Showing 267001 words to 270000 words out of 395027 words

Chapter 90 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Banfi mintuna goma sha a tsaye ba ya karaso wajen a cikin wata mota mai bala,in kyau don a gaskiya motar iyakan haduwa .

Haka duk wanda ke wajen a lokacin hankalinshi ya koma a motan don da gani sabo shigowace ba a santa ba sosai.

Haka kuma don aga waye a cikinta ya tsayar da motan ya fito shike tukin abinsa ya fito daga ciki yana rufe kofan motan .

Ya nufoni don tun tsayawarshi wajen ya hangoni inda nake tsaye ina jiranshi din na dan kawar da kaina gefe daya daga kallon da mutane keyiwa motan.

Inda nake ya nufo cikin takon isa da kaisata da matasan zamanin suke tafiya dashi idan suna jin sun kai done a daidai lokacin na juyo mukai arba dashi.

Nauyisa da kunya naji lokaci guda ya kamani shiko naga alaman ko ajikinshi don cikin dakewa ya tunkaro inda nake yana fadin shine kika tsaya a waje ai zan gane wajen tunda nayi trackinh dinshi a motan.

A hankali na dago kai da zuman gaidashi muka sake arba da juna karo na biyu dashi na sake kasa da kai ina fadin sannu da dawowa sir ?

Me kikazo nema wanan wajen ya tambaya yana kallona ido cikin ido mukayi lokacin dana dago in bashi amsa saida na danyi far da idanu ina fadin sai na shiga na gani Amirace nazoyiwa shopping.

Amira sunan kanwatace da nake matukar so a rayuwana tana da kirki ban sanarwa taku amiran ba ko takai tawa kirki ?

Dan murmushi nayi ina fadin finaly kadawo ashe har kanon ya isheka ke nan ka dawo na zata sai kayi sati daya a can din ka kara samun sauki ?

Ya dan gyara tsayuwa yana fadin gida baya isa mutum ai saidai ya barta ba don yaso ba .

Kayana suka iso jiya da dare shine nayi rushing nazo kada ai min ba daidai ba musanman wa yan nan motocin da suka iso kada a samu wanda yayi masu mark ban wurin kinsan wasu mutanen ba tsoron Allah suke dashi ba.

Ban fahinci me yake nufi ba na juya don shiga shagon don tsayuwan ya dan fara isata lokacin tare da fadin ya mutanen gida suna lafiya ya fada sunce a gaidake .

Saudat kamar tayi tsale don murna gaba dayansu gani sukeyi tankar sun gankine da suka ganni suna jin kamar su biyoni na kawosu wurinki yaron nan karami har da tambaya yayi yaushe yaya zata zo ?

A takaice dai ka rama ke nan kaima kaje gidan mu unexpected ba tare da sanina ba kayi irin abinda nayi ko to sannu da kokari angode sun fada min zuwanka da abin arzikin da kakai masu ai.

Banyi hakan don ki min godiya ba tunda da kika kaiwa ummah nata ai bakiji nayi godiya gareki ba ko ?

Au hakane ashe na zata koka godene ai yasa kaje ka rama irin yadda kake zaton nayi ma din kaima ka nemi gidan namu kaje ?

Kinga munyi one one yanzu ke nan inji yan kwallo anyi kunnen zomo a yanzu gidan mu sun san maryam naku gidan kuma sunsan Aliyu abin zaizo muna da sauki ke nan nan gaba.

Murmushi nayi na mika hannu na dauko packed din wani sweet dana gani mai yawa a leda haka muka jera muna dan taba hira mai kama da zolaya wa junan mu har na cika dan kwandon ba tare dana ankara ba .

Da hakan don komai ya ban sha,awa ga yaro sai in dauka muka je wajen biyan kudi ni kaina a lokacin nasan nayi zari wata kila dadin hira dashine yajani ga hakan ban sani ba ?.

Na bude jakkata da zuman dauko kudin dana ciro tun cikin school kan wanan sayayyan da nayi niyar yiwa yarinyar don yadda na barta da safe banji dadin hakan ba a lokacin.

