Showing 165001 words to 168000 words out of 395027 words

Chapter 56 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

fulanice ko something like that dai daga arewa right ?

Yes daga arewa take tazo nan ne kuma don kai akwai wasu company da takewa egent shine take son ta tallata maka ko kana ra,ayin hurda dasu.

No mutumina kasan ni bana abu haka kai tsaye duk da dai zancen ya fito daga gareka kasan kai ba irin mu bane komai zakayi kai tsaye kake abinka don fahinta meye suke dashi naji.

Ba a wajen nan ba zamu iya fita daga waje kadan muyi magana zance yake kamar yana ba wanan din umurni hakan Ok abinda kace .

Naga ya kira wasu sukazo suka danyi magana sai suka nuna mai sitting room dinsu tare suka jera ina bayansu yake fadin wai mutumina nifa nasan ba haka kake ba balle ince ka fara harka kai ma irin mu.

Be in your sense na fadama wanan din yar uwatace ita donshi nashige mata gaba a zanceb sorry bada niya na fada ba mutumina.

Zama sukayi nice nashigo da dan siriryar sallamana karshe suka amsa min shi mutumin ke fadin cleare naga alaman you are dsame family ko yanzu.

Kallona yayi cikin daure fuska yana fadin kiyi mai bayanin abinda kuke dashi din nan na soma bayani yana gyada kai nace mai zaka iya tambayanshi irin sauki da riban dake ciki son shima ya jona da wanan wajen.

A gurguje ya soma bashi amsa yana mai bayani har ya amshi tayi mu amma da sharadin cewa shifa ba irin wanan na farkon bane don dole za a zo a sameshi ayi duk abinda ya dace.

Yace kinsan ba daya muke ba mu sarakuna duk inda muke sai mun nuna aji shiko wanan shehin mune shine shugan mu na tunatar damu Allah idan mun kauce.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/27, 9:58 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

5️⃣2️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Zan iya cewa Rahaman ubangiji yanaga wanda yake shine idan rabbi yace saida kai sada kai din za ayi don ko a gabana ya bashi assuring din cewa zai saka hannu a company insha Allahu.

Daga nan ya mike yana fadin tashi muje banyi sanya ba na mike da sauri nabi bayansu naji sanda yake fadin tabbas a yanzu na yarda yar uwarkace shehi son inba dan uwa ba banga wanda zaka tsayawa irin hakan ba.

Jikina yayi sanyi da jin zancensu nan na kara yarda wanan mutumin ko akwai maganan da yake sonyi danine kada nayiwa kaina sakiya da babu ruwa barin ji abinda zai fada.

Wayana ya dan dauki tsuwa na duba Ozil ne a layi ina dauka yake fadin where are you mama girl mission done na fada kawai naji yayi wani dan ihu mai kara ikon Allah na fada can kasan zuciyana.

Sun dan jima suna magana da juna ina tsaye dan nisa dasu kafin ya juyo gareni yana fadin muje ko saiki dauka tare nake dashi dama saida muka fito wajen ya dan sauke ajiyan zuciya mai sauti yana fadin.

Tare dawa kikazo wajen nan lokaci guda ya rikide min ya koma ALEY ZAKI GWARZO yadda naga ya juyene yasa gabana faduwa ban san lokacin dana bude baki nace dashi.

Nida driver company daya kawoni nida Linda amma yan company suna wajen suma don a tare muke dasu dama duk inda zamu.

Good zaki jirasu ne ko zaki bini in saukeki don ni wanan wajen ba wajen zuwana bane ko yanzu dalili ya kawo har kika ganni a nan din ?

Ba matsala tunda nagama abinda ya kawoni na fada a cikin karfi halin dakewa ina ina hade rai yadda yayi din.

No idan kina tsorona karna sace ki zaki iya jiran wanda ya kawoki ku tafi tare ni zan tafi bayan shi kawai nabi bace komai ba don magana idan ya fito ba mai dadi zan fada ba a lokacin ya bude motar muka shiga saidai.

