Showing 123001 words to 126000 words out of 395027 words

Chapter 42 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

ya danji faduwan gaban nasa ya lafa a lokacin cikin yan kwanakin uwargidansa na yawan shiga zaria duk da ya nuna baison hakan amma saita kawo uzuri ta gitta da zaisa dole ya barta taje don kauyensu na kusa da garin.

Koda safe kafin ya fita daga gida saida yayi fadan rashin dawowan mai dakin nashi don batace dashi zata kwana biyu ba sai gata har kwana biyu gana ukku take a ranan.

Wanda dalilin hakan kuma malamintane yace ta dan dakata ya hada mata wani magani da zatazo dashi suyi amfani dashi wanda zaisa komai ya sauya a gidan nasu saidai a gani a wajensu kuma.

Ta dauko maganin amma Allah bai yarda an shiga dashi ko garin ba kaddara da alhaki ya kamata haka ya sameta bayan ya fito kuma ya samu Bilya danta yana brush shima ya haushi da fadan rashin tashi da wuri da basuyi ya dora da tambayan ko sunyi waya da mahaifiyar nasu yace tace a ranan zata dawo ai .

Donshi tunda ta kara kwanaki ya daina daukan wayanta saboda rashin bin umurninsa da batayi ba yana jira ta dawo suyi tsiya da ita.

Tun abin safe da hakan ya faru sai wajajen karfe hudu da rabine wani bawan Allah daya kaisu asibitin ya samu kiran layin Alh bai shiga ba don tayi serving din sunan da maigida.

Ya koma na danta Habib data rubutawa magaji akai sa,a nashi ya shiga ya dauka yana fadin kin dawone mama ?

Wani murya yaji na tamiji yana fadin ba ita bace mai wayan na nan Allah yayi mata hatsarin mota suna asibiti wuri kaza kuzo ku duba in bata cikin wa yanda suka mutu.

Cikin karaji yake tambayan mutumin bai tsaya bashi amsa ba ya kashe wayan don jama,a dake dafifin zuwa ganin abinda ya faru.

Rasa me zaiyi a lokacin ya shiga gida yai tsaye haka Amira tashigo ta sameshi tana gaidashi ya amsa da ido ja yace Amira ina maman ku ?

Tana ciki ta lazumi ta basu amsa tana wucewa zuwa part dinsu har ta danyi nisa yake fadin fada mata an bugo waya yanzu wai hjy tayi hatsari akan hanyar dawowanta .

Innalillahi ya fito bakin yarinya karama kalman dashi babba a gareta ya kasa fada tun faruwan abin saiga karamar yarinya tana ambatan hakan ta juya zuwa part dinsu da sauri .

Mama mama ga yaya Habib a waje yace in fada maki su mama sunyi hatsari a hanya da sauri ta dago kai tana ambatan innalillahi ta mike tsaye ta sameshi ido yayi ja take tambaya ya rude a lokacin nan yake fada mata kiran da akai mata wanda ko mahaufinsu bai samu kira ba a lokacin.

Ta daka mai tsawa akan ya kira mahaifinsu ya sheda mai da wautanshi wai fushi yake har lokacin da mahaifin nasu yasa ya kasa kiranshi.

Nan a gabata ya kira har Bilya ya fada masu kafin su kwasa zuwa waje su jira zuwan maigidan dayace gashi tafe a lokacin.

Hankalin kowa ya gama tashi yana isowa suka dauki habib din suka nufi garin a cikin tashin hankali inda suka isa anyi magariba haka suka daukota zuwa kano ba dadi a lokacin.

Haka kuma yan uwan sauran mutane da suka samu labarin hatsarin suke ta zuwa daukan yan uwansu dake cikin wani hali wasu kuma Allah ya karbi rayuwankasu saidai muce Ubangiji Allah yajikan musulmi Allahuma Amin.

Kafin magariba duk labari yabi unguwa yan uwa da abokan arziki s da suke da alhakin sani sun samu wanan labarin mara dadi a ranan Allah ya tsare ya kare.

Inda A kasan zuciyar hjy hauwa sai tunanen mafalkinta takeyi na ranan inda da asuba bayan tayi sallah tana lazumi dan barci safe ya dauketa a wajen.

