Showing 42001 words to 45000 words out of 395027 words

Chapter 15 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

innanku ba tsohuwa bace ta saura haihuwa nace ai nice yarta ta farko mama kuma ta fita girma tace waye mama ko innanku su biyune ?

Na amsa da eeh ita da mamane matan baba sai gashi tana jin labarina sannu a hankali daga bakina cikin hikima irin ta wanda ya girmeka din nan.

Muna nan falo a zaune tana jefo min tambaya ina bata amsa har mutumin ya gama ya fito yana fadin ya gama aikinsa zai tafi.

Naji tana mashi godiya ta mika min dubu biyu na bashi kudin mota yana ta godiya ya fita ni dai sai binshi nakeyi da kallon mamaki.

Kin gashi tausayi ya bani na daukeshi aikin abincin nan ya gama makaranta ba aikinyi kuma yana neman abinda zaici shine nace yazo ya dinga dafa min abinci dasu wanke wanke.

Mamaki ya kara kamani yadda kato kamar wanan ba zai koma gona ba itace ke fadin ku a can maza basu irin aikin nan ko ?

Nace shine ai gashi kato yaje kawai ya samu gona yayi noma ai yafi mashi aikin girkin nan girki aisai mata ba maza ba.

Cikin irin hiran ta fahinci wani abu daga rayuwata sallah yasa muka bar wajen zuwa la,asar sai gata ta fito tana fada min zata unguwa saita dawo nayi mata Allah ya tsare ta fice.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[7/3, 10:44 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

1️⃣4️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,

🀳AUNTY ZEE MOM MUJJAHID KATSINA 08262859027🀳

πŸ‘*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA*

*Maganin sanyi 5k*

πŸ‘*Maganin sanyi*

*5k*

πŸ‘*Maganin ciwon Qoda 10k*

πŸ‘*Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k

*MAGANINπŸ‘ MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*

πŸ‘*INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU*

*Maganin gyaran Nono πŸ‘8k*

πŸ‘*MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE*

πŸ‘*Maganin Rage Tumbi 7k*

πŸ‘*MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE*

*Maganin Basur 5k*

*MAGANIN CIWON SUGARπŸ‘ CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI*

*Maganin ciwon Sugar 10k*

*08162859027*

*09070027627*

*Location*KATSINA STATE*

*ACCOUNT NUMBER*

*8162859027*

*ZAINAB SHU AIBU*

*OPAY*

*OR*

*3968303018*

*FCMB*

*ZAINAB SHU AIBU*

πŸ‘ƒ*DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO*

Banda aiki a cikin yan kwana biyun da nayi a gidan daga in wanka sai cin abinci aikina kawai shine shara da goge gogen kayan falon .

Sai kuma wanke wanke wanan dai mutumin shike masu girki iyakarmu girkin safe da mukeyi na karyawa kafin Papa ya fita daga gida.

Allah ya gani a cikin tsanda nake cin abincinshi haka kuma nama bai dahuwa da taurinsa za a barshi kaita fama dashi a cikin bakinka.

Shikafan kuma a tsatsaye kamar anyi dahuwar half done shiyasa nake dan cakulawa in tashi ince na koshi ga mai dahuwan kafiri an koya muna akidar kyamar duk abunda ya fito a hannun wanda ba musshigansu donshi wanan akidar yake aiki a jikina da zuciya har gobe.

Gashi kuma a yanzu Allah ya kawoni zama garin da suke da gaurayen da musulmai don hatta iyayyan gidan nawa idan sunyi wani shiga sai kice su din ba musulmai bane ga shigansu.

A haka kuma su ban ganin sun damu saidai inta binsu da kallo ina mamakin wanan dabi,an nasu haka ba kunya koda yamma idan mijin na gida zakiga ya fito dagashi sai yar riga karama da wando iya gwiwa dashi zai fita idan fita ya kamshi inta anyanawa a raina baijin kunyar hakan ne da yakeyi.

Ita kuma matar zaki ganta da dan riga ko wandon da zai fitar mata da suranta waje da dan gyale karami iya kafada nikan wanan sai ya zamo min bakon abu abin kallo kuma a wajena.

