Showing 177001 words to 180000 words out of 395027 words

Chapter 60 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

abin zaizo maki da sauki don naga kina son madugara kina kuma son karatun ki so wanan ba wani abu bane mai wuya idan an tsara din.

A sake ina nuna farin ciki a fuskana nake fadin well idan hakan baida matsala a wajen nima nagode Allah kara budi da girman matsayi.

Ban daiji ya amsa min ba illa kallon lokaci da yayi a agogon hannunshi yana fadin magariba ya kusa ban son na rasa jam,i a rayuwana.

Ok ruwan ya rage ina iya fita yanzu ai na fada bayan mota naga ya juya ya mika hannu yana dauko leman dake aje a bayan ya miko min yana fadin karbi wanan kada ruwa ya tabaki nace dashi aida kabarshi tunda dan takawa zanyi nashige ciki.

Kin magana yayi sai miko min leman da yakeyi na karba na sake godiya a gareshi da halarcinshi zuwa gareni kai ya kada yana fadin na kara amsawa da wanan godiyan nafice da sauri ina dan hadawa da gudu zuwa dan coridon da zaka tsaya ka shiga namu block din.

Lokacin naga yayi ribas ya kunna full light din motan tana wani kara alaman engeny dinta mai lafiyace ya juya yana min horn ya bar haraban namu.

Ajiyan zuciya na sauke na juya tare da murda kofan don nasan a bude zan sameta don bamu damu da yiwa kofan key ba sai safe koda dare haka.

Zaune take a falon part dinta da aminiyarta wace tazo mata dubiya suna cin abincin rana da aka aiko dashi daga bangaren hjy hauwa ta dauki cinya takai ga baki ta yaga ta soma fadin.

Hjy Ladi gaskiya mutumin nan bai kyauta min ba gashi yanzu ya barni a zaune haka ina wahala ni kadai nasan irin bakin cikin da nake kumsa a wajen nan yanzu.

Gonata ta gado naje na sayar a dalilin dan banzan yaron nan don dai inga dagashi har uwarshi sun salwanta dan cewa yayi zai min aikin da rayuwansu zai gurbata su koma abin tausayi ga mutane karshe gashi nice zaune a yanzu Ladi ?

Duk na san da na samu nasaran yin aikin nan wallahi da kashinsu ya bushe a gidan nan don sai sunyi nadamar shigowa cikin rayuwana wanan karon.

Amma yanzun ma ai ba ,a makara ba ina nan ina tara dan kudin da nake samu ina jin sauki zan koma ayo min wanan hadin don gaskiya hankalina ya kwanta da aikin mutumin nan sosai.

Don bakin cikin da Alh ke tura min ko akan wanan jinyar da nakeyi abin yai min yawa Ladi hatta ruwa da zansha a gidan nan ta hannun wanan yaron kudin ke fitowa fa Ladi komai da kika gani yanzu gidan nan wanan dan iskan yaron shine mai turawa ayi Ladi.

Abin takaici wai shekaran jiya Habib yazo nan yana fada min a gigice wai yaron nan ya kara bude shaguna da zasu zauna shida dan uwanshi don shashanci da rashin sanin ciwon kai wai sune masu zama su tsare shagunan kamar yadda ubansu keyi a yanzu kudin sai a tura mai da abinshi.

Hjy Ladi dake tauna nama da karfi donta cika baki dashi lokacin tace watau kice min ana kura da shan bugu gardi da kwace kudin nai yana can kwance sun koma suna mashi wahala a nan ?

Hjy Naito din tace kin gane ke nan Ladi Allah ya sauwake hanyar jirgi daban ta mota daban ba zan taba yarda da wanan shashancin ba wallahi sai inda karfina ya kare .

Kwarai kuwa mutumiyar nasanki sarai nasan baki barin abu sai kin cinwa bukatanki a kanshi wanan karon idan za ayi ayi marus don Allah kowa ya huta haba suna ta wahal dake haka sun hanaki sukuni a rayuwan ki haba dai don Allah.

Kinganni Naito shiya duk gidan da zan shiga in dai zan aureka to sai na tabbatar daka gama data gida kafin in fada gidan idan kuma naje naga bakai min ba in gudu in barka da tsiyarka ku karkare a hakan yo ke na iya tsiya ?

