Showing 237001 words to 240000 words out of 395027 words

Chapter 80 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

zasu samu.

Saidai na nuna ba zanyi ba har hakan yana son jawo matsala a tsakanin mu a yanzu wanda ni kuma ba zan so hakan ya faru ba shine nazo in fadama .

Matsala as how yana kokarin shiga hakinkine kome ?

No no no ba haka nake nufi ba guy din nan na fadama ya taimaka min sosai matuka a lokacin da nake bukatan taimakon wani a kaina har yakai ya taimakawa mahaifina ya sama mashi abinyi yanzu mahaifina yana da madogara .

Sai naga ya dan dago kai ya dubeni da sauri nace suna sana,a yanzu haka da mahaifina a tsakaninsu ta sanadina.

Don har yakai yana aika mashi da dukiyarshi can kano yana juyawa into Naira ya turo mai da kudin idan an,saida kayan .

Wanan yasa kaga muna tare dashi sosai don yayi min matukar kokari sosai a rayuwana tun haduwan mu.

You mean Abban daya haifeki kike magana fa ya tambaya cikin mamaki, nace yes of course babana daya haifini ya taimakawa wanda ban taba fadawa wani wanan zancen ba sai kai a yau.

Ya fahinci bamu da karfi yayi dabaran samawa baba din madogar da iyalinshi ta,,,,😑 wai wani irin taimakone haka ?

Ya tanbaya fuska tubure kamar a ciki fushi na dan rausaya nace daahi mashin mashin da kekunan dinki da freezer yake turawa arewa gun baba duk ta hanyar dalilina hakan ya faru.

Why why maryam zakiyi wanan kasadan ba tare da kin fadawa wani ba baki tsoron ki jefa mahaifiki a cikin matsala irin wanan ?

Har ki yarda ya dauki dukiya ya tura mai wani iftila,i ya faru wa kike son ya biya wanan kudin gareki nan ?

Tsam na mike tsaye ya bini da kallo yana fadin ina zaki saida na dan fito daga cikin kujaran da kyau na soma fadin nagode dama nazone don nazata kana da kyakyawan zato a garemu ashe abin ba haka yake ba.

Kai a kullum zaton,ka kan mutum shine kaddara ta tsiya ya sameshi kai wakeyi ma wanan fatan nayi regret din zuwa nan a yanzu tunda har cigaba zai samu mahaifina kayi min wanan bakin fatan a gareshi.

Bai bashi ba haka kai tsaye ba don ban yarda ba saida mahaifina ya nuna shimai amanane akan abin wani .

Da wanan dalilin yasa muka amince har aka fara wanan bissiness din dashi.

Yanzu kuma nazo nan ne ba don komai ba don ganin kamar ka zamo wani dan uwana da muka fito ciki daya ko waje daya wanan yasa nazoma da shawara.

Kada sai nayi daga baya kaji kace dani meyasa na yarda na aikata hakan ban fadama ba ?

Amma nagode da irin fahintarka a kaina saidai ka sani ni Ozil ya taimakeni ba tare da wani manufa akaina ba kamar yadda kake zato ko tunane.

Yayi hakane shima don mu taimaka mashi saboda yana neman wanda zai rike mai amanan dukiyanshi.

kwarai kuma yaji dadin hakan don baba ya taimaka mashi fiye da yadda bai taba zato ba yanzu haka ban san meye a tsakaninsu ba ?

Don bani cikin wanan harkallah tasu a yanzu nazo nan wajenkane da tinanen samun shawara don a rayuwa idan mutum yaima irin alheri haka ?

Sai kaima kayi kokari ka kwatanta hakan gareshi koda da karfinkane ka taimaka mai kamar yadda ya taimaka ma

Bai dace irin alherin Ozil a gareni ba yazo min da bukata alhalin yasan zan iya hakan don nasha mashi amma nakiyi a yanzu a karo na karshe daya bukaci in,taimakesu.

Yana zaune yadda yake zama yana dan jujuya kan saman kujera sai faman bina da yake da kallo har na gama zan juya naji yace dani.

