Showing 375001 words to 378000 words out of 395027 words

Chapter 126 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

saudat .

Na dago ina fadin kinsan inna ba zata tareni ba ai sai mama a bayana naji sahura na fadin ga maman naki nan zuwa ai ta tareki.

Jin hakan yasa na juyo inda na hango mama din fitowa kamar me koyon tafiya da sauri na sake yaran zuwa gareta da alama nauyin kafan da hannu yanzu ke damunta na tareta muka fara gaisawa ina mata yaya jiki ?

Maganan ma sai a hankali take iya yi duk taban tausayi muka taka har kofan inna dake rungumar yayanta a cikin murna.

Banjin cewa sun taba haduwa dashi da inna duk zuwan da yakeyi saidai ya tsaya daga kofa bai shigowa amma a ranan har falon inna yake zaune.

Tare dashi mukaci abincin da inna ta tanadar muna na taron yayanta duk da ta kasa sakewa dan ganinshi ya jima damu dashi da yusuf din kafin su mike sukace zasu shiga gidan malam daga nan din.

Sai bayan tafiyansu inna ke fadin yanzu yaron nan shike da tarin arziki irin haka dama nina zata zan ga wani babban mutum sai inga yaro karami haka wanan aiko sanin gidan nan bai kaiba a shekaru ?

Dan karami mai kayan aiki ke nan inna haka ko ya kwashemu mun kusa mu ashirin zuwa umuran nan duk a karkashinsa muke yaya sahura ke fadin hakan wa innan mu.

Ni ai ban gajiya da kallonshi inna ga zafin nama ga mutunci kai bari maryam Allah ya hore mata miji na gwadawa duniya ba tsara ba kawai .

Inna idan Allah yaso ka tsuntuwa yake baka da a garin nan maryam take yaushe zai tsaya sanin wata maryam can aida yanzu an rufeshi da yan mata ba iyaka.

Yaya tun ina karama ya sanni fa amsan dana basu ke nan suka juyo nace kin tuna da idan aka aikeni da nake tsayawa in zanewa mutane mota da rubutu har daddy su salma ya kawo karana wajen baba mama tayi min dukan tsiya.

Suka kwashe da dariya nace tun a lokacin ina motar nan da ake ajewa a wajen katangan gidan malam mudi kekeke natuna na dai basu labari suna fadin ikkon Allah dama Allah yayi matarshine ke.

Kon gani ko innan mairo shiyasa akace zato zunubi ko yazamo gaskiya ki duba da ake fadin wai abokin shanshacintane dama tunda a can suke tare ashe abin ba haka bane kinji ko ?

Innan mu tayi dan murmushi kawai mai nuna na ciki na ciki a bar zancen yaya sahura ta hada da dan tsuki tana fadin ko wanan daukan alhakin bai ishi mutum ba don Allah ?

Ba abinda ba a fada ba a garin nan kuma duk a gidan nan zancen yake fitowa a juyashi gidan nan fa matar yaya ta tambaya ?

Sai naga kome yaya din ta tuna sai tayi shiru tana fadin Allah dai ya gyara kinji yama gyara ya kara fata nagari lamiri inji yan magana.

Yaushe mama ta dawo gida na kawar da zancen da tambaya matar yaya din tace yakai kwana takwasa yanzu an dai dawo gidane kawai amma ai har yanzu dai tana jin jikin.

Ina yaya murja na tambaya cikin son jin inda take sai naji tace kice uwar tuwo dai tana shago ai tace da wuri zata dawo yau ta tareku ga abinci ma data aiko dashi dazun a baku inna ta fada.

Tana bude abincin da gaskiya ya hadu tuwone an tukashi lumui dashi yana nason zufa a cikin leda irin tukin nan na yan tueon dake tashe sai miya da manyan nama.

Naji inna na fadin nasan sai zuwa anjima ku bukaci tuwo yasa na ajeshi gefe daya har anjima kuci nikan a raina nace badani ba wallahi.

Mun zauna anyi hira sosai a wajen kafin lokacin sallah muka watse don gabatar da sallah din.

