Showing 294001 words to 297000 words out of 395027 words

Chapter 99 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

sassauta murya yayi yace ban son in bata makine har ki fahinci hakan maryam tunda kin dauka hakane amma ni yanzu nake shirin aure dan naga wace tayi min ta kuma tsaya min a rai kuma kece maryam .

Ni kuma na fada cikin mamaki ina dan satan kalloshi yace yes saidai idan in ban maki bane kinsan komai ra,ayine ga mutum don ban shiga zuciyarki naga hakan ba.

Kamar yadda kika fada dazun nima haka dinne a wajena burina shine inga na farautawa mahaifana rai ta yadda zasu dogara dani idan na zama wani bango a garesu.

Alhamdullahi kuma Allah ya amsa min addu,ata a yanzu hakan ya samu gareni saura neman abokiyar zama wace tasan darajan kanta da kimar iyayyena don duk wace zan aure bata san darajan iyayyena ba kinga nayi aikin banza ke nan a yanzu ?

Ido na lumshe a hakali ina nazarin zancenshi don duk wani hanyar da mutum zai bi ya nuna so da kauna ga mutum mutumin nan ya nuna min hakan illa iya ka bai furta bane sai yau.

Daya fito fili baro baro ya tunkareni da zancen aure haka ido da ido dagani sai shi a cikin motan ni yanzu me zance dashi ga wanan abin ?

Dan satan kallonshi na sakeyi yana nan yadda yake ko gezau baiyi ba na dan zakuda ina fadin daddy na dade da fahintar manufaka a kaina.

Amma hakan abune dake bukatan natsuwa kaga yanzu ka fadi cewa iyayyenka nason aura maka wasu matan da suke ganin dacewansu dakai ko ?

To haka zancen nan at list abune wanda yake son natsuwa a cikin sa for me dai a yanzu banda wani matsala a bangarena tunda na kusa gama karatuna hakama a wajen iyayyena banjin za a samu matsala irin haka.

Sai naji yace dani cikin katse min maganata kin amin ce ke nan ko ?

Na kusa saidai ina son lokaci kaima hakan ka kara nazarin kafin komai ina ganin hakan zai fi sauki a garemu baki daya naji yace shike nan zan iya jiraki ai ki kare nazarin .

Cikin nishadi sai naga ya saki mota muka hau titi da kyau bai fi yan mintuna ba muka kai shagon green land din sabanin yadda yake tafiya da farko da motar.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/8, 9:40 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊8️⃣8️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Shiru Alh yayi yana sauraren matan nasa har takai zancen maganan ta inda ta kare da fadin idan yayi haka kasan zumuncin namu zai sake raunine kuma yanzu ?

Shike nan dama abinda kike son fada Alh ko baka fahinceni bane wai kai kadai zakaiwa babana magana yaji.

Nasan idan yaji kana bukatan hakan kai ma zai yarda yaje yaga yarinyar su shirya da ita don yanzu na rasa gane kanshi gaba daya dana dauko mai da zancen sai yace bai kaunan maganan ga baki daya.

Amma hauwa kinsan Aliyu dai ba mace bane ko ko macene kinsan banda wanan ra,ayin na tauyewa yaro kan muradinshi wanda kikaga inayi bayama kuskure aka samu hakan yai ta faruwa a lokacin.

Namijine yasan abinda yakeyi haka na tabbatar duk macen da Aliyu zai gabatar muna a gidan nan gaban mu mace data fito gidan tarbiya da kamun kai.

Banga abin wani tsayawa tsoro ko nauyi ba a nan abinda take so maiyi yace baida ra,ayin hakan suje ai dangi nada yawa a gari a nemi wanda yake ra,ayin hakan a hadata dashi din mana.

Amma Alh banji dadin zancen ka ba na zata zaka fahinci me nake nufi ka tilastawa yaron nan tunda yana tsoronka kai kadai yanzu zakace yayi yayi hakan ba gardama.

Kike ganin hakan ko to kada kiyi mamaki idan na sashi yayi yayi min irin abinda yayi maki kan zancen nima don haka idan zakiji shawarata ki barshi ki samai ido yayi abinda yake so da gidanshi.

