Showing 33001 words to 36000 words out of 395027 words
Chapter 12 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
maza yace ya hana gaba dayansu wani hurda da gidan nasu salma.
Hakan ya damu mama sosai don me inna zata jawo masu kashedin rashin shiga gidan su salma bayan ansan yadda suke da hjy duk da bata bari ba taji zafin hakan sosai a ranta .
Ita kuma anty Fati tayi aikowan duniya akan nazo sai inki zuwa don Allah ya gani ba zan juri shiga gidan haka yadda take so na dinga yi ba.
Sai can ba a rasa ba nake dan lekawa na dubata ba zan dade ba kuma nake fitowa har lokacin kuma bamu ga maciji da yan gidan nasu.
Ga fitina a kullum don anty Fati bata yarda da mulkin da hjy Tani ke son nuna mata ba a gidan hakan kesa ana jinsu ko yaushe suna fitina su tarar mata ita da yaranta.
Sau daya na taba ganin mammam bello tun bayan rabuwan mu dashi wata rana da yamma zan tafi kasuwa in sayowa innan mu kayan sana,anta ina tsaye bakin titi sai gashi cikin motar gidansu shida abokin shi.
Har ya wuce ya gane nice ya dawo baya da mota har inda nake tsaye suka tsaya kaina kawar naji yana fadin yan mata ba gaisuwane kin wani dauke kai haka ?
Nunawa nayi ban sanda mutane wajen ba nayiwa mai Nape hannu ya tsaya na shiga na bar wajen tun wanan lokacin ban sake ganinshi ba kuma ko inji daga gareshi don shima salis nayi mai kashedin kawo min zancenshi kamar yadda innan mu ta kwabeni dayi.
Na dawo makaranta muka hade da mama ta fito cikin shiri zata unguwa nayi mata a dawo lafiya ta fita na shige gida.
Wanan fitan na mama da muka hade shiya jawo dalilai da yawa a rayuwata mai kyau da mara kyau don kuwa ya jawo min sanadin rabani rayuwa a tsakanin iyayyena haka kuma ya zamo sanadin komai gareni.
Don kuwa mama gidan kakannin mu taje wanda ita dai nan ne asalin nasu gidan da iyayyenta ke nan saida ta gama da bangaresu ta nufi na kakan mu din data samu kakan namu da yan uwanta sunzo aka tsaya aka gaisa dasu.
Tana zaune sukaci gaba da maganansu nan ta fahinci zancen da akeyi wanda dan matarne dake magana suke son a samawa matarshi yarinya da zata zauna da matarshi dake da ciki a can lagos.
Take shedan ya zuga mama a wajen ta tsoma baki da cewa kakan mu ga Mairo nan ai zatayi daidai umma nasan kuma malam ba zai hana ba ai.
Kinji ki da wani magana kuma wata mairo can ni ban faye son tabawa Ai diyanta ba kin san halinsu kuma yar nan itace yar babba a yanzu a gaban uwarta a dauke mata ita kuma ?
To meye mama tunda ba talla takeyi ko wani abu ba ai zata iya nake gani tayi hakan ne kuma don kawai ta kuntatawa uwata a lokacin.
Keme zai hana ki bada guda a cikin yayan ki Rakiya kakan namu ta fada cikin bacin rai sai yayan nata tace yar madaidaiciya dai haka ai ake so ba wace ta girma sosai ba.
Nima shina gani ai umma, mairo din dai zatayi daidai da zuwa ko banza iyayyenta sun huta ai ga zancen aurenta ya lalace a yanzu ba wani kuma tsayayye a yanzu.
Yar har takai munzalin aurene ba karama bace ke tunda har ana zancen aure gareta kawai dai rigimace fa dududu batafi sha hudu zuwa biyar ba yanzu ai mama ta fada tana kallonsu.
A,a karamace kan daidai haka shima yace yana so ai wace zata dai iya kama masu komai a can din zata iya kwarai ma ga uwarta ta koya mata komai tun yanzu ta fada don gyaran zancen.
Mama bata bar wajen ba saida ta tabbatar da zancen ya zauno a kaina lalai zasu daukeni har sun tafi ambar zancen akan kakanmu zatayiwa baban mu magana suka tafi sanan itama tabar gidan cikin farin ciki.