Nan tayi mafalki ana fadin tashi ki duka ga ubangijin ki ki roki Allah yayi maki tsari dake da iyalan ki ga masifa nan an tunkatonku dashi gidan nan.

Zubur ta mike a daidai lokacin Alh ya dawo daga sallah kallon yanayinta yayi ya fahinci ba dadi yake fadin yaya kuma tace wallahi wani mumunan mafalki nayi niko mafalkine ko kuma dai idona biyu oho ?

Nan ta bashi labatin abinda ta gani a mafalkin har yake mata sheri aike ba a fada sai anyi sadaka koma meye Allah ya tsare ya kare duk wani masifan da aka nufimu dashi.

Tun daga lokacin bata kwanta ba tana aikin abin karyawa amma mafalkin yaki fita ranta bayan tagama ta sallami kowa har maigidan ya fitane ta kira yayanta tana labarta mashi wanan mafalkin yace ta nemi almajirai ta basu sadakan abinci mai dadi a ranan.

Duk da tayi abinda yayan nata yace hakan bai mata ba saida ta tura Amira takai mata sadaka gidan wasu marayu tunda sauran safiya hankalinta ya dan kwanta.

Saiga wanan mumunan labarin dayazo masu na hjy din da hankalin kowa a yanzu yake tashe don bata san inda take ba har lokacin.

Gaba dayansu suna Asibitin a cikin daren sai Amira da Na,ima aka bari a gida suka gargame gidan don tsoro da gudun bata gari.

Likita ya duba hjy inda ya fada masu cewa ta samu kariya a kafa biyu duka kuma ta gwauce a kafadanta na dama ga sauran miki duk jikinta.

Kowa yasan ba kasafai ake buge kare ko agwagwa a wayen lafiya ba duk driver daya buge wa yan nan dabbobin yana da wuya ya take gaskiya hakama na tare dashi ko mutum bai mutu ba yana nakasa.

Haka buge kyanwa shima baida kyau ga mutum ko kayi sanadin mutuwansu sai wani bala,i ya samu mutum wanda sai hankalin na tare dashi ya tashi.

Nan dai dole bayan baiyan likita akace matan su rage su dawo gida Bilya ya dauki hjy hauwa har da yaran ita hjy Naito din mata daketa kuka don ganin halinda mahaifiyarsu take ciki.

Wasu tsofi biyu yan uwan mahaifinsu suka zauna da ita ana jiran tsamani don gaskiya yana da wuya ta tashi a yadda take din nan sai wani ikon Allah.

Sun dai dawo gidane amma sam hankalinsu baya tare dasu gidan da duhu sosai koda suka shigo saida suka kira Na,ima ta waya suka fito suka bude masu gida don lokacin karfe daya har ya gwauta na dare.

Alwala tayi ta zauna tana roko Allah haka suka kwana a cikin fargaba da tashin hankali kada suji mumunan labari daga asibiti.

Shi kanshi Alh ta maza kawai yakeyi amma ya katse da yadda yaga yanayi maidakin nasa wace bamu fita ga ubangiji mu ba ranan.

Dashi aka kwana wajen saida akai sallah asuba suka dan shiga zuwa lokacin numshinta ya fara dawowa normal nan hankali ya dan kwanta amma har lokacin bata san wanda ke saman kanta ba gaskiya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

YAURI KEBBI STATE

[8/11, 10:15 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,

4️⃣0️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15- HAWAYEN KADA🐊 1000.

_Account No._

_*ZAINAB IDRIS MAKAWA*_

2254380105

ZENETH BANK

PHONE NO.

08036959257

Yau da gobe a bangarena baibar komai ba don ido ya bude sosai a yanzu na zama cikakkan yar lagos duk wani iya shegen dan lagos nasanshi amma ban yarda hakan ya sauya min addinana ba.

Tarbiyana yana nan saidai idan ka ganni zakace duk mune yan lagos ladies da wayewane kawai zallah.

Wajen dana shammacesu shine shiga duk da yanzu ba wai kayan arewa na faye sakawa ba ban kuma yarda ina saka na shedana ba.

Sutura idan Ozil ya dawo daga wasanshi ko bussiness dinsu haka zai kwashe mu kaf din mu aje a sayo tufafi da kayan ciye ciye da sauran abubuwa na more rayuwa wanda har nakan hado da Amira.

