Showing 132001 words to 135000 words out of 395027 words

Chapter 45 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

Yake fadin ya gane komai zaisan yadda ya bullowa zancen shike Okenah cewa yayi we thank god ba cewa yayi zai daukeki zuwa a rewa ba.

Arewa din ba Nageria bane koya dauketa zamu daukota mu dawo da ita ta karasa karatunta nidai jinsu kawai nakeyi don nasan basu san irin tarbiyan da akeyi a arewa ba yasa suke fadin shirmensu.

Tun wanan ranan kuma antyna ta dauki fushi sosai dani a gidan har tayi kokarin hanani hurda da yarta hakan bai samu ba dole tabarmu.

Nima na koma ban kula lamarinta saidai ban daina yi mata girki ba kodon yarta don nasan ba iyawa zatayi ba idan ma banyi ba.

Mai karatu zakiji zancen kamar shirme ko labari kawai wanda iya gaskiyan kenan idan kinyi la,akari da rayuwa irin na kabilu abinda nake fada ba karya a cikinsa Allah ma ya gyara nazo da wayau na har lokacin ina bisa tarbiyan da iyayyena suka dorani tun a gida nasan aibu shagala da duniya idan ba haka ba da ba karamin kalubali zan tsunci kaina a cikinshi ba a zaman can din.

A takaice zama mukayi na kusan wata biyu a hakan bansan meta gani ba a lokacin ta sauko don kanta ta dan rage fushin da takeyi dani din sosai tana danyi min magana jefi jefi can ba a rasa ba dama matsalan ai daga garetane ya fito.

Da gaskiyane da akace mai hakkuri yana dafa dutse na yarda da hakan don ba karya bane zancen sai kayi hakkuri da lamarin duniya kake kaiga manufa a rayuwa.

Zancen gidan mu dai mama tayi haukanta ta gaji ta bar zancen a yanzu kowa ya koma harkan gabanshi na rayuwa.

Shi kishine tunda ana tare ba fasawa za ayi ba sai wani ikon Allah kuma duk da ana taushe zuciya amma har yanzu ana taba fada na fili dana boye.

Don yanzu abin yayi nisa kuma saboda abinda ya faru mama ta dauki karan zukau tasawa inna da yaranta badama yaro yayi abu yanzune zata shiga rigab arzikin yaro da zagi da cin mutunci a bakinta.

A cikin irin hakane wata rana ta fita zuwa makwabta ta dawo da zancen haihuwan salma ta zauna na tsakar gida tana fadin.

Kai wasu dai basu san takaici ba waifa yarinyar nan salma itace ta haihu ashe tunda tayi ciki yaron nan ya kaurace mata ya daina dan kulatanta da yakeyi.

Koda yake ance ba banza ba tunda ance asiri akai masu koda anyi auren kada su zauna lafiya gashi har ankai ga samun rabo amma ba zaman lafiya har yanzu.

Don ace tantirin yarone neman mata yayi mashi yawa gashi fasiki duk yarinyar daya zauna da ita saiya lalatata kwadansa ke fadawa.

Wasu dai inma yana haka yanzu ya fara bayan rabuwanshi da yayan mu kuma sai a nemi wanda yai mai asiri ai ?

Waya saura zancen wani Bello yanzu, bellon da ko zuwan nan da yayan mu tayi saida ya dinga binta, yayi tabinta yana bata hakkuri, amma bata taba tsayawa ta kulashi ba har ta tafi me za ayi da wani bello can kuma yanzu.

To yar iya dake nake zance na koda uwarki ke Saudat ina kallon take taken ki a gidan nan kinfi kowa danyen kai a dakinku.

Toni bari kiji maganin ki zanyi yarinya don ko yarki datayi min iya shege na san inda na sayata balle ke karamar alhakin nan.

Maganina akan na fadi gaskiya to ta Allah bataki ba mama ta fada cikin gunguni ta juya zuwa daki tashige nan ko mama din ta hau bakinta tana hadawa da innan mu da tun farkon zancen bata tsoma bakinta ba.

Daki ta shiga ta fito wanda mama din ta dauka halin hakkurintane yasa ta kaucewa zarin nata da dama tana so amayeshi tun safe akan mama do kawai ganin da tayi da baba zai fita waje sana,anshi da safe yabawa yan kannena kudin a hannunsu shike nan hakan wai ya batawa mama din rai ashe.