Aini ban iya zaman irin wanan naku na gigi a waje daya gara a raba hannun jari in aje nan in aje can duk wanda ya fadi muna da kaso yafi min irin naku din nan na jiran tsamani.

Amma ke kan ba mutumiyar arziki bace ke mutum a haka a cikin irin halin nan na bautan Allah zaki zauna kina nausar da ita hanyan halaka ?

Yayan hjy Naito Amina itace tsaye a kansu take wanan jidalin dasu don a lokacin tana kuryan dakin tana nafila suna falo zauna sam sun manta da cewa tana gidan saboda mugunta dake cin zuciyarsu.

Dole kika hakan Naito dolene abinda kika daukone ya koma kanki dama ance abinda ka shuka shi zaka girbe kin dauko da sunan yaron nan Allah ya juya abin akanki ke wanan duk bai isheki ishara ba Naito ?

Karsheb ki halaka a kafurce naito matukar baki tuba kin koma ga Allah ba zakiyi mutuwan da ba,a son musulmi dashi naito.

Ke kuma in dai abinda ke kawoki ke nan gidan nan zan fadawa mai gidan nan ya dakatar dake da shigowa gidanshi haba Naito sai yaushe zakiwa kanki fada ?

Matukar kina bin irin mutanen nan da babu Allah a gabansu to karsheki dai saidai Allah ya kyauta rashin imanin nan naki yayi yawa .

Ki duba meye nan a gabaki don Allah daga ina ya fito daga wanan matar da danta ko wanan abin da suke maki bai isheki tunane a kanta ba Naito.

Duk abinda kikeyi kamar taki kike zubawa rayuwansu tunda su basu binki da mugun nufi irin haka kinga ke nan duk abinda kika dauko kanki zai bare Naito ya kamata ace kinyi hankali hakana don Allah.

Ke kuma don Allah kwashi takalman ki kibar gidan nan kafin nasa yan gidan nan suyi maki tujara na karshe a cikin gidan nan tunda ba alheri ke kawoki gidan nan ba.

A hankali hjy hauwa ta juya da zumar barin wajen hankalivtashe da abinda taji gun yar uwar kishiyar nata ya tabbata ke nan hjy Naito taje masu sherine ya koma kanta da Allah kadai yasan abinda ta nufosu dashi lokacin ko ita ko danta ko kuma dukkansu ga baki dayan tunda duk bata kaunasu gidan.

Har ta juya sai kuma ta saike juyowa tashigo dakin da sallama a bakinta jikinta na saye cikin babban hijjab blue mai maiko.

Take fadin yaya ina daki na juyo muryanki haka na taso ina lafiya dai gaba dayansu suka kurawa yaya Amina ido sai cewa tayi bari hjy Hauwa ke dai wanan abu yayi yawa wallahi.

Ayi hakkuri yaya don Allah rayuwa sai hakkuri duniyan nan har nawa take gun bawa mu dinga saka hakkuri a cikin lamarin mu.

Ko wanan abin daya samu yaya ai isharace a garemu mutum ya fita lafiya ana sai kin dawo sai an dawo Allah ya saukar da ikonshi akan bawan shi wanan kadai ya isa mutum tunane ?

Koma meye mai wucewane idan akayi hakkuri rayuwama bata daure har abada ba balle abinda rayuwa yake nema din .

Ke kika san wanan hjy hauwa wasu kam ai duniyace kawai a gabansu zakice su suka halice kansu da kansu ba a mutuwa a koma ga Allah.

Ta juya ta fita don ta fahinci hjy naito bata so shigowan nata dakin ba lokacin yadda ta daure fuska ba annuri kamar wace taga mugun abu.

Fitan ta yayi daidai dana hjy Ladi wace ta mike da sauri tana fadin hjy Naito ni zan tafi Allah kara sauki saidai idan munyi waya kuma ?

Daga haka tafice daga gidan nan yaya Amina ta zauna da Naito din nasiha masu ratsa jiki take mata zakice ta dauka a lokacin don yadda tayi shiru tana saurarenta a haka har yaran nata mata biyu suka shigo gidan suka samesu sai a lokacin tayi shiru.

