Showing 3001 words to 6000 words out of 395027 words
Chapter 2 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
wani tare mata yanzu ka hana ayi magana.
To yanzu me nace don Allah halin mairone kuma bako a gareki kikanso bata ranki a banza wani lokacin ta juya zuwa dakin ta ba tare da tace mashi komai ba.
Tunkan ta karasa muryan maryam din ke fadin ina abincina mama cikin daga murya yadda zata iya jinta ko kallonta batayi ba ta shige daki yarinyar ta bita da kallo.
Muryan mahaifintane a shake yake fadin yaki nan zoki dauki gutun nan kije kici kema kinsan halin mamaki ai tunda kukai haka ba zata baki abincin nan ba yau.
Inna dai dake duke tana wanki batako dago kai ba har sukaci suka sude batace komai ba sai zancen zucin da takeyi a kasan zuciyarta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/18, 9:02 AM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Yanzun dai malam karana Aliyu ya kawo gurin ku yana ganin ni ban isa nasa shi yin abinda nake so a rayuwata mena rage rayuwan Aliyu dashi malam ?
Babu tsohon ya bashi amsa cikin katseshi saidai ina son kayi amfani da iliminka ka tuna ba a canzawa mutum kaddaransa.
Addu zakayi Allah yasa hakan shine alherinsa dashi damu baki daya iya gata yaron nan ya samu kuma an nuna mashi amma kaga ya nace shi karatu zai tafi ya karo ba zai tsaya kasuwanci sai kayi tunane ka barshi.
Rayuwa fa kowa da kalan tasa haka ra,ayin wani daban da naka koda kuwa kana ganin ka isa juya mai naka ra,ayi .
Kwarai kuwa malam don gashi nagani Aliyu ya nuna min bam isa ba niba zan hanashi zuwa karo karatunsa ba tunda hakan yake ra,ayi.
Saidai ya tattaro min kaddarana ya mayar min da abina naba wa yanda suke min hidima suke tausayina suka san zafina da martabana yace sai yayi diploma na barshi yaje jami,a malam yamzu kuma ya dauko zamcen wani karatu can har kasan waje ?
Allah ya bashi sa,an hakan malam ya gyara zama tace Amin yanzun naji kayi magana muyi addu,a Allah yasa hakanne alheri ya amsa a cikin bacin rai da amin.
To kokai fa dan yau ka barshi kawai yace aina barshi amma ya dawo min da motana da,,,,,,, Alh yakubu na dai fahinci bada son ranka yaron nan zai tafi ba ?
Ko daya wallahi tunda bashi kadaine Allah ya ban ba mai zaisa in kwallafa raina gareshi yaje Allah ya bashi sa,a Amin malam yace don ba zan gaji da amsawa ba gareka.
Ranan dai basu tsaya wani dogon zance ba tsakaninsu yadda suka saba su fadawa juna damuwansu idan su hadu duk da yanzu sarakuta ya shiga tsakaninsu hakan bai hana halakansu tafiya yadda yake ba.
Wanda hakanne kuma ke kawo matsala a tsakaninshi da iyalinshi da hjy Naito matarshi ke gani don suna aminai da malam di har ya auri yar malam din basi fasa hakan ba a tsakanin don haka malam din ke kitsa mai wani abin yakeyi wani lokaci.
Ai Aliyu bashi bane dansa kadai don yace shi karatu zaiyi ba kasuwanci ba zaisa aita biye mashi ana faman kashe mashi kudi shi kadai ita wanan abun tana ganin kwaruwane a gareta ita da yaranta.
Domin yayanta suke kasuwa da mahaifin wanda ta cusasu da karfi da yaji tare da uban da bin boka da malamai da komai haka suka shiga harkan kasuwancin mahaifin nasu ake damawa dasu.
Yayin da itako take cikin walwala don diyanta sune a kasuwa suke abinda suke so donshine bata rabuwa da kudi ita ko wani lokaci.
Hakkurin kishiyar ta yasa take nuna halin ko in kula da duk abindake gudana a gidan ta cire rai ga komai da sukeyi a cikin dukiyan mijinsu duk da wata rana ana dan kwantala mata sai dai hakan ba sosai ba sai can ba a rasa ba.
Duk da hakan kuma baisa an barta ba anbar ko a bar dan tilo daya danta a cikinsu ba wanda kamar ya tsone masu ido yake a wajensu duk da bai saka kanshi cikin harkan da suke kyashinshi saboda ganin da suke suke da yawa a gidan.