Saiji mama tayi na fadin yau dai Rakiya ki fito a debe raini a gidan nan tsakanina dake a san yaro asan babba nagaji da wanan halin naki wallahi.

Mamaki Ai ni kike cewa Rakiya haka gatsau a gaban yayanki da kowa inna ta amsa da cewa ba sunanki bane Rakiyan ko an canza maki sunane banda Rakiya bamu sani ba ?

Eeh Ai yau kin fito min a Ai,in kina baya watau lalai aikiko ya taso min a gabana babba kuwa don zama bai ganki ba tunda baki da aiki sai mugun nufi ga kowa baki bar na gida ba balle na daji ke.

Anyi sa,a a ranan inna tayiwa mama kwal wanda ba mama ba kowa dake gidan saida yaji tsoron yadda inna ta rikidewa mama din tana fadin ta tanka a wajen ranan su debe raini da mama ita abin ya isheta ta gaji da halin mama.

Kullum ba,a fadin alheri gareta balle yaranta ko mama tana ganin bata iya daukarwa kansu incine wai bafa tsoro bane kkawai dai halarcine kawai take mata .

Saiga mama ta koma shiru ta kasa furta komai don yadda taga inna din ta taso mata dole saudatu ta koma jan innan mu zuwa dakinta don ta kyale mama don suna ganin wai iska inna ta hau a lokacin.

Data gane haka ta soma fadin ke saudatu sakeni banda iskan komai yau so nake a debe raini tsakanina da wanan matar ta gane ba tsoronta nake ji ba dama.

Kin shiga kin fita kinyi sanadin raba yarinyar nan da yaron nan bamuce komai ba mun barki da Allah dake da abokan sherin naki kome ya faru da Salman hjy Tani a yanzu wanan matsalan kune ai kedasu mu nan bai shafe mu ba.

Amma zaki dawo kina kokarin kulawa yarinyar da bata nan sheri kuma me yar mama tayi makine wai a rayuwanki don Allah ?

Duk da yarinyar nan tayi nisa damu a yanzu baki barta ta zauna lafiya ba a rayuwanta saida kika san yadda kikayi kika bita da munafuncin da kika saba a can din.

To ya isa haka Allah ya baki ya bani naki dana sama da farko basu taba tsone min ido ba sai nawa da haifa bayan naki zaki tasa min su a gaba da sheri irin naki ?

Mama dai tunda aka iza ta taje lungunta bata leko ba bata kuma bada amsa ba don tasan da gaske inna keyi ranan zata iya hada kafada da ita kamar yadda ta fada.

Don har dogon wando baki taga inna ta saka ashe tayi shirin kokuwa da ita ke nan da gaske itako tasan ba zata iya irin haka ba a yanzu.

Wanan abin da inna tayi saudatu tace shine suka samu lafiya a gidan yanzu suna fita suna walawa kamar kowa saidai ba ruwan wani da wani a cikinsu.

Ke mai karatu da zaki auna kishin mata saiki gane gidan tallaka anfi gidan mai kudi zafin kishi sosai don su ko yaushe a cikin kishi da jin haushi suke fiye da gidan mai hali a yanzu.

Koda Baba ya dawo ya samu labarin abinda ya faru ya fito tsakar gida shima yayi masu tas ita mama ya soma yiwa fada akan mugun halinta saidai ya bita amma ba yayanshi ba.

Ace mace mai irin shekaru kamar naki Rakiya har yanzu bata bar yan uwanta da kalamin bamza sai yaushe hankali zaizo maki ki daina ?

Ke kuma Ai kiji da kyau gidana ba gidan dambe bane ki barni inji da abinda ke gabana kada ku dada min wani nauyin a kai kuma yanzu ?

Malam nagaji ne da halin yaya nagaji da sheri kullum gara ayita a kare a debe wanan rainin zaifi ta dauka tsoronta nakeji ko me ita ta sani ban tsoronta girmata kawai nake bata amma bata ganin hakan ita ta zata ina shakkuntane ko tsoronta yasa a kullum take kokarin takani gidan nan.

