Showing 12001 words to 15000 words out of 395027 words

Chapter 5 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

mama wallahi.

Itama mama cikin mamaki rake binshi da kallo tace shigar mata zakayine yau kuma baban baby ?

Yace ko nashigar mata laifine ne yarinyar nan tayi makine haka kika dauki karan tsana kika dora mata ita da yaranta haba komai nason dan marmari mana da ace tayi wani abinne sai ki samu dalili ta hau fada yace shidai ya fada mata bai son hakan tabar mutane suji da abinda ke gabansu don Allah.

Karkice tallan dana fara ya rabani da Salma muna nan har yanzu tare da ita gidansu daine na rage yawan shiga a yanzu ba don komai ba sai irin yadda mahaifiyarta take nuna min tsana a filin Allah don dai kawai Allah ya hada jinina da salmane muke tare .

Akwai wani dan kusa da unguwarmu koma ince a unguwarmu din saidai akwai dan nisa a tsakanin gidajen mu dasu ba kamar yadda muke kusa da kusa danasu salma ba.

Yana yawan skn wasa dani ko wani lokaci shi din dan gayune sosai yana don yana daukan wankan zamani bai son saka kaya irin tamu ta gargajiya saidai irin su jeans da t,shirt haka ko yaushe zaki ganshi cikin kananun kaya a jikinshi.

Sunanshi mammam Bello haka naji ana kirashi da sunan yana zuwa wajen samarin dake makwantaka da gidan mu hirane shi .

Tun ranan daya biyo ya samu muna wasan turanci da Salma tace ban iya ba nace na iya muke gasa a tsakanin mu itace take tambayan salisu waya fadi daidai yasa min suna wai beauty sunan dayaso ya bini a unguwarmu ke nan.

Yana da son wasa ya rike hannun mutum yana wasa dashi niko tun ina karama inna mu ta horeni da inyarda wani namiji yana taba min jikina , koma wayeshi ko yaya muke da maishi kada in yarda ya rike min hannuna don dan iskan namiji keda wanan dabi,an na taba mace don ya lalatata,.

Jin hakan yasa na fara daure mashi fuska don banson yadda ko yaushe yake kokarin kai hannunsa a jikina din nan da sunan wasa.

Akwai wani ranan daya kamoni yana kokarin rugumeni a jikinsa yana dariyan shakiyanci da sunan wasa na tureshi ina kai mai bugu tare da fadin an fadama ni yar iskace da zakana rike min jikina ?

Abokan hiran nashi guda biyu suka kwashe da dariya suna fadin kai mutumin fa yarinyar nan kwarkwasace a wajen wayau bata yarda da irin wasan nan ba.

Talla baisa ta yarda da hakan ba kana ganinta wajen nan shegen wayaune da ita kamar kwarkwasa tana wani juya manyan idanuwata kamar kwallo.

Baiyi fushi ba don ba a alaman hakan a fuskanshi yace banga laifinta ba wanan da kuke ganin babban iri ce a nan matar ajewa a gaban motace kuna ganinta nan haka.

Tun wanan ranan suke min shakiyanci dashi tunda suga yadda nayi fada na barwajen suke kirana da mairon mamman bello.

Tun ina fada dole nagaji na kyalesu saiga sunan yana son bina a cikin unguwa kinsan mutane da son batawa mutum sunashi da sunjine sun rike kamar ana jira.

Nasan ya koma school ne don na barganinshi lokacin ban ma san cewa yana wani abu wai karatu ba nidai abinda na sani kawai shine dan unguwarmune shima.

Wata rana daya daga cikin abokansa yazo sayen abinci yake min ba,a da cewa kodai ki tambayi mutuminki mairo ?.

Nace wake nan yace mamman bello mana ai yana school ya koma kinsan karatu yake a jami,a yama kusa karewa nake gani.

Kai haba shiyasa yake dan gaye ashe dan bokone shi Salma take fadin keko ba a fada ba ai kinsani baki ganinsa wayayyen mutum ?

Hakan da yake shine wayewa salma mutum kullum a tamke kamar biri yana shiga kamar iyamuri Allah nina dauka kafirine shi bai sallah sai ranan danaga yana alwala nasan musulmine shi.