Da sauri naga yasa hannu a aljihun gefen wandonshi ya ciro wrafan yan dubu daya lokacin mai kirga kayan ya dago ya fada mai yawan kudin kayan da muka dauka.

Naji yace yana zuwa naga ya juya ya koma cikin shagon inda ya dauko wasu kaya ya dawo dasu aka hada aka kirga ya bada kudin.

Ina waya da baba a lokacin daya kirani yana min zancen Ozil da har yanzu bai dawo kasan bane koya kira wayanshi bai samun ?

Don ga kaya sunyi kasa sosai suna bukatan balance a karo wasu mutane suna tambaya sosai ana son kayan a yanzu haka.

Baba akwai bayani zan kiraka idan na koma gida ya dan kalloni daga inda yake tsaye yana biyan kudin kayan akai muna parking dinsu waje daya tare da rakamu mota dasu baya ya bude aka loda kayan a ciki muka shiga wani sanyi naji a motan dayasa na dan saci kallonshi lokaci guda .

Tankar baiga action dina ba a lokacin ya nuna saida muka fara tafiya yake tambayana sai ina yanzu nace gida na nufa banda inda zan tafi a yanzu.

Dama da zaran an tashi school gida nake nufa direct sai irin haka idan zan sayi abu nake tsayawa yau ma na bar Amira tana rikici bata zuwa school saboda bata sha tea ba da safe yasa na tsaya in samu mata abin tafiya makaranta.

Yaran yanzu sunji dadin su a baya duk da iyayyen mu nada halin yi muna hakan basu yarda sun saba muna wanan dabi,an ba ko yanzu gida da yawa a arewa bayan dan kudin da suke ba yaro hamsi saidai yaro yaje da yunwarsa ya dawo gida ya samu abunda yaci.

Anan gaskiya basu hakan dabi,unsune wasu iyayyen arewa suka dauka na kashewa yaro kudi tun yana karami akan karatunshi.

Nima lokacin dana zo garin nan nayi ta mamakin abubuwa da dama yadda idan zan tafi school uncle ke ban kudin break bayan abincin da zan tafi dashi.

Ya nisa yana dan dukan sitiyarin mota tare da furzo iska daga bakinshi na dubeshi ina fadin sorry.

Gashi ka kara wahala a kaina bayan wanda kaje jiya kayi a kano lalurar bai karewa a tallaka sai ranan da rai ya karewa bawa .

Naji yace kowa da irin rayuwan da yazo yi a duniya ai dama a hakan da kike gani kinfi dubu idan dubu sun fiki So ki godewa Allah ki dauki hakan yana cikin dalilin zuwanki nan lagos a cikin yan uwa.

Nakan yi tunanen hakan idan naga ubangiji yana buda min duk daba karatu nagama ba amma haka Allah yake rufa min asiri ta hanyar ire irenku dake taimaka min.

Ina samu abin dogaron da iyayyena zasu huta tani ba tare dana kaucewa mahaliccina ba Allah nagode kwarai da taimakonka gareni sir.

Ashe kinsan hakan na dauka haukan kurciya nan taki ba zai bari kiyi tunanen hakan akan ki ba ai wanan shine kabar mutum a yadda ka ganshi baka san cikin zuciyanshi ba kome kaga bawa ya nayi kuwa a rayuwanshi.

Lokacin danaga kina moving da yaran kabilu din nan maryam raina yayi matukar baci da hakan na dauka totaly kin gama lalacewa a wajensu gaba daya ba kamar wanan ranan dana ganki kwatsam a falon Alh sambo.

Hakan yai matukar daga min hankali sosai don a gaskiya na girgiza sosai wallahi tun lokaci naji zuciyana tana izani da kawai na taimakawa rayuwanki ko banza zan samu ladan idan nayi hakan a wajen Allah.

Kawai na shigo rayuwankine da wanan manufar sai gashi lokacin da nayi dabaran kizo aiki a tare damu kuma a karkashin mu na fara nazarin halaiyanki a hankali sai naga ba abinda nake tunane bane halinki.