Nakai sati daya banda wanan maigirkin ba wanda ke shigowa gidan saidai inta zama ni kadai a falo tana daki ita kwance don bata faye fitowa haka waje sosai ba koda yaushe.

Nocking din kofan da akeyi yasa na mike daga inda nake kwance ina tunane tun safe dana fito falon na kwanta kofan na nufa na bude wasu mata masu shigan kafirai nagani a kofan don dukkansu babu mai mayafi a cikinsu.

Ke madam dinki na ciki suka tambaya cikin harshen turanci ban basu amsa ba sai juyawa da nayi zuwa cikin gidan dakinta na tsaya a kofa nayi sallama ta amsa min daga cikin dakin na zatama barci takeyi a dakin ashe idonta biyu.

Anty kina da baki a falo da sauri ta dago tana fadin ke kin san sune da kika bari suka shigo muna gida ke kuma kin shigo kin barsu a falon kin sani koba mutanen kirki bane su din ?

Da sauri na koma na samu har sun zauna suna hira a tsakaninsu sai gata ta fito naji tana fadin a,a madam lawisa kune a tafe ashe ?

Tace min wasu baki har ina fadin ta dawo taga su waye tana fadin hakan har na dauko masu ruwa da kofi na aje a gabansu tare da gaidasu a cikin hausa suka amsa min wani iri.

Wait wooo badai yar aikin da akace an kawo maki bane daga arewa dayansu ta fada tana kallona dukkansu din kallona sukeyi a wajen .

Suna irin turancin kabilu da mukeji kamar yare a wajen mu saidai ka canki guda guda a cikinsa don ko a lokacin na dan ji abinda suke fada kamar haka.

Ke madam Faruq kika yarda aka kawo maki wanan yarinyar mai kyau a matsayin yar aiki baki tsoron tazo ta kwace maki miji yadda akace sunayi a arewa.

Wanan sister din muce ai me zaikai man dina duban wanan sa,an yar cikinshi common don Allah ku bar zancen nan ita din sister din maigidanane uwarsu daya.

Yanzu naji magana wanan kan zaki iya zama da ita saidai duk da hakan sai kinyi a hankali kira sun turatane tazo leken asiri sai naji tace koma meye ai ta zauna dai ba abinda ya dameni da zamanta nan.

Injin dai bata jin turanci wata ta fada ta amsa da bata jin turanci sai hausa ai sunfi ganewa yarensu na hausa.

Sun jima da matan suna hira inda nake jin suna gulman matar data haihu a unguwar akai suna har naji sun mike sun fita donni tunda na basu ruwa suka soma magana na koma dakina na kwanta saidai ina tsinkayo abinda suke fadi a lokacin.

Ba abinda yai min dadi kamar cewan da tayi dasu nidin aiba yar aiki bace yar uwar mijintace ni nazo tayata zama don haka bata da shakku a kaina.

Data dawo daga rakasu ta samu na kwashe kayan ina gyara falon tace kai ina yinki maryam kinsan aikinki wallahi waiko kin taba zama a wani wajene kafin nan ?

A,a nadai iya komai ina taya innan mu aiki a gida tace gaskiya innan ku ta kyauta ta baku tarbiya mai kyau zan dai samu lokaci mu kira inna din nan mu gaida ita duk zancen ki ba a jin kince baba saidai inna a kullun .

Nayi murmushi tace min kinyi karatu ai na amsa da eeh tace to meyasa kika bari nayi kasa da kai nace ban bari ba saida nazo nan ko ranan da mukazo har na shirya zan tafi school saiga umma tazo gidan mu tace min tafiyane a ranan dole na cire uniform din.

Kai fa akan zuwa nan kika dakatar da karatun ki maryam why zasuyi maki haka su rabaki da karatu har kinyi nisa haka gaskiya ba a kyauta maki ba.

Duk da dai naji dasin zuwan ki nan sosai nice aka taimaka insha Allahu zan duba ki fara karatu nan gaban unguwar nan akwai wani makarantar gwauni saiki dinga zuwa can ki karasa Allah yasa kina da kokari kada su mayar dake baya da yawa.

