Showing 234001 words to 237000 words out of 395027 words
Chapter 79 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
kuwa na zama din don tanbelena bai taba kawoni wajen nan ba sai wanan ranan a fakaice nake satan kallon wajen don na kusa dani din dako baiyi magana a lokacin ba zaiyi gaba idan na zure.
Nan mushiga nan mu kurda nan da mota har muka kawo babban ginan dake wajen wanda ke nuna offices din ma,aikatan wajen ne haka.
Aka fito nidai ina biye dasu har zuwa wani ~office babba muka shiga nan waiting room muka zauna don akwai jama,a a wajen masu jira suma a lokacin.
Shine yaje har gaban table din mutumin dake zaune a matsayin sectary din wanda zamu gani yayi magana dashi ya dauki waya shikuma yai magana bamu jima ba aka bamu izinin shiga office din .
A tare gaba dayan mu shidda da mukazo daga wajen mu din suka Akira a gaskiya bayanai sun nuna motocin nan naku ba haka bane yadda kake nufi.
Na fadama wanan karon ba zan yarda da hakan ba nasha daukan kaddara amma wanan karon duk inda kayana suka shiga zasu fito don ba zan kyale hakan ba.
Yanzu ina shedan abinda kake dashi din nu gani ya juyo kaina yana fadin karanto muna maryam muji wanan abinda na baki jiya ya fada a cikin harshen hausa a takaice.
Dan zabura nayi na soma karanto masu din zakice ba sytem din nake karantawa ba a lokacin yadda na haddace har karshe duk sukai shiru suna saurare nakai karshe.
Dattijon ya mika hannu ya karbi computer a hannuna ya dan kurawa bayanan ido na dan lokaci kafin ya turo min yana fadin is okey za a bincika din aji inda kayan suka shiga nan da awa hudu is better ya fada ya mike muka mara mai baya zuwaotocin mu.
Mun dawo company ko awa hudun bai cika ba akace wai angane sauran kayan nashi anyi kuren jirgine wajen sakawa nikan na koma ba sukuni a jikina don yadda abin ya kaya.
Muna gab da tashine na mike zuwa office din nashi na samu yana waya mai kama da dan fada a lokacin a cikin harshen hausa.
Ba nace ka dauko likitan ya dinga zuwa gida yana duba lafiyanta ba kai yusuf idan ba zaka iya abin nan bafa in sani sai inbar aikin da duk yake gabana in koma kano in kula da ita har ranan data haihu.
Ina jin hakan na juya da sauri don nasan magana yake a kan iyalinshi a lokacin don haka ba lalai bane in tsaya haka ya zama kamar gulma a wajena.
Ya dago yana fadin lafiya kin shigo kuma zaki fita No sir bari ka gama wayan zan dawo No ki tsaya aiba wani abu bane sabo.
Mummy dinace bata da lafiya kuma sunki su kai min ita asibiti don tace ba zata tafi ba shine suka yarda da hakan.
Subbahanallahi Allah ubangiji ya bata lafiya nace a hankali ya amsa da amin yana aje wayan tare da kallona yana fadin.
Lafiya dai ko ya dago yana tambayana hakan No sir dama nazone ince daga week din nan ba zan samu dawowa nan ba don zamu koma school ranan monday .
Na sani ya fada ya dan gyara sassauta abin wuyanshi da maza suke sakawa su daure wuya wanda ya fado a gaban riga nick tied ya dago kai tare da tsureni da ido yana fadin.
Ko akwai wani abune bayan haka no kawai na fadane da wuri kada kuce min baku sani ba idan baku ganni ba next week din.
Akwai shirin da zakiyiwa komawan nakine a yanzu banda shirin komai yanzu a gaba ina dai taken excuse ne a wajen ku.
Banjin karatun ki zai iya shafan aiki ai don ko a week end zaki iya zama ki tura bayanan dake nan ko kuma idan muna da bukatan ganinki a nan din I will let you know wanan ba matsala bane.
Ba zamu yarda aikinki damu yashafi karatunki ba don muna bukatan ki kammala lafiya right ?
A raina nake fadin dan rainin wayau din yana kule da komai kamar wani mai tukyan tsafi dake ganin har hanji a rayuwa nikan na boni da wanan mutumin dan kwakwafi gaskiya.
Sai daga bayane nake ganin laifina meyasa ma na fada mai hakan don kada yayi tsamanin cewa kamar ina mashi tunine akan kudin albashina na wata biyun da nayi aiki a tare dasu duk da wata bai gama cika ba lokacin balle har in sa rai da zan samu na wata biyu cif a wajensu.
Dan kudin dake hannuna zasu isheni manejin rayuwata duk a kudin mota yawanci lokaci kudin nawa ke tafiya donshine abu mai wuya a jeka ka dawon da nakeyi din.
Na iso gida an fara yayyafi don garin yagama rikedewa da hadari dake alaman ruwa yana gab da saukowa dama lokacin.
A falo na samu antyna zaune don haka na nufo falon suna min an dawo muka gaisa da ita na samu wuri na zauna inawa Amira dake fushi magana tana kwance tana rubuta home work din ta.
Na dago da zuman yiwa anty tambaya na samu tana min wani kallo na mamaki hakan yasa na dakata ina dubanta.
Maryam kin sauya gaba daya kin sauya lokaci guda komai naki ya canza a yanzu wanan kayan na jikinki yaushe kika sayo su ?
Sun dan kwana biyu na dana saya bandai saka bane sai yau din nan naso in barsu sai zamu koma school sai kuma na saka a yau din kayan sunyi kyau ke nan nake tambayanta don shashantar da zancen.
Sunyi matukar yi maki kyau over kayana da sai ka isa kake da irinsu ni gaba dayama kin juye min daga maryam din dana sani a baya a yau.
Kudi ke nan masu gidan rana inji manya don kudi suke nuna kansu a hannun wanda ya mallakesu ba shi zai fito ya fadawa duniya akwaisi ba.
Maman Amira nace ko kinga min inda aka aje salt a kitchen No ban amfani da salt ai tunda naji bai bada lafiya ga jiki ko miyata ai hakana nakeyinsa da maggi kawai.
Mikewa nayi na bar wajen don ba zanwa yar raini hankalin matar nan magana ba haka na yanke a raina zan zauna yanzu a gidan da ita.
Tsuki tayi tana fadin karyan banza sai kace mutum dan wasu ni wanan iskancin ba zan dauka ba ai in mutum yayi zuciya ya mutu.
Na fada ban daukan hakan ga dan kowa wallahi tunda na kusa haihuwan mutum balle yarinya ta kawo min iskancin banza.
Malama kin taba ganin maryam da plate din abincin ki gidan nan ba ko wani jagalgale maryam ke ciba madam baki da kulane da kin gane kafin kice kinyi min rowa niko kallon abincinki banyi saboda kazantar ki.
Ubankine kazami maryam haba haba abin har da zagin iyayye kuma haka bai kamata ba gaskiya yarinyar nan koda ta dawo bata tanka maki ba.
Kece kika fara zancen da tun jiya Paapa ya katse zancen nan a gidan nan ai ?
Paapa din me da zai kashe aida ya fadi gaskiya baya tsaya bin ra,,ayiku ba zan iya da kowan ku a gidan nan nan kuma gidan mijinane idan mace ta isa taje nata gidan mijin mana ko ta koma nasu gidan idan zai komu gareta ?
Saukin abinda mace bata rasa miji komai muninta kuwa Allah zai kawo mata daidai da ita an auri wa yanda basu da fasali .
Tsawa antyna tayi min wanan yasa nakoma daki na barsu a wajen don wace take fadan donta bashine a gabata ba lokacin.
Nikan ko kura ta barni a bakin jini yana da wuya ace yau ga mutum mu zauna a waje daya lafiya lau dashi dole sai wana baki jinin nawa gun mutane ya biyo baya.
Akance min ina abu isa isa ko izza da takama wanda ni nasan abin ba haka bane kawai halittane min a hakan da mutane ke min wani fassara a kai.
Naji mamakin shirin mu da yan wajen aikin nan namu da ba,a jin fadan mu dasu don ni kaina nasan cewa ina da wani hali da haka kawai zan kyale mutum in fita hanyarshi.
Sai bayan na gama komaine na kira gida a ranan inna na fara nema dinni na mance da zancen kiran da paapa yace inyiwa baba a lokacin na cire blocking dinsa da nayi a wayata.
Nasamu ta dauki wayan a lokacin muka gaisa take fadin sunyi nemana basu sameni a layi ba nace wayarce ma a kashe inna.
Ya jikin mama na tambaya ta ban amsa da sauki tana dai asibitin har yanzu don tana jin jiki gaskiya Allah ya bata lafiya nace ta amsa min da Amin.
Sai naji tace dani ashe kin turo masu kudine na jigilan asibitin dazun nake ji da yaran nan sukaje dubiya wai abin ya zama masu rikici a can din kinsan Audi ya dawo jiyan ai .
Na da sauri na amsa da haba ashe ya dawo garin tace ya dawo murjace ta kirasu ta kwashi karya da gaskiya ta fada masu akai ya dawo da tujara yaje har kasuwa ya samu mahaifinku yana iskanci wai uwarsu bata saku ba wallahi.
Oo ni har yanzu wanan halin nashi na tabara yana nan ashe bai daina ba idan ya daina yaci me sun samu sahura da fada wai kudin da kika turo ta taushe saura taki fitarwa duka yaso ya nada mata duka a asibitin saida ta boye.
Wanan abin kunyan kuma fa na fada take fadin ai baya suka ba kunya su bayan ya gama zaginki kuma a karshe ya dawo yana fada akan kudin ki da mutane.
Don har yanzu bai fasa ba yace idonshi idon sahura sai ya karya ta an mata dori kafin ya bar garin nan ke ni tashin hankalin ma ya isheni wallahi.
Mun dan jima da ita a wayan kafin ta kashe na mayar da idona ina tunane a sanin da nayiwa yaya Audi tun yana karaminshi bansan shi da halin kirki ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/18, 9:34 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊7️⃣2️⃣🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Nikan ba abinda zance a yanzu sai Alhamdullahi don koba komai na samu experiences ga wanan aiki uwa uba ko albashi nake amsa sai na dauki lokaci ban hada kudi na sai alherin dana samu gun mutumin nan ba.
Kayana duk wanda nasa sai an kalla an kara kallo tare da tambaya a kamsu duk da kayan a yanzu nagane manufarsu kayane irin na musulunci zance don yadda suke rufe min illahirin jikina duka haka kuma ga dan gyalen da zanyi rolling a kaina wanda ke kara fito dani musulmata ko bahaushiya musulma yar asali arewa ko dai wani kabila masu kaifin musullunci irin arewa a wani kasan.
Compound kowa yasan ni musulmace saidai wasu basu san cewa ni yar arewa bace don dabi,ata kadan ne zai nuna maka bahausa nake sai a dauka ni ruwa biyu ce.
Satina biyu ke nan da komawa school inda na daina shiga company a yanzu karatuna da nake gab da karewane a gabana saidai a yanzu ba wanan wasan ko shoriritan karatu wai na hada da neman kudi yadda nakeyi a baya don samun madogaro.
Don ko a dan dawowan nan Ozil yaso yayi min tayin wani contrac naki yarda da hakan don yanzu na gama fahintar komai mai sunnan baba ya yawar min dakai sosai kan wancan sana,an kaddara da nakeyi a baya.
Idan kuwa ba illa ba ba abinda zai kaini kuma amsan wanan tayin nasu a yanzu duk da kudin da suka kara a tunanenshi kari nake son suyi min a yadda suke ban.
Amma na nuna mai iyayyena sun hanani wanan abin saboda hatsarin dake cikin shi kuma hakan yana hanani karatu ina tauye kaina da yawa don haka suyi hakkuri na daina wanan harkan a yanzu.
Har fushi yayi dani ban kula hakan ba da ace shi mugune na gaskiya a nan lagos din da sanadin hakan yadda na fito fili na fada mai gaskiya da zai iya jefa rayuwana a hatsari amma sai baiyi hakan ba shi.
Iyaka dai mu,amulan mu a lokacin ya dan ragu sosai don muna kwana biyu bamuga juna ba dasu sai wani lokacin muke dan haduwa sama sama dasu din a gaisa.
Ina zaune na kara littafi a gefena Okenah yazo ya zauna a gefena hakan yasa nadogo kai na dan dubeshi ya soma fadin a gaskiya Ozil baiji dadin abinda nayi mai ba.
Yayi hakkuri zancen iyayyena dake rikona yana gaba da komai da zanyi cikin garin nan yanzu idan nayi hakan kamar ban godewa rikon da sukai min bane.
Ya tura wasu suje wanan harkan amma sukai fail dinshi basu iya business din ba yanzu wasu company suna kokarin sayesu ga harkan kinga ke nan zasuyi hasaran hakan ya shiga cikin damuwa sosai da abin nan yasa na taso don in ganki.
Ba laifina bane don naki nasan Ozil mutumin kirkine da saidai inba wani labarin hakan don yayi min abinda ban tunanen ya taba yiwa wani hakan amma zan duba in gani idan hakan zai yuyu gareni daga haka muka tsayar da zancen dasu.
Bawai zancen ya fita raina bane a,a yana a kasan zuciyana saidai bansan yaya zanyi da maganan bane a lokacin don Okeh ya ban takardun suna a hannuna.
Ganin banda lecture da safe sai wajajen sha biyu a ranan yasa na shirya shiga company don wanan dalilin tara saura na fita gida a ranan na dauki drop zuwa company din aka kaini a cikin sauki.
Ni kaina nasan wanan abin zai taba rayuwana saidai zaman lafiya ga mutum yafi kai wanine wani lokacin akan duniya ba zan taba jefa kaina hatsari ba ko in zubarwa kaina da mutunci .
Sama na hau kofan office dina yana rufe yadda na barshi duk da nayi handling din key din wajen garesu ranan da zan tafi din muka gaisa da Biodu yana dan washe bakin ganina nake tambayanshi oga yace min yana ciki suna magana amma bari ya fada mai zuwana.
Ya dauki waya ya kira layin yana fadin miss maryam ce tazo tana son ganin ka sir yace a barni in shigo yana mamakin zuwa na din a ransa da bankirashi ba nazo da kaina haka don yasan akwai dalilin zuwan da nayi din .
Don ranan karatune ai balle ya dauka banda lectures ne a lokacin ko kuma jerabawan da yake min ne zan fadi gareshi kome ?
Yana zaune saman kujeranshi ya kwabe couth din jikinshi ya rataya a bayan kujeran su kuma bakin nasa sun mike zasu fita daga office din a lokacin nashigo.
Tun kafin in zauna na jefa mai gaisuwa da ina kwana sir ?
Iam not you dad ? you are my daughter now, tunda sunan Abba gareni ai na danyi murmushin iya baki ina kaiwa zaune yana rubutu har lokacin bai dago kai ya dubeni ba.
Niman nayi ina dan nazarin abin da zan fada din a lokacin ina zaune shiru na dan lokaci can ya gama ya dago yana fadin umm,humm ina jinki maryam ?
Yaya akayi baki shiga school ba yau koba karatune yau din kika fito aiki damu ?
Akwai nazo akan wani maganane ko ince shawara wanan guy din ne da muke aiki a baya tarene tare dasu yake bukatan in taimaka mai kan wani contrac da yake hasashen