Hakan sam bai taba damunshi a ransa tunda ya taso ya gane suna hattaransa a cikinsu don tun yana yaro suke nuna basu kaunar ya shigesu.
Su hudune maza jere mahaifiyarsu ta haifa sai tazo ta samu mace tajerasu har su ukku mata bayan mazan tana goyon danta na ukkune Alh yakubu ya auro maman Aliyu da suke kira da Hauwa gatsau ba sakaye kamar yadda uwarsu take kiranta dashi a bakinta suma haka suka taso suna kiranta da Hauwa ba wanda ya tsawata daga uwar har uban.
Saidai yadda hjy Asmau taso hakan bai samu ba kasancewar Alh yakubu mutum ne mai ilimin addini duk abindake gabansa bai hanashi zuwa daukan darasi daya taso yana dauka don asalinshi karatu ya shigo dashi gari dama.
Dalilin haduwanshi dasu malam Inuwa kenan abin ya juye ya zama masu zumuta har kuma aure yashigo tsakaninsu kamar yadda akasari a kasan hausa ake wanan gamayan.
Wanda yasa hjy Asmau daukan hakan a cin amana don komai da akeyi gidanje a tarene amma basu duba hakan ba suka dauki ya suka bashi aure don a ruguje mata farin cikinta.
Alh yayj kokari a lokacin wajen tausa Asmau ya lankwasa ta komai ya tafi mai daidai ake zaman lafiyan zahiri ba fitina saina boye da akeyi kamar yadda nayi bayani a baya.
Koda zancen tafiyan Aliyu ya fito ta kasa boye bakin cikin a lokacin hakan yasa ta hau fada tunda safe tana fadin halan shi wayafi da zaice ba zai tsaya ayi wahala tare dashi ba saidai a kwashe kudi masu yawa a mika mashi yaje yayi bushashanshi dasu wai yaje makaranta.
Ita ta gaji da wanan gaskiya dole a canza lissafi yadda aka bashi kudi ya tafi hakama yanzu za a rika ba kowa daidai da abinda aka bashi.
Ta gane watau wahalane ba a son yayi shiyasa aka tsiru da karatu meke cikin karantun yanzu banda wahalan banza me ake ganewa ga boko don kawai a cucesu za a dauko zancen zuwa karatu har kasan waje.
Duk abin nan hjy Hauwa na daki tana ji bata leko ba duk da bata kira suna ba tasan da Aliyu ake wanan fadan hakan yasa ta shiga tunane watau kiran dayace malam nayiwa mijin nasu ke nan akan karatunshine yakai karabn mahaifin nasu ashe ?
Jin abin tayi yawa haka kuma rashin lekowanta shima fitinane yasa hauwa din mikewa ta fito tana fadin hjy wani abu ya farune kuma ?
A hasale ta juyo tana fadin haka zakice mana dama banda Aliyu daya mace kan saiya tafi wanan karatun shiririta naahi harda kai karan Alh wurin su malam yayi.
Tunda su suka haifishi kuma matsoraci yana gudun su debe mashi ya kasa cewa ,a,a to ba zan yarda ba yadda aka bashi kudin tafiya haka za aba ko wani yaro shima matukar ana son zaman lafiya a gidan nan.
Ya dai matsa sai yayi karatun nan karatun nan ni kamar dole narasa me yake damun rayuwan yaron nan uwar ta fada a sanyayye ita kuma hjy Asmau a cikin hasala take fasin koma dai meye shiya sani ni ina ruwana nadai fada wanan karon ba zan yarda ba kura da shan bugu gardi da karbe kudin shi.
In anyi magana Alh yace ba ruwanshi a cikin zancen karatunsa to nagaji da jin wanan shirin da kai bai dauka ta juya ta shige dakinta.
Koda ya shigo gidan daukan abin karyawa yana gaidasu a ciki hjy babba ta amsa mai gaisuwan nasa ya juya ya tafi don ya saba ganin hakan a gareta wani lokaci abinda ka taso a cikinsane kasani.
Dakin mahaifiyarsa ya nufa ya sameta zaune tayi tagumi ya gaida ita da kwana duban inda suke aje mai abinci yayi ya hango kulanshi don gidane da tunda safe za a karya da shinkafa da wake da mai da yaji ko ayi dan wanken filawa da koko shine abin karyawansu gidan.
