Showing 339001 words to 342000 words out of 395027 words
Chapter 114 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
fada.
Hakan ne yaba mijin nasu dariya amma cikin dakewa yake fadin kamar ya bai isa ba tunda albarkanki yake so kan lamarinsa yace ya fasa tunda batayi maki ba ko ?
Ya mike ya fake ga waya zai fita yaji tana fadin tunda zabinsane shi zai zauna da abinsa ni meye nawa a ciki yanzu ?
Zancen yaya hanne kuma ita tajawa kanta kuma ai lokacin da take ganin kowa ba komai bane batayi tunanen irin wanan lokacin na iya zuwa ba ?
Ni ba komai bane don kada aga tana so nine ban tsaya akanshi ayi wanan hadin ba amma komai ai ita ta lalata abinta da hannunta.
Haka suka kwasa a tsakaninsu dashi a ranan amma bai fada min komai daya faru a gidan nasu ba .
Tunda safe aka fara rabon sadakan da yace kamar yadda antyna ta umurta da anyi nayi mamakin zuwan yan gidan su Paapa da wasu yan can Family house din mu sai kace bukine za ayi.
Karfe biyu bayan an sauko jumma aka hadu gidan mu don baiko din inda su malam da yan uwan Abbasu sukazo da komai nasu a lokacin kamar yadda yake ga al,adan bahaushe.
An hadu sosai a wajen kamar ba baiko ba bayan an gama anyi addu,a tare da fatan Allah ya nuna lokaci lafiya malam ke fadin sai a yanke sadaki a wajen dayani .
Nan aka tsaya muhawara baba bala yace ga babana nan dake tayar dani tunda Allah yasa dashi a wajen ba zasuyi mashi katsaladan ba kuma kamar yadda sukai mashi a wanan din .
Paapa Yaji dadin hakan da akai me inda yace yarshi bata sayarwa bace ai sadakinta kamar kowa su bada dubu dari biyu da hamsin a lokacin.
Malam ya dauko kudin ya bada a gaban jama,a yana fadin nayi tunanen hakan duba ga irin yanayin sanin mutunci da ahalin nan ke dashi irin namu na al,ada yasa na fito dasu da niyar hakan.
Gasu ikon Allah aka kirga akace sun cika Paapa yayi shiru can ya dago yace toni malam me ya saura ga addini kuma akan aure yanzu aida an daura auren nan gaba daya a nan tunda ga waliyan duka mun hadu.
Mena fada maku shawaran mu kusan dayane a yanayi tunanen da nakeyi ke nan a raina ka rigani furta hakan ba bata lokaci akai sanar da daurin auren lokaci guda haka sanarwan yazowa kowa a bazata don halin manya.
Wanan ya tabbatar da daura auren mu da Aliyu a wanan ranan wanda yazo muna a bazata don baba balane yazo da wanan albishir din don ya sanarwa mata abindake faruwa a gidan.
Ni dai ina daki kwance ina jin hayaniyarsu ana ta ciye ciye da hira da dararaku a tsakar gidan can naji matar baba lawal na rangada guda tana fadin masha Allah abu yayi kyau wallahi har auren aka daura kuma ?
Da gudu saudat ta fado daki tana fadin wallahi yayan mu an daura maku aure ga baba bala can ya shigo yana fadin ba baiko kawai akayi ba aure aka daura gaba daya.
What na fada ina mikewa tsaye ta hanyar dagowa daga saman katifansu da nake kwance da sauri ta tarboni tana fadin me zakiyi yayan ?
Zuwa zakiyi kice dashi baki yarda ba kome ki godewa Allah daya nuna maki hakan gurin inna da addu,an ta yau ya cika a kanki an daura maki aure a cikin mutunci a kuma cikin yan uwa ba yadda ake maki fata ba.
Kkmawa nayi na kwanta lamo saman katufan kafin na kara zabura cikin zafin nama ashe tana tsaye kaina har lokacin bata fita ba tace dani.
