Showing 309001 words to 312000 words out of 395027 words
Chapter 104 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
haka yake ba gwaggo.
Koma meye aje dai bashi zai bada kudin motarsu ba yace yanzu zan aikawa ita hadiza dashi lawal idan ya shigo kada a girshesu da zancen.
A haka suka aje maganan an fadawa kowa shi baba lawal ne yaso ya nuna ba za aje ba din gwaggo ta fito tana fada tace lawal gara kuje ku gano muna gaskiyan zancen nan don Allah.
Ni surutun nan ya ishemi haka ikko dai cikin kasan nan ne ba wata kasa ba da za ace sai an shiryawa zuwanta anyi gurizi ance kwana biyu ma sai aje a dawo .
To gwaggo ba akin ta manya idan anje din zaifi komai dadi ko banza shi Faruq zaisan yar tana da gata da mutunci ya kara rike muna ita da amana.
Lawal har kana wani zancen riko kuma a yanzu shekaran yar nan nawa yau fa yar nan tacin ma ashirim ina shekaran rasuwan malam aka haifeta dai koda malam ya kare tana a zanin goyon ta lokaci ?
Ai kawai a dawo da ita gida azo a wanketa ko sadakane a bada ita ga wanda ya dace yafi wanan zaman na zargi a kanta.
Gwaggo adai bari muje din mu dawo in aje anga ba haka bane aiko zancen ba zamuyi ba kada suga mun raina masu haka dai aka aje maganan.
Hankalin baban mu bai kwanta ba ni dai ya kira yana tambayana cewa na tabbatar da karatuna yana tafiya daidai na bashi amsa da yanzu haka baba ai yan watani ya rage min ma in kammala insha Allahu .
Sai naji kamar yayi ajiyan zuciya yana fadin Allah yayi maki albarka maryam ubangiji Allah ya tsare ya kare muna ke duniya da lahira Allahuma Amin na amsa kasa kasa ga addu,anshi.
Mota ta musanman baba ya dauka shata da zai kaisu har lagos ya dawo dasu kano a cikin kwana biyu wanan ya kara sa mazan kara tunane akan tafiyan.
Inda baba bala ya samu baban mu shago don suyi magana ta zumunci tsakanin dan uwa da dan uwa.
Baba ya tabbatar mai da shima abindake ranshi nayifi son ai muna girshi aje din haka zaisa a tabbatar da gaskiyan da ake son sani a kai din baba bala ya gamsu sosai da baba ya fahinci shima yana a cikin damuwa da abinda ake fada din kaina.
Nan ya koma fadin akwai tsiya da Rakiya idan zancen nan ba gaskiya bane yaya don ita ta zauna ta fadawa matan nan karya da gaskiya da sukaje gaida ita a satin can daya gabata shine suka dawo suna fadin labari ba dadi a cikin gida .
Yasa hankalin gwaggo tashi don tace hatta abincin gidanka yanzu daga Maryamu yake fitowa ko ruwan gidan ka itace ke biya baba ya amsa da Allah ya nufa ai fatane ta alheri tayiwa yarinyar bata sani ba ?
Saida darene malam sama makwacin su baba yasan da zasuyi tafiya inda baban mu da kanahi yazo ya rokeshi kan ya taka masu a wakilci su baba bala zuwa duba inda ake rikon yar wajenshi a can ikko.
Baiyi mussuba don kamar mahaifi yake a garesu yace Allah ya kaimu donshine suka cika mota daya suka kama hanya zuwa garin ikko din da sanyin yamma suka bar garin kano wajajen karfe hudu saura.
Kowa jin tafiyan yayi a bazata don ba asan da zasu tafi ba sai da tafiyan ya tashi haka kuma tsegumi da surutune ya taso a cikin dangi kowa da irin abinda yakw fada ankashe kunnuwa ana zaman jiran tsamanin dawowansu aji yadda zancen yake a can.
Karfe taran safe suna cikin garin Lagos din duk sun jikita ga tafiyan tunda dare aka raba ana tafiya driver yasan gari saidai bai san gida ba don haka yasan barikinmu da aka fada mashi sunje har bakin barikin namu.
