Showing 48001 words to 51000 words out of 395027 words

Chapter 17 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

fadin ni barin koma kada in barta ita kadai ke yanzu har school kika yarda aka sakata kina kallo don wauta ?

Nicema nabashi shawaran ya sakata school ta karasa don tana karatu a can haushine ya kama matar tace amma sariya ke banzace wallahi ban taba tunanen baki da wayau ba haka sai yanzu ?

Ta dawo gida ta samu nagama komai ina daki ina cire kaya zan shiga wanka tashigo don ina kokarin kiyayye dokanta a kaina na kazanta data kafa min tun zuwana gidan.

Wai har kin gamane ta fada eeh na hada anty a duba koda gyara in koma in gyara ta juya ta fita ba tare da ta tsaya min magana ba.

Ni dai har nafito wanka nasa wani dogon rigan atamfa a jikina naji tana kirana a falon lokacin yamma yayi sosai magariba ya gaba to.

Na fito da dan kwali a hannuna ban riga na daura ba sai kaina dana kulle gashina da roba don banda ribon da zan daure dashi yasa nayi dabaran daurewa da robalin .

Kujaran gefenta ta nuna min tana umartana dana zauna a hankali cikin tsoro nakai zaune a inda ta nuna min din hankalinta yana ga wayanta ido na dan zuba mata sai can dago tana fadin.

Yau maryam ko aiki yayi kyau sosai nagode saidai ina son in tambayeki kinsan dai na fada maki banson munafunci ko karya a rayuwata tun zuwanki gidan nan.

Kaina gyada mata alaman eeh tace good so ina son tambayanki meye dalilin da aka turoko a rayuwan mu da sauri na dago na dubeta ta dago tana fadin yes.

Ina son ki fada min tsakani da Allah meyasa iyayyenki da iyayyen Papa suka zabi turo muna ke gidan nan yanzu da sunan yar aiki a wajena.

A cikin yar murya nace wallahi anty ban sani ba bayan haka kuma banjin akwai wani dalili don zuwan nawa a nan Allah ya kaddara saina zo nan dai na kwashe duk irin abinda ya faru tsakanin mama da baba har da inna na fada mata komai da akayi kafin nazo na gama na dago ina dan kallonta .

Nisawa tayi tana gyara zama tace hummm mutane wani lokacin sukewa mutum mugun fata wurin bakin hasashensu.

Ba ruwanka da lamarin mutum amma saiya dauki naka zancen ya ara ya yafawa kansa yanzu yan unguwar nan cewa sukayi dani in maidake gida maryam.

Da sauri na dago kai ina kallonta tace kwarai nidai baki min komai ba wallahi don ban ganki da wani hali mara kyau ba gaskiya.

In ma kin boye min Allah ya gani a yanzu kallin kanwata da muka fito ciki daya nake maki maryam saboda irin halinki yayi min daidai kina da kokarin kiyayye duk abinda zaisa ran mutum baci dake.

Don haka idan kun cuceni kanku kuka cuta ni ban cikin irin mutanen nan masu nunawa mutum kyama ko nuna kai ba kowa bane donshi kikaji ina fadin ke yar uwar mijinane don ma kada wani ya kawo maki rashin mutunci kamar yadda nake ganin sunawa yan aikinsu a gidajen su.

Ballema a yanzu da naji irin abinda ya faru tsakanin iyayyenki wanda fida karfi akai masu akazo dake nan ba tare da son ransu ba don haka maryam zan rikeki amana a gidan nan da fatan kema zan samu hakan daga gareki.

Duk wanda ya tambayeki kice dasu babanku daya da Papa har yam uwana idam sunzo gidan nan abinda zaki fadawa kowa ke nan mu kashe mu bisa zancen nan a tsakanin mu matukar kina son zaman lafiya da kowa garin nan.

Kinsan wasu sun dauka gazawane ko talauci kesa a turo yara irin haka neman kudi sai kiga an nemi hanyar wullakantsu aci masu zarafi da yankar kauna banson har hakan yakai ga kasancewa a tsakanin mu insha Allahu.