Shikuma yana barin wajen mu gidan malam din suka tafi an gaisa malam yaji dadin ganinshi a lokacin sosai sai dai yake fadin gadanga ka rame mana ka fada kamar aikin hajji ka tafi ba umurah ba ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[11/4, 10:02 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊1️⃣0️⃣0️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Murmushi ya sada kai kasa ya soma fadin malam lafiyata kalau kawai dai jigilace yayi min yawa ko a can ban zauna ba don ina kulla wani bissiness da za a fara yasa ban samun hutu.

Amma duk da haka ka rage wanan a yanzu kai magidancine ka koyi bawa iyalinka hakkinsu suma iyali suna da lokaci ya kamata anayi ana basu hakkinsu don gujewa fadawa fushin ubangiji.

Baba kaida kaje ibada da hutawa ina kai ina daukarwa kai wani harkan kasuwanci kuma yanzu a can aida ka bari idan ka koma daga baya saika jona wanan din ?

A dinga kula sosai da hakki akan mutu domin shi amana da kake gani kamar tsiro yake yado yake yai yawa har yaso yafi karfin ka abinda kake gani ba komai ba shike zama komai wata rana .

Malam nagode ya fada a cikin ladabi ya dora da fadin idan na huta zan dawo in sanar dakai abinda yake gabana din ko in kira a waya in sanar maka komai.

Hakan zaifi don a yanzu kana bukatan hutu ita matar taka tana ina tana gidansune ko ta koma lagos din ko ?

Tana nan gidansu yanzu muka saukesu sai zuwa jibi da safe zamu wuce lagos din dasu don zata fara zana jerabawanta na karshe a jibi in Allah ya kai mu.

Sun dan jima suka tafi sai yammane malam iliya ya shigo da kayan mu gida aka saukewa kowa nashi don ba bace suke ba kowa da sheda a nashi don haka na bangarena gaba daya aka sauke a gidan mu nasu kuma a can gidansu akai saina bangaren gidan malam din shima tare akazo dasu da namu sai muce Allah ya saka da alheri kawai a wanan hidimar don an fitarwa dukiya da zakkanta a lokacin gaskiya.

Nan kowa yaja nashi ashe Paapa yana gari a ranan ya iso don tare sukazo da antyna suka kwashi kayansu zuwa can gidansu.

Da ace tun farko basu saba min da in munzo in sauka a gidan mu ba wajen iyayyena da dole ina can tare dasu wanan lokacin amma haka suka saba min dashi yasa ko wanan katon a gidan iyayyena na sauka ba wajensu ba.

Don lokacin da suka zo daukan kayan bansan dalilin antyna na cewa muje can din ba da sauri paapa yake fadin No ta zauna nan ai tun farko baki saba mata da hakan ba ?

Da can zata zauna dole yanzu ai abinda nake fada maki ke nan a baya yanzu gashi yana faruwa bansan dai akan me suke zancen nan ba sun gaisa dasu inna sunyiwa mama ya jiki kuma suka tafi.

Na bude dan jakar dana riko tsaraban yan gidanmu su inna mama sai baba da kannena Abdul da muri sai kuma salma da yaranta biyu sai anty fati har da yaranta dukka ukku salis ma da isa na basu jallabiya iya abinda na riko ke nan sai dozin din jallabiyan mata da zan bawa matan barikin mu idan mun koma lagos duk da ban sallami kowa ba da zamu zo din ita anty banjin ta fada masu zamu tafi din.

Saudat nabawa a gabana washegari ta kai na gidansu anty fati din dana salma data dawone take bamu labarin yadda hjynsu tayi dataga sakon.

Ta rasa me zatace kadan kadan ta nisa tace o,o mairo ashe bata manta da kawancensu ba har yanzu ?

Sai yamma yazo ya daukeni muje asibiti dubo hjy gidansu dake can din duk da ban dauka a dawanau take ba sai da naga signboard din asibitin na fahinci kan zancen.

Ba a dakin mahaukatan nagidi take ba amma dai ai girma ya zube duk wanda aka kai wanan wajen ba a taba daukanshi cikakken mutum mai hankali kuma ?

