Showing 18001 words to 21000 words out of 395027 words

Chapter 7 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

kun shigone ashe ?

Kamar ba zasu amsata ba cikin wani kasalalen murya Amira din ta amsa mata da munshigo tundazun to ina wuniku ta dandaga labulen dakin tana fadi.

Suna zaune sun game kai da uwarsu keda ganinsu kinsan wani abu mai muhinmanci suke tataunawa a lokacin ga yanayin zamansu zaki gane hakan.

Ashe ku dukane ta kara fada yaya gida amsa a wullakace suka batashi cikin takaicewa ganin hakan yasa ta sake labule ta juya ita bata tsaya tambayan yaransu ba yadda aka saba idan sunshigo din.

Ba sai an fada mata ba tasan dalilin hakan bai wuce kan zancen nan da akayine uwarta fada masu suke wanan abin don haka kyalesu shine alheri a gareta lokacin.

Dakinta takoma ta samu wayanta na kara ta dauka yar uwartace ta kirata akan bukin da zasuyi gidansu hakan ya dauke mata hankali harta manta da zancen su.

Rayuwa na gidan Alh yakubu baida kyau don ma yana namijin tsayene a gidansa nasa don hjy Naito ta kasance irin matan nan dake zama da yaransu tana cusawa diyanta kiyayyan ubansu a zuciyarsu.

Don yau ka samu sabani da namiji ka saika zauna da yaro kana fada mai dukka damuwanka kana bata uba a wajen yaro dole yau da gobe yaron nan ya rage ganin mutuncin mahaifinsa a idonka .

Saboda kana bakantawa uwarshi ko wani lokaci ba abinda yakai uwa girma a duniyan nan yau da gobe sai dan ya nemi raina uban nasa kan wanan abinda akewa uwarshi.

Akasarin mata a yau irin rayuwan dake gudana ke nan a gidajenmu wanda a baya can iyayye basu bari da yasan akwai sabani tsakanin keda mijinki saboda hakkuri irin na matan lokacin baya.

Koda zasu fita gidan basu sallami hjy Hauwa ba din muryansu taji suna dararaku da uwarsu da habib daya dawo lokacin donshi yana don son shiririta a cikin harkanshi yasa basu faye jittuwa da mahaifin nasu ba sosai.

Yaso ya tsameshi cikin dukiyansa amma uwar tafi karfinshi dole ya barshi yaci gaba da dan zuwa shagon saidai duk motsinsa uban yana kallonshi.

Gida fasalinsa a kewaye yake bangaren hjy Naito yana daga dama haka daura da nufar kofar maigidan sai ginan part din hjy hauwa dake can daga yamma iccen unbraler yana sakiya yana ba ko wani part na gidan iska.

Koda suka fita daga cikin gidan sun jima a waje can ma kara tattaunawa akeyi akan dai hjy hauwa da yayanta musanman Aliyu daya ketare ya tafi kasan waje waishi karatu wanan abin yanawa hjy Naito dadi ganin yadda a yanzu yaranta suke cikin dukiyar mahaifunsu dumu dumu suna yadda sukeso dashi ba tare daya sani ba.

Bayanta shigone hjy hauwa din tana waje tana gyara kayan miya take fasin har sun tafi ke nan ta amsa mata sa eeh a takaice ta shige dakinta.

Allah ya kyauta ta fasa a sanyaye ta juya zuwa kitchen dinta don girki takeyi lokacin kowa kuma kitchen dinsa yana gefen part dinsa amma akwai main kitchen na kowa da kowa a gidan.

Takan zauna tayi tunanen danta dake uwar duniya bataji koga wani irin halinda yake ciki abu daya ta fake shine addua da sadaka tana nemawa rayuwansu sauki a kullum.

Yayin da shi kuma dan yake can yana samun karatun da yake da burin yinsa a rayuwansa shi Allah yayishi mutum mara son hayani da kuma kwazo akan duk abinda yasa kanshi yi.

Wanan yasa uban ke son zamashi shago don hausawa ba wani camfi da sukw cewa wani yafi wani sa,a da fuskan kasuwa idan ya tsiri zuwa shago mahaifin nasu yana ganin haske sosai a lamarin kaauwanci.