Waike meyasa baki da fahintane ?

Don idonki yana a tsakiyan goshi yanzu me kikaji nace da kike wanan halakon haka ?

Kinzo akan kar naji kin koma ruwa ko inyi kara ko in dauki matakin da nace zan dauka idan naji kin kara wanan sana,an ?

To ai baka hana kwado zama kusa da ruwa ?

Ya taimakeki kina son kema ki taimakeshi ki rama mashi halarcinsa gareki good & fine bissimillah sai kije kiyi mai din tunda har Abbanki shima ya taimaka.

Don haka ba zan hanaki ki taimaki wanda har Abbanki yasan dashi ba maryam idan nayi hakan ban kyauta maku ba har Abban naki.

Sam bansan da abin yayi karfi haka tsakanin ku ba ai har yana taimakon iyayyenki da suka haifeki kwarai maryam yana da kyau ki taimaka mashi kema a nan.

Saidai ina son baki shawara kibi a sannu ki dinga sanar dani komai da kike ciki don gudun bacin rana a gareku wanan sana,an akwai hatsari a cikinsa sosai wallahi.

Nan lagos ce ba kamar kano bace da zaka san halin mutum lokaci guda nan sai mutum yabi a sannu kafin ya iya mu,amula dasu ni ban zargi kowa ko zato nake maki ba mutunciki nake karewa kawai maryam ?

Kasa nayi da kaina lokacin daya kai karshe yana fadin okey you can go Allah ya tsare sai naji kunya da sanyin jiki a lokaci daya sun rufeni wajen.

Na dago kai da niyar bashi hakkuri na samu ya soma jawo sytem dinshi don yayi aiki hakan cikin dauriya na juya don in bar wajen ba tare dana furta komai gareshi ba.

Idan kin fita hamza na waje zai saukeki school din ya fada na dan juyo nace ya barshi zan karasa ai nafice ban jira abinda zai fada ba kuma.

Naga driver nashi na kawar da kaina gefe daya ina fita na tare taxi zuwa school din mu ashe ya koma ya haushi da fada yace ya koma ya daukeni yace ai a gabanshi na shiga taxi na tafi.

Har na isa school ban cikin natsuwa don abinda ya faru na rasa sai yaushe zamu fahinci juna da guy din nan dako dayaushe yake min kallon wace bata san komai ba.

Yanzu yaya zanyi wanan dan canfin yai min baki ga aikin nan Allah ya gani naso in taimakawa Ozil koda hakan na nufin karshene a gareni amma kuma ina tsoron ai dama na fada maki kikaji ina tsoron abinda wani zai min baki a kai.

Dole na fara share zancen nacigaba da harkan karatuna shima dai ba waya mukeyi ba balle nace ga halin da suke ciki a can wajensu din lokacin.

Bayan kwana biyu dayin wanan zance ina zaune Okenah ya sameni yake ban labarin abinda ya faru da mutanen da ake son naje nagani ashe mayaudarane basu da komai sunyiwa wani scamming sun tafi mai da kudi.

A zaune nake ban san lokacin dana mike tsaye ba yace true true maryam iam telling you munyi arziki da baki riga kika tafi wajensu ba ai na yarda da Ozil ke kiranki da lucky girl kina da matukar wayau.

Kamar kin sani kika amincewa da wanan tayi kika nuna ba zakiyi ba sam ai zai shigo yace yana son ya ganki a kan zancen.

A hankali nakoma na zauna ina runtse idona tare da tunanen karin maganan bahaushe na fadin ko riga shiga kwana zai rigaka tashi daga barci.

Watau wanan mutum ashe gaskiya yake fada min ban dauka ba don yafini sani lagos da abinda ya kumsa hakan yasani kara natsuwa tare da zurfin tunane akan lamarin rayuwa.

Dole inbi a hankali kafin in rufta kaina cikin tsaka mai wuya garin neman kudi in jawowa kaina fitinan da ban iya dauka tunda duk mai kaunana yana fada min in daina irin wanan harkan akwai hatsari a cikinshi sosai.