Yayan mu kada ki yarda don Allah wani ya fahinci baki farin ciki da hakan ba a samu na juya zancen kinsan gidan mu gidan sa idone don Allah ki koma ki kwanta.
Kai na dago na dan dubeta nace for god sake saudat a daura min aure haka kamar wata bazawara don Allah ?
Bazawara kuma kamar dai me gata wanan ai auren gata akai maki yayan mu wake samun hakan daga baiko sai daura aure lokaci guda sai wance ta isa dai ?
Ta hanani yin duk wani motsi a dakin tana ta zuba min dadin baki naji wata abokiyar wasan mu tana fadin ina amaryan take dama da shirinsu ashe suka zo garin nan na aure ?
Kinji ko sun soma fada balle kuma ki bata zance a barsu a hakan ta baibai basu san baki sani ba kema a tafi da kun sani dama kukazo.
Nikan bansan komai ba na fada a hasale saiga jummai din ta shigo tana fadin iyee amarya dama wayau da kukai muna ke nan ashe keda su kawu ?
An rufe ance damu wai baiko za ayi din ku shashatar da makiya aiko yau kun ba makiya kunya sunce ba ayi adaiyi baiko gashi Allah yayi an daura har aure ta kara rangada wani guda da ya kara sa gidan hargitsewa kafin kallo ya koma biyu.
Don kuwa mama ce ta fashe da kuka tana fadin dama ita aka rufewa aure za a daura min don ana zaton zatayi min mugun abu kome da za a rufe mata zancen ?
Yadda kikajin nan haka kowa yaji daurin auren nan bada niyar daura aure aka hadu ba ance ganin har sadaki sunzo dashi yasa akace a daure auren dayani a lokacin.
Sai bakin yan uwa ya kasu biyu shigowan su babane ya tsaya tsakar gida yana fadin idan ance karya akai maki Rakiya ?
Duk daba hakana bane ba aje da niya ba amma ko haka din ne ai ba ayi karya ba tunda nan shekaran jiya ba irin babatun da yarki batayi a tsakar gidan nan ba kan mairo.
Wasu a cikin dangi na fadin to me zaisa ki damu da hakan ma wanan aiba ke kadai ya shafa ba tunda har Ai data haifi abinta ita da yaya basu san za a daurawa mairo aure yau ba .
Kafin wani lokaci labari yakai duk inda ya dace yakai shima Aliyu suna wajen baikon ta waje zaune sukaji ana sanarwa za a daura aure a lokacin.
A zatonsu wani aurene za a daura yana sauri ya tafi don yace a ranan zai koma lagos sai ji sukayi ana fadin za a daura auren Aliyu Alh yakubu mai glass da mairo Aliyu Na,ibi akan kudi dubu dari biyu da hamsin .
Tunda na juya na bada baya ban juyo ba saidai ina jin abinda kowa ke fada game da mama da kuma baba da yashigo yana sababi sai fadi yake.
Yaushi bai cikin kuka ko tashin hankali sai zallah farin ciki da godiya ga Allah ubangiji a gareshi a rabu da mama duk borin kunya takeyi don cika bakin da tayi a baya kan ba zan taba aure yayanta na gida zaune ba ?
Toke Allah ne Rakiya wanan abin kawai ya isheki hankali idan kina da rabo a wajen Allah abinda baba yayi ta fada ke nan da kyat aka izashi ya fita waje badon ya gama ba.
Nikan mairo naga takaina saboda mama a rayuwa ranan da yakamata ace ya zamo na farin ciki a gareni da yan uwana ga kuma mama da nata sabon sallan a kaina tabar muna tsegumi an samu abin fadi kuma akanta da ni a yanzu.
Shigowan hajja yabi da ake fada min cewa ga hajja yabi nan shiyasa na dago don mu gaisa da ita tayi baki ta rame abinda idona ya fara hangowa ke nan a gareta.
Sai furcinta datayi wanda Allah bai sa yan amin sun karba mata ba cewa da tayi in aure banzane inyi tagani mana ai samun miji ba wasa bane banda wanan dan iskan da yake marana wa nake dashi na kwarai bayanshi ?