Mun samu yaranta kaf a wajen suna daga waje zaune sunyi shiru da alama akwai wani abu mai muhinmanci da suke tattaunawa a lokacin muka iso.

Bayan mun gaisane tare da anty Sadiya yar ta da muka je umurah muka shiga ciki don duba mahaifiyar tasu.

Sai Rukkaiya ta biyomu daga baya muna shiga naga wata bakar mace a zaune ta dan manyanta a shekaru tana ganin mu ta mike tsaye.

Ta dago kai tana fadi tau kun iso ba sai ku kaini gida don Allah ina ne nan kuma suka kawoni don a kasheni ?

Dama ku nake jira kuzo mu tafi gida ina da sisin gwal guda da azurfa wallahi zinarena ai kinsan da zamu yelwa na badashi ?

Saita daga hannu tana nuna muna yawansun hannunta tana fadin daham dina babban akan banza na karyashi fa ?.

Gabana ya soma faduwa fal fal fal don yadda take kallona gata bakar mace sosai gashin kanta duk ya cushe a waje daya baka ko gane wani irin kitsone a kanta don dadewan da kan yayi a haka ?

Haba mummy matar Aliyune fa daya aura tazo amaryanshi ke nan da mukaje umurah da ita ?

Tazo gaida kene da jiki kuma kike haka yunkuri daya tayi sai gata ta a gabana kamo hannuna tayi tana fadin to to to zo ki zauna a kusa dani kinji zauna tana nuna min wajen zama a gefenta.

Ba komai a bakina lokacin sai addu,an da duk yazo min a baki gashi tayi min wani irin mugun riko irin kwace mu gani din nan sai zaran ido nakeyi ina mai da numfashi guda guda saboda tsoro.

Tana fadin yarinyatace data bata ashe kina nan kika gudu kika barni ina kika shiga ina neman ki ban ganki ba ?

Sai wa yan nan shegun nan nake gani kullum munafukai kaiwa sai Allah ya tsine maku gaba dayan ku ku kai mu gida nida yata nace.

Mummy za a kaiki gida sadiya din ta fada tace saketa sarakuwarki ce fa kin kuma riketa haka tana kokarin kai hannunta ta kwaceni.

Barsu naji yace da sai lokacin yai magana tunda muka shigo wai Aliyun hauwane nan dama kun hada kai ko ?

Aliyu idan bakasa aka kaini gida ba kasan halina zansa a halaka min kai a wajen nan don Allah mummy saketa mana ki natsu yar nata ta fada.

Ku kaini gida nace daku ga yata tazo ku kaimu gida inyi mata shimfida ta kwanta duk dai a kaina take zance tun shigowan mu tana ban labari da baida kai ko gindi irin na marasa hankali.

Yanzu me likita yace akanta ya juya yana tambaya to mun daice a bamu sallama don kamar ciwonta bana gargajiya bane yace sai Abba yazo .

To a kaita gida mana da alama tagaji da nan din yasa take ta maganan haka tun dazun akaita gida din zaifi ya kara fadan hakan.

Aliyu aiba komawa gidan ba wa zai zauna da ita a gidan wanda zai tsaya ya dinga bata kulawa yana dubata ko wani lokaci ?

Don me zakice haka haba dai in dole ya kama ai dole a tsaya ayi kamawa yayi hakan ba wanda yafi kusanci da ita yanzu bayan ku.

Hannun nawa dake rike da nata ta daga tana fadin ga kusancina tazo ai nace daku yata ta dawo gata kuna gani.

Kowa yayi shiru a dakin ya nisa yana fadin zancen nan na hjy dole a koma addu,a tunda tana fahintar komai ake fadi kinga kada a ajeta a nan abin yazo yafi haka kuma ?

Su dai ta maganganunsu kamar an tsikareta ta sake hannun nawa ta kamo nashi tana dubawa kamar tana neman wani abu a jikinshi a hankali naja baya na fice daga dakin.

