Showing 210001 words to 213000 words out of 395027 words
Chapter 71 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
fito falo banjin anty taba uwar amsa don ina zuwa take fadin.
Kingani mena fada maki yanzu ki duba danta ta dauko inba tare suke munafuncisu ba meya kaita daukan dan kishiyanki ?
Ke munafukace maryam kinwa yata juju keda iyayyennki har bata yarda taga laifinki daga ita har mijinta dama wanan da tazo ta zauna masu kerere a gida da wani damin duwawunta kamar baho ?
Yafi na yarkine yasa kike zagi da mamaki na juyo ina kallonta tace bari maryam nagane wanan tsohuwar ba tsohuwar arziki bace wallahi.
A nan fada ya barke sosai da tonon asiri da cinzarafi da kazafi kowa nawa juna nan naga rashin hankali a ranan inda uwa ta zo ta zauna donta shigawa diyanta kishi wani abu sai kabila kinji.
Sai ince wanan fadan ya jawo tafiyan mommy gida bata shirya ba don Paapa ya rufe ido yace saita bar maigida ta koma gidanta tunda ya sai mata gida ai.
Shiya biya judin gidan da suke zaune a cikin sa ihun da hajja yabi ta saka ya dan firgitani wai duk a cikin kishi take fadin andai ji kunya wallahi ba zancen hura hanci yanzu gareta.
Sosai antyna ta ban tausayi na fada maku ita macece da bata son hayaniya asalima fada sam bata iyashi ba hakan yasa ta kama kuka a lokacin.
Saukin abin uncle na matukar sonta gaskiya kukan da takeyi din yasa ya juya kan yabi di kuma da fada yana fadin meye haka kikeyi kuma ?
Ke nafa gaji da wanan iskancin haka tunda kika zo gidan nan gaba daya gidan nan ya barkace min har ban kaunan in fita in dawo gidan nan wallahi.
Aina sani sabodani ba da dana nasani ba sai ka fada ba dakina na nufa dama nasani da ban shiga ba don dakin da zarnin bowli ya tareni daga shigana saida kyar na samu na hado abinda zan dauka har laptop dina na fito dashi zuwa falo .
Har kuma lokacin tsohuwar na bisa bakinta hakama yabi na zauna z cikin takaici da bakin ciki nikan wanan wani irin rayuwane don Allah ?
Dan tsukin da najane yasa antyna fadin dauko min magani saman drower dina na mike na dauko mata ta hade panadol ne nasan hayaniyan ko kukan da tayi yasa kanta ciwo.
Saida kyat tsohuwar ta samu ta koma daki nasan koshi fitsarine ya tayar da ita daga falon muka samu shakat don yabi ta koma daki ta barta.
Abin ma ya koma ban dariya na,urata na hada ga wuta na dawo na zauna nan take tambayana yaushe nayi gyara haka gyarab yai min kyau sosai ya fito dani da kyau.
Nabude mata kaina da akai min wani kitson ghana na natural hair duk ta rude tana fadin yayi kyau sosai wallahi nace zan kai amira wani sati a gyara mata kanta itama.
Nan dai na dinga janta da hira don kawai inga ta washe ta dan sake din kuwa tundai da nake mata hiran office da abinda ya faru ranan da ogan mu.
Nan take tambayana waye mai wajen namune nace wallahi ban sani ba ban ma taba kula da intambayi hakan wajen wani ba.
Maryam ta fada hakan yasa na juya ina kallonta tace abinda Paapa yayi min yayi daidai ke nan don Allah don rashi ya baci har saiya tona asiein abinda ke tsakanin mu ?
Nima banji dadi ba nace tayi hakkuri bacin ran abinda mommy tayine yasa ya fadi hakan gareta taja tsuki tana fadin.
Na fadawa mum tun safe ta bari tun fitanki ake haka tsakaninta da yabi yanzu kinji abinda take fada ai na dai dan bata shawara a wajen shirun da tayine yasa na soma diban wayana ina duba sakon da sukace sun turo min din.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/9, 10:13 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊6️⃣5️⃣🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Tun bayan gama wayan nan ya hada hanayeshi wuri daya ya dafe gonshin shi da dungun hannun ya fada tunane kafin ya dago idanuwanshi da sukai mashi ja lokaci guda.
