Showing 300001 words to 303000 words out of 395027 words

Chapter 101 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

Murmushi tayi tana fadin harmu ke nan koda yake nasan zakiga laifina nidana fada mai kin fita a lokacin ganin wani ko aini na zata shine wallahi yazo a lokacin.

Amma abinda na fada mai kawai ke nan naga ranshi ya baci sosai a lokacin nace dashi kina zaune aka bugo maki waya.

Bansan yana da zafi haka ba wallahi saida naga yadda ransa ya baci a ranan dake nayi dana sanin fada mashi hakan ai.

Yanzu dai yace min zaizo bansan a ina ya samu lambata ba ya kira ni dashi nima nayi mamakin jin shine ke magana dazun din ?

Nace wanan kamar mayene ai duk abinda yake so yana samunshi a take ko kudine zai iya sai yasa ya sameshi.

Ni ban iya harka da zargi wallahi ya barni in huta please hakan yafi min sauki amma irin wanan niba zan iya ba gaakiya.

Tayi murmushi tana fadin sonki yakeyi da yawa idan kinga haka maryam da baisonki aiba zai tsaya bata ransa kan dan wanan maganan ba.

Don yana sona sai kuma ya dinga min fada haka anty haka ake son mutum kullum ana zarginsa ?

Har idan nabi ta nasa ba zan gaisa da kowa ba a garin nan saboda shi wanan course mate din nawa fa Okenah shine ya kirani na fita muke magana dasu.

Sone ya kawo haka ta kara maimaitawa gareni na bata fuska ina kawar da kaina daga gareta don wani irin zafi da nakeji har kasan zuciyata a lokacin.

Anyway zaizo yace zuwa anjima sai ki daure please ki saurareshi don Allah da bai damu dake da gaske ba yadda kukayi din nan dashi ranan dabai dawo gareki ba kuma .

Don da saidai ke ki bishi ki nemshi a yanzu kina dodofan ya dawo gareki tunda kece kikai mashi laifi ai .

Wani laifi anty ko aure aka daura min dashi ai ba zai hanani magana akan abinda ya shafi rayuwana ba mutanen nan yace bai son hurdana dasu nayi hakkuri na barsu yanzu kuma ba wani uzuri ya hauni da fada kamar yana zargina da shashanci.

Maryam maryan hankalinki yana ina zancen nan baikai haka ba don Allah ki tsaya ki natsu kiyi tunane kada ki dawo daga baya kina cizon yatsa.

Shiru nayi na kasa magana don a lokacin takaicin zancenta nake ji har kasan raina har tagaji tafice min daga dakin nan na samu daman mikewa ina jan tsuki.

Wanka nayi na saka wasu simple material din bubu mai fadi sosai mai filawowi baki da fari na dauro gyalen fashimina a kaina fari tare da dan sako jelanahi gefe daya na zubosu kamar suma haka suka kara haska min fuskata ya fito.

Cornflakes na jika a cup donshi kadai zan iyasha a lokacin falo na fito na zauna inda suke zaune tare da wata makwabciyar mu data shigo suna hira.

Muka gaisa na samu gefe daya na zauna ina shan abina a hankali ina kallon tv kuma ban tsoma masu baki ba duk da nasan hiran da sukeyi a lokacin.

Ina jin lokacin da wayanta yayi kara ta dauka tana amsawa naji tace muna gida bamu fita ba aiba inda muke zuwa inba fitane ya kamamu ba .

Jin hakan yasa na dan dago kai ina kallonta sai kuma na juya kan abinda nakeyi din a hankali tana gama wayan ta dubi makwabciyan namu ba kunya take fada mata .

Sorry maman Ayo zanyi bako yanzu wani dan family issue zamu tattauna da bakon nawa da sauri maman Ayo din take fadin ba matsala mm Amira nima yanzu nake son nakoma na gyara gida oga ya kusa dawowa aiki yanzu.

Ta mike ta rakata zuwa kofa a can wajen kuma suka tsaya suna mai da miyau irin na mata sam bamji dirin motarshi ba saboda lafiyan injin dinshi sai dana tsinkayo muryan anty na fadin.