Saidai bai san gidan ba don shine suka tsaya kwatance sai da kyat masu gadin get din suka bari suka shiga estates din namu nan aka fara tambaya gidan oga umar a cewansu.
Maman teema aka kira da tambaya yayi tambaya ana bincka don duk wanda aka tambaya sai yace ba barikin nan bane gaskiya.
Tana zuwa sukace Mairo ta nuna bata sani ba itama ana ta kwatance sai can tace wai woo maman Ayyo ko dai gidan Oga faruq officer suke nema gidan su maryam ?
Wata farar yarinya dake karatun jami,a a nan dogowa mai zubin fulani kwarai kuwa daga kano uncle dinta yake ai ?
Kofan gidan namu tayi gaba suna biye har zuwa kofan ta shiga dukan kofan don gidan yana rufe muna ciki muna barci a lokacin bamu tashi ba don ranan bamu fita school.
Dukan kofan naji yayi yawa yasa na taso dagani sai wando da rigan barci a jikina kaina banu ko hula sai zanin dana daura a sama zuwa kirjina.
Kofan na bude a hankali ina fadin who is that nocking door like this you wan break d door sha ?
Arba nayi da maman teema a tsaye take fadin ku fito gyare kowa ya tashi kuna ciki kuna hutawa bakine sukazo wai daga kano suna neman wani gida muna ganin kamar gidan nan suke nema ?
Dan lekawa nayi don inga ko suwaye din a lokacin baba bala da yaso kama da mahaifinmu na sheda don ya fito daga motar saboda gajiya yana mike kafanshi.
A daidai lokacin kuma antyna ta fito tana fadin waye a wajen maryam nace bakine daga kano tace kano su waye nace yan gidan mune anty ?
Cikin mamaki itama ta leko tana fadin ikon Allah yanzun nan suke tafe dama kinsan da zuwansune nace a,a wallahi daidai lokacin muka isa sunji abinda muke fada din muka soma masu sannu da zuwa a cikin murnan ganin su.
Duk na rude don murna da mamaki nice dai dinna iya taro mukai masu iso zuwa falon mu da yake gyara ba wani abin makusa a cikinsa sai faman wai matan keyi muka shiga daga ciki idonsu yana kaina suna kare min kallo a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[10/13, 10:04 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊9️⃣2️⃣🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Mairo kece haka wai gwaggo Lami ke fadan hakan tana zama dan murmushi na sake a fuskana a cikinsu na rasa wanda zan tunkara naji sanyi a raina saboda ganinsu da nayi a bazata kamar a mafarki .
Ruwa da drinks din da muka saka a fridge har anty na tambaya me za ayi dashi haka dana saka a cikin fridge din nace Amira mana ke sha da kuma wanda rabonshi ya haukai.
Sai gashi ashe rabon iyayyena ban sani ba nan take na shiga kitchen bayan mun gaisa na fara aikin abinci da yake gas ne ban dauki wani lokaci ba na hado abinda zasu karya dashi na kawo masu.
Tun bayan isowansu na kira wayan oga Aliyu ina sanar dashi isowansu a cikin mamaki yake tambaya lafiya kuwa sukazo ba tare da sanin kowa ba ?
Nace dashi ban sani ba ko wani abu sukazo yi nan suka zo ganina yace min yana tafe saida ya tambaya kosu nawane na fada mashi yawansu.
Har zan kashe waya yake tambaya maryam kodai aure zasuyi makine sukazo ?
Tambayan tashi taban dariya nace aure kamar wata yar tsanar wasan yara muka kama dariya yace gashi dai tafe banso hakan ba amma ba yadda na iya dole in kyale din yanzo su gaisa.
Naji dadin yadda antyna ta taresu kuma tanata yaba kirkina da halina a gabansu ban taba tsamanin jin hakan daga gareta ba duk shigowa nayi suna zaune dasu tana masu hira akainane.
Sai kallon juna da sukeyi suna musayan magana da ido a tsakaninsu itace ke fadin cewa ai maryam kila gida zata koma dan wani dan kano yanzu ya soma nemanta da aure.
Duk sunyi murnan jin hakan sosai har suke tambayan dan inane a kano tace gaskiya ba zata sani ba saidai ai kila yazo su gaisa dashi din.