Muna fita daga get din wajen ya hau titi naji ya soma fadin you are very stupid idiot up you kinsan irin hatsarin da kikai kokarin jefa kanki kuwa a nan din.

Kin kuwa san waye AAJ din nan da kikazo gani shi din dan iskan yaroneshi baida tarbiya ki dubi kanki don Allah yadda kikai shiga takar diyar arna dake ?

Kina yar musulmai zakiyi wanan shigar ki fito haka a cikin wa yan nan watsarsun mutane da duniya yake rudansu koda baki da makwabi ai ki tuna da akwai Allah yana ganin ki.

Idanu na zaro a tsorace sannan bakina yana rawa nace saukin abin Allah ke hisabi wa bayinsa ba mutum dan uwansa ba.

Kada ka zargeni kan abinda baka sheda ba don kawai ka ganni a nan ka dauka bansan abinda nakeyi ba ?

Ina fadan hakan na kawar da kaina zuwa windon motar ina kallon yadda garin yai duhu sai hasken fitilun wutan nefa da sukaiwa garin kawanya suka koma kamae taurari a kasa a lokacin don ni ba gwaunar fitan dare bace dama.

Ashe yana kallona a cikin maki lokacin saida na dan juyo kadan na ganshi nayi kasa da kaina naji ya dan karkato i zuwa gareni cikin gaggawa na dan ja baya inda a fusace ya soma fadin.

Tare da nunani da yatsa ke ni zaki rainawa hankali ashe haka kike ban sani ba no wonder kika iya shigowa wurin nan haka kai tsaye ba tare da tunanen komai zai iya faruwa dake ba ?

Gaskiya iyayyen ki sunyi sakaci da suka barki a wanan mugun gari haka kina abinda kikaga dama ba tare da kinsan ciwon kanki ba ?

Gashi har kina kasadan neman jefa rayuwanki a cikin hatsari haka wanan waje na yan iskan tantiraine wa yanda suka zabi duniyansu bisa ga lahira ke akwai wani da kika gani da shiga ta arziki a wajen nan ?

Idonsa sun canja zuwa tsantsar bacin rai yake maganan haka nima a lokacin domin sun daga min hankali ta yaya haka kawai zai zargi iyayyena da basu san hawa ba basu san sauka ba a rayuwana.

Don haka na runtse idanuna na bude ina jin wani bacin rai da tukuburin zuciya a lokaci nace dakata malam ka daina yaba min magana haka kamar yar cikinka kasanine koka san a inda nafito da zaka nemi yarfawa iyayyena bakar magana haka dani ?

Cike da mamaki saida yaja wani burki motar ta bada dan kara a saman titi da har yasa naji tsoro a zatona ko hatsarine zamuyi lokacin.

Cike da mamaki har lokacin yace what ashe haka kike dama maryam baki da kunya fiye da yadda na zata ?

Kanki daya kuwa kinsan nauyin hatsarin da kike jefa kanki a ciki kuwa a wanan yaudaran da mutanen nan suka sakakiyi masu suna cin riba dake ?

A fusace na juyo nace dashi kaina goma malam baka san da mara hankali kake ba ashe ?

Haka kawai daga taimako zaka daukoni ka fara tuhumata babu kyakkyawan bincike haka kawai daga ganin mutum saika jefa mashi zargi rayuwanka malam ko nawa ?

Aiki kuma nasan hatsarinsa amma dole inyi hakan don kare mutuncin kaina dana iyayyena ko bayan hakan da nakeyi binciken ka ya nuna maka ina wani abin assha bayan wanan ?

Aiki kuma nina zabi zanyi hakan ba wanda ya turssa min yinsa ina kuma yine don kariya a kaina nafika sanin zafin kaina dana iyayyena malam .

Kamar yadda kace ina jefa kaina a hatsari nagodewa Allah da yake ban kariyansa ba gashi yanzu ya turoka ka taimakeni ba.

Don haka ina ganin wanan damuwatace ba damuwanka ba malam ka taimakeni fine nagode amma baka dinga zargina akan abinda baka sani ba.