Kodana koma gida kasa natsuwa nayi don ina ganin kamar ban kyautawa kaina ba da mai sunan baba da yake kokarin ganin ya kare min mutuncina na matsayina ya mace yar arewa kuma ?

Nayi juyi a daki barci ya ki daukana gashi ranan ni kadaice a dakin don Amira ranan tana wajen mamanta bata zo nan mu kwana da ita ba.

Ban kyauta ba nake fadawa kaina nima dai din ban san ya akayi nake tsayawa har in rufe ido ina wanan fitinan ba wani lokacin sai nayi daga baya zanga rashin kyautawan hakan da nayi in koma ina dana sani kuma daga baya.

Haka halina yake a haka na taso bani daukan ta kwana ga duk wanda ya shiga gonata banda tsoro ko kunyar tsaya ina noke noke.

Zan fito garan da garan in fadawa mutum abinda ke raina lokacin nifa a tunanena daukar yar iska wanan mutumin keyi min.

Wanda nasan ni kuma ba yar iska nake ba don haka ba zan yarda ya zarga min rayuwan da bansan dashi ba ina kokarin kare kaina da hakan a ganina.

Shiruma ance maganace don haka ya zama dole in kara kama kaina da mutuncina ko don watan watarana ina da bakin bada amsa saidai abu daya ya tsaya min a rai lokacin.

Fada mai sirina da nayi akan mahaifina da wani fassara zai dauki zancen duk da abinda ya fadi ai gaskiyace abi a sannu din ba laifi bane.

Don amana wuyan sha,ani ke gareshi duk yadda ka iya rikawa sai ubangiji ya jerabi imaninka wata rana ya gwada ka kan abinda ka dauki amananshi din.

Abinda wanan yake son lurar dani ke nan amma na kasa fahintar shi ido na lumshe ina rokon ubangiji ya tsare ya kare min mahaifina daga hakan .

Baba wanda aka yanzu idan na ganshi ya sauya don yayi kyau ya tsayawa gidanshi dama rashine ba halinsa bane tauye iyali inna da kanta take fada min tana fadin Allah dai ya saka da alheri sukan yanzu sun godewa Allah gaskiya idan Ozil nada rabo a wajen Allah ya keboshi zuwa addinin musulunci na amsa da amin.

Har take fadin irinsu iya addu,an da zakai masu ke nan su gane hanyar gaakiya su shiga addinin Allah da Annabinsa idan suna da rabon hakan wajen ubangiji.

Matsalana da hajja yabi sai abinda yai gaba don kuwa ita ta sauko daga abinda take ji a game dani nice dai kamar a lokacin tayi min wanan abin kullum haushinta karuwa yake min a kasan raina.

Ranan koda na dawo gida gaba dayansu har Paapa da ranan yake gida suna falo zaune dana shigo na gaida Paapa da anty na juya kawai nasa kai don zuwa dakina.

Maryam baki ga yabi a zaune bane muryan Paapa dake fadin hakan yasa na juyo kafin nakai ga bashi amsa ta karbe da fadin ina ruwana Oga ko ta gaidani ko kada ta gaisheni uwarsu daya bata isa dai ta fitar dani gidan nan ba.

Inma wani ke turota tayi hakan ta makara wallahi tunda nashigo ba yadda za ayi dani shi na dan daga kai na duba a lokacin shima din ni yake kallo na amsa daga inda nake tsaye na ganta Uncle.

Shi kuma yana fadin look yabi banfa son irin shashancin nan waike wata irice da baki so a zauna lafiyane ?

Wa zai turota tayi maki hakan halinkine dai tagaji dashi tunda abinki ba marmari a cikinsa da kowa kina fitina ke baki dubaiya.

To tun wancan ranan take gaba dani har yau din nan batayi min magana haka kawai itama ta iya shareni nice ba zan iya ba don ta samu waje take ganin kowa tana iya takawa yanzu.

Tunane nayi me zan tsaya yi kuma kawai saina sa kai zuwa dakina din inda na dosa da farko ina jin abin ya koma masu kamar fada a tsakaninsu kaina ?

