru.

Budan bakin ita Amira sai cewa tayi to me zaisa ki damu mama tunda kinci bulus ba,a dai iya kwacewa a wajen mu ko ?

Saidai a kawo mata wanin banga me zaisa har ki damu haka illa ki bari kwana biyu kice a kawo maki wani wanan din sun lalace dole dai a kawo maki din.

Waima Abba fa Abba shi zaiyi fada don an bamu abinsa wallahi na yarda wanan matar da gaskiya shige shige takeyi da har Abba zai tsaya fada a kanta.

Ina fada ai kuna gani kamar sheri nake mata abindata gada kullum ana wanke allo ana bashi ya kurbewa da sunan sa,an kasuwa aida hakane aka sameshi aka mallake tamau ya kasa hanyar gudu.

Shima baba wallahi ya rasa wace zai kwaso sai wanan matar ga mace nan wata kala da ita ,,,,,, daga kofan dakin muryan hjy hauwane ke fadin Amira


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login