Showing 282001 words to 285000 words out of 395027 words
Chapter 95 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Aikin shagon baba ya kankama gadan,gadan masu aiki ke aikinsu nahada shagon duk wanda ya wuce sai ya kalla abin ya bashi sha,awa don yadda suka tsara wajen.
Duk daba wani gina bane akayi banda office ukku dasu an ginane sauran wajen kuma design din shi akayi wanda ga katon photon mashin din da za a sayar wurin an makala a sama da sunan wajen.
Saboda wanan aikin da akeyi ayanzu Baba bai faye fita ba yanzu don tambayan da yake sha wurin mutane akan aikin gashi baida amsan da zai basu mai ma,ana daga bakinshi.
Wanan yasa yakan zauna a gida har wani lokaci kafin ya dan fita fita ya zagayo wajen watarana baima zuwa ya duba sai ankwana biyu.
Duk da hakan bai tsira ba a wajan jama,a yana fitane za ace malam Ali mota ashe likafa tacigaba haka ?
Wallahi munga wuri ya kara girma ya kara kyau kuma saidai yayi dariya kawai yakan basu amsa da mai wurine yake fadada wajen saboda tsaro ni kunsan ai yaron shagone.
Yanzu kan sun yarda daba shikeyin wanan aikin ba shima cin arzikine yakeyi don ganin irin aikin da akaiwa wajen.
Donshi a yanzu kowa yasawa sarautan Allah ido aga yadda za a gyara wajen asha kallo masu surutu kowa da abinda yake fada dai.
Kasuwanci ga dan kasuwa kamar sayen kaddarace garesu ko a fadi ko aci riba don shi cikin wata daya anshiga an fita anyiwa shagon baba tare da takardu da komai na gwaunati yadda akeyi a saura sana,a don waje ya kafu da kawo kaya .
Yan kwanaki tsakani baba na gida da safe baida niyar fita a ranan wajajen sha biyu saura aka kirashi yazo su hadu a kasuwa sune suka shigo da kayanshi yazo a sauke a gabanshi.
Yana kwance ya mike zaune zubur yana fadin Alhamdullahi to sannunku da zuwa yaya hanya sannuku ya kashe wayan yana fadin gani tafe yanzun nan insha Allahu.
Riga ya jawo ya saka fito daga dakin ya tsaya daga kofa yana kwalawa Inna kira a cikin firgita da jin irin kiran ta fito daga daki taji ko lafiya yake wanan kiran haka.
Haka a part din Mama da yaranta dake zaune sukai shiru suna saurare suji kome ya faru a lokacin suji me zai faru ya soma fadin.
Ai kinga abin Allah ko yanzun aka korani wai kaya sun iso Ai yanzun suka kirani wai mu hadu kasuwa dasu za a sauke min kaya.
Alhamdullahi tagumin zaman jiran tsamani yau ya kare a gidan nan damu dakai duka malam .
Ai kuwa yau kamar kin sani Ai don ganin abin nakeyi kamar ba mai yuyuwa bane yadda ake fada din nan har gashi yan gulma sun fara sakin magana.
Nikaina duk da bansan komai akan harkan kasuwa ba saida lamarin nan ya daure min kai sai gashi kuma abu ya tabbata dai yanzu tunda kaya sunshigo Alhamdullahi kwankwato ya kare ga kowa.
Sai ya kwashe da kuma dariya don tuno irin fargaban da yashiga cikin dan takin kwanakin nan jin shiru akan harkokinshi din don shi kadai yasan irin halinda zuciyarshi ta shiga a kan tunanen hakan ko zai yuyu koba zai yuyu ba.
A can dakin mama murja ke fadin Kunji baba ko shine har da kwasan dariya haka yau kamar wanda akaiwa bushara da gidan aljanna ?
Itako makira tana wani kashe murya matar nan yar duniyace ta boye wallahi ba dole ku shiga fargaba kila farkan nata batayi mai daidai yaso kwace kudinshi.
Kai haba murja ki daina irin zancen nan don Allah mairo dai yar uwarkice baki kuma tare mata komai ba a rayuwa kiji da kanki itama taji nata .
Bai kamata ke aji kina wanan zance a kan yar uwarki ba yarinyar nan tana matukar mutuntamu a rayuwan ta sosai wallahi.