Wanan yasa baiso dan ya daga kusa dashi ba yaso ya zauna sucigaba da kasuwancisu yadda aka saba amma shi tun yana karami yake matukar son karatu a ranshi.

Abinda Alh bai fahinta ba shine Aliyu bai taba ha,intarshi bai taba kudinsa ko ya rage suko namu duka ana raba daidaine tsakaninsu da mahaifin nasu.

Haka kuma idan Aliyu yaje kasuwa ba wanda ya isa yai wani ha,incin da za a cuci mahaifin nasu don idon shi nakan duk wani motsi nasu wanda hakan ke matukar bankata masu rai yasa suka fara tsanan zuwan nasa kasuwan da yakeyi har suna suka saka mai da sarkin ajiya baici ba ya hana a taba.

Yayi sa,a ga tafiyanshi din inda ya samu wani aboki musulmi da suke tare yaron dan masu kudine saisai dan kasan ghana shima karatu ya kaishi kasan amma yasan rayuwan wajen .

Shine ya hada Aliyu din da wani abokin babanshi da yake neman wanda zai kama mashi aikinsa suke zuwa tare dashi idan basu da karatu.

Kamar yadda nan gida mahaifiyarshi take a cikin damuwa kanshi shima dai din hakane don duk abinda yakeyi hankalinshi yana gida wajen iyayyeshi.

Balle a irin halinda ya baro mahaifiyarsho na tsngwaman hjy Naito duk da ya taso ya samesu a haka ana kishin mumuke a gidan.

Saidai wana karon yafi mamakin hjy din yadda ta shafawa idonta toka take faman sakin maganganu game da tafiyan nashi.

Wani irin cin mutunci hjy Naito din tayi akan bata yarda da yana tafiya ana kwasan kudi ana bashi ba alhalin yarantane a tsaye wajen neman dukiya donshi a yanzu.

Yaketa kokarin neman na kashi don baiso sam idan ya dawo ya kara saka hannu a cikin dukiyan mahaifin nasu kuma.

Furuncita yasa ya kara fahintar bata taba kaunanshi dashi da yanuwardshi da suke daki daya duk daya don gani take sune kadai dakinsu suke cin dukiyan mahaifin nasu da ayi zancensu jiki na rawa zai biya masu bukatansu

Wanda hakan ke kara bakanta mata zuciya har take jin zallah ki yayyan uwasu da yaran ga baki daya a gidan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[6/22, 10:13 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

7️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,

🀳AUNTY ZEE MOM MUJJAHID KATSINA 08262859027🀳

πŸ‘*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA*

*Maganin sanyi 5k*

πŸ‘*Maganin sanyi*

*5k*

πŸ‘*Maganin ciwon Qoda 10k*

πŸ‘*Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k*

*MAGANINπŸ‘ MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*

πŸ‘*INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU*

*Maganin gyaran Nono πŸ‘8k*

πŸ‘*MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE*

πŸ‘*Maganin Rage Tumbi 7k

πŸ‘*MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE*

*Maganin Basur 5k*

*MAGANIN CIWON SUGARπŸ‘ CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI*

*Maganin ciwon Sugar 10k*

*08162859027*

*09070027627*

*Location*KATSINA STATE*

*ACCOUNT NUMBER*

*8162859027*

*ZAINAB SHU AIBU*

*OPAY*

*OR*

*3968303018*

*FCMB*

*ZAINAB SHU AIBU*

πŸ‘ƒ*DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO*

Ba zan iya cewa ga lokacin da mama suka fara kawance da mahaifiyar salma ba mu dai mun wayi gari mun tsuncesu sun zama aminai.

Duk daba wani dogon hurda sukeyi sosai ba akwai dai halaka a tsakaninsu irin ana tare din nan.

Wani lokaci mama na zuwa gidan ita kuma maman can gidan takanzu namu gidan su dade daki da juna har na kula mama din bata son amsawa inna gaisun wata idan tashigo.

Da yake inna ko yarone sai sun gaisa hakan yasa ban rike wanan sosai ba a raina iyaka dai yanzu dana dan kara girma kurciya yana kakaba a jikina saina rage shiga gidan nasu sosai don irin wullakancin mahaifiyarsu.