Yana zaune ya kasa furta komai a lokacin sai tukin motan da yakeyi wanda kallo daya zakiyi mai ki gane jikinshi yayi sanyi sosai lokacin.

Mun dan taba tafiya a daidai round din mu nake fadin saukeni a nan malam yi yayi kamar bai jini ba yacigaba da tukin motarshi a hankali har zuwa bakin shagon maman bumi da ranan ya sauke mu a wajen nida Amira yana fadin ina nan kikace gidanku yake nasan ko inane ma baku da nisa da wajen nan take care of your self na fita bance dashi komai ba saidai a kasan zuciyana na furta godiya gareshi da Allah ya nuna min na fito lafiya wanan wajen.

Ni kaina nasan wajen da naje ranan wajene na musanman don shakawatawa da jin dadin duniya irin wajen sam bai dace da duk wani dan kirki a ganshi a wajen ba don ga shaye shaye iri iri da akeyi masu caca nayi masu latsa mata sunayi.

Toshi ma meya kaisa wajen shida kewa kanshi kirarin shi dan arzikine yaya na ganshi a wajen kaina naba amsa dana tuno da cewan da yayi akwai abinda ya kawoshi har naganshi wajen.

Ina tsaye ina jiran abin hawa na karasa unguwar mu tare da tunanen rashin nemana da Ozil baiyi ba kamar yadda muka tsara sai naji kiranshi a lokacin a cikin wayata.

Na dauka a fusace hannuna yana tare wani dan achaba da nagani tafe don ban yarda in shiga mota da daren nan in fada hannun bata gari.

Mai achaban ya tsaya na tattara rigana na hau ina fada mai inda zani ya halba saman titi murya Ozil ne keta tambayana where are you meiram on my way home na bashi amsa na kashe wayan.

Har bakin layin mu mai mashin din ya ajeni na zaro dubu daya daga jakkata na mika mai yana fadin ga canji nace yaje dashi kawai na juya zuwa wajen mu.

Da yake anty tasan da fitana sai bata rufe kofan ba tabar min a bude tana zaune a falo ita kadai tasawa kanta kallon tv dole ranan nashiga.

Saida ta mike tsaye tana daga hannaye take fadin thank god you are back serve insha Allahu na fada na juya inawa gidan key.

Itama bata tsaya ba muka kashe kayan kallon kowa ya nufi dakinshi Allah sarki shiyasa wani lokaci iyayyen mu maza suke zargin uwaye mata akan yayan su don duk abinda diya zatayi kusan uwa tasanda abin.

Yanzu ga antyna da ita kadai tasan ga inda naje koshi dolene tunda fitan ya kama da darene ranan ba abinda zan iya dole na fada mata tsarin nawa taso hanawa amma na nuna mata ba komai ta yarda gashi kuma na samu itama ta kasa sukunin rashin dawowana din a lokacin.

Ban yarda na tsaya dogon bayani ba koda take tambayana da yaya anyi nasara kuwa ga tafiyan na bata amsa da insha Allah nashige dakina.

Haka kawai barci ya kauracewa idona a ranan don abubuwan daya farune ya tsaya min a raina lokacin tayaya zai daukeni yar iska kowani abu haka na rashin kamun kai daga gani kawai yayi min fahintar da bashi ba ?

Wanan abin yai matukar bata min rai sosai a lokacin shine har ya hanani barci a ranan sai wajajen asubahi na samu barci ya daukeni.

Ya kasance weekend don haka washegari na samu nayi ramuwar barcin da ban samu ba a daren tare da kashe wayana don kada a dameni.

Bayan na tashi nayi wanka na gyara jikina kitchen na shiga don in samu abinda zanci abin haushi abin takaici na samu dukkansu biyun ba wanda ya girka wani abinda za aci a gidan .

Nasan suyi hakanne kasancewana a gidan don ina girkawa haushine ya kamani na juya zuwa daki na dauko wayata nafito muryan Amira naji na tsaya nasa mata kira tana fitowa na rike mata hannu muka fice daga gidan.

