Showing 273001 words to 276000 words out of 395027 words
Chapter 92 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
akace kin shigo dashi gidan nan kin kai dakin sariya ?
Nice na sayowa Amira kayan breakfast don fitinan dana fita dazun da safe na barta tanayi shine mukaje shago nayo mata sayayya .
Keda waye akace kunzo gidan nan din don na dawo ina jin wasu surutu barkatai da ban gane zancen ba ?
Tare da Oga Aliyune ya sameni a wajen ya rage min hanya shine yace na dauko duk abinda nake bukata na hado nazo dasu gida din.
To kinji ya fada yana kallon hajja yabi din dake zaune yana kuma kokarin daukan wayarshi yana neman wani abu ashe number Aliyu din yake nema saida naji yana fadin .
Yallabai Aliyu Abdallahi yakubu kano ya saka waya a hand free ta yadda kowa zaiji a falon ya amsa da officer barka da wuni an wuni lafiya ?
Lafiya kalau yallabai suka dan gaisa ya soma fadin na dawo gida ake fada min kokarin da kaiwa iyali nagode fa Allah ya kara girma da wadata.
Haba haba please kabar wanan zancen mana ka wuce nan a wajena din Allah ka daina ku manyane dole muyi maku ai ya daiyi dan maganan nan nasa da sauri sauri yana kaucewa zancen ya kashe waya.
Falon yayi tsit na lokaci guda wai don rashin kunya itace ta soma magana tana fadin yo na sani tunda za a iya akawo din daga gareka a boye min ?
Ke yabi ki shirya kayan ki wanan satin zaki koma kano idan kuma hakan bai maki ba saiki san mafita nagaji ke nagaji da wanan fitinan naki don Allah .
Dame kike son inji a duniyan nan ne wai duk inda kika biyu na daure saboda hjy data takura min a kanki amma kina ganin kamar kin daureni ban iya aikata komai a kanki yanzu .
Tunda kin hada kai da yan uwana ana zaluntana ta hanyar ki ke kin fi kowa sani a yanzu banda bandashi wallahi kuma ban maki karya don ban saba karya a rayuwana ba.
Tun aurenki yabi komai ya tsaya min a rayuwa wurun aikin da nake samu an daukeni daga wajen an mayar dani inda daga albashi sai albashi kadai ke shigo min a yanzu.
Tunda naji ya soma magana irin haka na mike tsam na bar falon zuwa dakina ina mai matukar jin tausayinshi a raina a lokacin naji yana fadin kudin da nayi aiki shi ake turowa amma ban taba nuna damuwana akan hakan ba sai ita da akecin abinda itace zata kawo mashi matsala kuma ?
Mugun tausayi ya ban sosai a lokacin watau karfin hali irin ta mazane kawai ke aiki a lokacin gareshi har ba a iya gane cewa yana cikin yanayi irin haka ashe ?
Karfin imanine da jajircewa irin ta maza ke sa idan sun shiga hali ba kowa ke gane hakan garesu ba sai wanda ya zama dole garesu zai gane.
Washegari da safe saida na gyaro daki na hada breakfast nagida duka tunda ga abin karyawa nan Allah ya hore sai son jiki zai hana ayi har amira na zuba mata a kulan zuwa school na koma daki nayi wanka bayan na fitone na soma neman layin baban mu a lokacin.
Muka gaisa yake fadin a,a maryam da zancen ki na kwana a raina sai gashi kin kirani da safen nan kuma ?
Wallahi baba dama zancen nan na jiya ne bayan mun gama waya sai kuma gashi ya kirani yace a dan dakata har wani lokaci yanzu za a turo da kudin gaba daya yace sai a sayo wasu kayan a turo dashi.
A,a maryamu ina ba takurawa bawan Allah nan kikayi ba kinsan fa yayi muna iya kokarinsa sosai kada mu tauyeshi mu hanashi biyan bukatanshi kuma saboda tamu bukatan daba karewa zaiyi ba ?