Babu komai a cikin dayan buhun sai kayan abinci irin taliya shikafa indomei macaroni cuscus da kayan shayi su maggi da sauran abubuwan amfani naci suna jido masu don wautana tun a can.

Dayan buhun kuma kayane na kannena da nake saye ina tarawa da sunansu sai reciever na decoder wanda zasu hada tauraron dan adam sai dogayen riguna na sister dina da turamen zani sabule omo su dan kunne dozen dozen masu kyau irin rakwashan Lagos da ake zubewa a ciki sauki.

Tarkace dai iri iri na hada masu apack din arewa da mukaje rakiyansu din shine naba driver kudi daidai wanda ya dauko mutum yayi min alkawarin zai kaita da kayan har gidan namu da nayi masu kwatance tun acan din.

Bin kayan baba yayi da ido kafin ya nisa yana fadin duk ita mairo ta turo da wanan abin duka kamar za a bude shago dasu Ai ?

To ai shine nima nake tunane don hankalina ya tashi gaskiya da ganin wanan abin haka tunda ba aiki takeyi ba a can wanda ke karatu ina yaga kudin sayo muna wanan abin ga kudi kuma bayan wanan wai mu sai shinkafa a nan na amfanin mu nan gida ikon Allah ya fada yakai zaune duk yaran suka bishi da kallo.

Tau Ai ni dai in badon baka shedan dan yau ba da sai ince nikan na sheda mairo ba zata kaucewa tarbiyan da muka dorata a kai ba.

Haka kuma har in wani abin asha Mairo keyi a can na tabbatar da labari yazo a kunnen mu yanzu duk da nisan dake tsakanin mu dasu yanzu.

Haka kuma na tabbata da Faruq ya kirani ya fada min don shedan gudun mu zargeshi kan hakan da zai kira yace muna ga halin da yarmu suke ciki da ita amma kinga bai taba kira yace wani abu ba.

Haka kuma tazo garin nan mungani bata rage komai cikin abinda muka santa dashi a baya ba kinga wanan kadai ya isa mu sheda abin mu da kan mu ba sai mun dauki jita jitan mutane a kunnuwan mu ba.

Saidai shi bincke din yana da kyau duba ga ba wani sana,a taje yi can ba a ina ta samu kudin da tayo muna wanan uban sayayyan haka masu yawa.

Don haka zansa kudi a wayana zan kira shi babban nata in fada mashi koda zamu tsunci wani abu sabanin tunanen mu kan zancen.

Ke uwale zo ki karbo min kati in saka idan na dawo sallah sai in kirashi muji ko yana da masaniyan hakan akanta ?

Haka yafi don,ni gaskiya hankalina ya daga da ganin wanan irin abin gashi har an fara jefa min magana ana fadin bariki yai dadi ke nan wanan irin sako haka ?

Rakiya ko aiki barta itama uwace kamar kowa abinda ka jefawa dan wani koda ya aikatane kaima sai ubangiji ya jerabaka da hakan akan ka wata rana addu,a ga dan kowa shine alheri koda kuwa kan dan kafirine don baka san ko watarana sanadin addu,anka gareshi ubangiji ya sauya shi zuwa islama ba.

Koda ya fito dakin mama na zaune wai tana gyaran wake tana jin duk kusan abinda ke wakana a dakin lokacin tunda ba tausa murya sukeyi ba.

Maganganun baba yasa zuciyan inna yin sanyi don gaskiya ya fada tambayan shine amfani a yanzu haka kuma duk da zuciyarta akwai fargaba amma shi tambayan yana dadi.

Sun gaisa a cikin mutunci tarewa juna tambayan bangajiya na taro lokacin ya fara fadin dama wani taimako nake nema gunka yasa na nemi lambar wayanka don in kiraka.

Ikon Allah a wajena kuma ehh duk da dai nasan zakai mamakin hakan amma nace bari dai in tuntubeka na nemi izinin hakan a wajen ka ?

Allah yasa abin baifi karfina ba uncle Paapan ya fada har lokacin yana mamakin dalilin kiran matashin dan kasuwan gareshi wanda shima ya sanshine ta dalilin abokinsa usman wanda yake yawan ganinsu tare lokaci lokaci a dalilin shi kuma ya biyoshi yazo mai addu,an sunan gidanshi.

