Showing 195001 words to 198000 words out of 395027 words
Chapter 66 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
fada min cewa an turo mai kaya wanan karon guda hamsin tare da wasu kayan part part nasu don sabbon shigowane mashin din.
Yadda naji farin ciki ga mahaifina yasa nasan wanan sana,an ta karbeshi sosai ke nan tunda har yake baiyana min irin farin cikin da yake ciki a lokacin.
Allah ke nan yau ina mama da akace tace diya mace aiba diya bace don ita nata diyan maza tunda suka tasa suka fita gida wai sun tafi nema a cikin duniya saidai suzo ganin gida hannu sake inzasu koma na mota ma sai an nema su koma.
Allah da ikonshi da zai tashi kawo mai tallafawan sai ya kawowa macen da take fadin an haifawa baban mu kashe gida diya mata haihuwansu ai kashin gidane duk abinda mutum ya rora a rayuwanshi ga auren ya mace yake karewa.
Ance tayi sheri tayi masifa wai iyayyena sunji dadi ina can ina karuwanci ina turo masu da kudin karuwanci suna ci suna jin dadi sunawa mutane daga hanci.
A ciki fadanta da inna take fadawa inna wanan magana inna tace karuwanci mai lasisi ke nan don da baki fada ana kawo muna kaya ba da kika kyashe dasu ankawo din munci ke bakici bane ?
Dama wanan ranan da zakice zaki min gori nake jira Ai nasan sai kinyi min gorin hakan wata rana ?
Da ace bamu san me yar naki dake can tana cin mijin matar mutane aboye yana tura mata kudi tana yadda taga dama dashi nan da yake baku da tunane sam baku gane hakan baku ?
Wai meyasa mama kike hakane don Allah wanan magana idan aka fada muna haka zakiji dadi komai iskancin mutum aiba zai zauna da mijin matar da kake hannunta ba.
Shiyasa idan an fada muna baki damuwa mama don kina zargawa yayan mutane abinda bashi ba ni ban son haka wallahi ta juya ta koma dakin nasu.
Anty sahura ke nan yar wajen mama murja na dakin tana dariya tace dama mama tace saita fada taji gashi ko ta fada din yau akwai bom a gidan nan ke nan idan baba ya dawo ashe ?
Jin hakan yasa kafin ya dawo mama din ta kwasa zuwa family house din mu wai ta kawo karan innan mu wajen kakarmu ta kora mata karya da gaskiya ta fada mata.
Tace yanzu ma wanan sana,an da baba keyi wani katon kwartonane ko farka yake turowa baba din da kaya daga Lagos yake sayar mai dasu nan kano din.
Ran tsohuwar ya baci tace sai a kira mata baba duk inda yake dole kaninshi yaje ya nemoshi yazo hankali tashe don dan uwan nashi ya soma fada mai abindake faruwa.
Koda tsohuwar ta kora mai zancen da mama tazo salati yayi yace Rakiya Allah ya isar muna kan wanan kazafin da kikai muna din.
Yanzu faruqne zakice yana turo min da kudi don yana tare da Mairo yana lalata da ita ban yafe maki ba Rakiya aka dakatar dashi daga fadan hakan tare da binciken yaya zancen yake ?
Nan baba ya tsaya koro masu komai yace a kira shi faruq din a binckeshi wani dan uwanshi ya hana hakan yace wanan avin kunyar dawa za ayishi.
Ni tunda Rakiya tazo da zancen nan na san kazafine irin nata su ummah ne har yanzu basu san wanan shedaniyar ba.
Nayi kuka ranan da inna ke ban wanan labarin don gaskiya kazafin yayi yawa sai antynace ke fada min cewa ke ko idan tayi hakan kinga ke nan yanzu sai kiji tsoron tura masu sako don gudun sheri.
Na rike wanan maganan a kasan raina najawa mama din Allah ya isa yafi a kirga tun zancen yana cina a zuciyata har yakai na manta da hakan a raina.