A,a baba ban takura mashi ba kudin nawane nashi yace milayan daya da dubu dari bakwaine cif maryam a turo baba zuwa jibin nan kaya zasu iso insha Allahu.
To ta naki account din zan tura ke nan nace eeh baba muka dan taba hira yana fada min yadda abubuwan ke cigaba a yanzu ya kara ban tausayi sosai a raina.
Sai naji kamar ancire min kaya lokacin da muka gama waya da baba yake fada min yanzun nan daya fita za a turo da kudin hakan yasa na mike na shirya a gurguje don in fita banson dogon zance a gidan nan yanzu don haka dole in boye sirina.
Bayan nagama shiri zan fito sai lokacin naji budan kofan antyna ba mamaki itace ta fito don yarta data fara karatu yanzu da badon haka ba sai yayi masu dadi suke fitowa daga dakin musanman ranan da paapa baida aikin safe idan yana dakinta sai sukai wani lokaci basu fito waje ba.
Amma idan yana wajen hajja yabi ita kan gaskiya tana fitowa da wuri zakajita kitchen tana kwaramniya da kayan kitchen din tana aikin abin karyawa don bata wasa da cikinta gaskiya.
Muka gaisa da ita nake fadin zan fita har take tambaya kona karyane gashi ta fito dora ko ruwan shayi asha.
Nace ban karya ba amma breakfast na nan na hada tun dazun don kada Amira ta makara tayi mamakin yadda na tashi nayi aikin da safe haka ni dai nayi mata sallama na barta zata shiga kitchen din ta duba nafice abina don haushi.
Koda na fita ban kira Oga Ali ba don kada ya fahinci zumudina a lokacin don ban sani bako ya tashi ko kuma tare da matarshi ya dawo wanan tafiyan naje izgilancin kiransa injawa kaina matsala kuma ?
Har na isa school don ban samu matsalan abin hawa ba a lokacin na shiga class ina duba takarduna har muka fara lectures duk abin yana raina.
Sai wajajen karfe dayan rana muka fito ina kunna waya ba,afi mintuna goma ba wayanshi nashigo min na dauka a cikin sallama sai naji ya amsa tare da fadin .
Dama nasan yanzu kun fito break ya karatu lafiya na bashi amsa yace yaso tun dazun ya kira yaji ko na samu magana da baba sai ya tuna ina class a lokacin.
Yanzun nan muka fito na kirashi ya turo da kudin na tsaya ina mashi bayani naso kiransa kafin in shiga lectures in fada mai sai nayi tunanen bai tashi daga barci ba ban kuma san ko tare da madam ka dawo ba wanab karon yasa naji tsoro ban kira ba .
Aikuwa dai tare muka dawo tamace tana son ganin wanan daughter din tawa data sace mata zuciyan miji lokaci guda haka a cikin dan kankanin lokacin da bata nan.
Tayi hakkuri don Allah tuba nakeyi abin uba da yarsane kawai a tsakanin mu ubane ke son ya taimakawa yarsa sai ki jira inkun hadu kiyi mata bayani da bakinki .
Ina aiki yanzu abinda nake so ki turawa yaron nan duka kudinshi yanzun nan ban son kwandalanshi ya saura a hannun ki I hope duka kudinsa aka turo dai ?
Nace insha Allah ko kwandala ba a rage ba har kudin riban da aka samu bai cire nasa ba dama haka sukeyi idan an turo yaga abinda aka samu sai ya turawa baba da nasa share din.
To ya bari yanzu haka har na tura aje can shagon baba din a duba a fara aiki zuwa jibi kuma mota zata tashi daga nan lagos zuwa kano da kayansu.
Dif nayi cikin wani irin jin nauyinsa da kunya kina jina ko ya fada na amsa da ehh daddy saida kunya ya rufeni don bansan lokacin da bakina ya fadi hakan bama.
Ok idan kin bashi kudin yayi wani korafi ki kirani inji kome zaice anjima idan mun hadu zan maki bayanin komai take care .