Ko shine akace yana zuwa kai da kai wajen iyayyeta wanda shima kabilane baba bala ke tambayan hakan ga anty jifa sherim mama don Allah wai Oga Aliyu kabilane akace.
Ni dai sun tambayeni nayi murmushi kawai ban tsaya munyi mamakin jim cewa waiga gobe zasu juya su koma dama dai ganina sukazoyi tunda aka badani ba wanda ya taba zuwa ya dubani daga gida.
Haba dai aida baku wahal da kanku ba don Allah saiga kuma maman teema itama da abinci lafiyayye ta girko masu nan ta zauna tana ta yabona wanan abin yayi matukar dadi sosai yadda sukaji din.
Karfe biyar na yamma bayan sun hutane ya iso a cikin lafiyayyen motarshi tare da shiga irin ta diyan hausa da yai mashi matukar kyau sosai a jikinshi.
Antyne ta fada masu isowanshi aka shiga shiri suriki zaizo su gaisa ya shigo da sallama ya gurfana har kasa yana gaidasu.
Kamar yadda sukaiwa anty bayanin halakan mu dasu haka ta soma mashi bayani itama yana gyada kai a cikin gamsuwa da bayanin nata.
Baba Bala yake tambayanshi da ance kaima dan kanone wani shiya kake yace aunguwar kabo nake baba kabo dai kabo wani gida ya dan murmusa tare da fadin gidan Alh yakubu Audu mai glass yakubu mai glass na kwari yace na,am.
Kace kai dan gidanema baba Sama ya fada ya soma fadin aini kamar yaronshine nake don shike ban kaya a baya lokacin da nake sana,a.
Shiya taresu da fadin mahaifiyata ai yar unguwarsu maryam din ne ana gadon kaya gidan malam Innuwa mai almajirai .
Salati baba Lawal ya sa yace wai malam innuwa nasu malam hamza ke nan dai yace su din yayyun mahaifiyatace ai mahaifisu daya da ita.
Ya mike yana fadin zai koma yaushe zasu koma suna hada baki wajen fadin gobe insha Allahu daga inda gwaggo larai take tana fadin aikwabari mu huta wanan zama da mukasha.
Shi kuma Aliyun yace a,a baba a dai bari ku dam huta yanzu inkun kitsa sai a kaiku masauki ku dan huta an kama maku waje baida nisa da nan uguwar idan kun kintsa maryam zata kira azo a kaiku can din.
A,a kada ka wahal da kanka don Allah bamu zo nan don dorawa kowa nauyi ba suma nan yanzu nagama magana subar wanan wahalan akan mu zamu kwana a nan tunda gobe insha Allahu zamu kama hanya.
A,a baba don Allah kuyi hakkuri har jibi idan kun huta sai kubi hanya hanyar nan ba dadin zama ke gareshi ba abari zuwa jibi don Allah ?
A,a wanan da kake gani driverne munyo shatanshine a biyashi kada kudi yai yawa mukuma mu tauyeshi.
A barshi ba matsala driver ya fada daga inda yake zaune yana saurare baba ninaso badon shi ba kubi jirgine ku koma kano ai saboda zaman motan ba dadi sai a sallameshi ya samu lodi a nan ?
Jirgi dan nan haba dai ka barshi kawai na fadama bamuzo nan don muba kowa wahala ba ya dai mike tsaye din yana fadin idan ankamala sai a kira akaiku masaukin zuwa anjima.
Suna mashi godiya ya fita antyce ta kwala min kira tana fadin maryam kizo oga Aliyu zai tafi banyi saurin fitowa daga dakin ba sai zuwa can na fito da hijjab dina har kasa suka bini da kallo har na fice.
Ajiyan zuciya gwaggo hadiza ta sauke sai dayan gwaggo din tace kedai bari yaya duniya akwai tsoro sheri ko ina kake sai anyima shi wanan ko wa yancan dake gida ai basu kama kafanta ba wajen kitsuwa da tarbiyan kwarai.
Nina sani yaya tun da naji shi gadanga ya bada kwarin gwiwan azo kai tsaye na fahinci ba abinda ake tunane bane zamu tarar kawai dai na bada hadin kai azo din ne a wuce wanan zancen .