Wanan fitinan yasa aka danji dama sosai a yanzu amma dai still ba zaman lafiya irin kazo ka samu komai anayi a tare akai zuciya nesa a taushe kishi a zuciya a boye ana mu,amula da juna irin a baiyane din nan kamar ba komai a kasa sam namu gidan bai samu hakan ba gaskiya.

Don a fili iyayyen mu ke nuna kishinsu karara duk wanda ya shigo saiya fahinta duk da kokarun damu yayan mukeyiwa junan mu muna girmama manya suma kuma suna tausa muna a matsayin kannensu tundai yaya Sahura ko abu ta sayo tun kan ta shiga part dinsu dashi zata kira yan uwana ta basu.

Don inya kai lungun mama yana da wuya abin ya shiga hannun yaran saidai a barshi ya lalace ko a zubar wani lokaci.

Izza da miskilaci daya zama hali a gareshi bai bari yayi dogon mu,amula da kowa sosai amma duk da hakan bai rasa abokan hurda a tare dashi ba wanan halin kuma duk wanda ya sanshi dashi ya sanshi hakan yake kuma mu,amulanshi dasu.

A yanzu ma tunda suka kamo hanya da yusuf dake driving sai shi yusuf dinne ke magana kala bai ce dashi ba amma yasan yana jinshi miskilancine kawai irin nashi don zancen bai mai bane daya bashi amsa ko sau dayane a lokacin.

Yusuf ya fada bayan tsawon lokacin da suka dauka dashi a motan shiru hakan yasa yusuf din amsawa da sauri tare da dan juyowa ya dubeshi.

Zaka iya tuna yaran daka watsawa ruwa ranan a unguwanku daidai kwatan nan da aka gyara a wajen muka samesu su biyu a ranan har,,,,,,

Yarinyar data hau mu da fada ko wace tayi sanadin samun kwalbatin a wajen aiba zan manta da ita ba ya akayine mu nemotane ko yaya ?

Ina zaka ganta balle ka nemota ranan na basu lift ita da yar uwarta sai gata kuma lagos na ganta dama before that mun hadu a lagos kuma saina ganta a garin nan kuma ?

Kafin nazo din nan still na ganta a ranan da zan taso zuwa garin nan da farko nayi zaton itace amma kuma sai banga ta nuna alamun itace din ba a fuskanta.

Cabdi amma ko idan ba ita bace ana kama kuwa a duniya i daut idan mutum dayace ya kara fada yana sauke numfashi.

Amma dai zan zuba ido in gani idan itace din saika tayani duba garin nan ko zaka sake ganinta zanyi trying na gwada wacan ta lagos din ko bahausace .

Yusuf ya karbe da fadin amma kuma fa har yau ni ban kara ganin yaran a unguwar nan ba ko daya daga cikinsu ban sake gani ba garin nan.

Ka daiyi yadda nace dakai din ya fada a gadarance yana gyara zamanshi ya kurawa titi ido lokaci guda yana nazari a kasan zuciyarshi.

Irin shigar da yaga yarinyar dashi ya bambamta da wace ya gani a nan kano duk da yasan komai yana iya faruwa akan hakan.

Amma ta yaya akayi har in itace take zuwa kano ko lagos din wani alakace tsakaninta da garuruwan nan biyu ?

Zuciyarshi yafi bashi cewa ba mutum daya bace kamane kawai dai daya amma ba yadda za ayi yarinyar daya gani a nan kano da hijjab har kasa yanzu kuma zai ganta a lagos da wani kama ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/17, 10:01 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/17, 9:50 Yamma] Seenabu Makawa: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com,SABON BUDURCI 🔥🔥🔥🔥 TAKEN TA KENAN WNN HADIN BABU SAUQI INA UWARGIDA DA AMARYA KU FITO INA MASU FAMA DA WULAQANCIN DA NAMIJI KUZO GA MAGANIN MATSALAR KU DA IKON ALLAH 🥰 YAR'SOKOTO TAZO MUKU DA KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KI SIYA KI DAWO KINA SAMIN ALBARKA MUNA MAGANIN SANYI KOWWANE IRI DA IZININ ALLAH AKWAI SET NA AMARE DA MASU JEGO AKWAI MALLAKA KALA KALA KUDAI KU GARZAYO KAWAI KAR A BAKU LABARI NGD 08069642829 INA SOKOTO INA AIKAWA KOWWANE GARI CIKIN AMINCHI DA YRDR ALLAH 🤝🤝🤝🤝🤝

[8/17, 9:52 Yamma] Seenabu Makawa: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

4️⃣3️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15- HAWAYEN KADA🐊 1000.