Shi kuma baba a hanashi dariya dashi da matar shi don Allah ita fa matarshi ce da kowa ma in yaso hakan indai babane ai yana dariya dashi a gidan nan.
Idan har hakan ya kama kafin yayi dariya da kaine yanzu gaskiya ba kusa ba amma ai da baba ba haka yake ba.
Nima ya fada min yana cikin damuwa sosai don daga shagon nan nasa da akayi ana gyaran nan hankalinshi ba a kwance yake ba wallahi don yana ganin kamar shagon zai fita daga hannunshi idan an gama yadda aka gyara wajen.
Dama ya fita din muga ta tsiya muga karshen hura hancin da ake muna ita a dole yartace maishi yanzu ni wallahi har mamakin innan mairo nakeyi yanzu .
Ashe dama zatayi jiki haka wurine bata samu ba yadda take so take faman kalmashewa tana soyewa a zaune ?
Lalai murja baki da hankali akan baba kike wanan maganan koma dai meye mahaifin muneshi bai kamata kina fadin magana kamar meyi da sa,anshi.
Daga inda uwar take zaune ta mike kafa jikinta na rokare da bango tace to ya isa haka don Allah.
Ballema banyi da ita ba dai a dakin nan da nake magana ta ko za a hanani fadan gaskiyane kuma nida bakina.
Sai hakan yaso ya zama fada a tsakaninsu kuma saida mama ta saka masu baki ta nuna bata son kara jin hayaniyan dayansu a dakin nan.
Baba yai wanka ya fita sai lokacin yaya sahura ta samu fitowa daga shiyansu din tana fadin ashe baba kayanshi sun iso yau naji yana fadi dazun da zai fita.
Inna ta nisa tana fadin ya fita sahura na zata ai barci kikeyi baki fito ba tace ina kwance ina kallo tun dazun idona biyu wallahi kar in fito kuma yace nazo gulma.
Ai baku yar hakan dashi mana kema kin sani ya dai fita sai ya dawo muji abinda ke nan kuma yana can dai ya kwasa ya fita tun dazun wai an kirashi kaya sun iso.
Duk wayan da baba keyi da sir Aliyune amma sam bai gano hakan bashi, tunda bai fada mai koshi waye bane a zatonshi dai wani bahaushene aka samu ya shiga tsakanin abin a yanzu kuma haka ya dauka a zuciyarshi.
Ba karamin girgiza baba yayi ba ganin motan terila a gaban shagon nasu tsaye lulube da kaya driver yana jiran isowanshi a lokacin.
Suka gaisa aka fito baba ya gana da wanda aka turo ya rako kayan wanan office din da akayi a wajen suka shiga yayiwa baba bayani kamar yadda aka umurceshi dayi har takardun mashin din dana resit an mika mashi komai saura gudanarwa kawai a yanzu.
Abinci lafiyayye baba ya tanada masu yana fadin baisan da zuwansu ba ai da girkin gida zai saka ayi masu suyi hakkuri da wanan din suka gama akai sallama suka tafi da yamma lis sai lokacin baba ya samu sauki a rayuwanshi.
Wuri kam yayi kyau sosai masha Allah kowa na saka albarka bakin titi baba yaje ya sai kosai da masa yayiwa almajirai sadaka aka raraba masu don samun albarka a cikin harkan.
Ina kwance ina karatu don munyi nisa da exam a lokacin kiran baba ya shigo a wayata na dauka da sauri don mu gaisa dashi inda ya soma fadin maryam ya kuke can nace lafiya baba.
Sai nashiga gaidashi yana amsawa a cikin fara,an da yafi ta kullum a ranan.
Naji yace maryamu sai ga kaya nagani sun iso haka wanan karon da sabon sallo kayan sukazo muna don ba wacan company da muka saba sayarwa bane wanan din.
Wanan kaya sunfi inganci da komai da kyau kuma kowa na fadin ba a faye samun su bama sosai don anaso greedy ne sosai wallahi ?
Kaya sun iso baba na tambaya cikin mama tare da fadin wallahi ban ma sani ba don jerabawa nakeyi yanzu banda lokaci ko yaushe muna fama da karatu kasan na kusa kammalawa ga baki daya yanzu
Nan naji ya soma yi min bayani a gurguje yadda wajen ya koma da irin kayan da aka turo mashi din a lokacin da yadda zai saida komai har ya dora nasa a kai ya samu.