Don kinsan karatun can ba daya bane da na nan dole saika iya rubutu da karatu a nan ba komai koda sun sareki ma sai kici gaba a hakan ba zan yarda a sanadina ki fasa karatun ki ba insha Allahu.

Wani dadi naji har kasan raina tsoron da fargabana na mugun kudirin da mama ta lissafo min kafin tafiyan nan duk banci karo dashi a inda nazo.

Gashi da zuwana sai alherine fara bina ga fuska data ban bana tauyewa ba kamar yadda mamake fadi kafin nazo ga kuma sutura ta ban uwa uba kuma wanan albishir din datayi min a lokacin.

Don haka bansan lokacin dana mike na durkusa a gabata kamar zan rugumeta ina zabga mata godiya da fatan alheri a rayuwanta abinda na kula addu,an zuri,an da nayi mata yafi mata komai dadi a lokacin.

Banda matsala fa matukar bakece kika canza halin nan da kikazo min dashi ba idan kika mike da hakan zamuji dadin juna dake a gidan nan.

Ni dai na fada maki abinda banso munafunci da tsegumi sai kuma kazanta idan kin kiyayye hakan zamu zauna lafiya dake.

Insha Allahu anty zan kiyayya kamar yadda kika fada tace bari Papa ya dawo zan mashi magana ya sama maki school ki fara zuwa yafi wanan zaman a gida.

Naji matukar dadi a raina don idan haka ya tabbata a gareni ko iya haka ai sungama min komai banda buri a lokacin sai inga na gama secondary dina wanda a tunanena nake ganin cewa idan na gamashi ai na cika karatu.

Ranan weekend suna zaune da mijinta a falo naji tana fadin Papa ina son maryam ta fara karatu don zamata a haka ba karatu baiyi ba wallahi.

Naji mijin yace da ita karatu kuma kamar wanan za a saka wani karatu yanzu ta soma daga ina ai ina ganin tayi girma ga karatu yanzu tunda bata farawa daga primary .

Yarinyar dake SS class a can gida sanadiyar zuwanta nan ne fa ta daina karatu amma a gida ai ss class take muka dauko ta.

What dama tana katatune suka bamu ita wallahi ta fada a hausanta dake da dan surkin yare don ita yare ya sata tsakiya uwa shuwa uba igala hausan dai anjishine cikin hukuncin Allah ga kuma miji dan kano.

Ina jinsu har suka kare shawara akaina inda mijin yake fadin yarinyar nada hankali sosai zan duba a kaita school ta karasa karatun ta wanan maganan shine sanadin komawata makaranta.

Don ba afi sati daya da maganar ba tazo min tana fadin in tashi in shirya zasu kaini makaranta ko za a daukeni a term din don anyi nisa a zango na biyu.

Munje din sun gwadani matsala daya shine rashin turanci a bakina amma duk tambayoyin da sukai min akan karatu ina basu amsa irin rayuwan bokon dan arewa ina ji ban dai iya fadane sosai don miyan kuka dake taushe muna bakin fadan harshen nasara.

Anyi muhawara inda a karshe dai wata malama tace a barni a inda nake din idan sunga zan iya cigaba karshen zango sai in tafi tare da sauran dalibai idan ban iya ba kuma a barni in sake maimaita ajin na shekara daya.

Papa ya biya komai a lokacin sannan aka auna tsawona aka ban uniform da littatafai da zan dinga karantawa dana rubutu mai tambarin makarantan .

Murna a wajena bai faduwa naso kwarai ranan ace ina kusa da wani na gida yaji wanan albishir din arzikin daya samemi saida ba wanda zanyi sharing din zancen dashi a kusa dani.

Muna fita get din makarantar ta fara fadin yau naji kunya dole in fara koya maki turanci daga yau ba zamu kara hausa a gidan mu bama sai kinji english zamu daina.

Ashe aiki ya sameku kuwa wanan bata biyo mahaifinta ba wajen kokari a lokacin shi yafi kowa kwazo a makarantar mu.