Haka ba abinda ya burgeni a cikin halin ki sai halin tsiwan nan naki na rashin tsoro da mai da martani akan gaskiyanki danko kinyi hakan daga baya zaki aikata abinda aka umurceki dayi din ki dawo daidai ?

Ya dan juyo ya dubeni nayi kasa da kaina ina murmushi yace Allah nayi maki fadan saka kananun kayan nan masu baiyana surar mace a fili waje duk da nasan baki daina ba har yanzu amma dai kin rage hakan sosai a yanzu ?

Hanyar daya dauka yasa na dan dubeshi cikin mamaki naji yace ba saceki zanyi ba madam, gani nayi suma nan a dan saya masu wani abin tunda suna bukata ai ?

Banyi magana ba har ya tsayar da motan ya fita shi kadai ya fita yace ki zauna basai kin fito ba inshiga in fito ya fada.

Kakan yasa ban fita din ba a lokacin na samu daman kiran mahaifina daya kirani don hankalina yana kanshi nasan zai damu da abinda na fara fada lokacin.

Muka gaisa nace baba dama lokacin ina hanyane yasa ban dauki waya ba yace Allah sarki ina dai kuna lafiya ko dama zancen yaron nan ne nace kaya sun karefa ina son in turo mashi kudin a sayo wasu.

Baba maganan nan akwai matsala a yanzu don gaskiya yau ya sameni da zancen yana son a hada komai a bashi kudinshi zai koma kasan waje da sana,a .

Allahu akbar wanan ai mai saukine maryam banga abin damuwa a cikin zancen nan ba kudi na nan ko yau yake bukatan abinsa ba sai an kai gobe ba mairo sai a turo a bashi .

Amma baba da dai,,,, a,a maryamu kudinsane fa amana suke a wajen mu yarda da mutunci yasa ya zabeki ya bamu haka kuma ina taka tsantsan da kudin nan don dukiyan yarone bana babba sa,ata ba kinga dole ko don mutunci ai in kula don haka ba wani ja in ja bari a bashi kudinsa don Allah.

Abinda na dan samu har nake dogaro dashi a karkashinsa wanda bai damu da dogon riban da za a samu da kudinsa ba duk da yasan ana samu din duk da nima ba wani riba nake sakawa ba mai yawa.

Gashi kuma duk lokacin yana ganin abinsa daidai na nake tura mashi kinga ai yaji dadin hakan yasa har ya kara yawansu a kwanaki kudinsa na nan cas a banki ban taba ba .

Ajiyan zuciya na sauke don hango shi tafe shiko baba yana fadin eeh ki kwantar da hankalinki inkin natsu sai ki kira in maki bayanin komai Allah zai kawo wani mafitan a samu madogara garemu ai ko hakan an samu an godewa Allah koda kadan kadan sai inci gaba tunda mutane sun gane wajen namu a yanzu .

Kit na kashe wayan a airplane mood don kadama ya kirani in rasa abin fada mai don ban son sam oga yasan da wanan zancen balle yace zaiyi wani abin a kai.

Ashe ban sani ba ance kowa ka gani tsaye lagos kada ka tambaye yadda ya mike don bai shigo ba sai da ya shirya shiga kwaram dinta .

Dan kuwa tun kafin ka iso ka santa kaji kirarinta kasan abinda zaka sama a cikinta don da wuya ka samu ainihin dan garin lagos a yanzu yan asalin garin saika tona don akwaisu haifafu yan garin masu sana,an kifi da kayan lambu.

Ashe ban sani ba motar da nake zaune cikinta duk security ne tare da record dinta zai iya ji komai koda wasu suyi atterm din dauke ko wani hayani a kusa don haka yana jin duk wayan da nakeyi da mahaifina.

Gareku mata masu zagin maza a bayansu wanan kalubaline gareku a yanzu duniya taci gaban komai da na,ura akeyinshi yanzu don kina cikin motar mutum kina surfa mai zagi har da kiran gara wasu keyi ga maza.

Bayan an gama saka kayan an mamatsa su motan ya dauka ya nufi gefen masu saida nama a bakin wajen shima aka sayo suka saka mai bayan mota ya shigo muka dauki hanyan gidan mu.