Ba zancen shan shayi ko wani kayan dadi saboda yawansu don ita hjy Asmau yaranta bakwai ga kuma yayan dangi biyu nata a hanunta datake riko suna kasuwanci da mijisu haka kuma akwai yan uwan shi Alh dake zaune a karkashinshi gidan suna tare dasu.
Yayin da hjy Hauwa a yanzu yaranta hudu masu rai biyu maza dake bin Aliyu sun rasu sai mata ukku a bayanshi shi shikadaine namiji a dakinsu ke nan.
Haidar karan malam kakai ashe wajensu malam kan zancen karatun ka haba Haidar meyasa kake son ja min magana a cikin gidan nan.
Fuskansa ya shafo ya kai zaune a kasa ya soma fadin mama idam ba can naje ba kinsan Alh ya kafe ba zai barni ba ni kuma ina son zuwa karatun nan wallahi.
Ka bar dangata yan uwana a cikin harkan gidan nan don Allah kana ja masu zagi da tozarci dama hanyar haka ake nema a fadawa mutum magana a fakaice.
Yanzu mama kada inje wajensu wa nake dasu bayan ku a duniyan nan idan basu ba nayi da baba ya barni jn tafi ga dama ya samu amma don wani dalili na baba sai yace ba zan tafi ba mama ?
Tunda ba dole bane tafiyan nan ka barshi mana don Allah banson abinda zai kawo fitina ya hana zaman lafiya kasan halin mamaku idan abinta ya motsa ?
Kiyi hakkuri mama don Allah ki barni in tafi ki dai min addua shi nake bukata a wajen ki addua ina yi kaima kasani nagode mama ya fada ya dukar da kanshi kasa shiru yayi yana tunane.
Yasan tunda uwar tayi magana dole akwai abinda ya faru dayasa harta tareshi da zancen ba kowa bane kuma yasan mamace zata bata mata rai kan zancen tafiyan nasa tunda yasan bata son karatunshi da yakeyi.
Muryan mahaifiyar yaji tana tambayanshi yaushene tafiyan naku ya dago kai da idanuwansa da sukai ja don damuwa yace karshen watan nan insha Allahu.
Tafiya yazo hakane kusa dama ashe kanata shiri akan zancen banyi tsamanin Alh zai taimaka maka da wani abu ba mai tsoka don haka zan baka sarkana kaje kasuwa ka sayar ka rike kudin ka kara.
Da sauri yace a,a mama bar sarkanki don Allah ba sai kin sayar da sarkaki ba akwai kudin dana jima ina tarawa a wajena ina ganin zasu isheni kuma gwaunati tace zata dinga tallafa muna idan muje sai inyi maneji yadda na saba a baya.
Amma kasan can ba nan bane wajene na kazo nazo ba zancen taimako a irin wajen nan yace mama kada ki damu akwai Allah ba zan zauna ba zan nemi abinyi a can din insha Allahu.
Tausayi yaba uwar tayi shiru tana ajiyan zuciya ita dai duk da ance uwa bata ganin laifin danta duk da haka bataga matsalan da ake kira mashi yana dashi ba ko za,ace yayi abu idan abincika shike da gaskiya.
Amma an dauki tsangwaman duniya a dora gareshi ko laifi wani yayi jafin a fadi suna mutanen gidan zasuce halan Aliyu ko ?
Irin hakan yasa ya koyi nisanta kanshi da kowa nagidan iyakanshi dasu gaisuwa kowa ya kama hanyar gabanshi suna mashi kallon dan wahala ne shi.
Koda Alh ya dawo hjy Asmau ta tayar da zancen cikin daga murya ya soma fada yana fadin na aikeshine da zan bashi kudina ko kwandala ba zan iya tabawa a kudina in kara mashi ba.
Shi da yace zaiyi sai yaje can ya nemi mafita da zai fisheshi shiya san dabara itako sai fadi takeyi ni da kada ai min barazana idan bangani ba akai mai ai Allah ya ganan min tasa kai ta fice daga dakin.
Sauri takeyi cikin kodaddun tufafin makarantanta da suka kode sukai fari don tsufa tayi bi a canza mata tufafi abin ya faskara ba halin hakan ana neman abinda rayuwa zaici ba zancen tufafin akeyi ba a yanzu gidan.