Ban jima a wajenshi ba na dawo don abincin da nake dorawa amma yace na bari har abin kari zai masu oda akai masu hotel inda yace har matan acan aka kama masu daki suma.
A takaice dai zance oga Aliyu ya nunawa iyayyena gata da mutunci sun yaba sun kara yaba irin kokarin da yayi dasu a lokacin.
Ranan da zuwansu suna shiga dakunansu inda ya kama masu mutum bibiyu saiga malam hamza kuma da kayan a leda na motsa baki har kayan tea da komai an hado masu.
Wanan abin ba karamin daddy yayiwasu baba ba suna fadi suna kari sunci dadi saida suka ture suna godiya suna kari inda suka gano waye Aliyun da suke gani a yamzu ?
Driver din shiya bincika aka bashi labari ya zaiyana masu ko waye a Aliyu da matsayinsa nan wani ban girma na musanman ya fara tashi a wajensu.
Kwanansu biyu gana ukku suka kama hanya cike da abin arziki don matan sun shiga kasuwa da anty mazan kuma malam hamza ya fita dasu.
A gida kuma ankasa an tsare ana sauraren labarin da zasu dawo dashi mai muni mara dadin ji kamar yadda yaya murja da mama suke yadawa ga mutane a kaina din.
Sai gashi ba,ako bari sun huta ba aka fara tambaya ina nake sun ganni baba bala yace Allah ya tsinewa makaryaci albarka hassada da bakin ciki lalai babban ciwone ga bawa.
Gwaggo kakanmu take tambayan ya akayi bala ina yar take ya juyo yana fadin gwaggo ai kinji abnda na fada ko nace Allah ya sakawa yaya gadanga da yarinyar nan su kuma marikanta Allah yai masu albarka.
Sai gwaggo Lamine aka samu tana fadan irin yadda suka sameni da abin alherin dake tunkaro zuri,an mu a kaina din gida yayi tsit ana saurarenta.
Tace abinda yaya Gadanga yayiwa gudu ke nan yaki fadan gaskiya tunda yasan hannun da yarsa take hannun arziki da mutunci ko yaran dake gidan nan kaf wallahi gwaggo ba wanda yayi tarbiyan yarinyar nan a yanzu kinga irin yadda yarinyar nan ta koma kuwa saboda daula da dasin da take ciki ?
Aini tunda mukaje makwabtafa gwaggo a bakinsu muka fara jin komai da yakamata mu sani tun kafin mu gane gidan da yabon halin yarinyar nan aka taremu garin.
Hakane daga can wata matar baba lawal tace angama kuwa don ga makwabcinka ake jin komai na rayuwan ka ai yanzu.
Gwaggo tayi shiru tana sauraren abubuwan da kowansu ke fadi da irin alherin da Oga Aliyu ya dunkulo masu suka dawo dashi ajiyan zuciya ta sauke cikin jin wani yanayi a gareta kafin ta furta cewa.
A gaskiya Allah da Annabinsa sunyi gaskiya da suka hani zargi ko mumunan zato ga yan uwan mu yau dai gashi gaskiya tayi halinta .
Allah ya wanke yarinyar nan da iyayyenta ya wanke su sol da soso da sabulo anje anga abinda ake fada a kansu babu kamahin gaskiya ko daya a cikinsa.
A yanzu na fahinci bakin hassadane da kiyayya kawai aka nunawa yarinyar nan da mahaifiyarta wanda hakan kuma sai Allah ya juya abin a garesu ya zama taki a yau gunsu sai hakan kuma ya kara dunkulewa ya kara komawa wani abu na daban wanda mutum bai fatan faruwan hakan ga dan uwanshi koshi kanshi ?
Gwoggo baki san wani abin sha,awa ba wajen yar nan sai yadda take nunamu ga kowa daya santa cewa mu din iyayyentane muka daga arewa.
Yarinya kazar kazar haka sai alheri da mukai ta samu a dalilinta makwabta nata kawo muna abinci daga gidajensu gaskiya gara da mukaje aka kauda zargin nan yafi .
Innata bata ji ba saida har akaje aka dawo ta samu labari tayi kuka tayi fada a ranan da