Sannu da zuwa ashe kana kusa koda ka kira waya ya amsa mata kasa kasa tace dashi bissimillah shigo mana daga ciki ka tsaya a nan kamar wani bako ?

Kaina dago lokaci guda a daidai lokacin da yake kokarin debe takalmin fatan dake kafanshi plat masu ruwan kasa jikinsa kuma wani farin lallausar shadane ba sai an fada maki shaddan mai tsada bace.

Hakama hulan kamshi ruwan kasace irin yar dara din nan ta maza ba yau ba duk ranan da yai shiga irin ta yan arewa musanman rananan juma,a yafi irin wanan shigar dama a jikinsa shiga irin ta gargaji a wayance ta malam bahaushe.

Bissimillah ga wuri nan ka zauna ta fada daidai lokacin da itama ta karaso tsakiyan falin take fadin hakan.

Da sauri nayi kasa da kaina daga kallon bazatan da nayi masa amma a wanan kallon har na hango yar matsanaciyar damuwa a cikin fararen kwayan idonsa da nayi saurin kawar da kai a lokacin don a bazata naganshi kwatsam yana shigowa falon namu.

Sam ban zata wai zaizo din ba koda ta fada saboda nasan irin zuciyarshi da kafiya amma sai ya sabawa tunane gashima a tsakiyan falon mu yana kokarin zama a lokacin da tayi mai tayin zaman.

Tsam na aje cup din dake hannuna tare da mikewa don barin falon naji muryan anty na fadin ina kuma zaki bayan kinsan sabodake yazo ?

Dan kallonta nayi da kyar na iya budan bakina a lokacin nace zan shiga cikine anty niba wurina yazo ba kan yanzu common banson shirmen banza don Allah koma ki zauna kinji .

Haka na koma na zauna saman kujeran tare da dan karkata kaina ina basu baya alaman banma tare dasu lolacin ke nan .

Ki kyaleta anty ai tasan donta na shigo gidan nan bansan meyasa maryam take da fushi haka ba abin nan anyi ya wuce tun ranan amma ta rike abu daya tana ta fushi akanshi tun ranan.

Ko waya nakira bata dauka idan na turo mata text take ban replay yaya take son inyi for god sake anty ?

Yana magana manyan fararen idonsa gaba daya sun fito waje sunyi jawur har wani brown brown suka koma jikinsa yayi laushi sosai magananshi na karshe yasa na sake kalloshi har naga wanan yanayin lokacin daya kare da fadin.

Ko don taga ina sontane haka da yawa take min haka oho nima bayina bane hakan Allah ne ya saka min sonki over a zuciyana haka har ban iya controling din kaina a kanki ?

Dariya abin yabawa anty tana fadin ayya ba hakana bane itama ai tana sonka don ta nuna hakan taurin kaine kawai irin namu na mata takeyin hakan.

Don itama ai rashin ji daga gareka ya dameta tunda gaba dayan mu gidan nan har Amira da take mutumiyar ta ta hada damu tana fushi ko meye laifin mu mu a ciki oho ?

Laifin ku shine hadani dashi da kiyi mana na fada a kasan zuciyana a fili kuma gyara zama nayi irin ban damu da zancen su ba din nan .

Murmushi naji yayi a bangarenshi har najiyo daga inda nake yace a bata hakkuri yanzuma shinazo bata bayan haka kuma .

Motartace ta fito yau kwana biyu ke nan da shigowansu so na kai mata wajen kanikawa a kara duba lafiyanta kafin ta fara amfani da ita aka kuma wanke ta yanzun nan aka karbota shine nace bari na kawo mata ita a yau din.

Mota kuma oga Aliyu ta kirashi kamar yadda takanji ina kiranshi a gabansu da ogaAliyu din dama maryam tana da motane ashe ?