Nayi mata shoping din kanta na koma wata rouged mara jin magana kallo daya zakai min ka fahinci ba damuwa cikin lamarina saidai natsuwana da kamala yana nan har lokacin ba inda ya gusa shi dadine idan kana ciki ko yayane saiya nuna kanshi.

Yakai zuwa lokacin ina zuwa saloon ina zuwa sauran guraren gyaran jiki amma fa duk hakan baisa na shagala da zancen iyayyena ba don a kullum muna waya dasu lokaci lokaci.

Suna kuma tunatar dani abindaya dace tambayansu kuma da fada shine in kama mutuncin kaina don Allah kowa yasan lagos bai bar tsoho ba balle ni yarinya ko yaya kaje saika cita indai lagos ce.

Don dole wasu dabi,u nakan a yanzu sun sauya sosai dan ya bambanta dana yan nan arewa sosai a yanzu.

Balleni dana koma ba kwabo saina Allah da iyayyena kome nayi don kaina duk da ina kokarin wajen yiwa kaina fada amma kallo daya zakai min ki gane tashin kabiluce ni.

Do ita kanta uwar dakin nawa kusan shiganta ke nan har garama ni nakan saka aribian gown da nake yawan sakawa a yanzu masu kyau masu tsada da tsone ido kusan sune shigana a garin.

Don a ganina shigan musulunci nakeyi ai saidai dan hijab dina iya wuya ko gyale ga takalman duk wani kaya da zan saka a jikin nawa.

Wana yasa nakewa Ozil addu,a a kullun Allah ya sauya mashi zuciya ya karbi shada don yaci riban taimako da jin kai irin yadda yake muna don bani kadaice yake daukan nauyi ba.

Kada kice ko Paapa baya zuwa lagos din a yanzu sam sam, yana zuwa bayan duk wata uku uku ko fiye da hakan kuma yana sako akai akai ga iyalinshi .

Saidai duk yawancin zuwan da yakeyi din gaskiya bai ganina kafin ya tashi na bar gida koda zan dawo kuma ya fita cikin gari lokacin.

Bai wuce wani lokaci mu hadu dashi da dare ba na dan fito in gaidashi a cikin kayan zaman gidana don haka ba wani fahintar sauyina zaiyi a lokacin ba.

Ina hakane kuma don nisanta kaina dashi don matarshi tayi tsakanina dashi don haka nake kare mutuncin kaina kada ta kulla min sheri duk da hakan ban tsira a wajenta ba.

Abinka da mai halin yare wani lokacin tana kai sukana wurinshi baidai, daukan hakane don bai gani ba bai kuma sheda ba haka kuma shima bai san cutan da take min ba a zaman mu din.

Sai wani zuwa da yayine ya fara fahintar hakan don ranan bansan abinda ya fito dashi da safe ba ya tsura dani a falo nayo sammakon fita irin yadda na saba.

Saida gabana ya fadi don girshi na ganshi zaune a falon duk da ina ciki shiga ta kamala don gujewa hakan idan yana gari ban faye saka kananan kaya masu matse jiki ba.

Jallabiyace kalar ja a jikina saidai sharp dinta yayi yawa na gayune sosai mai kuma tsada ga takalman kafana da jakka fara da dan hijab sai sheki sukeyi kallo daya zakiyi min ki fahinci kina tare da babban yarinya mai aji.

A dan tsoroce cikin firgici na dan rusunna ina fadin ina kwana Paapa lafiya kawai ya fada ya bini da kallon irin na mamaki ina kokarin shigewa in fice naji yace ke dakata .

Da sauri naja na tsaya cikin juyowa a hankali na dan tako zuwa bakin kujera na tsaya ina mai dukar da kaina kasa ina saurarenshi .

Kina wani matakine yanzu a karatunki na dago manyan idanuwana na sauke a kanshi kafin in sunkuyar da kaina ina fadin ina UG 3 na bashi amsa a takaice.

Ya dan kada kai yana fadin kin tabbatar da hakan na amsa da eeh Paapa zaka iya zuwa ka dubama na fada cikin murya kasa kasa.