Nikan dai sai mamaki nakeyi a kasan zuciyata don bayanin da baba din ke min kaina ma dai a kulle yake zance a lokacin .
Muka dan taba hira sosai dashi zuciyana duk a tsunke take kan abinda baba ke fada min din mungama mukai sallama dashi na aje waya ina tunanen irin kudin da aka kashe kan hakan wai su kudin nan ba nemansu akeyi bane halan ?.
Mun kwana biyu rabon da muyi waya dashi don yayi tafiya baya kasan duk da nan kusa ya tafi amma waya ya gagaremu tsakanin mu dashi.
Don dama yace zan jishi shiru na kwanaki don shine ban damu ba a lokacin don in har ya dawo shi zai nemeni idan yana son hakan.
Sai gashi tunda baba yace min an turo kaya nasa a raina ya dawo ke nan kila a lokacin duk da yana da wuya ya dawo ban jishi ba gaskiya.
Kawai ban jira komai ba na dauki shawaran zuciyata dake ingizani da inkirashi a lokacin inji ko ya dawone ina dannawa sunan shi kira naji ya shiga.
Wani irin ajiyan zuciya na sauke jin yana Nageria ke nan a lokacin tunda kiran ya shiga akai daidai da ya dauka yaji kuma abinda nayi din.
Baby na na zata aiba ko yau ba zaki kirani ba ko yau tun jiya da safe nake kasan nan amma baki kirani ba ?
Haba dai kaifa kace min kada nakira sai idan ka kira nasani ko sai kuma nayi kin sani kome ko matar nawa tana kusa ko nasan abinda kike son fada ke nan ai ?
Umm,humm na fada cikin murmushi nace ko nayi hakan ba laifi bane don na bata girmanta don nima ba zanso aimin hakan ba ai kadawo lafiya ya hanya na katse wancan zancen daya soma.
Lafiya gani zaune ana min tausa kinsanku mata tun jiya nake son samun hanya inzo wajenki inganki amma ab hanani fitowa daga gida.
Kit na kashe layin don zai iya amma bai kyauta min ba yana tare da ita kuma zai daga wayana wanan kome tayi min a lokacin nina jawa kaina ai.
Sannu a hankali nakai kwance ina lumshe idona wani iri nake ji ba dadi a zuciyana nakai tsayin lokaci kafin zuciyana ta tambayi kanta dake ina ruwanki da zancen matarshi wai ?
Ai yasan yana da mata yake zuwa wajen ki meye ruwana tunda bansan abinda ke tsakaninsu ba itama matar sakaraice ko ?
Ina da miji kamar wanan zan barshi a nan in koma arewa koma meye ina kusa dashi irin mazan nan ai farautansu akeyi ba abinda oga Aliyu ya rasa wanda ake so a wajen maza amma ta barshi ta koma can tayi zamanta.
Ai dole ya nemi inda zai dan dinga jin sanyi watau haka na nufin da tana garin nan ba zan gashi bama ke nan ashe akwai aiki kuwa ?
Don dan sabon nan da mukayi dashi yakan manta min da duk wani alkawari dana dauka kan maza a baya har nakanyi mamakin yadda nakan sake jiki mu dinga hira kamar bani ba.
A baya nace bello ya shani nayi hankali ba wani namijin da zan kara yarda dashi a duniyan nan sai gashi kuma ban ankara ba wanan ya shigo rayuwata da tsigar tausayi da kulawa har ban san lokacin da sabo ya shiga tsakani mu ba haka .
Don a yanzu ankai bai mintuna Shirin matukar dai ba school yasan nake ba bai kirani munyi magana ba sai during school hour yakan dan daga min kafa ina fitowa kuwa zan kunna waya kirashi zai shigo min.
Da farko na dauka don yawan aikin da yake turo min nayi ta adanasu a na,uran sirinsu dake wajenane sai daga baya kuma na fahinci abin yafi haka a yanzu.
No way gaskiya na fada ina lumshe idona don ba gaskiya zuciyana ta fada min cewa nafa kamu da son Sir Aliyu a zyciyata wanan yasani furta wanan kalman lokaci guda.