Tun kafin monday da zan fara zuwa aiki na shirya tsab jin ance da yan arewa zanyi aiki yasa na saka dogon riga saidai kaina babu wani mayafi kirki duk rabin somana a waje yake nan na fito shar dani na sallami kowa na nufi titi.
Na kan godewa Allah da Paapa bai kan bani lift a motarshi saidai inbi motar kasuwa duk inda zanje da sai makiyan Allah sun zarga min wani sherin zuwa arewa tsakani na dashi din.
Saiya kasance bai ra,ayin yin hakan shima saboda tsaro da kare kai da yake dashi din bus na samu zuwa apapa ina bin direction din da ma,aikatar nasu yake.
Har nakai wajen dogon ginan glass irin na zamani dake nuna wajen ma,aikatane wanda akafi gjnawa a yanzu daga kaina nayi na dubi wajen da kyau kafin nasa kao zuwa cikin company da masu gasi suka sakawa wani dogon karfe a kofa.
Na nuna masu takardana don wajen akwai tsaro sosai suka ban uzinin shiga m,aikatan kai tsaye na karasa ina tunanen ina zan dosa kuma ?
Don wajen in baka da ilimi gaskiya zaka wahala na shiga abinda zai hau da mutum sama zuwa wajen da office office dinsu suke.
Ka iya hango na waje daga ciki amma shi baya ganin ka duban office din market manage nayi na nufi wajen kai tsaye
ZAINAB IDRIS MAKAWA[9/6, 7:37 AM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
6️⃣1️⃣🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Wani mutum yazo zai shiga office din da sauri nasha gabanshi ina gaidashi na fada mai ni bakuwar zuwace a yau suka nemi ganina a nan ma,aikatan.
Ya dan dago kai ya dan dubeni kafin ya mika hannu ya karbi takardan ya duba ya dago yana fadin kije kiga director shi zaki gani ya nuna min office din da hannu yace kije ina jin yana ciki ai.
Godiya nayi mai ya shige ciki nikuma na nufi can office din daya nuna min kai tsaye na tura na shiga wani mutum ne zaune ya kafawa computer ido yana aiki jin anshigo yasa ya dakatar da abinda yakeyi yana kallona tare da fadin.
Zamu iya taimakon ki ban amsa da baki ba sai takardan dana ciro na mika mai lokacin ya karba ya dago ya dan dubeni yana fadin.
Ki zauna a nan director yana ganawa da wasu customers a yanzu inda ya nuna min in zauna na zauna ina bin wajen da kallo.
Ba laifi don wajen ya hadu sosai an tsarashi irin a zamanance komai a cikin kwanciyan hankali sukeyi a wajen inda na kula ko magana mai tsayi kamar ba ayi a wajen saidai inshort ake komai.
Ido na lumshe ina gyara zama ina tunanen ta yaya zanyi wani aiki a wajen nan me zan iya yi a yanzu yadda nagansu so busy din nan suna nasu aiyukan haka ?
Karan bude kofane don sai lokacin na kula da akwai wani kofa ashe manne da jikin office din wanan din da nake zaune da zaka shiga.
Mutanen suka fito suna magana suka fita ina dai zaune shiru har na fara jin takaici a raina ina jam guntun tsuki naga wanan mutumin ya daga da laptop din shi ya shiga wanan office din.
Yana zaune yana duban baiyanan bakin nashi aka shigo ya dago yana fadin ya dai Aminu wanda aka kira da Aminu din yace ranka ya dade kayi bakuwa ya dago yana fadin bakuwa kuma wacece ?
Watace tazo da takardan headding naka naga sa hannunka a ciki tana dai zaune waje nace ta jiraka kana da baki tun dazun tazo.
Kace ta shigo ya fada a kasalamce yana maida fuskamshi kan abinda ya sameshi yanayi a office din da
Bai wani jima a ciki ba ya fito yana fadin miss ance zaki iya shigowa na mike na gyara rigata na kutsa kai zuwa cikin inda naga ya fito din nasan nan ne zan shiga lokacin.
Nashiga da dan siririn sallama tunda Uncle ya fada min wanan din ai dan arewa ne it should be shima musulmine ai kila ?