Gidan maman Teema muka shiga wanda nayi lokaci mai dan tsawi bata ganni ba sai a ranan bayan mun gaisa tana min sherin cewa ashe dole ba zata ganni ba na samu lafiya haka naga yadda na koma kuwa gaba daya na canza nayi kyau sosai.

Murmushi nayi mata abinda ban tabayi mata ba shi nayi a ranan nake tambayan ta abinci don ban karya ba har lokacin.

Maryam ga abinci nan mu har na rana ai mun gama har salim ya fita kaiwa mahaifinsu nashi a shago akwai kuma sauran abin karin safe duk a kitchen din tashe ki duba wanda yayi maki ki diba kuci .

Kunun gyada sukayi a matsayin abin karyawansu na safe na zuba muna a cup biyu sai tuwon shimkafa a cikin leda mai zafi dake tururi na zuba muna a plate biyu cikin dauki na dawo falonta na zauna muna ci muna hira jefi jefi da ita.

Na fahinci ba shiri tsakaninta da antyna don ko yaushe sai kokarin sukanta a gabana take kokarin yi ina kaucewa hakan don ni a wajena gaskiya banda kamar anty na a rayuwana.

Don itace silar zamana haka a yanzu kuma ba zance dole sai ta gyara halinta a kaina ba don da abinta naganta dashi kuma zan barta din wanda hakan kuma sakacine na uwa data samu tun farkon tarbiyanta da ba ai mata ba shiyasa mutanen mu na Arewa suke gudun yar mace dan akasari zaki samesu ba tarbiya a tare dasu.

Wanan be dameni ba tunda nagama fahintar ta bata da mugun nufi a kaina dan matsalan da aka samu a bayama a tsakanin mu kaddarace da rudin shedan yakawo hakan a tsakanin ana son ka dinga dubawa mutum kuskurensa baka dauka hakan kiyayya bane.

Don na koyi hakan tun a zamana gida a gaban mama wanda bayan sheri da kafi da cin mutuncin da mama zatayi min abinta ni kadai ke cinsa duk da sai ya kusa lalacewa zata dauko ta ban haka zan daure in karba da murna inyi amfani dashi.

Wanan yasa a yanzu ban dauki hakan akan komai ba kishin mijintane a yadda zancen yazo mata ya jawo hakan lokacin tsakanin mu wanda har gobe kuma tana nadaman yin hakan a zuciyarta.

Mun kai wani lokaci a gidan sai bayan sallah la,asar muka fito zuwa gidan mu a falo muka samesu su dukka har Paapa yana gida lokacin.

Tun shigowan mu naji hajja yabi na fadi a gyatsire to gasu ai sun dawo ka damu ina suka shiga tun dazun nasan akwaita kila na gaidashi da dawowa bai amsa ba sai tambayan da yakeyi ina kukaje tun dazunne wai ?

Nan gidan maman Teema nashiga ai yanzuma kuna cikin unguwar nan ashe duk neman nan da muke maku ?

Muna gidan maman Teema ai ba ko ina naje ba tsuki antyna ta dan ja tana fadin na fada mashi kina cikin unguwan nan baki tafi ko ina ba don baki fada min zaku fita ba yau.

Ban kawo komai ba a raina sai zancen inda naje jiyane yazo min ko watakila har Paapa ya samu labari ko shine yake tambayana din.

Sai naji muryan antyna tana fadin wai sayayyan taron da za ayine yake son kije kasuwa ki sayo abinda ya dace don kin fimu iya shopping.

A fili na sauke ajiyan zuciya don jin dalilin neman nawa da sukeyi naji Paapa na fadin ai yanzu kam yamma tayi saidai a bari gobe idan Allah ya kaimu taje.

Kasan gobe sunday ba kowa bane ke fitowa akasari garin nan ranan sunday basu bude shagunansu a ranan monday kuma school zata fita.

Yanzu yaya za ayi ya fada yana tambayana baida matsala uncle ayi list din sai gobe in fara fita in rage sayowa akwai dan wani mini market a can unguwar sukan fito a ranan don hausawa sukafi yawa a wajen.

Gata nan ya nuna antyna datayi maki list din komai da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login