Ki daure ki fitar da iyayyenki kunya ki natsu ki maida hankali kiyi karatun ki mai kyau nayi maki alkawari sai idan kece kikace kin gaji da karatu a rayuwanki matukar muna tare dake gidan nan.

Nagode anty na fada ina sharan kwalla don jin cikar burun mu da iyayyena a kaina zai cika kamar yadda baba yasha fada min.

Jin karan motar mijinta yasa na mike da zumar barin wajen tace zauna a binki mena fada maki daga yau ke yar uwarsace ta jni kada ki kara irin boye boyen nan da kikeyi.

Sanan kuma ya kamata ace an taimakawa mahaifinku don ya samu abin da zai dogara da kansa ba sai ya jira wani ya bashi ba akwai tausayi ga rinsu irin bayin Allah da ake karyawa kai tsaye da sunan kwace kaya akaryasu da rana tsaka har in ba ai hankali bama sai kiga wani ya fada jinyar da bai tashi wanima ya haukace ta sanadiyar hakan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[7/6, 9:55 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,

1️⃣6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,

🀳AUNTY ZEE MOM MUJJAHID KATSINA 08262859027🀳

πŸ‘*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA*

*Maganin sanyi 5k*

πŸ‘*Maganin sanyi*

*5k*

πŸ‘*Maganin ciwon Qoda 10k*

πŸ‘*Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k

*MAGANINπŸ‘ MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*

πŸ‘*INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU*

*Maganin gyaran Nono πŸ‘8k*

πŸ‘*MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE*

πŸ‘*Maganin Rage Tumbi 7k*

πŸ‘*MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE*

*Maganin Basur 5k*

*MAGANIN CIWON SUGARπŸ‘ CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI*

*Maganin ciwon Sugar 10k*

*08162859027*

*09070027627*

*Location*KATSINA STATE*

*ACCOUNT NUMBER*

*8162859027*

*ZAINAB SHU AIBU*

*OPAY*

*OR*

*3968303018*

*FCMB*

*ZAINAB SHU AIBU*

πŸ‘ƒ*DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO*

Keda shiga gidan nasu a yanzu zaki fahinci al,amura sun tsaya cak ba irin da dakomai yake haja haja anayinsa a cikin wadata ba.

Tun daga kofan gidan zaki fara fahintar hakan don yanzu ba yaran almajiran nan dake zama amsan sadaka sun mayar da kofan gidan matattarasu saboda hasken fitila dake jansu haka kuma da rana suna lemewa a saman simintin dake shimfide a kofan gidan su ragewa idonsu nauyi don masu gidan da basu takura masu.

Hatta ruwan famfon da aka fitar daga wajen gidan ayanzu ba komai a wajen sai ganyayayki da suka fado kasa suka bushe suka zama shara a waje.

Abin gwanin ban tausayi a garesu rayuwan dabai saba da wahala ba yazo ya tsunci kansa a hakan yana daban tausayin gani a lokacin ga zukata masu tausayi.

Daga dakin hjy hauwa Amal ta fito da cooler abinci ta nufi dakin hjy Naito dashi a kofa ta tsaya tana sallama da kyar ta amsa mata ance mai hali baya barin halinsa.

Don duk da babu komai a yanzu sai hakkuri a gidan wanan iko da mulki na hjy Naito yayana nan daram baije ko ina bashi saima abinda ta kara a sama yanzu.

Sallama yarinyar ta sakeyi daga ciki aka sake amsawa da fada ta hanyar cewa wai waye zai isheni da bakin sallama da rana tsaka haka don Allah ?

Hjy mama N nice mama H tace na kawo ta tabe baki tana kallon yar matashiyar budurwar data karaso ciki da kula zuwa gabanta ta sauke kana ta dora da gaida maman da wuni.

Meye kuma haka ta fada a gadarance yarinyar bata fada ba illa sake fadin cewa da tayi mama tace in kawo kice angode ta fada yarta baba tana kwance saman kujera ko kallon kanwar nata batayi ba har ta fice daga dakin.

Taja tsuki tana kara hade fuska cikin takaici sai lokacin sahura din ta juyo tana fadin wai meye mama ?