Koda ta dawo gida bata nunawa kowa komai ba ta share zancen a ranta cewa ai wanan abin sai ya taba innan mu sai taga yanzu yadda innan mu zatayi a gidan.
Dama nice karfin komai da innan mu takeyi to yanzu taga ta tsiya tunda ban gidan dole inna ta koma rugume hannu don ko sana,an ba iyawa zatayi ba dama nice karfin aikin inna din ga komai.
Tun ma yanzu da innan mu keda ciki din nan a jikinta daba komai take iyawa ba nice dai a tsaye haka kuma bokon dana kwallafawa rai yazo karshe yadda diyanta basuyi boko ba nima haka ba zanyi ba duk a taru a lalace din taga kuma gorin da baba zai sakeyiwa yayanta din a kaina.
Don mama tana da riko da naci irin mutanen nan ne da suke rike zance tun ranan da yaya saudi ta kawo waya tace in nema mata wani layi na nema mata tace kuma in karanta mata sako na karanta baban mu yana zaune ya kama fada yana fadin.
Ai,shiyasa ake cewa kuyi karatun kunki kun biyewa uwarku kuna zaman lalaci wai talla ita dai a kawo mata kudi bata damu da makomar rayuwanku ba nan gaba.
Shine har zancen ya kawo masu fada a tsakaninsu da baba din sukai kaca kaca dashi bayan kuma kwana biyu saita fahinci cikin dake jikin inna nan kuma kishin inna din ya karu a zuciyarta shiyasa da zancen nan yazo tayi saurin bada shawaran a daukeni don kuntatawa a gare mu.
Ga fitinan da duk kwanakin sukeyi sai sakin magana take ga inna wanda yasa kowa ya fahinci cikin dake jikin inna din a lokacin.
Dama ace gidan da babu anfi kishi wanan zance ba karya bane don kuwa haka dinne don na gani a gidan mu yadda mutanen dake fama da kansu suke fada kuma akan samun ciki yanzu.
Zancen ba a tashi fadawa mahaifin mu ba saida akayi kamar wajen wata daya zance ya taso don mutumin da zai daukeni din zaizo gida daga nan ne kuma zasu tafi dani lagos din kamar yadda mama ta tsara min tana son kuma ganina a cikin wahalan haka .
Tunda tasan aikin bauta zan tafi yi karshema in lalace a can tunda lagos kowa yasan banda tambada babu abinda ake aikatawa a kasan yasa take faman sake sake da kullawa a zuciyarta har take sakin magana a kaina kan hakan.
Takance a haka za a kare wajen boyi boyi dama shine daidai damu ai don shi aka gada a lokacin ba a san dalilin fadin hakan ba akanta.
Sai da baba taje gidan kaka shine bayan sun gaisa ta soma magana tana fadin zancen tafiyan yarinyar nan mairone ya taso.
Mairo ina kuma zata ya tambaya cikin mamaki itama kaka din tace dashi duk dadewan nan ita Rakiya batayima bayanin komai bane ?
Batayi min ba ina mairo din zata ya koma tambaya take fadin a,a amma Rakiya taban mamaki don anyi maganan nan da ita a gidan nan.
Itacema taba da shawaran cewa ga mairo nan a dauke ta ai donni banso basu kowa ba a nawa bangaren don sai wajen wahala Dije tasan dani da zuri,ata .
komaqn shi naso kwabe zancen amma yar bakin nan Rakiya na kusa ta tsoma baki tana fadin wai aiga mairo nan zata dace da zuwa din.
Kaji yadda akayi tafiyan ya fada akan mairon ku din nina dauka cewa ita Rakiya tayima bayanin komai tun lokacin yasa ai ban maka ba .
Ta yaya zatayi min bayani bayan tasan sherin data kulla a nan in har gaskiyane ta dauki cikin yayanta ta bayar mana aje dasu ?
Da zata dauki yar kishiyarta ta mika da sunan zuwa wata kasa yin boyi boyi a can amma ba matsala zata dawo nan umma ta bayar a cikin yayan dakinta.