Amma ke mairo ko sunansa da kikaji ai kinsan musulmine nace ni ina ruwana tunda ban taba jin wani da suna irin nasa ba ?

Aiko zan fada masa mekice na murguda baki nace sai me idan ka fada mai to ina ruwana dashi na juya nacigaba da sayar da abincina.

Sam na mata da munyi haka kamar sati biyu tsakani na fito a cikin yakutattun uniform dina da talauci ya hana aimin sabo a lokacin don idan na dinka uniform sai nayi sauyin aji sau biyu dashi ban damu ba.

Tufanema nakan dan samu kuncen sisters din Salma na gyara don haka banda yunwar tufafin sakawa a rayuwata don duk suka fitar ni suke kira suba nakaiwa wata makwabciyarmu ta gyara min daidai jikina wasu kuma innan mu nake barwa tasa hakan yasa baki gane rashin mu a yanzu.

Uniform kuma tunda ba a school din mu suke karatu ba yan gidansu yasa ban samun kuncen nasu nake fama da nawa hakana.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[6/20, 9:55 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

5️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Mairon mamman bello aka fada a bayana muryan salis abokinsa da nake yawan ganinsu a tare nkuma inajin saboda salis dinne yake yawan zuwa shiyan namu hira.

Na juyo idona ya sauka akansu su biyune tafe ni kaina sai naji na tsargu da irin kallon da yake min a lokaci badon komai ba sai don irin yanayin shigana da tufafin makarantana daya nuna talauci zalla a jikina.

Dan daburcewa bayi ina yake kafin kuma in mayar da fuska in daure kamar yadda shima fuskansa babu walwala a cikinsa lokacin.

Ke haka kike zuwa makaranta abinda ya fada ke nan da muka hade ni kuma cikin tsiwa na mayar mai da ina ruwanka ?

Kallon abokin nasa yayi sai baice komai ba juya kawai na wuce zuwa school rai bace duk da ban damu da abinda mutane kecewa ba wanan karon sai naji na tsargu da nashi maganan.

Hakan yasa da zan dawo gida ban yarda nabi ta hanyan da suke zama ba don kada mu kara haduwa dasu inji kunya nabi ta baya zuwa gida.

Munyi haka da kwana biyu ranan lahadi ina wanki bayan na sayar da sana,an safe saiga wani yaro mai zakin murya ya shigo yana fadin wai mamman bello yace mairo tazo.

Na dago da mamaki jin sunan daya fada din nace kaje jace bata gida don a lokacin duk iyayyena suna tsakar gida har baba yana gefe kwance da redio shi dayake saurare kullum kamar mai jiram albishir .

Yaron ya kara sallama yana fasin wai ance ana sallama da mairo a wajen karan redio baba ya rage yana fadin wata mairo kuma mairo ko yannanta ?

Mairo akace in kira baba ya sake fadin waye yaron yace bansanshi ba wasune a mota nazo zan wuce sukace in shigo in kira masu mairo sai naga baba ya mike zaune da sauri.

Mama ta katseni daga kallon mamakin da nakewa baba ganin yadda ya zabura yake zaro ido a cikin mamaki jin ance ni yar shekara goma sha ukku nice akewa sallama ba jiga jigan yan matan gidan mu su murja da sahura ba.

Itako mama sai cewa tayi yau dai gaskiya yayi halinsa gara da akayi a gabanka yau in anyi magana kace ga wa yanda ke neman bata maka suna a unguwa.

Fitan baba yayi daidai da shigowan yaron daya dawo yake fasin wai mairon mamman bello ake nema kai muje inga wani dan iskan ne da wanan maganan haka.

Suna tsaye wajen suka hango baba fitowa daga cikin gida yana dan dube dube karasowa sukayi wurinshi tare da zubewa kasa suna gaidashi.

Ya amsa fuska daure kafin salis yace baba dama abokin nan nawa dan gidan Alh musa mai yadi shine yaga yadda mairo ke fita boko sai hakan bai masa dadi ba ya yanko yaddi ya dinka mata tunda yaga tana da ra,ayin karatu har takalma da jakkar makaranta da littatafai ya hado mata gasu .