Shima inya gama dani ai gaba yayi ya gudu ya barni a haka zan kare a rayuwana ba masusuni akaina .
Wasu hawaye masu zafi nake ji suna gangaro min a fuskana lokacin ni mairo inma da gaskene mama ta saka ruwanta a bakin jini yako saku don a gaskiya nakayi tunanen hakan wata rana ?
Nagoge fuska a hankali jin Saudat na fadin amma duk hawayen farin cikine haka yasa na fahinci gyaran da take min a lokacin na in natsune.
Saudat ta zamo kanwata kuma kawata a wanan tafiyan don itace ta koma a matsayin kawata aminiyata badon ita ba bansan ya zan kasace ba a wanan tafiyan mai rikitarwa a gareni.
Hannu nakai na share hawayen na kallo Al,amin daya zuba min ido ina fadin Al,amin zo yaron yako zo don kamar bai manta dani ba nan uwar ta soma fadin.
Mu gamu munzo ace kunzo garin nan baku tako gidan mu ko yanzu paapa ya bugo min waya ai nazo yace ana nan an hadu don an daura maki aure a yau da aka hadu kowa na can gidansu suna nan ?
Ban fita bane amma ina da niyar zuwa ingaida ku ai ba zanzo banje na dubaku ba ai inga al,amin kuma mutumina na fada donta gane badonta zani ba .
Muna daki aka kawo mata abinci don bata fita inda anty da mommy fati suke ba sune a tsaye suke raba komai dadin shiri da mutanen arziki ke nan abinda naso su saudat su gane ke nan da suke maganan don me zan kara janta a jiki bayan abinda tayi min a baya ?
Bagasho zaman lafiya da fuska da mutunci yasa ta koma kamar yar uwar inna bace ita a wajen tunda itace tsaye ga komai da ake ci ana fita dashi don har samarin shiya in sun aiko tana daukan ta basu su sheda.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[10/23, 9:41 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊9️⃣9️⃣🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Taron mutanen dake shiga gidan sunawa Alh yakubu murna wasu su tambaya ina take don su gaishe ta saboda jimawa da sukayi basu samu shigowa ba duba yasa take tambayan daga ina hakane yau ?
Dayan dan uwan mijin nasu ke fadin munzo daurun auren Ali ne Ali Ali ta tambaya cikin maida duk hankalinta gareshi don bata kawo cewa shi ake nufi ba a lokacin .
Ali dai Aliyu mana gadanga na gidan nan kinsan da daniyar baiko mukazo sai kuma abin ya koma aure aka daura har da auren gaba daya.
Ance yarinyar a can take zaune lagos itama tana karatu wajen dan uwan mahaifinta can suka hadu dashi suka shirya aure.
Aliyu dai na gidan nan dan wajen hauwa kake magana yace a hjy bagashi ina maki bayani ba shifa aka daurawa aure muma munzone muyiwa Alh bayanin yadda abin ya juye a can ya zama aure.
Don kawunsa ya biya sadaki a take da aka yanke sai akaga me za a tsaya jira kuma tunda ga ladan aure a kasa shine aka daura dayani yanzu saura al,ada ya rage tunda anyi mai wuya.
Shike nan komai yakai karshe a gidan nan yaron nan ya tabbata dai shine shine dai shine shike nan kuma komai ya karasa cabe min ke nan kuma a gidan nan ?
Ban fahinceki ba hjy baka ganewa Musa yanzu ace har aure Aliyune gaba da yan uwansa yana karami baya baya a cikin yayyunshi amma ace kai Aliyu komai Aliyu muko me mukaiwa Alh ne haka wai ?
To ni nayi nan zancen nan ya soma fin karfina banda abinki hjy ai Allah shike tsara komai ga bayinsa yadda yake so.
Idan kince hakan da alama kinawa Allah shishigi a cikin lamarinsa ke nan yau ko uwa daya ta haifesu a ciki daya in Allah ya tashi fifitashi ai haka zaiwa yan uwa tazara irin haka ?