Uwar tace waya sanar masu da kilibibinsu can ta yunkura ta sauko saman kujeran tare da bude kulan doyace fara sol tana turiri a ciki sai manja da yaji da baki bakin albasa da aka soya aka lema a sama yayi kyau har ya gaji.

Doyace fa mama diyar nata ta fada tana karkatawa uwar kulan abincin tace nikan barin dauko plate in diba don dama yunwa ya isheni wallahi.

Shima bilya ya fita ya share mutane tun dazun bai dawo ba daga ya amso muna ko taliyace a dan sulala ya tafi ya zauna abinshi.

Basai yana da kudin zai sayo ba Sahura tunda kikaga bai dawo ba bai samu kudin saye bake nan ta nufi kitchen ta dauko plate tare da debo ruwa a cup tafito.

Tana fadin mu dai hashim bai kyauta munaba wallahi banso ace matsalan nan daga dakinmu ya fito ba gashi yanzu komai ya tsayawa baba cak a rayuwa ace abinci ma ya gagari gidan nan saboda Allah mama ?

Haushin daya kume uwar yasa ta kasa magana da yar nata tasha toka ta kyaleta saida ta mikowa uwar doyan ta kalla ta sauke ajiyan zuciya tana fadin .

Kekin dauka wanan abindaya faru yin hamshin ne aike da gani ko ba a fada ba kinsan hannu aka sa mashi har haka ya faru dashi.

Anyi aikin da za a lalata komai da suka rika saboda ana ganin dadi yazo muna duka yara sun girma sun shiga harkan kasuwanci da mahaifinsu.

Shine aka nemi hanyar da za a salwantar min da rayuwansu to ai gara dani tunda ina ganinsu nasan halin da suke ciki ko yayane dai zan san abinyi akan hakan.

Ita nata tana zaton na kyaleshine ai ya tafi kenan ba waiwaye ko kallon gida balle har yazama abin kwaran da suke tsamanin ya zama nan gaba.

Tana nufin zata lalatamin zuria ne in zuba mata ido nasa an turashi duniya can ko zancensa ma yanzu uban baiyi tun lokacin danasa akai min aiki a kansu.

Sai ita uwarce ke faman zuba karya ita kallonta mai saman ruwa wai itani zatayiwa barkado har da fadi kwanaki ance angashi a wani kasa yayi kyau yana aikinsa.

In gaskiyane ya dawo gida idan dawowa banzane ai yadda tayi aikin nan saina nuna mata ita da yan uwan nata masheranta karya sukeyi wallahi.

Saida yar takai doya a baki ta gutsura ta dago tana fadin niko mama idan an barni sai ince wallahi ba wani asiri akan yaranki karya kawai suka sawa kansu haka ya faru.

Shifa hamshin har karuwai yake bi mama kuma kin sani shiko yaya habib duk inda wata yar iska ta kwana a garin nan yasan kofan gidansu shikuma ,,,,,,,,,

Ke rufa min baki da zancen banza meye hakan inba asirin da nake fada maki ba haka kawai zasu kama wanan halin tunda ba gada sukayi ba ai duk wanan yana cikin bakin kulin da akai masu din.

To mama N tunda kinsan haka a fadawa baba mana a dauki mataki kar a kaiga kashe mamaki yaya don wanan bin matan dasukeyi yayi yawa wallahi mama.

Sahura yaya zanyi yanzu habib ne kadai nai dan dama a cikinsu dan gara dashi ina ganjinshi gidan nan wani lokaci .

Shi bilya kamar kada akai ga rufe shagon Alh gaba daya abin nasa ya kara sukurkucewa shiyasa nake son zuwa gida in kwana biyu idan naje a san abinyi.

Don na kula yanzu Alh basu ba harni kaunan ganin mu a gidan nan ga zagi kullum.da yake aika muna na bakar ja,iba nidasu .

Itako tana jun dadi to yadda nayi kuka sai hauwa ta fini kuka a gidan nam don ko yaya matan nata ba kyale mata su zanyi ba ai lalacewan mace yafi na da namiji tashin hankali ai .

A,a mama kada ki taba mata yara don Allah ki barta da diyanta saboda Allah abubuwan nan fa mama anata fadawa mutane illan hakan kada yazo ya kaamce bata da alhakin ki abin ya juye ya dawo kanmu kuma haka malamai sukace yana kasancewa.

