Showing 72001 words to 75000 words out of 395027 words
Chapter 25 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
Duk iskanciki da rashin mutuncinki kada ki hada da uwata ko don kinga ina kyaleki karya hjy din ta fada da ace kin kama kanki a baya hjy zata hana in aurekine ?
Duk abinda kuke kitsawa akai ina sane karkuce ban sani bane aiba komai akewa ba sai tarbiya dama gashi kuwa kin nuna ke din mara tarbiyace agaban kowa.
Mara mutunci kawai ke idan kina da tunane duk abinda mummy keyi min na rashin mutunci kin taba ganin na tsaya kulata ?
Ko kinga na taba ko mussu da ita sai nawa iyayyen don kina sakarai mara hankali zakice zaki kawowa rainin hankali don kin maidani dan iska ko ?
Wallahi kiyi a hankali kuma abinda kikaji ta fada gaskiyane gara in aurowa diyana mace mai tarbiya da in zauna da mara hankali irinki mara mutunci ta cika min gida da yaya marasa tarbiya ke inkina da hankali ai yanzune ya kamata ki nuna kina da tarbiya a wajensu bakizo da hslin banza da kike tunanen shine wayewa ba a wajenku .
Jin fadan da sukeyi yasa Amira fashewa da kuka ta manne a jikina nakara rrungumeta ni kaina tsoro abin ya bani sai kuka anty keyi ta dafe gefen kumatunta inda ya mareta din da hannu daya.
A yanzu nake fahintar wasu abubuwa daga cikin zancen nasu da sukai cacan baki a gabana dama wanda ke faruwa tun muna gida.
Alama ya nuna kamar sunyi zaman banza irin na barikine kafin aurensu da ita wanda har mahaifiyarshi ta nuna bata yarda da aurensu ba a lokacin saboda rashin tarbiya da rashin kamun kai da bata dashi ke nan.
Duk wata uwar kwarai ba zatayiwa danta fatan kasancewa da irin matan nan ba sai idan Allah ya kaddara hakan kamar nasu din a yanzu.
Inda ita anty din tayo tattaki tabiyo mahaifiyar nasa nan har kano tana bada hakkuri amma mahaifinsa yaki yarda a karshe sukaje sukai aurensu a can bariki ba tare da yardan iyayyenshi Paapa din ba.
Wanan ne abunda yasa ba jituwa a tsakaninsu a yanzu ashe don anty da mahaifiyarta farko sunci galaban rashi son da iyayyensa basuyi mata don har ya daina zuwa kano ga baki daya a lokacin.
Sai daga baya da addu,an iyayye yayi tasiri akansa suka rinjayi sherinsu har dansu ya dawo garesu ya dawo yana zuwa kano lokaci lokaci don har yanzu ba sosai din nan ba gaskiya.
Wanan yasa har yanzu da ita anty din ta rike zancen a zuciyarta take ganin basu isa ba don basu kai mata can ba tunda basu so aurenta da su.
Don haka tashiga ta fita ita da uwarta anyi auren batare da yardansu iyayyen nasa ba don haka basu da daraja a idanunta, saboda watau na kabila dake damunsu.
Allah yasa mufi karfin zukatan mu muyi kyakyawan karshe mu da zurian musulmi baki daya Allahuma amin.
Tsab na zayyano komai a hasashena wanda haka dinne sai naji anty ta sure min a raina lokacilo guda don wanan rashin hankalin data rafka a gabana.
Gashi yanzu tasha mari a banza da wofi yama raga mata da bai duketa a tsakar gidansu ba saida aka shigo mota take batanci ya doketa.
Muna fita daga motar ya fisgi motarshi ya bar wajen a cikin fushi saida muka jaye don tsoron yadda ya zama Umar faruq din gaske a ranan.
Muna shiga ina biye a bayanta da sauri da yarta a hannuna sai kukan da take famanyi tana fisge fisge wai zata hada kaya tabar kano a ranan ban san lokacin da bakina ya furta mata cewa kije ina Anty ?
Kanki daya kuwa yau antyna ina hakkurin ki da hankalinki ya shiga yau da kike neman yiwa kanki wanan abin anty ?
Ina hankalinki ya shigane kike wanan abinda koni ba zan taba aikata hakan ba ga wanda ya fini balle ke anty uwar mijiki fa kikaiwa haka a gaban danta don Allah ?