Nagode na sake fada cikin wani irin murya mai karya zuciyan mai saurarenta daddy nagode nagode nago,,,,,,
Kukane yazo min a lokacin da sauri cikin wani irin murya da sai a office nasanshi dashi ya soma fadin ke ke ,,,,
A cikin hausa stop that please ban son shirme don Allah duk yadda kukayi in sani you let me know insan abinda ake ciki naji ya kashe wayar tashi.
Nakai mintuna goma yasha biyar a zaune inda na idar da sallah bansan me zanyi ba kafin cikin karfin hali na dauko wayar tawa inawa Ozil transfer din kudinshi kai tsaye daga account dina.
A take kuma aka turo min da bank details a lokacin ajiyan zuciya na sauke na tattara kayana na mike zuwa aji bamu fito ba kuma sai hudu da rabi.
Ina fitowa daga haraban wajen mu na hango Ozil din a zaune saman motarshi a inda yake fakin tare da Okenah.
Na karaso wajensu don mu gaisa in tambayeshi ko yaga kudinshi irin kallon da yake min a lokacin kallone da yake nufin kwankwance mutum har na karaso ina fadin guy how far now ?
Okenah ya iya ban amsa da babban yarinya ya kike ne na fadama ai meram babbace yanzu tana aiki da company yasa take muna daukan kai a yanzu.
Ni zan fadi hakan Okenah don kuwa na sheda jiyan nan fa mukai magana a yau din nan ta nuna min gaskiyan abinda kuka fada min a kanta.
Ke nan hakana nufin kamar tasan da shirinmu dubasu nayi ina fadin wani shiri ke nan kuma ki tsaya ki saurareni please banyi wanan abin ba sai da shawarab abokaina maryam.
Na rasa hanyar da zaki dawo da hankalinki gareni a yanzu shiyasa suka ban wanan shawaran nafito maki da zance kudi don mun zata babu su a gurin ku sai gashi kin nuna min ku hausawa ba irin mu bane ashe ?
So dama yaudarana kuka so kuyi ke nan tun farko tarko kuka hada min dani da mahaifana ashe ?
Tabbas dan uwana yayi gaskiya dayayi kokarin rabani daku kudin ashe ba yadda na daukeku kuka daukeni ba kunyi amfanine da daman ku a kaina don ku yaudareni ko ?
Ozil ya soma magana motar oga ta zo gefe ta tsaya ya sauke glass hakan yasa na shedashi na dan dubesu kawai ban iya cewa komai ba a lokacin na juya na wuce zuwa wurin shi.
Ina isowa ya bude motar tashi nashiga muka bar wurin ina zama wani irin kukane yazo min lokaci guda bansan lokacin dana fashe da kukan takaici ba .
ZAINAB IDRIS MAKAWA[9/30, 9:32 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊 8️⃣3️⃣ 🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Duk da naji motan ta tsaya alaman alaman bata tafiya hakan baisa na dago daga yadda nake ina darzan kuka a kife ba.
Shima bai min magana ba illa idon daya zuba min hannusa dukka biyu saman sitiyari ya zubawa sarautan Allah yana bina da kallo a cikin mamaki da tashin hankalin da yake ji kasan zuciyarshi a lokacin.
Ya rasa dalilin wanan kukan mai tsuma zuciya da nakeyi haka kuma ya kasa tambayana ko meke faruwa nake kuka.
Munkai kusan mintuna shida a haka yayi karfin halin fadin idan kin gama mu tafi bansan me kikewa kuka haka ba duk daba son ji nakeyi a yanzu ba .
Tunda darajata a wajenki baikai ki fada min dalilinki na kuka haka ba so idan kin kare kukan saiki fada min mu tafi don banbin hanya haka dake kina kuka a dauko ko nasatoki ne.
Duk da abinda yake fada banyi shiru ba saidana kara kamar mintuna ukku a kai kafin na fara rage sautin kukan sannu a hankali.
Yana zaune kawai yayi shiru yana saurena kingama mu tafi ya tambaya yana dubana a cikin yanayin daure fuska sosai kallon tambaya ya sake jefo min ba tare da yayi magana ba.