Kai kuwa don me zakace hakan bayan har kwatancen shekarun ita mairo din anyi masu kasan halin Rakiya da bakin tsiya ba abinda bata fada masu akan mairo ba sukace tayi.
To aishine nace yanzu saita sauya ta bayar a dakinta donni dai ba makwadaici bane kuma banyi lalacewan da har zan dauki yata in tura yin aikatau ba a gidan mutanen.
To ai yanzu dai so kakeyi ka nuna min ban isa ba kenan ko don dakin ita Ai ne yasa kake son watsa min kasa a ido ka bata min zumuci dani da yar uwata ?
Idan uwartace kake tsoro baka iya fada mata nika bari zan fada mata duk abinda ake ciki inji in zatace ba zata bayar ba ?
Umma uwarta kan aiba zata uffan ba kema kin sani koda hakan bai mata dadi ba kuwa nidaine kawai ban yarda da hakan ba tunda yarinyar nan a yanzu itace ke kamawa uwarta komai a gidan nan.
Eeh lalai kuwa Ibrahim kakai yau nice kake nunawa ban isa da yarka ba ko to jeka ba komai jeka rike yar taka tunda har ka isa kaja dani a gidan nan.
A,a umma niba haka nake nufi ba a dai duba aga dacewa don Allah yarinyar nan karatu takeyi umma sai a dakatar mata da burin rayuwanta wahalan data sha ya tafi a banza.
Ai nace kaje ko ibrahim yanzun maiya saura kuma tunda har ka iya duban idona kace bab isa ba aina dauka ko ban raye yaya tazo da bukatan haka a gareku ku masu dubawane kuyi mata ?
Shiru baba yayi don kome zai fada umma din ba zata saurara mashi ba a lokacin hakan yasa yaja bakinshi yai shiru bai kara magana ba.
Ganin umma din ta fita daga dakin tabar mashi dakin yasa shi mikewa a cikin sanyin gwiwa don barin gidan .
Sallama ma da yake mata a ciki ta karba ya fice daga gidan kafa kawai yake kadawa baisan inda yake sakawa ba har Allah ya kawoshi gida lafiya.
Tun a tsakar gida ya soma ihu kiran sunan mama a cikin murya mai nuna bacin rai tana barci ta dan samu hutu ta taso tana amsawa .
Rakiya tsakanina dake Allah ya isar min wallahi Rakiya me nayi maki kike son ganin bayana dana yayana a duniyan nan ?
Me mutanen nan sukai maki a rayuwanki me suka tare maki a cikin rayuwankine wai yau ace wai har kin dauki diyata kin bayar da ita ga aiki ban sani ba Rakiya.
Wace diyar taka wai nikazo ka hauni da fadan da bansan dalilinsa ba ya watsa mata wani kallo yana fadin inako zaki sani ke maigida da iyalinsa aiko ba zaki sani ba ai ?
Ban taba zato ko tsamanin kiyayyar ki ga Ai har yakai irin haka ba ai wai har ki dauki yarta ki mika gidan hjy gwamaja da sunan zuwa da sunan zuwa wata uwar duniya da ita.
Au zance yazo gareka ke nan aina dauka duk dadewan nan da akayi kana da labarin komai sai kuma akace da kai nina bayar da ita can din ko ?
Ke rufa min baki mara mutunci kawai mara imani wace bata da hankali idan gaskiyane aida ki dauka a dakinki ki bayar ko hakan kadai zakiyi a san kinyi don Allah.
Ranan fada sosai akayi tsakanin baba da mama Allah dai ya gyara ba a kai ga saki ba saidai baba yace matukar umma ta dauki zafi dashi itama a bakin aurenta shiya gaji ya gaji wallahi.
Itako mama din sai fadi take tana kari ni aina dauka taimakonka nayi aida nabada mairo din dama ai aikatau ya dace da ita tunda uwarta ta koya mata aikin wahala.
Yaya in kiyi min hakane da wata manufa na roki Allah sarkin da ar sarki yasa tafiyan yarinyar nan ya zama muna alheri damu da ita baki daya dukkan mu.
Na roki ubangiji Allah yasa tafiyan nan naki mamu alherine ta kara fada tana kokarin juyawa zuwa dakinta don cikin jikinta da bai bata lafiya yanzu.