Amma ace yarshi ko zo in kasheka ta kasa fada da turanci idan zaki maida hankali ki saurari abinda sukeyi ki mayar inba hakaba su mayar dake baya kamar yadda suka fada.

Ina baya zaune tsuru tsuru ina kallon yanayin garin dan ban taba fita ko ina ba sai wanan ranan tunda nazo ina gida kumshe kamar kayan wanki ban zuwa ko ina daga falo sai daki .

Labarin tafiyana kamar an kada ganga a cikin unguwa duk mama tabi ta barada cewa na tafi aikatau lagos .

Kwadayi yasa mahaufiyata ta turani gidan masu kudi inyi boyi boyi don inna ta samu kudi tofin Allah waddarai sukeyi dan me inna tayi wanan sakacin a kaina saboda abin duniya.

Allah da ikonsa tana irin maganan nan a gidan buki wata makwabciyan mu tace kai amma Rakiya baki da tsoron Allah yarinyar da kece sanadin tafiyanta kika hada kai da sarakuwarku aka bada ita yanzu kuma kin biyo baya kina masu wani kazafi.

Duk Allah ya isan da mijinku keyi ranan muji komai wallahi nan fada ya kaure tsakanin mama da innan habiba don gidan mu hade yake da nasu .

Wanan fadan na gidan buki yasa wasu suka san kazafi kawai mama keyi don kawai ta batawa inna suna haka kuma hassadan mu yasa mama tayi min hakan.

Suke fadin ko zancen rabani da saurayina ai da hannun mama ciki don tana bakin ciki na samu matsaya diyan ta da suke manya basu samu ba .

Yasa taje suka hada kai da hjy Tani suka kulla min sheri sai gashi yan unguwa sunji komai wanan yasa mama ta shafawa innan mu lafiya a lokacin.

Ga zancen auren Salma daya soma rawa don Mammam belli yace shi sam salma batayi mai ba don ba kalan macen da yake so bane ita.

Hjy Tani data kwallafawa auren rai ta soma fadi tashi taga sun jawo hankalin Bello din zuwa ga yarta sunyi sa,a ya dan karkato don dayazo gari yazo wajanta har sau ukku kafin ya koma.

Tayi habaici tana fadin duk wanda yaci tuwo da ita ai miya sha badai tuwo ba da anso zancen nan ya wargaje ai mata dariya itako ko tsirara zata tafi sai taga anyi wanan auren matukar tana raye .

Anty Fati data gaji da habaicin ta fito daga part dinta ta kafa farar kujeran roba a tsakar gida ta soma fadin wanda ya damu da shirmen mutu ai sai a fada mai.

Yawo tsirara dama ai gado mutum yayi ba saiya fada ba don baida banbamci da mahaukaci ai lafiya bata kawo haka har mutum ya fito yai bugun gaban shi ya isarwa kansa baya son taimakon Allah.

Da batan kashedin da mijinsu yai mata akan yunkurin dukan anty Fati tunda ta fahinci shigan cikine a jikinta tasoma hauka akan cikin irin na maman gidan mu .

Shine mijin nasu yayi mata iyaka da ita yace duk ranan data taba mashi mata da ciki a bakin aurenta don saisu taruwa anty Fati din ita da yaranta dake tayata fadan kishi da amaryan nata anty Fati.

Duk da hakan saida sukai cacan baki a tsakaninsu din kowa ya fadawa dan uwa abinda ke cikinshi anty fati tace dama ai ansan gwanan shige shigen bokaye da malamai kike wanan kowa ya sani don haka ba sai kin fada ba.

Keda yarki kun zama macizai da baku ramin kanku saina wani idan yar abin kwaraine aidata nemo nata da bata saya da kwacewa kawarta da kowa yasansu tare saurayi ba.

Kuda kuka zama abin kyama a shiya don baki san ciwon kanki ba har zaki fito kina fadin ya dawo mai bakin ciki ya mutu me mutum zaiwa bakin ciki a nan indama abin kwarai kuka kwata ba wanan dan yaudaran ba daga Maryam tayi arziki Allah ya rabata da wahala me maryam zatayi dashi a yanzu ?

Ran hjy tani ya baci matuka ita da yayanta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login