Har lokacin jikinshi yake ji wani iri kuma ba zaice ga dalilin hakan ba saidai yana da yakine abinda hancinshi ya shako mashine mafarin saukar mai da hakan daga farko.
Sulaiman ya turo office din ya shigo a karo na barkatai yana fadin antura Sir sai lokacin ya sauke hannayen a yadda suke yana mai dago kai ya subi sulaiman din yace cikin sauke ajiyan zuciya.
Ka tura yadda zata fahinta screen short din pepper nayi na tura mata da komai ok good yanzu saika jira muji zata gano muna wani abu a cikon hakan ?
Sir ina ganin wanan aikin yafi karfin maryam fa a yanzu haka kake gani ko ya tareshi da fadan haka yarinya data iya gano wanan abinda aka baibaiye ta baya itace kake ganin ba zata iya fitar da wanan ba ?
Wai naga wanan din shi Bayo yafisu kwarewa wajen tsiya is hard a iya gano sallonsa sai ka bari muga talent nata a nan kuma ?
Gaskiyane amma matukarko ta gane wani abu gaakiya yarinyar nan ko ta dabance ita lokacin da nake fadama abinda na hango a tattare da rayuwanta baka dauka kawai don nakai kaina kusa da ita bane na kawo dabaran haka ?
Yanzu ai na gama fahintar komai sir meka fahinta No a bar zancen sir ba yanzu zan fada ba sai lokacin ya tabe baki yana lumshe idonshi.
Irin yaran nan dake tattare da baiwa a kasan nan yawa garesu amma lalacewan gwaunatin mu da kowa yahau kashin ya sani yasa dan tallaka masu baiwa gararanba a wahalce cikin kasa.
Wanda wani lokaci baiwan nasu da iyawa kesa za aga suna wasu abubuwan a dauka lalacewane suka dauko yi kaga ashe taimakon makusanta da gwaunati suke bukata a daidai lokacin da duk aka kula yaro ya fara kirniya kada a tsaya saka mai baki kamata yayi a fahinci meye baiwanshi tukunna ?
Sulaiman kaje ka fito da mota ka kaini gida ina son inje indan huta a yanzu ka tsaya sai zuba wani shirne da kakeyi mu dai Allah ya gyara kawai ya gyara ya kara gyarawa amma kana wani zancen gwaunati a yanzu.
Gwanatin su waye gwaunatin da kansu kawai sai yayansu da yan barandansu wanda basu ba diyansu tarbiyan tsatsan hausa ba irin na dan arewa tun yaro na karami ya gano meye dogaro da kai sai zalla jin dadi da shagwaba ta ya za ayi kasa ya gyaru yanzu zukatan daba Allah da annabinsa sun koma jagoran mutane ?
Allah ya kyauta ya fada ya juya ya wuce ya barshi nan a zaune yana mai jin zafin yadda kasa ta koma bisa jagorancin yan arewa amma ba a iya taimakon tallaka yaje gaba kamar ba wa yanda suke koyi da sunnan Annabi ba kowa ya samu a yanzu kanshi ya sani bai iya aikata alherin da zai bishi har makwancinsa ya tarar da alherinsa gaban ubangiji.
Wayan sulaiman daya shigo maine yasa ya mike ya kwashi kayanshi yana rufe office din don gaba daya shi a rayuwanshi bai yarda da wani da zai barwa key din dukiyan daba tashi bace shi kadai gamayya ne tsakaninshi da aminnanshi yazo yana juyasu a nan kasanshi.
Yarda da amincewa yasa suka zabeshi a matsayin wanda zai jagoranci na wanan wajen don haka yake cikin taka tsatsan da dukiyan amana a wajenshi.
Ko a gidan tunda ya shigo suka gaisa da Abdul ya hau sama bai sauko ba wanka yayi tare da debe tufafin da yake jin shine ya sato mai kamshin wanan turaren mai birkita kwakwalwan mutum.