Dama yarinyar nan ta gidanka wace ke sana,an engent tare da company V O limited nake son don Allah in samu mace bahausa wace na yarda da ita zata danyi aiki nan tare damu na dan lokaci .

Kai haba madallah naji dadin jin hakan malam Aliyu hakan yayi sosai ba matsala insha Allahu saidai gaskiya matsalan da za a samu dayane don bata karasa karatunta ba har yanzu.

Don ko wanan aikin da takeyi na dakatar da ita don sam aikin bai min ba tafiyana mission din nan dana danyi shine na dawo na samu tana wanan aikin a yanzu kuma na dakatar da ita da yinsa don sam bai kwanta min ba don ba tarbiya a cikin wanan irin aikin garemu hausawa.

Murmushi yayi yana fadin I know wanan yasa da muke nema naga mu dauketa kawai a wajen mu zaifi don munyi wani deal da ita a nan na santa.

To gaskiya bata hada karatunta ba har yanzu kaga kuwa akwai matsala ga hakan gaskiya da sauri yake fadin.

No no no wanan aiba matsala bane abinda muke nema dama kwaraiwa aikin ba wani aiki bane mai tsanani haka sosai ai tura sakone da bayanan kamfani ta email din mu .

Godiya sosai Paapa ya fara mashi inda suka dan taba hira kafin suyi sallama don haka ya dawo gida da murna yanawa matanshi albishir akaina din.

Kodana dawo Paapa ya fita antyna ta soma ban labarin zancen da mijin nasu yazo dashi din na samo min aiki a wajen wani abokin hurdansu kuma shima dan kanone mazauni lagos.

Sosai nayi mamaki dajin hakan a fili nayi farin ciki da hakan amma a zuciyana ina tunanen yaya zanyi da wacan mutumin dake shiga rayuwata wanda yake da bukatan inyi aiki a tare dasu don sam ban kawo zancenshi a raina ba lokacin.

Ban hadu da Paapa din ba koda zai dawo lokacin har nayi barci haka kuma da safe nakan fita basu tashi daga barci ba a gidan.

Wanan yasa sai inyi kwanaki bani ganinshi shima hakan a cikon irin kwanakinne babana ya kirashi a waya.

Suka gaisa bayab gaisuwa ya tambayeshi iyalinshi ya amsa da suna lafiya yake tambaya ashe an samu karuwa harda rabo basu da labari ?

Ya shiga bawa baba hakkuri saboda nisa yasa ba kowane yasan da zancen auren nashi ba yaro yaci sunan Al,amin yayi mai Allah ya raya.

Baba ya dora da fadin muma muji saida wanan yarinyar ta wajenka ta turo muna da sako wa mutanen da sukaje suna shine muka sani.

Nace yarinya da rigima sako haka kamar wata wace taje sana,a harda tsaraba haka mai yawa ta turo muna dashi gida fa ?

Haba dai kasan da yake nan mutum bai zaman banza to anturani iyakar boda aiki na yan shekaru a bayana shine ta soma aiki da wasu kamfani tana dan samun canjin rikewa a hannunta naji dadin jin hakan sosai wallahi don maryam akwai hankali da sanin ya kamata sosai wallahi .

Kallon Inna mahaifin mu yayi da mama dake gefenshi yace banda abin mairo bata jira ta karasa karatun nata nan haka sukeyi yana da wune kaga yaro yana zaman banza haka a gida sai ya dan samu abinyi.

Nan dai a cikin zancen suka fahinci inda na samo kudin harda ajiyan zuciya saida inna ta sauke a fili kowa naji tana godiya ga ubangiji halittan talikai Allah .

To kinji Ai kinji ai da kunnuwan ki yanzu ko dama na fada maki insha Allahu mairo ba zata aikata abinda bamu dorata a kai ba.

Kin taba ganin barewa tayi gudu danta ya tsaya rarafe mairo nada hankali da tunane shima gashi ya fadi a yanzu ai kinji kuma ?

Mama dake gefen baba zaune ta soma fadin dadin babban gari ke nan ance ikko dama ko kashi kake saidawa sai ka samu me sayan shi haka suke kamar mu nan kano ai a wajen neman kudi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/31, 10:15 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

5️⃣6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4-


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login