Ke rufe min baki don Allah kinji kefa na kula baki da wayau Sahura idan da ban kafeku ba tuntuni da matar nan yanzu bataga wallen mu a gidan nan.

Haka kawai ta shigo da rana tsaka tace zata fini komai don kawai anga muna zaman lafiya da mijina suka daukota suka cusa mashi sai sunganni su kama wani rawan kafan tsiya su gasu munafukai.

To bari kiji yadda tayi min karfa ta shiga lamarin diyana koni sai nashiga na fita gaba daya diyanta sun lalace a gidan nan .

Suwa zasu lalace habib daya shigo ya tsaya daga kofa yana tambaya ya dubi uwar ya dubi yar uwarsa kai takai kasa tana fadin magana mukeyi da mama wai hjy H tayi asiri duk lamura suka lalace muna yanzu gidan nan.

Asiri kuma mama ba wani asiri fa cikin zancen nan karewan arzikin baba daine yasa komai suka tsaya haka lokaci gida don bashin da yake biya na mutane.

Kuma ba a hada dukiya da zinaba sahura ta fada ya dan kallota tace eeh mana badashi kuke ta neman mata ba ya habib maganan gaskiya ayita idan yazo .

Abinda kukeyi gaskiya yayi yawa kowa na magana a garin nan ita mama ta kasa gane cewa kudine ya bude maku ido kuke haka sai ta dauka wai wani ya lalata maku lamarin ku.

Murmushi yayi yana fadin ba haka bane mama don Allah habib kada ka biyewa sakaran nan ku baku san komai ba nafiku sanin waye mutanen nan ?

Namu gidan kuma tunda akace an saka ranan bukin salma da Bello innan mu bata cikin kwanciya hankali don mama dake tada fitina don kawai ayi tsiya.

Don tun ranan data fita gidan da sunan zuwa tarbo lefe ta dawo tana sakin arashi wai haihuwan kwarai ke nan dama ai ba a canzawa tuwo suna ba rabo ba gadon arziki balle muga wanan kayan a gidan mu.

Ta fadi irin zancem nam yakai sau ukku ga na ukkun ne data fada cewa yayan arziki na inda suke mu gamu nan sai cika muna gida akeyi da mugun iri ko yaushe wa yandama aka haifa sun zama alkakai balle a karo muna kashin tsiya a cikin gida waya san kalan tsiyan da aka kwaso muna kuma bana ?

Kalan dai dana sama kina zubawane na tashi daga inda kika tsaya ai saidai duk da hakan akwai bambanci kwarai da gaske don gara da nawa diyan har angani an taya su .

Wanda kare baija sai alade fa mama tasan hausan da inna ta mayar mata a ranan ita an taba tayani ai nata diyan ba mutumin arzikin daya taya sai lalattatun tsofin unguwa dake tare da nata.

Fada ya kaure don mama sai tayi abu kamar karamar yarinya ita zata fara jan magana idan an mayar mata kuma tace ai mutum bai isa ba .

Nan ta hau zagin inna nan mu da yayanta tana muna bakar baki a kan mu tana muzanta mu da fadin kalaman da basu dace ba zuwa garemu.

Zakice bada inna take fadan ba don yadda tayi banza da ita bayan ta soka mata maganan da take tsamani ba wanda ya sani a gidan tsohon unguwar mu mai dan hali shike saye sana,an wasila yana shiga shagon shi da ita ranan akai masu a ture aka kamasu akai rufa rufa don diyan mutumin aka rufe zancen.

Sai gashi mama tajo inna na mata maganan a fakaice shine ranta ya baci ta shiga aika muna da zagi ta uwa ta uba inda har take fadin.

Wallahi inna damu kadan muka gani don sai mun zamu mujiya cikin unguwar nan don da goyo ko cikin shege zan dawo garin.

Zagi dai na mugun uba shine mama taita aika mun a lokacin mahaifin mu ya dawo ya samu sunayi yake tambayan ba,asi kowa ya fada mai yake fadin wai Rakiya in tambayeki.

Shin akan mairone aka fara nema aki auren


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login