Ya dago don ganin waye bakuwan a nan muka hada ido dashi ya dan gyara zama tare da kawar da kai yana maida hankali ga laptop din ya kara daure fuska kamar bashi ba a wajen.
Ganin hakan yasa nima na daure tawa fuskan da hannu ya nuna min kujera ba tare da yayi min magana ba na taka zuwa bakin kujeran dake fuskantarshi din na zauna.
Duk jikina a sabule na ciro takardan da Uncle Paapa yace ance idan zanje nazo dashi na mika zuwa gabanshi na aje na kara dakewa kamar yadda shima yayi din ina jiram inji me zaice dani.
Saida ya gama ikonsa har ina batun tashi in fita naji ya dago yana fadin So you are wellcome to A A I Limited muna maki barka da zuwa aiki damu kamar yadda muka nemeki a cikon mu.
Dama kune ku kaiwa Uncle dina tayin aikin a kaina aiban zata ba don da ba zan karba ba yanzun ma ban sani ba nazo ai.
Ko kin sani me zakiyi akai babu na fada ina mikewa takardan danazo dashi na aje agabashi ina fadin ga takardanku nan sai anjima.
Ohh realy na fahinta kinfi son wacan aikin da kike hurda da maza iri iri suna karewa halittanki kallo kinga dole yafi namu nan da zamu sayaki a waje daya kamar matar kulle.
A naka tunane ke nan kawai dai ban ra,ayin aiki a karkashin wani balle a takurawa rayuwana da doka da oda gashin kaina nake ci nakuma fi jin dadin hakan.
Idan sun kallenima zasu barni inda suka ganni tunda ba yawon shedanci nake fita yi ba neman na kaina yake fitar dani ba tare dana dogara da kowa ba.
I see sosai kuwa naga hakan a tare dake yanzun nan sam ban taba zato ko tsanmanin kinkai haka ba sai yanzun nan da kika nuna min true clour din ki na zahiri.
Ashe ka gane tunda ka fahinta ina rokonka da wanan ya kare a nan daga yau don Allah yanzuma muka soma idan kin gama rashin kunyar taki sai kije a nuna maki inda zaki zauna.
Ba zanyi aiki da wanda yake min kallon mara tarbiya a idonshi ba don ko kabilun basu dubeni haka ba balle bahaushe da dan uwana dake neman bata min suna a,,,,
Sulaiman kana inane kazo ka tafi da yarinyar nan ka nuna mata wajenta don Allah tazo nan zata dameni da shirme ina aiki.
Abinda naji yana fada ke nan dayasa na dago kai ina kallonshi bai fi dan second ba wanda aka kira din ya shigo yana fadin.
Sir itace wanan itace kuje don Allah kada ta bata min lokacina da shirmenta kasan har yanzu ajebota ce ita ba wai tasan me duniya ke ciki bane.
Murmushi mutumin ya dan saki don bai taba ganin boss din nasa cikin yanayin daya sameshi ba don shima din murmushi yake a lokacin.
Hakan yasashi gane akwai wata a kasa tsakanin mu dama koda ya kirkiro aikin da zanyi dasu saida yaso jin ba,asin hakan ya katseshi a lokacin da cewa kayi abinda nace kawai sulaiman banson dogon bincikenan naka kamar dan jarida.
Ya juyo gareni yana fadin malam muje ko ya fada yana nuna min hanya da hannu dan hararashi nayi kafin na juya zuwa binshi din.
Suna da abin mamaki a wajen don cikin wanan glasan da suke din kofofine ashe manne da office din dayan ya bude min yana fadin bissimillah shigo daga ciki.
Sunana Sulauman nine PA din maigida duk wani aikin siri daya shafi maigida kusan nice mai gabatar dashi amma yanzu tunda kinzo aikina zai rage don kusan aikin mu daya dake a nan saidai dan bambamcin kadanne a tsakanin mu.
Banjin zanyi aiki daku wajen nan da sauri ya juyo yana fadin saboda me hjy wajen ne bai maki ba a gyara maki tsarin office din ?