Ajiyan zuciya ta sauke irin na bacin ran nan ya dago yana fadin kinso ki wahal da kankine akan haka don kinsan ba abu bane da zai yuyu a gareku.

Aliyu ba zai taba yarda da zancen nan ba hjy Hannece fa kinsan yadda suke da yaron nan tun yana karami sai yanzune tasan shidin dankine take son a hada zumunci da jinin ki ?

Amma Alh yarinyan da yake zance ba tashin garin nan bane tashin kudune ita yadda yace kana ganin akwai tarbiya ko kamun kai wajen irin yaran nan da idonsu ya riga daya bude da duniya ?

Dake zata zauna ke nan ko kece zai aurowa ita bashi zai zauna da abinsa ba jinan hauwa zancen da kike so dai na fada maki ba zanyi hakan ba.

Sai ki jira ya kawo yarinyar kafin ki fara korafi kanta idan kinga wani abin muni a gareta saiki sa ya rabu da ita ina shike nan haka kuke mata da daukawa kanku wahalan da bai gane ku ba kuke.

Alh yau dai na gaji idan akwai igiyar aka kaina nima a dawo min da girkina gidan nan muryan hjy Naitoce daga kofa take fadin hakan a cikin bacin rai.

Don kuwa tayi tsayi har ta gaji tana dakon fitowan hjy Hauwa amma bataga fitowanta ba daga turakan inda zuciya ya debeta ta dogara zuwa kofan part din mijin nasu.

Gaba dayansu suka dubi junansu lokaci guda din jin muryan hjy din da abinda take fada daga kofan data tsaya din inda a bangareta jin shiru din yasa ta maimaita abinda ta fada da farko din na zancen abata girkinta ta gaji da irin cin amanan da ake mata a gidan tana kallo.

Haushi da takaicine ya kama Alh ya mike ya sameta a kofan yana fadin in kin gaji ai kinsan hanya ko ?

Girki kuma ba za a bayar ba kije kiyi duk abinda zaki iyayi nace ba za a baki girki ba gidan nan lalai na yarda da mutanen unguwar nan da suke fadin tabin hankali ya sameki ashe ko hakan gaskiyane ?

Idan an baki girki kija gindi kiyi ko me zaki iya barkatawa a cikin girkin dagaskene ashe kin samu tabin kwakwalwa ban sani ba ?

Yau nice mara hankali Alh ?

Ni sadiya naga takaina hauwa lalai kun nuna min ku diyan malamai ne yau ni Alh zai kalla ya kirani mahaukaciya don kun shiga kun fita danki yayi kudin jini.

Ai isane kudin jinin bana jini ba kona kwarangwal kika samu zakiyi ke din nan da baki da imani balle tausayi don kince dukiyan jinine Allah ya bashi kowa yasan kina hassada da hakan amma kuma a ciki kike ci keshan kudin jinin kema kin zama yar shan jinin ke nan ai ?.

Aiban san abin na gori ake ban ba ina karba daga yau din nan a bari na yafe indai gori za ai min sai ki dawo da duk abinda kikaci daga dukiyan nashi na shan jini yanzun nan asan kinyi fushi saboda ba danki yayi nasaran samun dukiyan jinin ba ?

Allah ya saka min Alh don kaga na koma haka yanzu kake gudana matarka Hauwa itace mata diyanta sune yaya a gidan nan ?

Haka kamar yadda kika maidani a baya kece kawai mata a idona yayanki sune kawai yaya a idona to itama hauwa yanzu lokacintane na rama hakan garemu.

Nina godewa Allah daya nufa har ta rama hakan tun ina raye ba sai naje lahira an tuhumeni kan laifin dabani na aikata ba.

Yar son kai kawai matsa ki ban wuri ko yanzu in karasa karyan kafan nan daya da kike chokalawa a wajen masifaffa mara hankali kawai.

Duk wanda zaki fadawa na karbe girki a hannunki Naito kije ki fada ba zaki kara girki a cikin gidan nan ba har abada tunda ba imanine dake ba.