Hakan yasa na saka hannayena biyu ina kokarin share wayen dake min ambaliya a fuskana har lokacin duk dana rage sheshekan kukan da nakeyi a lokacin.
Handkerchief ya miko min na dan kalloshi da sauri na karba saboda irin kallon da yake min na rai bace na mika hannu na karba ina goge fuskan a hankali .
Its Okey kuka ya isa hakana ya fada yana kokarin tayar da motarshi don mucigaba da tafiya hakan akayi saidai inayi ina dan shan majina alaman har yanzu da sauran kuka a raina.
Mun dan taba tafiya kadan a haka naji muryanshi ya soma fadin me yaron can ya fada maki ?
Shiru nayi na kasa maganan komai a lokacin don haka shima yasan ba sai samu amsan da take so ba a lokacin saidana kara goge fuska na dago gareshi ina fadin.
Daddy nagode a cikin muryan kuka da zancen bai fita dakyau a lokacin saboda muryata dake dan rawa ga abinda nake fadi din.
Nagode kwarai da taimakonka gareni banda abinda zan sakama dashi ina ma adduan fatan alheri da nasara a kullum cikin rayuwanka.
Yadda bai nuna dashi nakeyi ba a motan sai faman tuki da yakeyi da hannu daya lokacin nima ban kallo gefen da yake zaune ba don a yanzu nida zai saukeni yafi min saboda nauyi da kunya daya lulubeni nasa.
Tsayar da motar yayi ya fita ya karbo abu a wani shago ya dawo zama yayi lokacin dagashi sai shirt din maza fara mai long slip sai necktie daya daura a wuya.
Baki rabashi da diyan kabilu idan yayi wanan shigar dake fitarwa maza da ainihin surar jikinsu ko tsoho kake kayi wanan shigar takan fitar ma da kurciya da yanayin yarinta ne .
Balle matasan da suke jin kansu suna son wanan shigar mai cin kudi a garesu saida ya zauna ya bude ledan ruwan gorane kamfanin faro dan madaidaci ya miko min .
Inda ba gardama na mika hannu na karba daga hannunshi ina godiya na dan bude ina kafa kai na kurba kadan na rufe ledan sai lokacin na sauke ajiyan zuciya.
Yayiwa motar key muka cigaba da tafiya tambayan dazunne ya kara jefo min karo na ukku me sukai maki nace ?
Cikin karfin hali na iya furta basu min komai ba daddy but its a track to me sunyi setup ne a kaina idan na fada su juyani yadda sukaga dama tunda kudinsu yana hannuna.
Gutun murmushi ya dan saki ba tare da yai magana ba sai can yace zan kaiki gida ki huta yanzu anjima idan kin natsu zan kira muyi magana.
Ko kai ban samu dagawa ba balle amsa ji nake kamar a lokacinne farkon haduwan mu da wanan gan din ta tsiya na yarda da duk wanda yaki sharan masallaci zai share kasuwa.
Allah ya rufa min asiri bankai ga kasuwan ba balle in duka shara ubangijina Allah ya turo min wanda zaiyi sanadin kareni daga kaidin wa yan nan diyar arnan .
Ba karamin kariya Allah yayi min dasu ba lokacin da suke gaba da lalata min rayuwana wanda ni nake kallo a so da kauce da tausayi a wajena.
Ashe abin ba haka a wajensu kokarinsu shine Ozil yaja ra,ayina da kudi yadda zai rudeni ya samu ya daukeni zuwa kasan waje ko kuma idan idona din ua bude ba karamin riba zasuci dani ba kafin na gane hakan.
Da farko yaso nayi saurin yarda sai ya gane ina da kaifi akwai akidan yare da addini har lokacin a zuciyana da haka suketa amfani dabadaransu wajen nuna min kauna din.
Yazo ya fahinci abinda wuya gaakiya don dai shi ba wai haka zaiso ya yaudareni kawai ba inda bude ido in iya kalan barikancinsu don bussiness din ya