Ikon Allah na fada ina shiga daki na jefa jakkata saman gado ina fadin mena tsarewa wanan matar kuma ni maryama kura mai bakin jini kowa dai maryam maryam meye haka wai ?

A iya sanina dai nasan ina bata girmanta a matsayinta na matar uncle dina kuma marikina haka kuma na nunawa danta so da kauna amma tun a kan yaron na fara fahintar sauyi a gareta.

Ban damu ba don bata gabana ni abinda ya dameni shine inga na ida karatuna na samu madogara ba wanan fada nata na kishi ba da bai karewa masu sai randa rai ya kare garesu kila ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[9/19, 9:32 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊7️⃣3️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

An dauki lokaci bankira ba bai kira wayana ba tun bayan wanan zuwan da nayi office din inda ni nauyi ya hanani kiranshi.

Shi kuma busy yake kuma yana son kuma ya ban lokaci don ya fahinci kaina akwai hayaki har lokacin na kasa fahintar manufanshi a kaina nason ya mayar dani yar arewa musulma da yake kokarin yiwa rayuwana.

A hakan ma zance yafi min sauki banji koda munyi hutu a yanzu zan koma wajensu yin aiki kuma iya abinda na samu nagodewa Allah da hakan .

Nabar wancan aikin nasuma zan bari don kusan ba bangarena bane dukka biyun kinsan dan Nageria a lokacin da yake cikin giyan karatu bai fahintar abindake cikin kasa a lokacin gani yake yana gamawa aiki na samuwa gareshi.

Sai idan an kare din ne ido kan raina fata ba aikin gwaunati bana company din sai wuya yayi wuya za a fara nemawa kai mafita .

Allah ya kawowa kasan nan tamu agaji alfarman Annabin rahama sallalahu alaihim wasalam ina daya daga cikin masu wanan tunanen cewa kokarina zaisa ina gamawa in samu aikinyi.

Don haka nake kokarin watsar da daman da Allah ya ban a yanzu nake ganin inyi nisa dasu shine mafi a,ala a wajena bayan bansan Allah ubangiji bane yayi min gata a hakan ya jefo min wanan mutum a rayuwana.

Rawan kai da shashacina irin na kurciya ya hana in fahinci irin gatan da yake kokarin dorani a kai a lokacin bai kirani ba nima haka cikin rashin damuwa ban damu da hakan ba don bai kirani ba shima ?

Saidai abinda Allah ya nufa ga bawanshi bawa bai isa ya kaucewa kaddaran hakan ba a rayuwa shine abinda bamu ganewa wani lokaci yan adam kaddaran mu a rubuce yake garemu.

Nasan dan kokarina yaci nayi popular a cikin department din mu abin bai tsaya a nan ba ashe don gaskiya kamar ko wace maryam haka nake nima da zafin nama ga tsabta ga kokari ga duk abinda nasa kaina uwa uba kuma ko yaushe a cikin kwaliyana nake baki taba ganin maryam kazama sai idan ta maida kanta marmo.

Wanan yasa sukayi min tayin miss campus na shekara ban tsaya nauyin baki ba nake fadawa malaman hakan haramun ne ga addinina don nasan za a watsa hotuna da mujjala a sakani a bangonshi a tallan surata a duniya .

Wanda cikin hakan kuma wasu zasu bukaci da incigaba da masu tallan wani abu mai muhinmamci wanda nasan a karshe ran iyayyenane zai baci ga hakan idan na aikata.

Wanan yasa tun wuri na nuna ban ra,ayin hakan gaskiya don na san darajan kaina da yarena tare da girmama addinina daya haramta min yin hakan.

Nasani idan nace zanyi din zanyine amma kuma Allah yasa min matukar tsoeonshi da kaunan Annabi mu tare da koyi da sunnah .

Idan da nace zanyi din zanyine amma akwai tsoron Allah a kasan zuciyata ina tsoron ranan haduwana da ubangijina.

Badon hakan dake tare dani a zuciyana ba zan iya shiga wanan gasar har ingama ba tare da gidan mu ansan nayi ba don saidai idan sun gani ga tv


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login