Ba soyayya bace kaunace kawai mukewa juna saboda sabon da mukayi a yanzu na lumshe ido ina jin wani iririn abu ya tokare min zuciyata.
*KANO*
Na zata haihuwanki yasa kika shanye zanceb yaran nan da mukayi dake a baya sai yanzu na gane ba hakan bane kamar kuna da wani manufa dake da dan ki kan zancen nan hauwa ?
Manufa kuma yaya Hanne dashi da Fadila ai dukkansu abu daya suke a wajena son me zaki dayansu kuma kawai don bai dawo bane tun lokacin yace abubuwa sunyi mashi yawa a can.
Nafi son muyi maganan dashi ido da ido bata waya ba wanan yasa naji zan baki nan da yazo din tunda kince yana tafe kwanan nan idan yazo duk yadda kukayi inji tunkan in tunkari su malam da zancen.
Ai baikai sai su malam sun saka baki ba yaya hanne dashi da ita duk kina da iko dasu ga baki dayansu zaki iya hukuntasu ya zaunu kuma.
Abinda na gani ke nan nima gashi har na fadawa Alh zancen shine ma jiyan nan ya tambayeni nace bari na kiraki yau din nan .
Suna gama waya ta sauke ajiyan zuciya tana gyara zama don tuno da yadda sukayi da dan nata akan zancen bai boye mata ba tun lokacin baida wanan ra,ayin.
Abinda ta sanine kuma Alh ba zai taba yarda da wanan zance ba don baida ra,ayin yiwa yaro dole koga diya matanshi balle da namiji don haka zata kara lalabashi don ya amince ayi yadda yar uwar nata ke son a hada yar gida gida din tsakaninsu.
Tasan halin danta sarai da ace yaya hanne bata nuna masu haka a baya bane zata iya lalabashi a yanzu har ta samu ta shawo kanshi ya yarda ayi abin nan kamar yadda yar uwar nata ke so.
Amma irin abubuwan da yaya hanne din tayi gaskiya yana da wuya ko mahaifin yaron ya yarda da wanan hadin saulin abindai suke da namiji ba mace bace don da babu tantama sai yadda Allah yayi da zancen gaskiya.
Tasan waye yaya hanne da irin tarbiyan da tabawa yayanta donshine take dan fargaban abin Amirace ya shigo dakin ta zauna a gefe daya kusa da uwar tana hade rai.
Da akayi me kuma kinzo kina hade rai haka ba yaya bane yace wai inje in zauna da mama kafinsu yaya su shigo ni wallahi ban son zuwa dakin nan yanzu tunda Abba ya hanamu shiga tun ranan.
Bama zaki ba koda Abba bai hana ba don ita din bata bukatan hakan da sukeyi shime zai hana ya zauna har su shigo din inyaso ya fita ?
Matar da yakoma kamar mahaukaciyane a yanzu zaice ki wani je gurinta ki zauna kome tayi maki ai sakacinane wanan.
Muryan ya Auwal din sukaji a kofa yana kiran Amira din din ya jima baiga fitowanta ba hjy hauwa ta mike da kanta ta fita ta sameshi suka gaisa take fadin tana ciki yanzu ta sameni da zancen kace taje ta zauna da hjy kafin su iso.
Yace ina son fitane kuma kinsan da zaran aka barta ita kadai zata fara kuka tace mun barta ita kadai ba a son kulata shine nace taje ta dan zauna da ita din.
Auwal kasan ba zai yuyu ba hjy ba ai mata haka da ace itace da kanta ta bukaci hakan wanan ba zan hanata zuwa amma yanzu ina turata matsala hakan zai zama a tsakanin mu kuma ayi hakkuribta fada ta juya zuwa ciki tunkan ya fadi wani abu anan.
Bai tsaya mamaki ba don dama baida yadda zaiyine yasa yace yarinyar taje ta zauna da ita din yanzu uwarta kuma taki ya juya ya fice daga gidan.
Tsoro ya hana Amira shakat a lokacin dole ta zauna a part dinsu taki fitowa har barci ya dauketa a nan din shigowanshi gidan yasa yar uwarshi tashi lokacin da taji muryanshi yana gaisawa da mahaifiyarsu.
Dama kana tafe ashe kace kwanan nan ina tafe ummah na jima rabona da garin nan jiyan