_Account No._

_*ZAINAB IDRIS MAKAWA*_

2254380105

ZENETH BANK

PHONE NO.

08036959257

Sanadin zuwan Paapa school din mu sai ince ya zama min alheri don kuwa a yanzu na samu shiga cikin egency din company su Ozil.

Duk da ba wani aiki mai wuya bane kuma a sati ranaku biyu zuwa ukku kacal zamuyi muna kewaya masaya kayansu da new product da aka shigo dashi.

Wanda hakan bai taba min karatuna ba ko kadan amma manyan kudi nake jin saukansu ga alherin da aikin kedashi da muke samu wani lokaci.

Sai a lokacin na fahinci shi Ozil dai karatun kawai yakeyi ya samu kwalin amma da badon haka ba sai ince ba abinda zaiyiwa karatu shi don mahaifisa ya tara masu.

Gasu da akidarsu ta arna don su biyune rak a wajen iyayyensu dashi da kanwarshi nidai sai ince Allah ne ya jefani rayuwansa don inci daga garesu .

An kai a yanzu da abubuwa sukai yawa dole yafibawa kasuwancinsu muhinmanci sosai sai karatunshi ya koma karshin kulawan mu son an samu hadin bakin hakan daga makarantar yana dai shigowa amma wasu abubuwa nice mai tsayawa inyi mai sai hakan yasa share dina ya banbanta dana yan uwana.

Bai sakani cikin bussiness dinsu ba saida ya kira Paapa daga can ya sanar dashi komai kamar yadda nina zauna na tsara abin nake kuma son abin ya kasance min.

Alhamdullahi ance dare daya Allah kanyi bature shi dama tafiya alherine ga bawa don sai ince na shigo lagos da kafan dama nikan .

Zamana yar musulma kuma bahausa wace bata zubar da akidunta ba sai hakan yaja min farin jini don daga zolaya suna kirana Hijjan Girl saiga shi nayi farin jini saboda basirana na samu daukaka da suna wanda zance ubangiji Allah ne ya tsaro min hakan a rayuwata.

Don sosai nake jawo masu customers masu son daukan kayansu a duk inda muke zuwa yi masu talla yadda nake tsayawa in fahintar da dealer muhinmamcin kayan koshi ya isa mutum ya saya ya gwada sa,an shi akai.

Taura biyu a baki daya na hada lokaci guda ga karatu ga kasuwancina haka kuma nake kokarkatawa da ko wani don kariyan kai.

Sosai nake jin dadin hakan don yadda kudi suke shigo min ko yaushe sai na zama kamar nice idon arewa a company nasu karama dani amma hanya yasa na iya babban kasuwanci.

Tun inayi ba daidai ba insha fada daga na gabana har nazo na iya nima na koma abin kwatance a cikinsu saboda jajircewana.

Ruwa ake ta shekewa tun safe irin ruwan nan da sai ya tafi ya dawo gari ba rana kin dai san irin ruwan lagos hakan bai sa a fasa komai lokacin ma wasu ke jin dadin cuwa,cuwa da har kokinsu.

Ganin yamma tayi don duk abinda nakeyi karyane in bari yamma tayi min a waje tsananin dadewana karfe shidda har in nayi yamma a ranan.

Bani tare da kowa a cikin mu ni kadaine na fito wajen ciwaciwana a lokacin don karfe biyuma na bar school akwai wasu zabarmawa da muke son hada har,kallah dasu na bussiness gunsu na tafi ba ko tsoro gani ya mace ni takamana shine su din kamar yan arewa suke ai a wajena duk da wanda ya san bahaushe su sun dan banbanta damu kota wajen shiga balle magana.

Amma sai ganin su din ai musulmaine kuma aboki sai aka bar mjn dealing dasu don mutanen mune ai su din ga kaso mai tsoka da jawosu zai kawo min an kwadaita min hakan yasa na mayar da hankali gun har,kallah nasu.

Tun zuwana bayan azahar ban samu ganin shi Alh ba don abubuwa da sukai yawa ance yana ganawa da wasu bakinshi a ciki lokacin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login