Shiru nayi don imanina ya mutu a lokacin wanan hidima tayi yawa kwarai da gaske shi maiyi ne haka yake dai ina gani amsan da zuciyana taban ke nan a lokacin .

Na girgiza lokacin guda daya jefo min tambaya yana fadin yaushe wanan yaron yace yana son kudinshi ?

Da sauri na juyo a zabure na dan kalleshi yadda ya dake yasa na juya nima ban iya furta komai a gareshi ba don kila ba zancen dana gamayi yake magana a kai ba.

Bakiji bane zancen me kika gama fadawa baba yanzu ko kin dauka banji komai bane bayan fitana motar AA kike zaune a ciki fa a cikinsa duk motsinki yana ga idona ai.

Naji me kikai waya a kai yanzu da baba watau ni ban ci darajan ki soma fada min ba asan yadda za ayi kafin ki kira baba ko har yanzu banyi darajan sanin matsalan ki ba ?

Kin kuwa san nauyi da irin girman fadawa mutum irin zancen nan haka kai tsaye da kikayi yanzu ga mahaifinki ?.

Sana,an nan dashi dattijun nan ya dogara yana wahala sosai ba zama ba tsayi yaga ya kula da wanan nauyin kada aji kunya kamar yadda ya fada.

Ke baki san hakan da kikazo mai kai tsaye da zancen yana iya haifar mashi da hawan jini ba don haka ki kirashi a turo da kudin zuwa gobe ni zan san abinyi kafin nan da wani sati insha Allahu .

Shiru nayi a lokacin na kasa furta komai kaina a kasa duke wanan shine no way to escape da ake fadi banda hanyar musawa akan komai daya fada a yanzu don yafini gaskiya.

Haka shine rayuwan lagos din da ake fadi ka dafa wanan ka dafo wancan don ka mike tsaye kaima da kafanka babu kyashi babu hassada ga kowa mutukar ka iya rikon amana yanzu za aji sunan ka kaima a gari.

Tsayar da motar a kofan gidan yasa ni sauke ajiyan zuciya ana zafi a lokacin yawancin matan layin duk suna waje suna shan iska da yaransu tunda ba musulmai bane ba a damu da addini ba a rayuwa.

Haka suka zubo ido don gulma nasansu nasan dabi,ansu irin wanan zaman na marance zamane zaman saka ido ga sauran gidaje ana gulman wancan da wancan idan sun gilma.

Naji dadi lokacin da muka fito motar dashi tare ya fara taimaka min da kwasan kayan zuwa cikin falon mu yana ajewa nima na dauko na bayan sit din da basu da nauyi yake fadin waya sakaki bari in kwashe in samu ladana ni kadai.

Hakan ya dan sani sakin murmushi na koma gefe daya ina kallonshi kafin nayi dubaran shiga gida na taso da antyna dake daki kwance tana kallo a wayan tab.

Ina shiga nake fadin taso anty ki gaisa da Sir Aliyu a waje kafin ya wuce yayin dana juya na koma da sauri don nasan yana iya wucewanshi a lokacin idan ya gama kwasa basai yaga fitowana ba.

Aikuwa din ya aje last one daya dauko uncle rice irin buhun nan medeiums guda biyu yana dan kakabe jikinshi ya dago yana fadin okey take care sai munyi waya ke nan naji ya kukayi da baba lokacin antyna ta leko tana fadin a,a kika barshi tsaye waje haka maryam ?

Cikin dan kunya ya juyo yana fadin ina wuni lafiya ya baka shigo ba daga ciki ka tsaya a waje ance nazo ga Sir A A yazo na zata kana falo ai zaune ashe kana waje ?

Ka shigo mana daga ciki da sauri yake fadin a,a hjy ina saurine ayi hakkuri don Allah hanya muka hadu na rage mata next time zan shigo insha Allahu.

Antyna ai mashi godiya wanan kayan ya sayo muna what wanan abubuwan da nake gani haka haba dai haba ya zama wahala kuma for my surprice naga kayan ai nake kallo ina fadin ina muka samu abin arziki haka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login