Amma antyki tace dani kamar kin daina karatun yanzu kin soma shashanci tasha fada min hakan ban yarda ba sai yau din nan dana ganki haka idona ya tabbatar min dakin sauya a sanin da nayi maki a baya.

Da badon abin nan da kika lailaya a wuyanki ba sai ince kin soma fita kamar doki kina koyi da yayan arna ba sayi gareki kin fara bin rudin duniya da gaske.

Duk da nasan kina da tarbiya a baya amma yanzu da ban nan ba zan iya tabbatar da hakan ba gareki saina bincika nagano gaskiyan maganan kafin na zartar da hukuncin da nake son daukar akanki.

Na yarda ka bincika Paapa na fada kai tsaye ba tsoro ko shayin magana daya fito a bakin nawa gabanshi ba kamar yadda nakayi a baya ba.

Don a baya ban iya magana dashi haka garam da garam saina saya naga ya kada kai ya duka har zan wuce yake fadin ba a kara school fees bane har yanzu don banji kin fadawa antyki ba ta fada min ?

Tambayan ya ban mamaki don nasan dama a rina don ina zargin yana bayarwa bani kawaine batayi nace ankara haka nake hadawa inbiya tunda na fara biyan kudin da kaina.

Don sau daya aka biya min school fees ba,a kara biya min ba kuma tun lokacin da aka kaini school yanzu kuma sauran shekarun nan nke biya da kaina .

What ya fada cikin dan firgici da tashin hankali nayi shiru yace maimaita abinda kikace ba tsoro nace nike biyawa kaina school fees tun lokacin da sauran abubuwan rayuwana.

Innalillahi ya fara ambata daga bakinshi jeki zan nemeku anjima idan kin dawo ya fada a dan rude har yana hada takardun da yake aiki akai.

Najuya zan tafi a daidai lokacin na juyo naji Amira na kirana kanta na juyo na shafa na fice daga gidan tunda ta fito nasan uwartama zata fito a lokacin.

Cikkin hausanta mai muryan yare ta karaso falon tana fadin Paapa na dauka ka fitane ai da naji ka fito tun asuba da kyat ya iya budan bakinsa yace ban fita ba nan nake zaune ina aiki .

Daga haka yai shiru yacigaba da abinda yakeyi Amira ta nufi kitchen inda nake aje mata a binci ta dauko dan kulan abincinta ta fito zuwa falon tana kiciniyar budan kulan.

Uwar na fadin wait woo let me see what she cook for you today abi na Indomei or what doyane da kwai dana sulala mata ita kadai sani kaina na zuba zan tafi dashi inci.

Ganin ban soyayya ba yasa uwar fadin wanan yarinyar meke damuntane don kutumar ubanta doyan ma ba zata tsaya ta soya ba saita dafa haka da kwai ?

What wai meye matsalanki da yarinyar nan haka ina kula duk nazo kamar ba irin zaman dana barku a ciki kukeyi ba yanzu ?

Wani iri kuwa dama jira nakeyi ka dawo in fada maka ba zan iya zama da Maryam ba yanzu don tafi karfina idonta ya bude da yawa ta fada harkan bariki tana ganin tafi karfin mutane a yanzu.

Don kada in koreta daga gidan ba tare da sanin kaba yasa nayi hakkuri na bari har ka dawo garin nan inyaso asata mota amaida ita gida.

Karatun ta daina ke nan yanzu ko ya dago yana tambayanta don son jin amsa daga bakinta.

Waya sani tunda ba binta nake mu fita ba, ko tanayi ko batayi wanan matsalantane nayi regret din zama da yarinyar har na sakata karatu.

Kecema kika sakata ke nan wani kallo tayi mai tana fadin ko bani bace ainice na bada shawaran a sakata ko ?

Kina biyan kudin school dana transport da nake turo mata ki tabbatar da kina bayarwa dai ko ina son in samu evedece ne a kai koda yake ki bari sai ta dawo zamuyi maganan ai.

Nan ta soma yan kame kame tana fada dama an fada min karshenta hakane zai faru dani ai gashi kuwa saida mummy ta gargadeni da in mayar da yarinyar nan don irin haka naki ina gani basu sontane kawai ashe sunsan abinda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login