Ba zan mantaba wata rana ana buki a gidan kakaninsu don haka Salma tace tare zamu don ina matukar shiri da mai bukin a lokacin.

Don ada muna kakana zamu kwashi zugarmu ranan jumma,a muje masu yawon jumma,a ita kuma kakansu zata bamu goron jumma,a da sauran mutanen gidan.

Wanan abin yasa muke Allah Allah juma,a takewayo don muje mu karbo alawa da take raba muna a lokacin don mussanman take aje muna namu daban.

Ranan da banje ba kuma zata kumso min nawa a leda taba salma din ta kawo min har gida har dan canjin da take raba muna za a kawo min nawa.

Wanan zuwan da mukeyi yasa yan gidan suka sanni nasan kowa nasu yadda na saba da mutanen gidan su salma banko saba da nawa gidan kakanin haka ba .

Don gidan iyayyen mahaifina suna nan suma a gari amma idan mukaje haka zasu barmu tsaye zakice mu din basu ma san inda muka fito ba sai mungaji da rakubewa a bango muce zamu tafi kakan namu tace ku gaida gida ba wani irin jan jika din nan a jiki da kakanin keyi a garemu.

Koda yake zance garemu mu kadai diyan innan mu takewa hakan a lokacin son ina ganin yadda takewa diyan mama suyi ta mata iya shige tana dariya.

Yayan mu namijine kadai basu jituwa dashi don shi irin masu dauraren fuska din nan ne bai magana da kowa haka yake takance bakin rai yayi mashi yawa amma shirin da sukeyi yafi wanda takeyi damu don a hakan take jawoshi jikinta.

Tau har anko babansu salma yayi dani saidai a wajen dinkin ya bambamta don wai yadi bai isa ba na sisters din ta sai mama tace ayi masu a kara da yadina haka yasa akai mun wani dinki daban na jiki dashi hakana.

Niko ina murna aiko salma ta tuma ta kafe da aiba haka akace a dinka min ba yaya za a dauki yadina a dinkawa yan uwanta abu yakai har uwarta duketa wanan yasa uban yaji me akeyi ya shigo yana fada.

Tani ina hanaki dukan yaran nan bakiji yarinyar nan tana da gaskiyarta yadin nan na sayawa kowa nashi don me zaki dauku na kawarta ki dinkamasu ?

Alh don na kara da yadinta laifine hakan tunda ba iyayyenta suka saye ba ya juyo yace meya kawo zancen iyayye kuma a nan ?

Badon Allah ke nan mukai mata ba naso kibar yaran nan suyi alakansu Allahne ya hadasu baki san dalilin haduwansu ba don haka ki kyalesu don Allah suyi abotansu Tani.

Kinsan me gobe zai zama kina wullakanta yarinyar nan tun tana karama kuma kina cin moriyanta har yakai yanzu bata son shigowa gidan nan sosai duk saboda halinki.

Tace ni ban son Salma da ita duk wani iya shege itace ke koyawa salma hakan shiyasa na dai tsani yarinyar nan wallahi bandai son ganinsu tare da salma.

To aisai ki koreta aiba sai na koreta ba ita dai zata kori kanta a yanzu salma bata gane me nake nufi da haka sainan gaba kai kuma ka kama mata tomu zuba nida ita.

Duk a kan karamar yarinya kamar wanan kike magana haka Tani kamar kin samu wata babbar mace yar uwarki baki dai kyauta ba wallahi yaro fa baya mantuwa Tani.

Idan bata manta ba dukana zatayi kome an rage din in ubanta ya saye ko uwarta tace bazata sakaba mu gani ?

Amma kin ban mamaki da wanan kalaman naki yaci ace kin rike yarinyar nan da zuciya daya shi yaro fa dan kowane balle ita da ko yaushe tana gidan nan tare damu.

Yaja tsuki ya fice waje yana jiran fitowan su niko cikin rashin damuwa kodana shigo na saka kayan suka daura min dankwalin duk da nawane dan karami a ciki kuma kudin turmi aka bayar kamar na kowa.

Yadda naga mama ta amsa min gaisuwan yasa nasha jinin jiki a lokacin ga kuma salma da alamanta ya nuna tayi kuka a fuskanta na tambayeta tace ba komai na shige daki wurin sisters dinta.