Annabi yayi gaskiya daya haramtawa mata saka turare haka a jikinsu zuwa wajen daba muharamansu ba yau shi shedan hakanne a wajensa don shedan dake shiga cikin hakan irin yadda yake kokarin yi mashi a yanzu.
Wankan da yayi dabarab tayi don yanzu banda tashi kamshin baijin wanan kamshin kuma saidai mutuwan jiki da kasala daya sauka mai kawai.
Gado ya haye ya jawo laptop dinshi ya shiga bin bayanan baya da suka shude yana tarawa a waje daya tare da bin kwakwafin komai daya danganci ma,aikatan.
Har ace yarinyar dake matsayin gwaji a waje tazo ta walwale matsalan da accountocishi suka kasa gano hakan meye amfanin aiki dasu a yanzu ?
Sallah da aka kira ya mike ya shiga yayi alwala ya fito suka hade da Abdul dake zaton ko barci yake a lokacin yazo tayar dashi don ko abinci bai nema ba dama kusan ko yaushe shi mutum ne da bai wani damu da cin abinci ba sosai.
Okey ka zata ina kwancene ya fada Abdul din ya dan rusunna cikin ladabi yana fadin naga an kira sallah banji motsin ka ba ?
Tare suka jera suka fita zuwa masalacin da suke sallah a nan gaban gidan wanda sai tsararun mutanene ke halarta suko ako yaushe suna kokarin gani sun shiga jam,i a cikin taro.
Ina zaune ina aikin har wajajen karfe daya gidan namu yayi tsit kowa ya kama gabanshi a lokacin nan uncle ya dawo ya sameni a gaban computer ina aikina.
Na gaidashi ya shige ciki ya barni a wajen ban gane komai ba har kusan karshe saina so ganewa sai kuma in rikice in danbale aikin ya dawo kasa.
Ina zancen in kwantane na gano bakin zaren inda nagane dabaran da sukayi wajen kwasan makudan kudi masu yawa da saida na tsorota.
Bani na kwanta ba sai wajajen karfe ukku na dare na samu na dan mike a nan saman kushin da niyar hutawa ashe barci ya daukeni hakan har da mafalkina na ban tsoro wasu mutane ukku da wani jan kaya sun sakoni gaba suna gab da kamanine ina Ayatul kursiyu na rintse idona.
Naji muryan hajja yabi a kaina tana fadin ke maryam tashi asuba ya kusa shigewa kada ki makara sai kuma naji rufe gidan uncle daya nufi masallaci sallah asubah.
Da sauri na mike zuwa sallah kamar yadda na zata haka na sama a dakin mommy a kwace tana nasari kamar dakon zai tashi sai zarnin fitsari da bashi dake tashi a dakin.
Allah ya gani ba zan iya shiga wanan bayin na sauke farali ba hakan yasa na fito nashiga dakin antyna itama tana kwance na wuce zuwa bayi har wanka nayi na dauro alwala na fito.
Na tayar da ita niko ta tashi a lokacin ban dai sani ba don falo na dawo nayi sallah na kwanta a nan falo din inda na kwana .
Motsin aiki hajja yabi a kitchen ya tayar dani daga barci don dana makara fita ranan dole na mike naje dakin har lokacin banjin wanan tsobuwar ta tashi don sallah.
Da farko ina tayar da ita saita dinga hawana da fada wai ita aiba musulma bace sai in musuluntar da ita ni zan gwada mata sallah kaf gidan mu ba wanda ya kaita sanin ibada.
Tun wanan ranan ban kara gigin tayar da ita ko yi mata wani katsalandan ba daya shafi rayuwanta nake kiyayye kaina da ita.
Karan rufe wardrobe dina ya dan sakata motsawa tana fadin abi wee,reni kinyi haukane baki ganin mutum a kwancene ?
Na rasa kayan da zan saka don wanan dan matsalan dole wani dogon rigana na adire na dauko na saka rigan gashi nan dai dinkinsa anyi ba ayi ba ni a wajena shine mai mutunci.
Na shiya na fito nayi sallama da mutanen gida na fita a kofa muka hade da uncle da zai shigo gidan shima nasan ya dawo ya shirya ya fitane na tsaya ina gaidashi ya amsa da maryan lafiya kika kwana a falo ?