Eeh nine nayi dabaran saya mata da kudin albashinta duk da dai na bada fiye da rabin kudin amma tun lokacin dana fahinci tana son motar nayi wanan dabaran na tara mata kudin albashinta a wajena yanzu da motar ta fito saina hada da nawa na karasa saya mata akai mata takardu da komai da sunanta.

Allah da ikonshi maryam taban mamaki matuka don daidai da rana daya bata taba zancen kudinta damu ba haka shima officer tunda nayi mai bayanin abinda ke nan yace ba komai ayi hakan .

Saida an kasa albashin gida hudune muna tura mashi rabi sauran kuma ana adawanawa a asusun ma,adanan masaya hannun jari irin wanan.

Shi officer yasan komai don da yardanshi aka rubuta yarjejeniyar tun farko nayi hakane don na sauwaka mata shiga motar hanya da sauransu saidai ban fada mata ba don nasan ba lalai bane ta yarda a bangarenta.

Tunda ya soma bayani na juyo ina dubashi don jin zancen nake kamar a mafalki wai nice da mota yau motan kara kona icce irin ta wasan yara ?

Wanan tunanen nake har na kureshi da idanu ban sani ba saida naji yace yes nasan kin iya mota tun lokacin da kike tare da yaran can wanan dalilin yasa bansa an koya maki ba ai.

Me mutumin nan ke zancene wai zuwa yayi ya rudeni da mota ya saye min zuciya kome yasa hakan ya faru yanzu ?

Na kira shi officer shine ma ya ban lambaki dana kiraki dazun nasheda mai cewa za a kawo mata motan a yau din nan insha Allah yace ba matsala a mika mata ta fara amfani dashi din.

Aiko bai kira ba har yanzu naji antyna tana fada yayin data mike tana fadin bari dai in dauko maka ruwa in dawo karmu barka da kishi zaune.

No ki barshi hjy yanzun nan da muka fito mosque na tafi gida don in huta yau jumma,a yanzu haka daga gida nake ai So ba sai kin wahal da kanki ba nagode.

Ya juyo gareni yana fadin to ke motarki da kika zaba ranan ce ta iso yaya zamuje ki gantane ko har yanzu kina cikin fushin ne a bari sai kin huce ki ganta ?

Dariya antyna ta kwashe dashi tana fadin fushin me wace alheri irin haka ya sama ba zato ba tsamani zata tsaya fushin banza ?

Ido na lumshe a hankali saidai ban motsa ba a yadda nake na dan murguda baki nace aini bance dakai ina son mota ba balle in zaba tunda nasan diyar tallaka nake balle inje rigiman son mota a raina.

Wannan wani irin shirmen banzane wai kike yi maryam ko kice kina so ko kada kice tunda shi yana ra,ayin hakan a tare dake ai uwarsu daya

Mota fa anty mota fani mota haba anty ince da mutane ina na samo mota a yanzu ni dake karatu me zan fadawa mutane akan motan idan an ganni da ita ?

Kice wanda za ki aurane ya saya maki inji wanda zaice don me akai hakan bashi kike tsoro ba dai ace namiji ya saya maki mota tunda mu bamu da halin saya din.

Yayi murmushi ya gyara zama kafin ya soma fadin i know what iam doing maryam kin san dai tuntuni ina da halin saya maki har abinda yafi mota bandai saye din bane a lokacin don nasan zaki fadi hakan .

Wanan hakkinkine zufankine da kika nema da karfinki da zuciyarki ba wai ra,ayin kaina bane hakan don ki samu saukin yafiya duk inda kike so na bada goyon bayan hakan nima akan motar ?

Kaina sada kasa izuwa yanzu bansan abinda ya rage in fada ba kuma kan wanan zancen gabana bai soma faduwa ba sai lokacin da naji ya dauki waya yana fadin okey kun karaso ke nan gani tafe ku dan ban yan mintuna don Allah ?

Ya kashe wayan ya dago yana fadin so anty ni zan koma don har yanzu ashe cikin fushi take dani so zanje sai zuwa gobe zan leko insha Allah.

Saidai na duba nan kusa kamar wajen naku ba security sosai duk da akwai yan get pass a nan bakin shigowa wajen estate din nan amma mota irin wanan dole saida security sosai a kula.