Ganin ta fita zancen shi ta soma jan gindi zuwa wajen da wayanta yake yasa ya fice daga dakin ya barta waya ta dauko ta soma kiran layin datake nema saida ya kusa katsewa aka daga.
Tana jin an daga ta soma fadin Laira tsakanina dake da malam Allah ya isa ashe duk abinda kike fada min malam yace akan aikin nan larai karya ne ?
Yau gashi don ki tabbatar wanda nake jiran mugun labari akanshi ya kara taushe diyana a gidan nan shekara nawa Hashim yaba yaron nan Aliyu ga haihuwa balle Auwal zuwa babbansu Habib wai amma yaron nan yayi aure yau ya bar yarana zaune suna tazuraci a soro ?
Nifa ban fahinci zamcen ki ba Naito wani yaro yayi aurene wai Aliyu dai da kikace nasa ido kwanan nan malam yace mugun abu zai sameshi to mugun abun ke nan dama auren da zaiyi din ?
Akan hakan ne dama kike ja muna Allah ya usa Naito da yamman nan ta jumma,a ?
Toki kara sai inda numfashin ki ya tsaya ga ja muna Allah ya isa ke wace irin azzalumace wai Naito har da aure kina bakin ciki dashi akan dan kishiyar ki don Allah ?
Allah yaga mugun aniyanki shiyasa ubangiji ya tauyeki ya mai dake zaune ya kuma mayar maki da diya irin yadda kike son ganin dan wasu ya koma tunda bai da alhakinki dashi da uwarsa.
Da kina da wayau da dabara Naito dakin rabu da yaron nan ko zaki samu sauki cikin lamarin ki saidai ina har yanzu baki bar zumunci da shedan ba tunda baki da rabo kila a wajen Allah
Barin gama da wanan nagabana Larai zan dawo gareku keda malam din don angani zaune za aimun hakan ku jira zuwana kanku kedashi.
Anci kudinki anci banza Naito kema a banza ai kika samu kudin dama wanda ya baki badai alhakinkine yaro na maki mutunci dako dan cikinki ba zai maki gata haka ba amma don rashon imani kice wai a halaka masu da ke wata itin mara imanin mace ce wai don Allah ?
Ko mayar dake haka da Allah yayi sanadin mugun abinda kikaje daukowa hakan bai isheki ishara ba Naito sai kin mutu kina yar wuta ta kashe wayan a bangarenta don kada hjy Naito din ta bata wani amsa kuma ?
Ke dawa haka hjy tun dazun muke nan tsaye muna jin duk abinda kike fada wai har yanzu mama ba zaki fita zancen yaron nan ba da uwarshi don Allah ?
Ina zata fita Sadiya tunda bata gama ganin mu a haka ba kome muka kama ya salwance mu bada laifi ba amma muke girban abinmu a hannun mu.
Tv ayi wa,azi mama waya ayi wa,azi mama a fili kafin gari ya waye sai kaji daga wani abinda zai kashema jiki ya tunatar dakai akwai ranan haduwa da ubangiji ka ranan gobe kiyama duk hakan bai isa ba mama ?
Idan Aliyu yayi aure kafin mu ai haka Allah ya kaddara muna lokavin yin mune bai yi ba tukun yaron nan bai barmu ba mama yana tare damu ko wani lokaci yana kokarin sauke hakkinshi na zumuci da Allah ya hadamu dashi ?
Amma kice ke duk hakan bai mako ba mama don Allah a kullum fa kara kusantan makwancin mu bawa keyi ba rage yawansa ba ko wanan ai abin mutum yabar shagala da duniyan nan ne ai ?
Wa,azi kukazo kuyi mun kome niba sakarai bace da hauwa zata shigo gidan nan tace saita fini da karfi da yaji a gidan nan ita da danta dama don hakan ta shigo so kuke in zauna ina kallon nama ja kare ?
Yaushe kuma mama ai nama ya dade da jan kare a gidan nan an dadewa kowa garin nan ya sanda yanzu Aliyu shine jigon gidan nan yanzu ?
Ya dan