Showing 276001 words to 279000 words out of 395027 words

Chapter 93 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

tafi daidai komai sai an hada da mace macen kuma wayayya.

Amma ni shekaruna da wayewana duk basu kai irin yadda suke son sukai din ba saboda wanan akidun nawa dana fada sai gashi sannu a hankali sun soma hango suna iya canzani din da dabaran nasu.

Amma lokaci guda kuma na bijere masu ga hanyar da hanyar da suke gani din sunyi nasara akaina duk kokarinsu naki amincewa acigaba din a tafi tare.

Sai kwatsam muka hadu da okenah a wanan ranan daya rage min hanya tun lokacin suka fahinci idan basuyi da gaske ba zasu rasa daman su a kaina baki daya.

Lokacin da yajewa Ozil da zancen aikina da wanan company din shima hankalinshi ya daga inda sukai bincike suka gano dan uwanane keda wanan ma,aikatan amma kuma ba wani zumuta bane ai sosai shima tashi manufance a kaina kila a lokacin.

Sunyi sunyi sai ya kasance ina kaucewane da gaskiya bawai alaman zan dawo garesu yadda suke tunane sai okenah ke fadin mai zai hana ya fito da wanan dabaran tunda akan kudi ai dole in given up in dawo garesu a lokacin kudin dana fada suna da matukar daraja a duniya sosai.

Sai gashi lokaci daya na basu mamaki a daidai lokacin da suke jiran abinda zai biyon bayan hakan sai ba a dauki lokaci ba suna zaune sakon kudi ya shigo masu har riban da komai ba abunda aka taba nasu wanan abin ya matukar girgizasu.

Shi Ozil dai ya san yayi wani hasaran shiyasa baiso amfani da wanan dabaran ba a lokacin tunda hanyace dako shi kadai ya rage yana amfani dashi ya samu daga gareni ai.

Yanzu gashi na dawo da kudin hakan na nufin ba wani dama ko hope kuma a kaina dan abinda yake samu din wanda ba karamin karashi yayi ba a lokacin yanzu zai tsaya mai ke nan kuma.

Wanan yasa bayan wucewan nawa yakaiwa Okenah dukan da saida yai kamar zai shude don haushi ya soma fada dashi yana fadin .

Na fadama lamarin yarinyar nan ba yadda kake zato bane ita din Northerners ce suna da dabara da hikima dole ance sai na bita a sannu zan sameta gashi yanzu komai gaba daya ya lalace muna da wanan banzan dabaran naka.

Idan na rasa maryam ka sani har kai zan rabu dakai ke nan don gaba dayan ku maryam tafi min ku amfani a rayuwana .

Yarinyar nada baiwa sosai komai tasa hannu a cikinsa yana albarka amma yanzu gashi saboda wani banzan shawaranka can ka lalata min komai ga baki daya.

Abin yaso ya kaisu ga tashin hankali don ya nemi ya kare kanshi daga dukan da yake mai din sai abin ya koma masu fadan gaske a wajen.

Har hakan ya kaisu police station inda daga baya dai aka sasanta maganan don kada yai nisa kowa ya kama gabanshi.

Amechi ne ya kirani bayan isana gida yake ban wanan labarin don shi ba a wa yan nan abubuwan dashi karatune kawai ya hadashi damu yake shiga cikin mu don nasa iyayyen suna da dan halinsu kuma suna tsaye kan abinsu.

Dama tunda na koma gida nake jin kamar zazzabi nason daukana ban yarda na kwanta ba waya muka soma da saudat dake fada min labarin gida.

Wai ashe ranan da yaya murja taga an sauke kayan nan da Sir Aliyu ya soyo gidan mu washegari da safe taje can family house tana tseguntawa mama .

Suka fara tsegumin irin maganganun da baba ya sake min ina abinda naga dama a can don ina turo mashi abinduniya sunaci yasa bai son a fadi laifina.

Tsegumin bai kare ba ashe har saida aka kai ga kiran baba kan zancen can gidan ya dinga jawa duk wanda yayi wanan zancen Allah ya isa.