Mamakine sosai a idon hjy hauwa din don batayi tsamanin jin wanan zance ba ga bakin hjy Naito donko iya kawaici har yanzu tana yinsa gidan don dai a zauna lafiya .

Haka ta fito ta rabasu zata wuce ta juya gareta tana changala kafa kamar zata kamota wani irin juyowa hjy hauwa din tayi ido rufe ta soma fadin .

Yau idan kika kuskura hannun ki ya taba jikina sai nayi maki dukan tsiya a gidan nan saidai aga rashin hankalina kan hakan haba matar nan me kike nema a wajenane haka ?

Duk abinda take nema aisai ta dauka wanan bata san mutunciba ko kadan in zaki daina daga mata kafa ki kama kanki gumma ki daina don bata san kinayi bama kanta kawai ta sani ita sai diyanta.

Wanan fitinan saida taga da gaske mijin keyi don har ya kira yan uwanta yace azo a tafi da ita shiya gaji da halinta takaishi makura ba zai iya ba lokacin ta fara sanyi don wanda ya kira din ya fita tujara da cin mutunci.

Gidan su mairo gidan danja tsaye inna tayi aka raba abin yadda ya kamata don baba yace ai yara yace yasowa don zuwa makaranta don me za a taba masu kayansu aje su dinga zuwa da abinsu school.

A,a malam ko a raba ko kada a raba duk karewa zaiyi yau da gobe zara baya barin dame meye a ciki idan an kasa aba kowa nashi rabon yanzu ?

Ai je kiyi yadda kike so nasan ai ta dalilin yarki aka kawo kayan nan don haka je tunda ban isa ince ga yadda nake so ba ya kada riganshi ya tafi.

Inna din tayi yadda yace amma ta debe wanda za a rabawa sauran yan uwa ta hada da kwalin indomei dana taliya ko wani guda guda tasa uwale ta dauka takaiwasu mama wajensu.

Anyi dace yaya murja tana dakin a lokacin koda uwale tashiga dashi tace mama gashi inna tace in kawo maku tana kokarin ajewa murja din tace.

Duk wanan uban kayan da aka kawo dan wanan za a debo a kawo muna kamar wasu almajirai can ki kwasa kice angode aiba za a gwada muna karya ba ?

Mama din ta daga tana fadin aini akace a kawowa yau kwana nawa inacewa ina son cin taliya kinki sayo min sai kin dawo zakice kin manta ?

Mama na fadin a je mata abinta ita kuma tanayiwa uwale din jan ido akan ta dauka ta fice

masu dashi daki aisu ba matsiyata bane balle ?

Ke uwale tafi abinki kice angode yaya sahura dake shigowa ta fada tana kallon murja din dama aike baki san takaici ba sokuwa kawai.

Ni kike cewa sokowa murja ?

An fada din me zakiyi idan ba sokuwa kike ba don me zakice a karbi wanan kayan tsiyar tasu taliyane bamu taba ciba ko indomei ?

Kada ki kara zagina wallahi idan an kara me zakiyi ki kara ki ga abinda zan maki kuwa an fada ance sokuwa kawa,,,,,

Tass tass ta kwasheta da mari biyu masu kyau daga inda take kwance din da sauri take kokarin dagawa tana gyara daurin zani don daura gabane kadai a jikinta.

Nan yar uwar ta shammaceta ta dinga kai mata duka nan fada sosai ya fara a tsakaninsu don kuwa ba komai yanzu cikin murja din dama shaye shaye ya cinye banza ba wani karfine da ita ba.

Duk yan gidan har mahaifiyarsu sun kasa rabasu sai faman fadi take saita kashe sahura din a ranan kamar Allah ya turo baba sai gashi ya dawo yayi mantuwa yazo dauka ya samu wanan tashin hankalin a cikin gidanshi kuma ?

Sanda ya jawo ya dinga dukansu dashi hakan yasa suka daina fadan yana zagi yana tir da halinsu har ya juya yake tambayan meya kawo fadan ma ?