Ban san manufarku na zabana zuwa wajen nan ba akwai graduated da yawa yayan hausawa a garin nan why saini zakuyi aiki dani ?
Zabin ogane ke kece ya zaba daga cikinsu don tunda nake da oga ban taba ganin yanawa wani yadda yai maki ba kallonshi nakeyi yace Allah ki yarda dani kinji nace Allah ai zakiji dadin hakan sosai nan gaba.
Dukawa yayi saitina kamar zai dauki abu ya rada min hakan ba halinsa bane gwadaki yakeyi a yanzu So kibi a hankali don Allah.
Nuna kaina nayi nace gwaji a kan me kuma na dai fada maki Allah ya bada sa,a ya juya ya fita har yaja kofan ya turo yana fadin kada ki manta idan kinga abinda bai maki ba a nan zaki iya magana good luck.
Ajiyan zuciya na sauke ina jingina da table din dake office din ido na lumshe ina tunane gwaji akan me ke nan zaiyi gwajinshi ya barni insha Allah.
Sunci albarkacin Paapa a wajena donshine a yanzu ba yadda zanyi dole in zauna dasu har in fahinci meye manufarsu ne a kaina ?
Tunda nayi abinda zaisa yaji haushi ya sallameni a yau din sai gashi wai har office aka ban a wajen inda zan dinga gudanar da abinda suke sonyi don ni ko aikin dai ban fahinta ba.
Zaune nakai saman kujeran dake office din ya fara dan juyawa dani sai hakan ya dauke min hankali nashiga motsa kujeran mai juyawa da mutum a cikin shakiyanci.
Intercom din dake office dinne ya shiga kara na daga kai sama na dubi inda karan yake fitowa bansan kona meye ba don haka na share hakan har ya gaji ya daina ringing don kanshi.
Haushi da takaicin dake zuciyana suka hani sukuni a lokacin don dole akwai manufa da yake dashi na matsawa nayi aiki dasu nan din duk daba karatu na kare ba balle ace an samo min aiki.
Indan don wancan aikin din da nakeyine ai wanan ina yinshine don kare wani abu daga rayuwata da banyi dabaran nemo dogaro da kai ba na fada wani mugun rayuwa da yanzu nabar iyayyena ko yan uwa da al,umman musulmai da kunya.
Shiyasa kabar mutum a yadda ka ganshi shi kadai yasan dalilinshi na fadawa halin da yake ciki abinyi in har rayuwan daka hango masa mara kyaune sai ka tayashi da addu,a shine mafita mafi alheri gareshi da kai kanka daka gani ko kaji.
Mutane da yawa daurewan rayuwa ke saka rayuwansu cikin wani hali wanda ba za a iya fahintar hakan a garesu ba sai a dauka kawai don ra,ayi suke hakan.
Kamar wanan mutumin ko wayeshi tabbas yasanni yasan koni wacece baidai ga daman fada min dalilin da yasa ya shigo rayuwana a yanzu bane.
Gashi ya daureni ya biyo min ta hanyan da ban iya dogon motsin daba zan iya gujewa tarkon da ya dana min ba ko zan kauce kuwa sai idan nayi da gaske tunda har ya hada da Paapa sunci albarkacin hakan don saboda Paapa din nazo wajen nan.
Saboda ko da daren washegarin da nazo saida ya kirani ya kara jaddada min da gobene fa zan fara fita aiki dasu ma,ana dai abin yana ranshi kuma ya dauki zancen da muhinmanci sosai a bangareshi.
Wai dan kwancin da nayi ashe barci ya daukeni wajen ina ruwan ba sabon ba don ban saba wanan zama haka ba kuma AC din dakina ya dade da mutuwa wani lokacin idan naji AC sai a cikin motan Ozil ko idan na shiga dakin anty.
Amma wanan sanyishi kamar na daban ga kamshi dake tashi a office din wanan yaja min barcin da ban shiryawa yiba a lokacin.
Table din da aka buga yasani tashi firgigit ina dan controling din kaina shine a tsaye kaina takarda ya jefo