Sam bai yarda sun fadi din ba saidai anje magana kan baba Sha,ibu da yace idan baba yana kunyan zuwa ya dubani yaga rayuwan da nake ciki a can don kada Paapa yace bai gode ba.

Shi baba Shaibu din zai shirya yaje ya duboni yaga halinda nake ciki aishi ba acewa don me yazo dubani din tunda ai Faruq din ya sanshi sosai.

Baba ya dawo gida yayiwa yaya murja cin mutunci sosai ta kwashe kaya tace zata bar gidan ba kuma wanda ya hanata yin hakan ta tafi.

Shine da can family house akaji labari kuma sukace tunda baba bai iya tsayawa ya kulawa mama da yaranta ta dawo dakinta tayi zaman yaranta ai ko banza nan din gidan dan uwantane.

Wai har gida baba Bala yazo yayi cin mutunci yana ta fadin idan baba bai sonsu don yana ganin uwarsu takoma haka su suna sonsu ai.

A bisa wanan dalilin dai mama zata dawo dakinta da zama inji baba bala tana gama fadin haka nace shiyafi ai Saudat ko inna haka zai mata dadi.

Don inba haka ba cewa za ayi saboda ita damune baba ya watsar da matarshi ta farko kuma yar uwarshi a dauki laifin daba namu ba a yaba muna mukara bakin jini a wurin dangi.

Ko mama na gidan a yanzu ai bata iya tare yaya murja saidai Allah to gara dai din ta dawo shi baba ya kyaleta tunda ya saba da halin abinshi.

Hakama innan mu ta fada tace gara mama din ta dawo zaifi muna sauki kamar yadda kika fada a yanzu itama hakan tace dama da baba bala ya fita.

Nace yanzu dai shi baba Shaibu zaizo nan lagos ya dubani ko zaman kaina nakeyi yadda suke tunane tace haka akace yace.

To Allah ya kawoshi lafiya sai yazo ni nafi son yazo din ai ko banza zanga na gida wanda na sani ai muka kwashe da dariya saidai mood dina a ranan ba dadi har ta fahinci hakan a lokacin .

Take fadin wai lafiya nake kuwa nace ba komai muryan babane da taji ya shigo ya katse muna hiran mukai sallama da ita.

Ashe ya shigo gida yana fadin shirmen banza shirmen wofi baga irinta na nan ba ace kada inyi fada ana aibanta min ya dole in fada don kowa haihuwansa akayi.

Shike nan sai inbiyewa karya ga gaakiya ta dawo din ai gidan gashi saidai su sani ba ruwana da cinsu ko shansu gidan nan.

Har ya shiga daki ba wanda yayi mai magana kuma ya fito yana kwalawa innan mu kira da Ai Ai kina ina ne wai haka ta fito daki tana fadin gani malam ai ina amsawa bakaji bane dai.

Yanzu don Allah ki duba ke Sahura ya juya kan yaya sahura dake shanyi kaya a tsakar gida yana fadin yau Allah da ikonsa fa ina zaune kawai Alh musa ya kirani yana sheda min cewa .

Wanan wajen da muke haya inda shagona yake wai yau ya zama mallakina ansaya min shi da sunana har masu aiki sun zo wai an turosune su gyara wajenan fa ?

Su gyara kuma malam daga sayan sai gyara waya sayama kuma abu kamar almara dai kuma ?

Wallahi Ai nima haka naji zancen yadda kikaji din nan kamar fa almara wai ashe yaron nan da muke sana,ane ya turo din ayiwa wajen haka ?

Daga can lagos din baba Sahura ta tambaya cikin mamaki kamar gatse yace daga can mana ku dai ku bari yanzu don Allah dan haka ke samunka ta sanadinshi har kana da bakin tsayawa zagin shi koka marawa karya gindi don Allah ?

Amma malam ni ban gane bafa don abin ya daure min kai ya shiga dai yi mata bayani iya abinda yasani da wanda mutatanen suka fada masu a wajen .