Yana kokarin mikawa baba babban ledan vacco da suka saka kayam a ciki dama shine muka korata ta karba bamu san kana ciki ba ai ?

Ina nan nikan nayi mamaki jin yaro yazo yana fadin wai ana sallama da mairo na dauka shakiyan duniya din nan ne yaran layi ban dauka ku bane ai .

Mune baba salis din ya kara fada cikin kwantar da muryanshi yace yadda take kula da son karatune ya bashi sha,awa ya sayo mata tufafin taji dadin zuwa.

Allahu akbar angode kaji angode salisu kayi muna godiya mairo ta gode kaji mairo kan nason karatu gaskiya saidai karfin mune bai kai ba yadda karatu ya koma a yanzu.

Ba komai baba insha Allahu za a kula a dinga taimakawa ai su kannen mune nima haka na fada mai tun kafin muzo .

Baba yayi masu godiya ya karbi kayan zuwa cikin gida har lokacin mama na kan bakinta koda ya shigo da kaya niki niki ya nufoni yana fadin karbi nan.

Ashe yaron nan dan gidan mai yadi yazo da salisu dan gidan headmaster da taimako akan yadda kike fita zuwa makaranta shine suka kawo maki gudunmawa dan ki maida hankalinki ga karatu.

Wata sabuwa maula kuma aka komayi a gidan bamu sani ba koda yake da gani an jima anayi tunda gashi ko ajikin maza ?

Ta yaya wasu kattan banza zasu zo su sallama su juye zance da wani magana har ka yarda gaskiya talauci baiyi ba wallahi talaici babban cuta .

Ikon Allah Rakiya nikewa wanan maganan haka har lalacewana yakai ace yau ni kike kira da dan maula nida iyalina saukin abin bandai dauki kwanon bara ina bin layi ba ?

Ai gaskiya na fada yau da ace dakinane haka ya faru da yanzu ance ina koyawa yara shashanci ke karbi kinji jeki dakin ki ki aje baba ya fada na karba da sauri zuwa dakin mu har lokacin gabana bai bar faduwa ba.

Jin baba baiwa inna wani bayani ba yasa saida dare yayi mun kwanta ni har nayi barci naji ana tasheni na zabura tace ke ki natsu tashi ki zauna magana zamuyi dake jin hakan yasa na mike zaune da kyau ina saurarenta .

Tace dani keyar yaya kin tabbatar bakece kika roki mutanen nan kayan nan ba ?

Da sauri na dago kai na fara rantse rantse ta tareni da fasin rufa min baki don Allah ke ba a siri dakene zaki daga min murya a cikin daren nan kinsan halin yaya sarai ki yaushe kunneta a kashe yake tana saurare taji wani abu daga garemu.

Nayi murya kasa kasa nace wallahi mama bani na rokesu ba na daisan ranan da zanje makaranta da safe na hadu dasu amma bance dasu komai ba .

Ajiyan zuciya naji ta sauke tana bina da harara tace to ki natsu dai don Allah kin daiga yadda ake muna bita da kulli gidan nan ban bi kowa da sheri ba amma fatan yaya a kullum taga wani mugun abu ya sameni dani daku gidan nan.

Wallahi mama gaskiya na fada maki ki dai natsu nace dake don Allah kada inji ko in gani a gidan nan kince karatu kike so to ki mayar da hankali akan karatunki .

Na koma na kwanta a hankali na takure a waje daya na kasa barci sai tunanen yadda zanciwa mamman mutunci nake a raina.

Har inna tagama dan kimtse kimtsenta da kullun saida dare takeyi idan kowa ya kwanta irin su boye duk wasu muhinman abubuwanta don satan da aka dauko yi muna a dakin .

Idan tayi magana kuma ace wata mayar barayi banda yaranta wa zai dauka shiyasa takewa kudinta mugun boyo a dakin a cikin dare.

Washegari da yake asabarne na fita da kunun safe da fanke na samu masayana suna jirana don komai sammako zan samu maza masu zuwa kasuwa suna jiran koko su karya dashi wasu su hada da fanke da sugar da muke kullawa.

Ba bata lokaci robon koko ya kare sauran fankenma aka saye don ba koko na tattara kayana zuwa cikin gida na samu inna tana wanke geron kunu dana sayarwa kayan na kai wajen wanke wanke.