Sukai shiru sai daya juyo kan yaya sahura ta soma fada mashi tana kukan takaici nan murja din ta tare tana eeh na fada aimu ba matsiyata bane da za a wani kwaso dan wanan abin a kawo muna kamar almajirai.

Kan inna baba ya juya yana fadin Ai kin gani ko kinga abinda nakewa gudu ke nan ki rabu da dan banza inda kika ganshi kawai ?

Na fada maki ki barwa yaran nan kayansu tunda wasu yace ya sayowa abin nan amma kikace wai wani alhakin ido to gashi.

Abar masu mana ai bamu rokesu ba murja ke fadi daga daki batayi aune ba sai jinshi tayi ya sake far mata da duka saida ta kasa numfashi ya barta.

Yake fada nasan don sahurane ko sahura ko a dakinki yake zata shigo ta dauka tunda bata sawa kanta mugun abu ba ita haasada irin nasu shike cin yarinyar nan har yakaita ta zama yar kwalta a yanzu.

Irin tashin hankalin wancan gidan shi akayi a gidan mu ranan don sai rana sosai baba ya samu fita kasuwa a ranan bayan kwakwaran kashedin da yayiwa innan mu.

Akan daga ranan ya kashe irin hakan idan mutum yana so yaci idan an dafa tunda basu san mutunci ba a karshe sai inna ce tasawa murja din ruwan zafi ta gasa jikinta dashi.

Gidan ya koma shiru don abinda ya faru din zuwa yamma gaiyan mashaya yan uwanta mata suka shigo gaida ita innan mu najin suna zage zage ba wanda ya tsaya kulasu.

Nikan sun kirani suna fada min nace su fita zancenta inna ta sa ido sosai akan yan uwana don Allah don irin su yaya murja yan daba sherinsu yawa gareshi.

Kada innan mu ta yarda ta aiki wani ba tare da dan uwanshi ba na kuma kirasu har mazan naja masu kunne sosai suka tsorata don sai lokacin kansu ya kawo wuta da lalai zasu iya illatasu tunda yan dabane .

Zama roget yanzu bawai maza bane kawai ke haka har matan idan idonsu ya bude da wanan abin sukan fitar da tsoro da kunyane uban kowa sunawa rashin mutunci su.

Nasa abin a raina sosai don kodaya kira muna waya da dare nake labarta mai abinda ya faru yace in bari zai sa a saka ido ga duk wani motsinsu tunda hakane.

Ban dauka zaiyi din ba saida Saudat ke fada min an aje yan tsaro a cikin unguwar mu ance yan iska sunyi yawa a layin mu din donshine aka aje muna masu tsaro a unguwa.

Nasan aikinshine yanzu haka kudi ya zube akan haka din sai kuma lokacinne hankalina ya dan kwanta ga tsoron yaya murja din da abokan lalacinta don ba karamar mara kunya bace dama ita duk kuma ta dalilin talla da rashin karatune ta fada wanan halin.

Da farko tun abin bai mata nisa ba data soma ana zuwa gida a fadi baba yaso ya hana tallan a lokacin mama tayi tsaye tace ina ya fito ?

Da zai hana mata talla yana dauke masu laluransune bayan abinci da dan kudin cefanen da yake bayarwa akwai wani abinda yake tsarewa yaran ne a gidan ?

Da sannu har ta rijayi baba a lokacin don kaishi kara da tayi gida kan ya matsawa yaran bai kaunarsu dan tallan da sukeyi suna samun kwabon kashi yanzu kuma an zugashi yana son hanawa .

Akai mashi ca akan me zai hanasu sana,a dan abimda suke samu aiko shi rufin asirinshine hakan dole baba ya hakkura da hakan ba don yaso ba ya kyalesu sukaci gaba da sana,ansu.

Nikan wanan dalili yasa tun lokacin na daina fita da abinci wajem kofan gidan mu da akeyi da safe hakan kuma baisa inna ta daina sana,a ba.

Don duk maiso zai turo yaro cikin gida a saye mashi daga baya kuma ta samu almajiri yana fita dashi waje inda nake ajewa.

Kuma a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login