Duk saurin maryam saida ta tsaya gaban wani mashin ta duba fuskanta kana ta kara gaba daidai kwanan gidansu ta tsinkayi kawarta mairo taji ta fada tun daga nisa don tasan bata son sunan donshi intaso batawa maryam din rai take kiranta da wanan sunan na mairo.
Fuska ta daure tayi kamar bata ganta ba hakan da tayi bai hanata karasowa wurinta ba tana fadin tun dazun nake nemanki ai in fada maki babanmu ya sayo sabuwar mota yace wanan a dinga kai mu makaranta dashi.
Nayi maku murna muma Allah ya bamu gidan mu kin jiki don Allah kuda ko maahin kuna nema a gidan ku bakiga tsaleliyar motar da Abba ya saya bane fa.
Muma wata rana Allah zaiba baban mu ya sayo muna ta kara fada dariya salman ta kwashe dashi maryam ta watsa mata harara ta nufi gidansu.
Haka din ne don da yamma taga motar a kofan gidan tare da baban nasu da wasu ana duba don gulman maryam tasa kai ta shiga gidan.
Sallamanta maman su salma din ta dago kai ta kallota ita dai kawai take jin tsanar yarinyar a ranta badon tayi mata wani abu ba haka dai kawai jininsu bai hadu da maryam din bane gata kuma da yarta tip da taya suke ko yaushe suna lake da juna .
In fada ya kama suyi dambensu ko a cikin gidansu maryam dinne ta fita da kuka ko bacin rai bai hana gobe kuma ta koma gidan acigaba don ko bataje ba salma din zata biyu ta har nasu gidan.
Labe labe ta soma yadda ta saba don koda take yarinya ta san irin tsanar da maman kawar nata tayi mata donshi take shan jinin jikinta idan mama din tana waje ta shigo.
Ke baki iya gaisuwa bane kin shigo kina zarewa mutane shegun idanunki kamar me neman wani abu to kawar taki bata nan sunje gidan kakansu tun dazun.
Saiki kama gabanki jin hakan yasa maryam din ta juya da sauri don barin gidan din bata da tsoron Allah take fadin nidai yaki nan zo ki wanke min kwanukancan kan ki tafi.
Maryam din duk da satan hanya tayi tazo gidan bai hana taje ta wanke kwanukan ba tana zaune tana waya tana bada labarin zancen sayen motan mijin nata.
Matar irin yan barikin matan nan ne masu coge dan kwali a goshi bakinta baki shi kansa maryam har gobe idan ta shigo gidan take yawan kallonta don mamaki take yadda yanayin bakinta ya bambamta dana sauran mutane data sani ga kuma tsaga a fuskanta wanan yakan bawa maryam din mamaki matuka.
Har takusa gamawa waya takeyi tana sauri ta samu tabar gidan lokacin su Salma din suka shigo gidan da yan uwanta bata kula da maryam dakewa uwarta aiki ba akbarkacin ta sai shagwaban data zube sunawa uwar suna bata labarin gidan kakan nasu.
Yarta ce ke fadin ke salma ga kawarki can fa tana muna wanke wanke sai lokacin matar gidan ta juyo tana fadin ai salma idan baki daina kwaso min yarinyar nan mai siffan yan ruwa kina shigo min da ita gida ba sai naci kaniyarki wata rana.
Haba dai mama gata tana maki aiki kina kuma zaginta kafin uwar tayi magana uban ya shigo yana fadin yauwa gakuma a hade baein baku alkawarunku tun kan na manta da hakan.
Yasa hannu a aljihu ya debo kudi sabbi fil yana mika masu saida yabawa kowa maryam na rabe a bango don tagama zata tafi saurawa dayan yar salma din tace ga mairo can daddy abata .
Wata mairo kuma mairo yarsace da za a bata ke kin gama kizo kije gidan ku banson gantali marance yayi haba dai keko ina kawar salmace bari man in bata ?
Ya mikowa maryam din wanda ya zaro uwar tabi da harara tana fasin daidai zaka bata dasu haba dai alh ina laifin ka bata ko dari biyu ?
Barta dai a bata rabontane ya ratsa da ita ya mikawa maryam din kudin har kasa takai tana karba tare da fadin angode Allah umfana yace amin yar albarka kunga yadda ake yaba kyauta ba kamar ku ba kun amshe babu godiya.
Wanan ce zata koya masu wani dabi,an kwarai ke fita dan Allah tun kan na amshe kudin nan daga