Na shiga daki dauko omo naji mama na fadin umm,humm gamu gani dai wai an binne tsohuwa mutum bashi yafi kowa kan talla ba da an fita a dawo kamar da gaske.

Waini me mukayiwa matan nan da bata bin mu da alheri nifa don innace nake mata komai ba wai tsoronta nake ji ba yadda suke nufi amma bari ai irin abinda nake tunane ke nan a zuciyana a dakin na fito na hada ruwa wanke kayan.

Naja kayan mama tsab na wanke har tukwane da duk wani abun amfani dana san namune na bar nasu a wajen ban wanke ba don suna daki ina jinsu suna dariye dariyensu.

Nasan shiri suke zasu kasuwa sayen kayan sana,ansu da kullun rana sai anshiga kasuwa an sayo idan anje kuma a jima har wani lokaci kafin a dawo gida a dora girki duk mama bata ganin hakan laifi a wajen ta saini.

Har barci ya soma daukana kafin lokacin dora abincin ranan da mukeyi can naji muryan anty murja na fafdin kam uban nan waiba naga kamar mairo tayi wanke wanke ba ?

Ta juya ta dubi inda muke aje kayan mu tace wallahi mama ki fito ga kayanki nan yadda suke mairo bata wanke ba ta dai wanke nasu ta kife.

Gaba dayansu suka fito daga dakin suna kallon tarin kayan dana bari a wajen don duk akasari kayan sune dama da wuya kiga kayan mu a waje haka yadda suke barin nasu.

Nice kuma zan wankeshi kamar jaka Allah ma yayini mai zafin nama ban tashi irinsu da son jiki ba don sam ita kanta mama bata barni ba tun ina shekara hudu kila na fara aiki a gidan mu.

Wata sabuwa naji yata sahura ta fada mama ra karba da fadin Lalaikam wata sabuwa inji yan caca ai dole keko tunda suna ganin yanzu sun kai tunda nagama ciyar dasu sunyi karfi ba dole a fara nuna min iskanci ba.

Ki tambayeta mana mama kila akwai abinda yasa bata wanke ba ko omone ba a bayar ba ta barsu nan yaya sahura ta kara fadan hakan ta juya zuwa dakinsu.

Omon me kuma bata san inda take daukan omo bane idan zata wanke kayan ban dai yardane su wanke min kayan tallansu da omona kawai.

Andaice kada ta wanke min ne in bashi ba ai mairo bata taba fashin wanke kayana a gidan nan ba yanzu uwarta tana ganin sun kai suna rike sisi a hannunsu ba dole yau ace za a kawo min rainin wayau ba .

Haba yaya ya kamata kiyi min adalci a gidan nan ko baki saniba ina sa inna isah tayi maki aiki ko kina nan ko baki nan ni wallahi bansan ma bata wanke ba.

Ni ba zan taba hana yaro yaiwa babba aiki ba don dadinshine hakan wata rana don me zance tabar maki kayanki a nan yau ?

Kin ma isa ki hanata Ai ?

Kai kai haba wai meye hakane don Allah dai banson wanan tashin hankalin wallahi kubar mutum yaji da abinda ya dameshi yafi.

Dole inyi jidali baban baby ace wai mairo tabar min kayana ta wanke nasu ta koma daki ita harta isa ta bar min kayana a nan ?

Kamar yaya ta wanke kayan uwarta tabar naki tace ai gasu zoka leka ka gani ga nasu can ta wanke ta kife tabar min nawa a nan cikin kwata kuda nabi.

Baba ya dan gusa ya dubi kayan yace ina kayan sana,an yaran nan ne nan ko ?

Ta amsa da udan sune fa ba zata wanke min ba kome don bangane tambayan da kake min ba a yanzu ke Rakiya wallahi kiji tsoron Allah ?

Kiji tsoein Allah kada alhakin mutanen nan ya kamaki dake da yayan ki kayan sana,an nasu za ace sai mairo ta wanke masu shi su suna me daba zasu fito su wanke abinsu ba ?

Ooh lalai yanzu naji magana in banji tsoron Allah ba da inji tsoronka kome ai dole kace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login