Kinga kin kyauta ke nan anty kiwa mahaifiyar Paapa rashin mutunci haka a gabanshi baki gudun suzo su tsani yarki laifiki yazo ya shafi yayanki nan gaba anty ?
Me Paapa ya rageki dashi a duniya nan anty burin ko wace mace shine miji yafi sonta fiye da son da take mashi kuma Allah ya hore maki hakan a yanzu.
Amma kina kokarin bata rawanki da tsale kuma anty don wanan abinda kikayi ko jahili bai taba yinsa wallahi.
Kin bada kafan da iyayyen miji suke hango mashi a gareki tun farko kin bude masu hanya harshi din hakan da kikayi zaisa a karo maki kishiya anty kishiyar kuma yar kasa yar cikin dangi ki gaya min me zaki iya yi a kan hakan idan ya faru ?
Zuwa lokacin kallon mamaki ta tsaya take min don bata taba zato ko tsamanin jin kalami makamancin hakan a kaina ba.
Wallahi dan iska bai usa don ubanshi in kuma ya isa ya gwada ya gani idan zai iya don sai in kasheshi dagashi har wanan gajan ko wacece kuwa wallahi.
Subbahanallahi anty yau kuwa kina cikin hakalinki kuwa anty don ba lafiya kuwa anty ta nuna kanta da nufin ita nake fadawa magana haka yau kai tsaye ?
Eh,mana anty kin dauki yuka kin dabawa cikinki kinzo har gida dakin mata kin nuna mata rashin mutunci wani irin mataki kike zato ya biyo bayan hakan da kikayi din ?
Anty kiyiwa kanki nasiha ki gyaro wanan matasalan tun baiyi nisa tsakaninki da mutanen nan ba yakai inda baki taba tsamani ba .
Cikin mamaki har lokacin take bina da kallo nace barin baki shawara ta gaskiya anty don naga hankalinki yau yabar jikinki.
Dolene na taimaka maki yadda kika taimaki rayuwana a gidanki a yanzu ya zama dole ki sauke duk wani girman kai da kike ji a zuciyarki in kina son gane kan mijinki da yan uwanshi.
Dole kiyi mashi biyayya dashi da kowa nasa duk wanda ya baki shawara idan kinzo kiyi hakka to lalai wanan babban makiyinkine anty bai kaunarki da farin ciki a rayuwanki.
Kiyi maza ki gyara kuskurenki ta hanyar shiryawa da hjy da kowa na Paapa haka shima mijinki kiyi masa biyayya fiye da wanda kikeyi masa a baya kamar yadda Allah yace a kula da mazaje a addini.
Abincinsa shimfidansa da yan uwa da abokan arziki sai a zauna lafiya kamata yayi ki nuna masu cewa wanan halin da suke zato a gareki ba hakan kike ba yanzu.
Zaune takai saman kujeran dake gefenta a dakin tana min kallon mamaki har lokacin kafin tace dani cikin saka min tsawa tana fadin.
Ke dakata har kin samu right din da zaki kalleni kice kina fada min gaskiya akan Paapa who are you by the way da zaki comfroting dina kina fada min magana haka ?
Bari kiji idan ma wani ya turoko ki fada min hakan Paapa bai isa ya sake min hali ba ke kika dauki wanan wata tsiya wai nayi masu biyayya don ina tsoro ko ?
Ni babu da namijin da zai juyani don yana takama ya aureni irin yadda naga sunyiwa mazajensu a nan niba zan iya daukan hakan ba .
Aure kuma da take fadin zata kara mai wallahi bai isa ya kara min kishiya ba na fada maki katseta nayi da fadin hanashi auren zakiyi anty ?
Inace sai ya barki a gidan har zaki hanashi kara aure ko idan yace ki bar mashi gidansa fa ko ya tafi ya barki ya dawo nan ya tare wajen yan uwa ya barki can.
Jin sautin budan kofashigowa gidan alaman wani ya shigo a lokacin yasa na fito na barta a dakin tana haukanta ba abinda ke raina sai tsoro a ranan .
Shine ya shigo gidan fuskanshi a daure bai shiga dayan daki da take ciki ba naga ya nufi dayan ya jima a cikin dakin ya fito ina daki naji yana kwala min kira na fito da sauri ina amsawa .
Ke shirya ga Sha,ibu nan waje ya saukeki gida idan kinje ki gayar min da senior zamu hadu kafin in koma insha Allahu sako na nan ki kai masu ki karbi wanan ki rika a hannunki.