Ki tashi mana ki taka mashi anty ta soma fada yayin data juya kanshi tana fadin oga Aliyu ni bansan kalan godiyan da zanyi ba a yanzu an gode sannu da dawainiya.

Kuyi hakkuri da abinda ya faru ranan tsakanin ku don Allah wai ashe abokin karatuntane ya kirata na zata kaine ai wallahi bansan ranka zai baci ba har na fada ma a lokacin.

Haba dai ai zancen ya wuce a wajena bansan a wajenta ba zan tafi driver na da muke tare ya karaso zai daukeni akwai inda nake son zuwa daga nan.

Nikan na kan na kasa dago kaina a lokacin don bamsan me zance dashi ba wajen ga antyna data hanani magana wanan babban zance da Sir din yazo min dashi yau ya girmewa tunane gaskiya.

Mota fa mota dai ta hawa koda yar corolace ai takai mota balle zancen da yake ba iein ranke ranken motar nan bace yake nufi.

Kusan a tare muka mike lokaci guda dashi don ganin kamar lalai tafiyan zaiyi yayin da antyna ta dan bar wajen a daidai lokacin

Dan motsa bakina nayi da zumar yi mashi godiya farko a lokacin naji yace kamar baki gane me nakewa anty bayani ba ko ?

Zaki iya tuna ranan dana baki option din mota ki dubawa matar wani abokina mota kika zaba mata wani da nace dake kudinsa yafi karfin hakan ?

To tun a wanan ranan aka fara adana maki kudin albashin ki don na mallaka maki wanan motar ta zama mallaki ki don naga kina da ra,ayi a kan motar.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/11, 9:58 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊9️⃣0️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Dolena na mike tsaye lokaci guda ganin shima ya mike yana da niyar tafiya a lokacin kamar yadda ya fada a lokacin na tabbatar daba mafalki nakeyi ba fa da gaskene wanan abinda nakeji kamar almara.

Haka dinne motarce ya kawo min wace take yanzu a matsayina quiet sure nasan a nan hakan ba komai bane wajensu namiji yasaiwa mace motar shiga don jin dadin rayuwa.

Amma a wajen mu arewa hakan mukan har gobe bakon abune mafi yawan mata masu mota wasu mahaifansu ke sai masu mota wasu kuma mazajenaune na aure ke sayawa matansu motan hawa don rage lalurori a garesu.

Amma a saiwa mace mota haka budurwa irina ya zama bakon lamari ga al,umma a arewa gaskiya dama ace ni din wani aiki nakeyi da kowa ya sani wanan ba zai zama cecekuce ba a jama,a amma ni ba yar kowa ba ba kuma matar kowa sai a ganni da mota ina tukawa a matsayin nawa dolene jama,a su saka min ayar tambaya a cikin lamarina.

Wanan yasa na zabura na mike nabi bayanshi don in sauke mai abindake zuciyana lokacin amma muna fita na soma fadin amma daddy wanan abinda kayi kasan bai dace ba gaskiya ?

Quiet my friend waye daddy ki please ko kin mata da kalman da kika fada shekaran jiya a kainane idan kin manta in tuna maki ni Aliyune ba daddy ba.

Mota kuma for my on safe na sayo maki ita haka yafi min kwanciyan hankali dake maryam wanan yawan bin motan haya da kikeyi yana daga min hankali sosai don security a kasan nan.

Yanzu hankalina zai dan kwanta tunda nasan duk inda zaki dole dai da motarkice zaki fita kada ki dauka wai don abinda ya faru tsakanin mu yasa yanzu na sai maki wanan motan idan kinyi tunanen hakan zuciyarki ta baki karya.

Don ni na jima da biyan kudin motan nan saboda dake kayane basu samu shigowa da wuri ba kin tuna na baki zabi a lokacin nace matar wani abokinane zan sayawa.

Idona lumshe don tuna da hakan da mukayi a office dinshi hakan yasa na dan kalloshi cikin kunya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login