Inda su a iya fahintarsu shine za a gyara wajenne gyara zamani a sake zuba kaya don a haska wajen da kyau yadda zai dauki idon mutane masaya

To shine suka sai wajen gaba daya a yanzu aka saka sunan baba tunda shine dan gari ai tasu fahintan ke nan a lokacin .

Yar uwa abune hakan mai wuyan fassara a gun iyayye da zasu samu alheri irin wanan ta dalilin yarsu da bata da aure kuma ba wani aiki da kowa yasan da takeyi mai karfi.

Idan wani ya yarda da haka ubangiji ya nufa a kansu wani ba zai taba yarda da hakan ba sai a dauka cewa sun mara mata bayane tana bariki yadda take so don tana turo masu abin duniya gida.

Akan manta da sanadin arzikin bawa kowa da yadda take zuwa mashi wani din ya samu ta hanya mai sauki wani kuma sai an samu dan sarkekeniya a cikin lamarinshi.

Wanda hakan wani hikimace ta ubangiji wanda Allah ya barwa saninsa a hakan da sai kaifin hankali zai iya hango hakan ga mutum.

Shi fa budi da wadata idan ubangiji ya turoshi ga mutum koda shirin karba ko babu sai yakai a hannun bawansa inda aka aikeshi gurin bawa.

Komai a rayuwa yana tafiya da zamanine a wani zamanin can baya hakan abune da ake ganin ba zai taba faruwa ba amma a yanzu fa ana fiyema da wanan halin rayuwan dayafi wanan din zafi kuma bai zama komai ba.

Ya Allah idan rabon mu yazo ka bamu ta hanyar alheri ta yadda zamu iya kare imanin mu da kimar mu ya Allah.

Kwance nakai bayan gama wayan mu da saudat ina tariyo abubuwan da suka faru dani a wanan rayuwan kai dan adam kaine zaka farawa kanka hukuncin halaiyanka kamar yadda addini ya koya munayi.

Ni dai a sanina ban aikata wani mugun abin asha da addinina bai yarda dashi ba ina tsoron ranan haduwa da ubangijina kamar yadda na taso ana horona da hakan a cikin addini.

To meye zaisa don kawai Allah ya nufi rayuwana a nan yan uwa zasu dinga jifana da kalaman da ba zasuso a jefesu dashi.

Shi rayuwa bawa kowa da kalan tasa haka zan daure inci gaba da rayuwana ina taka tsantsan da komai don bakin mutum bala,ine a cewan manya.

Ni dai gashi uwayen goyona tsakanina dasu babu takura anan amma gida har gobe sunana shine a bakin dangi wanda nasan hakan saboda mamace da har yanzu taki sakan min mara inyi fitsari.

Bako zata sake ba tunda bataga yadda take fata a gareni ba a cikin haka har barci ya soma satana can karan waya ya tayar dani lokacin.

Sir Aliyu ne a layin dama ina expecting din call dinshi tunda yana da wuya bai kira ba duk dare balle wanan ranan da mukai rabo a cikin rashin dadin rai dashi don ina fita naga yadda ya fisgi motar a ciki fushi .

Kome yayi shine mai gaskiya na gama fahintar komai a yanzu iya gaskiya gaskiyance ya nuna min badon shi da Allah ya jefo min a rayuwata ba da sai abinda Allah yayi dani gaskiya.

Duk da insha Allahu ubangiji zai karemu don irin taka tsatsan din da mahaifina keyi akan dukiyan da yasan ba tashi bane bana wani nasa ba.

Yakance dani Mairo bari inbi abin nan a sannu kinji dukiyan nan ta yaroce yaron kuma dan kabila yau ba abin kunya kudin yaron nan ya samu matsala a hannun mu.

Allah ya kare mutane zasuyi muna gwai da hakan gashi suce kwadayine ya kaimu ga dukiyan kabila ba zasuyi la,akari nima ina wahala a cikinta ba.

Murya sak ta wanda ke cikin yanayi nayi ya amsa sallaman a lokacin tare da furta to ya kike kin gama kukan koda saura har yanzu ?

Dan murmushi nayi kawai mai sauti a lokacin don banda abinda zance dashi kan wanan tambayan kukan da yake zance kuma ba zance kukan meye ba.