Kasa nayi da kaina ina fadin aiki nayi barci ya daukeni a wajen saina dawo yayi min ya shige gida ni kuma na tafi bansha wahala wajen neman abin hawa ba ranan na isa a cikin lokaci.
Mun kaisa da wanan dan yarbawa din na shige office shikan muna gaisawa iya gaisuwane kawai tsakanina dashi.
Yaso jana a jiki naki yarda hakan ya shiga tsakanin mu don ina gudun abinda zaija min barnan suna a wajen wasu.
Bayan haka alkawari na daukarwa kaina da ban tsayawa shirmen banzan soyayya akan namiji tun lokacin da Bello ya bata min lokaci a rayuwana.
Nayi wanan alkawarin babban burina da muradi shine in samu ilimin da zan zama wani abu da zan iya tallafawa iyayyena da yan uwana don na fahinci sunan maza da mata sukayiwa lakani iri iri a cikin duniya.
Wanan kuma ba karya bane da ace ina da ra,ayin hakan da tuni linda ta bata min rayuwana a wanan garin saita fahinci in tana shirmen hiranta fuska nake daurewa ko in canza waje.
Taso shammatana da farko ta koya min harkan bin maza ko shaye shaye na fito mata a mutum kuma yar musulma na nuna mata ina da addini a tare dani.
Wanan yasa dole ta barni tana abinta tunda su wajensu ba abin kunya bane wanan duk da akwai iyayyen dake nuna kyaman hakan a cikinsu kuma suna kabila din amma zuciyansu nada kyamar hakan.
Wa , yan nan dalilan yasa nake yawan kama kaina a cikin kabilun nan balle yadda nake din nan shar dani don ko wani irin shiga nayi zai karbi jikina ayaba.
Don dan tsayin da nake dashi da haske kowa ya ganni zai so kasancewa hakan ba wai yabon kai ba ni kaina nasan ko banzo sahun kyawawan farko ba to ban wuce na biyu.
Kara nazarin wanan bayanin nakeyi inda na kara warware abin daga inda ya dauko mafari tun kusan shekara biyu da rabi ana masu wanan zamba basu ganewa.
Waya ke dan haske daga gefe daya hakan yasa na kula da ana kiran layina lokacin na dauko na duba Oga sulaiman ne yayi min kiran.
Na daga naji yana fadin in karaso office din oga mu hadu na amsa da ok na kashe wayan na tsaya na tattara kayana kaf na mike zuwa office din.
Idan ban kula da kaina haka ina kiyayyewa lagos ce yanzune za a tsunci mutum tsirara a titi an gama dashi wanan ba bakon abu bane su sakarwa mutum juju ya haukace lokaci guda.
Nasan sherinsu yara kanana sunyi sheri balle manya ban mantawa a inda na gama school wani shekara akai wa wata yarinya sheri don taki shiga cult dinsu.
A lokacin ba don ina da rabon karatu ba da wanan sanadin yasa na daina karatu don na tsorace matuka da jin wanan abin.
Allah ya taimaka antyna yar garice ta zauna ta ban labarinsu kaf da yadda suke iya ha,intan mutum wanan yasa na saba da rashin cin komai daga wani sai na dawo gida nakan samu sukunin cin abinci.
Yanzune indai lagos ne za a gama dakai wajen tsafi iri iri har wanda mutum bai taba jiba a lagos zaiji kan tsafi da suna iri iri ban taba yarda cikin ikon ubangijina ba ban fita gida babu addu,an neman tsari daga Allah ba.
Na tura kofa na shiga suna zaune suna magana naso in gaidasu wanan me zafin ran ke fadin wani irin waya garekine an maki two miscall baki dauki waya ba ?
Wata na duba shima ya kalla daga inda yake yace no wander kina amfani da local waya irinta yara har akira mutum bai ji ba.
Zauna maryam Sulaiman ya fada na zauna din a cikin zafin rai da jin dacin maganan da wanan yake fadi a kaina.
Amm,maryam kinga sakon mu jiya a wayan ki yes sir nagani har nayi