Matar ta matukar ban tausayi yanayin dana ganta a cikinshi ashe kuma a dakin haka tayi ta dubanshi yana tsaye kurun kafin tace dashi ja,iri kawai ta sake mai hannun kamar a cikin fushi.

Ya fito suka samemu da wanan matar dake tsaye tana min labarin jikin hjy ina saurarenta iya wanan matar dan uwanne gashi ai kinsanshi ko ?

Rukkaiya ta fada ita rukkaiya da Na,ima halinsu yaso guda saboda nakasa ke garesu idan ka fara ganinsu sai kaga kamar suna nakasa kane a irin kallonsu.

Dama nazo da kaya bayan mota yanzu kuma ana zancen komawa gida yaya za ayi dasu ke nan ya tambaya ?

Gaskiya da a ajesu a gida kawai ko don gaskiya banson a kara kwana asibitin nan wanan inba dole ba mai zai kara tsayar da mutum wanan waje ?

Yanzu dai kayi mashi magana kai don munyi magana da Abban da safe ya hau mu da fada yana zagi don mun soma zancen komawa gida yaya zamuyi mu dai muka kyaleshi.

Ba matsala zata dawo barinta wurin nan tunda likita yace matsalan ba babba bane gara akoma da ita gida a fara wanda Abban yace za a kawo daga maiduguri.

Sun rakamu har wajen mota a nan ma sun tsaya sun danyi magana duk a kan uwar tasu inda suka yarda ayi allura din da likita yabada shawara duk suka amince da hakan .

A tunanena Nisai nake gani kamar sun matsune subar wanan wajen don wajene mai hatsari ga mutum gaskiya aiko bankai ga karshe ba yana rufe mota saiga wani mutum ya kurce an biyoshi da gudu yan uwa da malaman asibitin yazo ta gaban mu ya wuce a guje yace su koma ciki zai saukeni ya dawo ya kwashesu a koma gida.

Wanda sam da babu magana kota fatar baki a tsakaninsu in banda jin kai da isa da izza da takama da suke nunawa kowa don irin tarbiyan da suka bude ido dashi na jahilci.

Amma yanzu Allah ubangiji ya kawo masu maslaha ta hanyar da duk basu zata ba a tsakanin zumuncinsu an soma tafiya a tare irin na yan uwantaka.

Saida muka fara tafiya ya nisa yana fadin Allah ke nan maiyi yadda yaso da bayinsa yau hjyce a cikin irin wanan halin haka ?

Matar da komai girmanka ko darajanka baka da kima ko mutunci a idonta tana iya tsayawa taciwa kowaye mutunci ba tare da damuwa da abinda ta aikata ba.

Jahilci da kauyanci ya taru yayiwa rayuwanta illa tana ganin dan adam a matsayinda bakomai bane a wajenta saboda izza irin nata.

Wasu haka suke tana da bambanci da maman gidan mu don mama sam ba haka halaiyanta yake ba ita dai a barta da bakin kishin nan na mata kuma akan innan mune nata.

Ni kan dai wanan dakin da baban mu keja daga gefe yanzu shine ya daure min kai amma ina tunanen ko yaya Ibrahim ne zai zauna a ciki da iyalinshi sai kuma baji inna na fadin wai an samu wani dan gida nan kusa damu za a sayawa yaya ibrahim din su koma ciki don baba yace ya dawo gida hakana yanzu da iyalinshi.

Kinyi shiru mana naji muryanshi yana fadin hakan na dan nisa ina gyara zama nace ina dai tunanen duniyane kawai .

Dolene hjy niko mahaifiyata tayiwa fatan hakan da take ciki yanzu don kirarinta ke nan a kan mu tace min mahaukaci ko ta kira ummah da sai sunnu da bakin ciki ya kasheta a gidan mu.

Yanzu gashi mugun fatanta ya koma kanta itace dai bakin cikin yakai ga hakan a karshe ba komai bane yasa kwakwalwanta tabuwa sai rashin imani da yarda da Allah ?

Abubuwa Allah ya kawosu a lokacin da bata taba zaton hakan ko tsamaninsu ba sai gashi taga abu ya juye ya koma yana son fin karfinta a yanzu.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login