Ya miko min kudi masu yawa wanda nasan ba zato ba da matarshi yaba ba zasu fito haka da yawa ba duk da zata bani din amma sai ta rage min yawansu.
Na durkusa na karbi kudin gami da godiya a gareshi ya juya yana fadin zaizo yanzu don haka ki shirya na amsa da to Paapa ya shige dayan dakin.
Gurin anty na nufa nayi sallama yanayinta zuwa yanzu har kara ban tsoro yadda na ganta din a dakin haka na daure na dan ambaci sunanta ina fadin antyna .
Ta dago kai a wani irin yanayi ta watso min idanuwanta tana fadin meye kuma ko kin dawo ki kara fada min wani maganan da kika mantane baki fada ba ?
A,a anty Paapa yace in shirya zani gidan mu yanzu gashi ya ban yace in rike a wajena wai wani zaizo ya daukeni.
Ok ki tafi mana meye ruwana nace anty kiyi hakkuri don Allah kiyi hakkuri ku shirya da mijiki da yan uwansa a garinsu kike yanzu.
Shirun da tayine yasa na dago don barin dakin har nakai kofa naji ta ambaci sunana na tsaya take fadin ina Amira koda ita zaki gidan naku ?
Da sauri nace a,a anty tayi barci zan daukotane in dawo da ita nan saidai don Allah idan ta tashi a tuna a bata magani don har yanzu akwai mura a jikinta.
Nan ma batace dani komai ba na juya na dauko mata yar nata a kafadana na kawota dakin na kwantar a saman gado.
Na gyarawa yarinyar kwanciya na dan dago ina fadin zan tafi ina kallonta kamar bata san ina dakin ina magana haka yasa na juya don in fita kamar farko nakai kofa naji tace maryam kema kina tunanen ko na zautu ko ?
Kaina girgiza kafin in bata amsa nace a,a anty ban taba tunanen hakan a gareki kawai dai nasan bacin raine ke damun ki a yanzu amma kiyi hakkuri don Allah.
Jeki kawai ki gaida umman taki idan ban tafi ba zan leko gidan naku mu gaisa zuwa gobe jin hakan yasa na dawo na durkusa a gabanta ina fadin.
Anty kiyiwa Allah ki shirya da mijinki kada ki abunda zai dawo ya dameki daga baya ki duba baby Amira ki sassauta zuciyarki.
Jeki ba damuwa ina gaidasu hakan yasa na fahinci ta fara saukowa daga dokin fushin da ta hau din da farko na kara mata da sai anjima na fice daga dakin.
Na karasa shiryawa duk na hada kayana da nazo dasu din don ban sani ba ko Allah zaiyi komawata can tare dasu ko kuma iyakar zaman namu ke nan dasu.
Ashe tun farko dana fita kalamina na farko shine yasa jikinta sanyi inda nace bata tsoron ya iya rabuwa da ita ?
Hakan dana fada yayi tasiri sosai a zuciyarta don ko gabantane ya shiga faduwa sam ta mace hakan karamun aikine ga mijin bahausa tsab zai iya rabuwa da ita duk yadda take ganin suken kuwa ?
Tana wanan tunanen ne na kada ta zama bazawara samun namiji irin Paapa zai mata wuya sosai a rayuwanta yanzu yadda ta zama.
Duk karyanta dai a yanzu shine dama shine dake sakar mata naira take yadda take so daga ita har uwarta tasan tana rabuwa dashi angolu zata koma gidanta na tsamiya.
Duk fafanta yau idan akace ta zama bazawara koda mutuwa mijinta yayi duk wani gatanta ya kare ke nan a gareta saidai abinda ya fito daga Allah kuma.
Mai karatu zaki mamaki irin matsayina a gidan har na tsaya ina fuskantar anty ina fada mata magana irin haka kai tsaye ba tare da shayin komai ba ?
Eeh dalilin hakan shine irin shakuwar dake tsakanina da ita yakai tana fada min wani damuwanta kuma har in bata shawara tabi tace taji dadin hakan.
Kinga kuwa din yanzu naga abinda zai cuta mata na tsaya kai tsaye na fada mata gaskiya duk da nasan ba lalai bane ta dauki shawaran amma dau na fada mata din.