Wani irin dariya mama ta kwashe dashi tana fadin wai daga baya ke nan kuma bayan anga ba mafita aikatau daine sai anjeshi ko ba aso abinda akewa fatan auren mai dan manda manda yanzu za a kare kuma ga aikatau cafdi jam ina ruwan uwar yarga aikin gidan masu hali.
Baba kan ya kafe akan ba zaibada yarshi ga aiki ba don duk lakacewanshi kwadayinsa bai kai can ba don haka shi sam ba zan tafi ko ina ba.
Nasan daya fadawa inna yadda sukayine ta bashi hakkuri akan ya kwantar da hankalinsa yabi umurnin mahaifiyarshi Allah yasa hakan ya zamo min alheri.
Saidai daga inna harni a ranan duk bamuyi barci ba a dakin mu nayi kuka har nagaji kafin safe idona duk sun kumbura suyu sumtum ba dadin gani. .
Tun dai da inna tace itama bata san mutanen da akace din zasu daukeni ba ai haka kuma gashi wuri mai nisa za a tafi dani ba nan kusa ba.
Duk kukan da innan mu tayi haka baisa ta yarda mama taga bacin ranta a fili ba itako mama kamar wace akaiwa albishir da gidan aljanna sai wani busha,sha da sukeyi ita da yaranta suna kwasan dariya a daki .
Wanda munsan damu suke dariyan a lokacin har wani lokaci su fito fili suce ina ruwan yan ga aiki kila asamu mai gadin gidan a hadani aure dashi mucigaba da aikin mu na aikatau din.
A cikin hakane dai sati na gusowa ranaku na kokarin juyewa zuwa sati har kuma lokacin baba baicewa mahaifiyarshi komai ba akan tafiyan .
Haka yasa umma din ta sake neman baba don ko yar uwarta ta kara jaddada mata cewa yarinyar ta zauna a cikin shiri mai daukana yana nan tafe.
Hakan yaso ya dagawa baba hankali tunda ya fahinci cewa mahaifiyarshi bata daina maganan ba ashe ga laifin data dauka ta dagwarawa innan mu tana ta zaginta da cewa.
Dama dan tallaka bai iya samun waje ba ai ace wai kamar Aice dake fama da talauci wai ta samu wirin fadin yarta ba zataje yin aikatau ba ?
Wakuma ya fadi hakan kuma yanzu umma Ai da tace Allah yasa hakan shine alheri inbar maganan tunda daga gareki ya fito ita ba zatace komai ba ?
To haka Rakiya tazo ta fada a nan tace ba irin cin mutuncin da Ai batayi min ba tace sai Allah ya isar mata baba yayi salati ya sanarwa ubangiji yace lalai mama in batayi hankali ba tun a duniya bata ganin Annabi.
Ya kwashe komai ya fadawa umma din tace lalai Rakiya takai mishon battada musulmi dama saida Amina tace min bata yarda Ai zatayi haka ba a gidan nan .
Koma meye aita gama magana tunda tayiwa yarta fatan alheri nima tafiyan ba nasoshi bane ai amma kuma yaya zanyi yanzu tunda na riga nayi alkawari kan saba saban bakin Rakiya din .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/1, 9:44 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
1οΈβ£2οΈβ£
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,
π€³AUNTY ZEE MOM MUJJAHID KATSINA 08262859027π€³
π*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA*
*Maganin sanyi 5k*
π*Maganin sanyi*
*5k*
π*Maganin ciwon Qoda 10k*
π*Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k
*MAGANINπ MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*
π*INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU*
*Maganin gyaran Nono π8k*
π*MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE*
π*Maganin Rage Tumbi 7k*
π*MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE*
*Maganin Basur 5k*
*MAGANIN CIWON SUGARπ CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI*
*Maganin ciwon Sugar 10k*
*08162859027*
*09070027627*
*Location*KATSINA STATE*
*ACCOUNT NUMBER*
*8162859027*
*ZAINAB SHU AIBU*
*OPAY*
*OR*
*3968303018*
*FCMB*
*ZAINAB SHU AIBU*
π*DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA