Showing 87001 words to 90000 words out of 395027 words
Chapter 30 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
ta koma wanan wajen abu da gani ba addini ko wani tauhidi ga mutane har ka karayiwa yarka fatan komawa waje.
Murmushi inna tayi tacigaba da gyaran wanken da takeyi itama bata tsaya yiwa mama din magana ba a ranan hakan yasa bata ja zancen ba.
Sai zuwa can anty hajara ta fito tana fadin mama yanzu don Allah in akace Mairo bata komawa ai kema kina cewa a barta ta koma .
Koke ai kin morewa zuwanta koni na samu zuwa indai hakane ai wallahi da gudu zan tafi me zan tsaya tsunta garin nan kuma ?
Don ma Allah baiyi mairo mai rigima bace wa zai shiga jirgi bai dawo yana hurawa mutane hanci ba shi wanine inba ita ba ?
Nikan wallahi in an samu mai daukata irin haka da guda zan tafi in bar garin nan waki arziki kin tsaya kina wani zance can mama ?
Sun shiga daki kus kus da yayanta tun zancen jirgin nan danayi da mahaifin mu don kadama yace zai wahal da kanshi wajen sayo wani abu don in koma dashi din gara ya aje kudinshi suyi amfani dashi zaifi.
Nakan je gidan su anty har kwana nakayi a can din in gyara mata gida da yan wasu aiyuka hakama nakan zo da Amira ta kwana biyu a gidan mu.
Ranan ma na shirya tsab don zuwa gaida Anty data bugo waya in shigo da safe hakan yasa muka shirya nida yan uwana su saudat .
Nakan mata da arewa nake in saka hijjab koma na saka din a yanzu bai jimawa a jikina nakanji ya dameni sai na cire don rashin sabo dashi din danayi yanzu.
Wasu atamfane masu launin ruwan bulue da dan ruwan kwai zanen filawansu manyane kwarai donshi na dan yafa yalalon gyalena shima yello da plat shoe da suka kasance kala daya da gyalen sai kalan ya saje da dan adon zanin yellow din.
Mun fito zamu nufi inda zamu samu mota zuwa unguwar nasu saidai sakon da za a karbo mata wajen anty fati yasa nace su shiga ni zan tsaya waje don ban son yawan tsareni da mama keyi da ido duk na shiga gidan nasu hakan yana sani tsarguwa da yawa da ita.
Motar dana gani a dan hanyar daya raba gidansu din da wani mahada yasa na nufi wajen don jiran su fito daga gidan muci gaba.
Harna tsaya na jingina jikina da motar sai kuma na juya ina kallon daurin dankwalina da kara gyara fuskana kamar yarinya nakai hannu a jikin motar na zana sunana kamar yadda na saba saidai wanan karon ba full na rubutashi ba.
Suma yayi zaune daga cikin motar yana tunane shi kadai a ransa waiko gamo yakeyine ko me ko yaushe wanan yarinyar ya hadu da ita sai tayi nai zane a jikin mota yau ma kamar kullum saida tayi shin wace ya saba gani din ne kuwa ko gamo idonsa ke mashine wai ?
Ganin fitowan su saudat da nayi yasa na yunkura daga jingin ina fadin kun karbo suka amsa min da eeh muka kama hanya muka bar wajen don nufar inda zamu.
Sai lokacin ya yunkura ya bude motar dama fita zaiyi sai gani nazo na jingina jikina a jikin motar yayi hakan yasa ya fasa fitowa motan yana kare min kallo.
Har lokacin da muka bace daga kwanan yabar ganin mu a hankali ya sauke ajiyan zuciya saidai akwai tambaya me yawa a kasan zuciyarshi kan idonsa ke masa gizo ko kamace ko kuma gaskiya inba idonsa yayi karya ba tabas yarince da ya gani a Lagos.
Duk da dai waccab din ta lagos yana kyautata zaton kabilace ita don irin shigarta na dan buje makaranta da sukeyi a can din yaushema zata zo nan kano kuma ?.
Wanan kuma yaga kamar bahausace don yan uwata daya gani saye da hijjab itace dai mai karamin gyale a cikinsu kamace dai ta ko ina Allah yayi har hin duk iri daya sak ?
Tsuki yaja yayi gaba yacire wanan tunanen a zuciyarshi kai tsaye ya tunkari kofan gidan malam innuwa din daya hango dandazon jama,a kamar yadda aka saba zama a wajen yana da wuyane mutum yazo ya samu kofan gidan ba magidantan unguwar dake karin ilimi a wajen malam din.
Cikin kamala ya karaso yana debe takalminsa nan malam din ya farga dashi ya soma magana yana fadin yauma a can kabar motar ke nan Ali ?
Wallahi ina tsoron wanan kwatarne malam kada ya bata min mota yasa nake barinsa a can kwatan gidan Alh iliyane mutane da yawa suna complain akan hakan kuma har yau Allah baiba da ikon a gyara muna shi ba.
Gaisawa suka soma da jama,a harda baban mu dake cikin ayarin wajen don jin fatawan safe da malam kanyi a irin wanan ranan ya sanda hakan shiyasa ya kwatanci da angama a lokacin.
Saidai duk da hakan wajen akwai jama,a dake zaune tare da malam din wasu hira sukeyi wasu kuma na gefe suna bitan abinda suka dauka zakiga manyan mutane sosai a kofan gidan kowa da abinda ya kawoshi wajen.
Bayan gama gaisuwa ya mike ya nufi ciki nan malam din ya soma yiwa jama,an bayani da dan wajen Alh yakubune mai glass dayaje turai karatu shine ya dawo yanzu aka shiga sa albarka don ganin bai sauya dabi,unsa ba jinkai yadda wasu idan sun fita kasan sukewa mutane wani lokaci kamar sunje wani aljanna.
Malam bai dauki lokaci mai tsawo ba a wajen ya mike ya sameshi ciki yana zaune dakin da yake kamar falo ko zaure haka ga tulin litattafai a gefe daya wasu da gani an jima ba a tabasu ba a wajen.
Malam ya shigo yana fadin na fadawa malam hamza zuwanka zasu kimtsa saisu fito mu tafi yanzu don mu samu Alh a gida duk da yanzu ko wani lokaci mutum yaje zai sameshima a gida don bai zuwa ko ina yanzu.
Zakice ba dashi tsohon yake magana ba saida tsohon ya sake fadin sai dai ina son duk abinda za yace kada kace zaka amsa mashi duk da hakan ba halinka bane.
Amma malam inda sonane nafi bukatan naje gida ni kadai zaifi ba sai kun wani rakani ba yadda kuke nufi tsohon ya dago yana fadin haka kaga yafi Aliyu ?
Kwarai malam meye a ciki iyaka dai mu gaisain kuma yi mashi bayani kamar yadda kace yana bukatan ji daga gareni .
Karka damu malam ba abinda zai faru insha Allahu to kadai rike addua a bakinka Ali don wanan matar yanzu na tabbatar da tasan da dawowanka kasan nan ko .
Murmushi ya sauke a fuskanshi yana fadin malam kada ka damu a yanzu ba ita ba koma waye ba abinda wani mahaluki kuma zai iya yi min ya kamani saidai idan hakan yana cikin kaddarata dama.
Shigowan su malam karamine ya katse masu hiran inda suka gaisa bayan sun gama yake masu bayanin abinda dan nasu ya fada .
Hamza yaso ace anje dasu don yayiwa hjy din tas a lokacin saidai malam innuwa din yace a bari dai din yaje shi kadai a haka shawarane mai kyau tunda iyayyensane ai.
Zuwanmu kuma a tare zai iya kawo wani tsegumi ga wanan matar ku barshi kawai yaje shi kadan a hakan aka aje magana ya dan jima dasu kafin ya tafi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI KEBBI STATE
[7/25, 10:58 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
2️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15- HAWAYEN KADA🐊 1000.
_Account No._
_*ZAINAB IDRIS MAKAWA*_
2254380105
ZENETH BANK
PHONE NO.
08036959257
Daga nisa yake bin motar da kallon mamaki har lokacin da motar taja ta tsaya a daidai kofan gidan Alh yakubu mai glass a cikin unguwar.
Ikon Allah yaushe rabon da naga irin haka a kofan gida Alh yana zancen zuciya yana kallo yana kuma mikawa yaron dayazo sayen sabullo canji da sabulun.
Har lokacin hankalinshi naga motar da ba,a bude din ba gata kuma ta tsaye gab da kofan gidan Allah din wanda haka ke nuna maishi yana ciki yana wani uzuri lokacin ba Sule mai shago bane hankalinshi ke wajen har sauran mutanen dake zaune suna majallisa a sauran wajajen gidan hankalinsu naga wanan motar suna son ganin wanda zai fito daga motan can aka bude kofa ya sako kafa waje amma bai karasa fitowa daga ciki ba.
Lokacin daya yunkura ya fito jikinshi saye da bakar corth ta maza da ake kira suit sai yar farar shirt daya dan bayana daga ciki kadan ya gyara ya rufe motar zuwa cikin gidan inda yaja ya dan tsaya kadan kafin ya sa kai ya shiga ciki lokaci guda.
Tambayan juna sukeyi a wajen wayeshi wani ke fadin nikan idan ba idona ke min gizo ba wallahi kamar Aleyco ne fa ?
Aleyco kan yaushe rabonsa da kasan nan wanda akace ba,ama san duniyan da yake ba ko a mace ko a raye kai wallahi ban yarda ba wancan Aleycool sai naje nagano idan bashi bane .
Ya mike da sauri ya sameshi daidai zai shige kofan da zata sadaka da cikin gidan nasu yaji daga bayanshi ankirashi da sunanshi daya taso dashi na baya na kurciya wanda abokansa na kurciya kadai ke kiransa dashi haka Aleycool.
Duk da shekarun da aka dauka bai manta da wanan muryan ba don muryan abokinshi munir da suka taso tare dan makwabcinsu Alh Abbas .
Jin hakan yasa ya tsaye cak a waje daya tare da juyowa yana fadin bashow a hankali kamar baison budan bakin shi maki Abbas din ya nufeshi sai kuma ya juya zuwa waje yana kiran yan uwansu da suzo ga abindake faruwa.
Nan sukayo ruuuuu da wa yanda ya sheda da wanda bai shedaw ba duk sunzo gareshi sun bashi hannu anata gaisawa da juna a cikin jin dadin sake haduwa.
Bashow ne ya soma fadin Aleyco akace damu ka dade da mutuwa tun bayan tafiyanka muka samu labari wai an kamaku an harbe tun a hanya.
Wasu kuma sunce ba wanda yasan inda kake tunda ka tafi aka batar dakai an dai samu labarin ka mutu wasu suce muna kuma an kulleka a can turai daurin rai da rai maganganu iri iri munji a kanka Aley hankalin mu ya tashi munyi ma addua mun kuma zo mun samu Alh matsayin mu na abokanka munyi mai jaje a kan hakan saidai Alh ya nuna muna ba ruwansa dako meya sameka a can tunda ya hanaka tafiya kaki hanuwa.
Murmushi ya dan sake a fuskanshi tare da hada hannayensa waje daya alaman godiya a garesu yana fasin ya gode amma yanzu shigowanshi ke nan zai gana da iyayyenshi su jirashi a waje har ya fito .
Shi bashow yace ai tare zamu shiga dakai ciki a ganmu aga yadda muka taroka in yaso sai mu fito mu jiraka a waje har ka fito.
Kwarai bashow kayi gaskiya dole mu dafa mai baya har gaban hjy mu rakashi Allah yaiwa danta arzikin dawowa gareta yau a cikin sutura.
Yasan halinsu gaba dayansu don da a baya tare dashi ake wanan kiriniyan saidai tafiyanshi yasa a yanzu ya daina komai a rayuwansa natsuwa da hankali yazo masa.
Kafin yayi aune sunyi gaba suna fadin Alhamdullahi Allah yayi yau Aliyu mu ya dawo a cikin salama a garemu cikin mutunci
Jin hakan yasa mutanen gidan fitowa da sauri suna mamaki meya faru har cikin gida haka yana tsakiyansu suna ta hayaniya suka shigo har tsakiyan gidan dama wasu dake binsu a baya cikin murna da ihun dawowan Aliyu din dan hjy hauwa.
Mama dake zaune da diyanta falonta yartace ta mike tsaye tana fadin hayaniyar me nakeji hakane dayan tace nima tun dazun nake jin gumzan mutane a wajen gidan nan fa ?
Aleycool oyooyoo samarin ke ihu kamar da gaiya har tsakar gidan adai ,dai lokacin mazaune gidan ke rige,rigen fitowa daga sassansu don jin bindake faruwa.
Alh yayi karfin halin fadin Aliyu wai da gaske dama kana raye duk tsawon lokacin nan ?
Aliyu fa wani Aliyu dai kuke nufi suwaiba tace Aliyun maman H dai ta gidan nan mana Aliyu namu gashi a gabana fito ki gani .
Zani take kokarin daurawa yana sabule mata sai kamo bakin zanin takeyi da hannun guda yaki kamuwa saboda sauri da shiga yanayin rikicewa da take ciki a lokacin.
Tsakanin falo zuwa barandar kofan dakinta saida ta kusa faduwa ukku Allah ya tsareta tana sambatun wai Ali dai Ali gidan nan shine ya dawo dama yana rayene ?
Haba mama wanan rudewa fa kama kanki don Allah kina abu kamar wani abu ya hau kanki a gaban mutane haka Aliyune mana gashi tsaye kina ganinsa mama .
A hankali ya tako zuwa gaban mama din ya gyara tsayuwa yana fadin mun sameku lafiya mama kallo daya zakayi mai ka gano jin dadi tare da walwala a ilahirin jikinshi wanda ya nuna kanshi ba sai an tambaya ba.
Kafin ya samu furta wani abu muryan habib a bayansu yana fadin kai kai kai wa nake gani haka kamar Aliyu wai kana nan ka boye haka don Allah ba labari ko kira a san inda kake tsawon dadewan nan ?
Ai anyi arziki tunda Allah ya dawo muna dashi lafiya abokinsa ya fada daga gefenshi suka amsa da wallahi wanan murnan ai gaba dayan mune wanan abin ya shafa
Baiyanan mahaifinsu yasa aka shiga yiwa Alh murna da farin cikin dawowan yaron nasa yana godiya duk abin nan banda kanninsa da suka fito hjy hauwa na daki bata fito ba saboda kawaici da farin cikin karan da mutane suka nuna mata.
Bai samu kanshi ba don dattijan unguwa dake zuwa tayasu murnan dawowanshi garin cikin yan uwa da abokan arziki.
Muryan mahaifinsune dake kiran kannesa da suzo su gyarawa dan uwan nasu dakinsa da aka mayar wajen aje tarkacen gidan wanda hjyce tayi wanan abin da kanta ta kirkiro a dinga aje kaya a cikon dakin nasa don kawai ta bakantawa hjy hauwa din rai ta nuna ba danta a gidan kuma har abada don har dakinsa na gidan ta kashe a tarihi.
A cikin muryansa daya nuna zaman turai zalla a lokacin yake fadin No su barshi na sauka a wani wajen a can na sauka tare da wanda mukazo tare.
A ina ka sauka kuma bayan kasan muna cikon garin nan Alh yake tambaya cikin mamaki habib ke fadin ai kaji yace bashi kadai bane da alama tare da wasu yazo ke nan ?
Eh tare nake da yarana suna can na barsu a gidan nazo nan in duba ku yara kuma ya dan amsa a sanyayye yana fadin eh suna aiki a karkashinane don haka dole duk inda zan tafi muna tare dasu.
To ai abinda ban gane ba ke nan tun farko yasa nace sai kazo don a ganina kayi kankanta Aliyu da har zaka mallaki wasu abubuwa da kake lissafo min a yanzu ?
Wani shu,umin murmushi ya sauke a fuskanshi sai yaji habib na fadin amma baba zamanine fa Allah ya kawomu cikinsa yanzu ko wayar nan da kowa ke riko a yanzu lokaci daya saita mayar da mutum attajiri .
Ni sam banji komai kan yadda Aliyu ya dawo kasan nan ba baba inka tuna da irin zuciyarsa na dagewa akan gaskiya tun yana karami.
Kai habib kaja min baki kayi shiru ka barni da dana muyi magana bada kai nake magana ba a yanzu ina magana da danane.
Yi hakkuri baba amma ni gani nayi wanan abinda kake kokarin yi kamar baka yarda dashi bane yasa kake tuhumarshi ?
Idan na tuhumeshi daidai nake don inta baci ba wani daga waje zai soma min gori ba uwarkuce