Ina daki naji sallaman wanda zai saukeni din na jawo akwatina na fito daga dakin sai gashi ya fito yana fadin yauwa gashi nan yazo ka karbi kayan kakai mota na mika mashi akwatin kayan nawa yaja zuwa waje.
Dakin nata na koma na sake sallamanta saidai na samu ta kurawa yarta ido tana kallonta nace cikin daurewa anty yazo yana waje zan tafi sai munyi waya idan na isa.
Murya a dakushe take fadin is ok ki gaidasu zan shigo kila nace to na daga nabar dakin zuwa waje na sameshi a tsaye saidana zauna a motan yace ki gaidasu ya juya zuwa ciki muka tafi.
Tunda motar yabar gidan nake jin wani iri nagama da wanan yanzu bansan yaya zan samu gidan namu ba kuma a lokacin ko abu yayi sauki ko har yanzu yana nan yadda yake oho ?
A hankali yake jan motan yayin da nake bin ko ina da kallo gaba daya garin ya canzawa sanin da nayi mai a baya abubuwan cigaba da dama sun samu a yanzu.
Muryan sha,ibun naji yana fadin a wani layi gidan naku yake tarauni na fada mai a hankali kamar yana nzarin layin dana fada din sai naji yace ai zaki gane ko na amsa da eeh insha Allahu.
Haka muka karasa ina nuna mashi wajen har muka isa kofan gidan namu dana danga canji don zauren gidan mu dana bari ya duka kamar zai fadi a baya yanzu a gyare na ganshi tsab an daga shi har da canza mai fasali ga sabon fenti da akaiwa wajen shiga gidan.
Ido na lumshe a hankali ina sauke ajiyan zuwa tare da fadin yayi ya tsaya gab da kofan yana ribas haka ya hanani fitowa daga motan don tsaya juya kan motar da ya tsaya yi.
A hankali na bude gefen da nake zaune kofan ya bude na sako kafafuwana da suka sha takalman gayu masu tsini irin na yan birni.
Mutanen dake can zaune kafan gidan wajen da nake aje shimkafar sayarwana a da da har yanzu wajen na nan a yan hada hadan rayuwa ga masu karamin karfi irin iyayyena dake neman na kansu.
Suka zubo idanuwansu don ganin ko waye zai fito daga motar na fito a ciki ina gyara dan siririn gyalen daya yafa a kafadana nayi mai wuri mai kyau don kada ya fadi na duka na dauko hand bag dina da wani leda dana riko.
Saiga kanwata ta biyu ta fito daga gidan tare da yara maza biyu suna biye a bayanta cikin tufafin dake nuna na islamiyane kayan.
Ido ta dan zuba min tana kallona kafin can kome ta gane a gareni naji tace anty Mairo da karfi na amsa da na,am uwale ?
Makin tayo kaina saita baza da gudu ta koma cikin gida tana ihun sunana tana fadin wallahi ga anty mairo tazo anty Mairon mu .
Hakan yasa yaran dake biye da ita fashewa da kuka don tsoratan da sukayi suma suka juya zuwa cikin gidan suna kuka sai gasu kuma tarw da sauran sun sake fitowa da ihunsu.
Anty Mairo oyoyo suka yo kaina da gudu a ciki murna na hadesu na rungume a waje daya muna murna da ganin juna a rana .
Gani haka yasa wasu tasowa a ciki harda mahaifina yake fadin mairo kece ni naga mota ya tsaya a kofan gidan nan na tsaya ina mamaki waye ashe kece mairo ?
Sannu da zuwa ya fada yana kuma lekawa a cikin shakku yana duban wanda ya kawo din da mamaki karara a fuskanshi nayi saurin cewa dashi.
Baba tun jiya mukazo ai muna can gidan Paapane shine yau sukace inzo gida yasa wanan ya kawoni sai naji baba din yace tototo madalla abu yayi kyau sosai wallahi anzo lafiya ko ya fada yana kallon saurayin dake bude bayan motar don fito da tsaraban da Paapa din ya labto mi wanda nima ban sanda shi ba sai a lokacin.
Kai kuzo don Allah ku kwashe kayan nan yace in koma da wuri zai fitane hakan tasa kannen nawa komawa zuwa wajen shi a daidai lokacin mama data kasa hakkuri ta fito tana fadin mairo fa ina mairon take tana rabon idanu tana nemana ?
Gata a gabanki Allah ya dawo min da ita bada