Wajen shiga mota kirikiri hjy tace ba waje ma,ana dai nice ba zan samu waje ba hakan yasa naja baya suka shiga na juya na koma gida duk da hakan kurciya baisa na damu ba sai murna da nakeyi da sabbin tufafin dana samu na anko din bukin nasu.

Gidana koma bakin cikina a lokacin shine rashin yin sana,an da bamuyi ba a ranan don saboda bukin don mama taso hanani zuwa amma dana ce mata har anko aka dinka dani saita barni inje din kinsan dai irin zumunci da akeyi da makwabta ai hakane a tsakanin mu.

Kai Tani duniyace ashe ko saida ta tabbatar da nufinta wai su kare ba a san harara ba ka nace a wuri ana nuna maka kora da hali amma kwadayi yasa ka nace koda yake dama kudi wajen kwadayin yakan mutu ai.

Maganan mama yasa inna shan jinin jikinta ina daki da yan uwana banda mugun wasa ba abinda mukeyi muna yan dararaku a tsakanin mu.

Inna ta shigo tana fadin ke Inna Isah wai ashe ba wani abu bane ya faru basuje dake wajan bukin nan ba don naji yaya na magana kamar tasan da wani abu?

Nikan innan mu ba ai komai ba nadai shiga naga maman salma kamar fuskanta a daure itama salma din kamar tayi kuka nake gani ?

Kin tabbatar babu komai da kikai masu ko akai maki ni inkibi ta nawa wallahi dakin daina zuwa gidan mutanen nan ,,,,,,,,,

Sallaman salma da yan uwansu na can gidan sa,oin mu da suka shigo tana fadin Mairo badai ta fita ba ko ?

But na fita na tsaya a kofan dakin mu ina binsu da kallo duk sun sha anko iri daya da nawa din dana salma suna tsaye suna gaida mama innama ta fito suka fara gaida ita.

Salma ta juyo tana fadin ai muna zuwa anty Fati taga kizo take tambaya na fada mata shine tace muzo a daukoki sai baba ya ganmu a waje na fada mashi ai mama tace baki shiga motan mu yace azo a daukoki.

Yanzu ke salma har kun isa shine kika dawo don wahala dolene sai taje wajen bukin halan nikan in bada itaba aiba zanji dadin wajen ba .

Har mun fita inna ta saka min kira na dawo kunne ta jamin irin na ya da uwarta akan in natsu in kama kaina jikinta na bata wani abu mara dadi game da mutanen nan yanzu a kaina.

Hakan yasa jikina sanyi koda muka je gidan ita wanan da ake kira anty Fati itace take sona wai da daughter itace ta rike min hannu ko ina zata muna tare ko inda su maman salma hjy Tani suke ban taka ba tunda naji innan mu ta fadi hakan ina tsoro ko abinci ban sake jiki naci ba sosai.

Saiko gashi sherin hjy Tani daya tashi ido rufe wai an daukar mata post din kudinta ta hargitsa waje da tashin hankali na aka fara zarge zarge kan mai bakin jini.

Haka tasa aka kirani daga can lungun da muke Allah yasa anty Fati bata sake min hannu ba koda akace mama Tani na kirana tace meye sukace ance dai inzo yasa ta mike tana fadin muje don nasan matar nan tana iya maki wani abin kuma a nan.

Tunda tace ba zatazo dake ba dama haka muka kama hanya zuwa part din suke aiko daga nesa aka kuro min idanu muka karaso anty Fati na fadin meyr meya faru ?

Hjy Tani tayi kokarin fisgoni daga hannun anty Fati tana fadin ke yar iska bani jakata da kika dauka a nan ?

Cikin mamaki ba dago kai nace jakka jakan me mama tayi kokarin mangarata anty Fati ta sake tarewa tace Babyna kinzo nan ne ban sani ba ?

Nace tare da girgiza kai wallahi banzo ba bansan jakkar da mama take magana ba nan hayaniya ya tashi anty Fati ta rikeni tamau salma kuma tana ja min hannu tana shirin kuka a lokacin.

Haba anty Tani har yaushe yarinyar nan tazo wajen nan da za a dafa mata sata inma tana satane wanan dai ba ita ta daukar maki shi ba.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login