Finaly dai kin fahinci zancena a yanzu wa yan nan mutanen ki barsu kawai inda kika gansu Allah yayi rayuwan mune a cikinsu ba don suna son hakan ba damu.

Shi mutum yau akace kabilaneshi to wuyan sha,ani ke gareshi tunda addini da al,adan mu ba daya bane dasu .

Tun kakani ansakawa juna kiyayyanmu a zukatansu is hard su soka da zuciya daya sai dan wani bukata nasu a gareka komai sabon dake tsakanin ka dasu.

Ni san hakan na kuma gani saboda wanan abin da suke cusa maki a rayuwa suna cin riba dake basu damu da hatsarin rayuwanki zai shiga ba.

So ai abin yazo da sauki ba wani matsalan tayar da hankali a yanzu zaki fita zancensu ki nuna kwata kwata baki san ma sunyi maki hakan ba kiga yadda zasu koma shock a kanki.

Ko yanzu ai kin basu mamaki tunda kudinsu ya dawo hannunsu a lokacin da basu tsamaci hakan ba wajenki dama kuma hakan nake son ya faru din don hatsarine dasu sosai.

Ke mace ce ba zaki gane irin hatsarinsu ba da nake nufi so ki bari na duba ina wani planning a kanki wanda zaisa su kara nisantanki a yanzu.

Zan danyi waya da Abba saidai da safe in Allah ya kaimu haka ya dinga magana ina jin shi ban samu daman fadan wani kalma ba a lokacin har muka kashe wayan.

Najima banyi barci ba ina jiyo hayaniyan yan gidan namu a falon mu har dawowan Paapa amma ban fito ba haka kuma ba wanda ya nemini ma a lokacin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/1, 9:53 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊 8️⃣4️⃣ 🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Washegari na dai tashine na soma jin kaina na dan sarawa amma ban dauki hakan komai ba na kimtsa na fito hajja Yabi ce kadai a kitchen har na fice bamuyi arba ba.

Dama duk ranan girkinta dana tashi zan shirya infice abina don ko antyna ba fitowa zatayi ba wani lokacin Amirama a dakina nake shiryata wani lokaci don zuwa makarantar ta .

Ina shiga school tun daga nisa na hangosu zaune saman motanshi kaina kawar tankar ban gansu ba don babu tantama da gani isowana yake dako a wajen shida wanan dayan abokinsa.

Hakana nufin Okenah bai iso ba ke nan ko kuma dai akwai abinda ya faru don is hard kaganshi ba tare da Okenah ba.

Duk kiran da yayi min don in tsaya banko kallo inda suke ba balle in nuna naji kiran a lokacin na nufi deparment din mu nashiga duk tsiyansu ba zasu shigo a lokacin ba tunda an fara lectures.

Bai samu ganina ba don ana tashi nabi kofan baya inda malamai kadai suke bi tanan na fice daga school din tun kafin lokacin tashi yayi a school saboda kaina da har lokacin yake min ciwo sosai.

Na isa gida sallah nayi na kwanta ban tsaya nemawa cikina abinda zan danci ba a lokacin ina nan kwancene barci bai kaiga daukana ba kiran Oga Aliyu ya shigo min a lokacin.

Ina dagawa yana fadin sorry maryam ban samu kiranki ba inji yaya ba wani matsala dai tsakaninki da yaran nan ko ?

Babu komai ban gansu ba yau a yanayin maganata ya fahinci kamar banda lafiya a lokacin yake tambayan ya naji muryan ki hakane ?

Hammane yazo min lokaci guda da nake fadin ina gida kwance kaina ke min ciwo na dawo gida tun dazun gida kuma naji ya tambaya cikin mama ?

Ya matsa min na dawo gida to kinsha magani ko na girgiza kai kamar yana gabana a lokacin ina fadin bansha komai ba ko karyawa banyi ba tun safe .

Azumi kikeyine ya tambaya nace a,a bandai iya cin komai a yanzune wayan naji ya kashe lokaci guda na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login