Showing 321001 words to 324000 words out of 395027 words
Chapter 108 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
abinda kike fadi kuwa ko kinyo shaye shayen nakine dakika saba kada kizo ki haukatani wajen nan don Allah ?
Ni malam jibo fa mai rawani fari na gangare da ake tururuwa akansa nake maki zance ba shirme ba don ya tabbatar min da mairo bata taba aure a duniya ga bakin jini da zai saka mata ?
Wallahi duk karya yake maki mama baisan komai ba dan iska cutan mutane kawai yakeyi murja kisan me kike fadi ki dawo hankalinki don Allah ?
A to mama zan maki karyane shi din fa dai wallahi kibar wanan wahalan bin malamai din da kikeyi duk makaryatane ba gaskiya suke fada ba .
Su debo abin juji suba mutum da sunan magani mutum yazo yai ta wahala yana shan kazanta ni ba mairo ba ko uwale da take karamansu zata kawo miji gidan nan haka bai taba damuna wallahi.
Zufa mama din taji yana karyo mata sai yaya sahura ne tayi karfin halin budan baki tace ke murja har kina ikirarin fadin wanan kazamin maganan yanzu don Allah ?
Ato yaya me zan boye mata ba ita ta turani ba itafa takaini wajenshi lokacin ya ban sa,an samari dana kasuwa take turani anso magani shi kuma kwana wajenshine kawai banyi a lokacin amma aiya moreni ba iyaka indai wanan mutumin ne ?
Toke da kike fadan hakan ke nan dabane kowa zaki kawowa guntun wa,azi a nan yanzu kuma ?
Wallahi sam bako irin watsewar nan naki ba murja ni dai ki barni da Armi a lokacin nasan kan munyi rayuwa dashi amma tunda yayi aure ya barni nasan maza mayaudarane na daina shiga harkansu.
Shiyasa nakiraki yanzu ba don komai ba kada kizo kina biyewa karya kuna hauka a cikin gida don Allah wanan abindai zan iya cewa alhakine yake biyan mu haka gaskiya uwar ta dago kai ta kallota.
Tace wallahi mama inba Alhaki ba me muka rasa a jikin mu da za ace maza basu son mu saida lalata shi Armi a lokacin ai aure yaso muyi amma mama kikai tsaye kika hana kikace wai baida ko sisi fakirine.
To gamasu kudin basu zo ba su kuma daidai mu din idonsu ya kawu akan mu yanzu ga matasanan sun taso masu jini a jika me zasuyi damu yanzu haka ?
Shiyasa nayi dabaran komawa karatun nan ko dan aiki mutum ya samu nafadawa mairo tako taimaka min da kudi lokacin nayi komai ba gashi yanzu ina batun kammalawa ba ?
Shike hadani dakw yaya ki dinga zubar da kanki wajen yarinyar nan kina roko kin daukesu yan uwa komai sirinki duk sun sani yanzu suko nasu ba mai taba ji ni wallahi haushi kike ban da wanan abin da kikeyi.
Taja tsuki tana hayewa gado yar uwar ta dubeta tace ba zaki dibi ruwa ki watsa ba zaki kwanta haka murja ?
Mu kike nufi zan kwanta maku da kazanta kome saukin abin dai ba dakinki bane nan dakin kowane gidan ubanane ba mai hanani in sakata in wala a cikin dakin nan.
Ni ba haka nake nufi ba aiko don dadin jikinki ki watsa ruwa murja ya kamata zuwa yanzu kin natsu kinyiwa kanki fada murja lokaci bai jiran mutum fa a rayuwan nan ?
Sannu malama banyi niyar wanka ba kuma uban da ya isa yasani abinda banyi niyar yinshi ba yanzu ni wancan dayan dakin ma da akayi shi zan koma ciki ingyara inbar maku nan keda mama.
Ido uwar ta dago ta dubeta tana fadin ke abinda akw cikima bai dameki ba murja ana zancen aure kina batun gyara daki cikin gidan ku kiyiwa kanki fada fa murja yanzu yar uwarki dake gida ko wani lokaci hakan baiyi mata dadi ba itama ke baki koyi da hakan don Allah ?
Su zaman gida manya mama in zauna gida uban wa zai ban kudin kashi dana sauran lalurana idan na fake a cikin gida ?
Takaici ya hana mama din yin magana a lokacin don haushi ba abinda take tunane sai zancen malam jibo da murja tagama a lokacin.
Inko hakane malam Jibo din yakai macuci azzalumi zata je yau din nan ta sameshi tayi mai cin mutunci kan ha,intanta da yayi irin haka.
Ta yarda dashi ta bashi amma yarasa yar da zai hake sai yarta yar cikinta yar da takeso kamar ranta itace murja da yanzu ta famfare ta zama masu matsala a kaf zuri,a wanda take ganin saka hannune da akaiwa yar nata takoma haka don a bata mata rayuwa.
Mai karatu nayi mantuwa din baba ya saka gyaran gidanshi a baya wanda ya shiga bakin mutanen unguwa don ganin yadda aka dauko gyaran gidan namu.
Inda dakunan su mama aka kara mai fadi akayiwa kowa ciki da falo har da baranda da kitchen ya fidda gidan bangare hudu har da nashi dama akwai fili taciki data waje duk yanzu ya hade ana gine mashi.
ZAINAB IDRIS MAKAW
[10/18, 9:39 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊9️⃣5️⃣🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Ina daki kwance naji muryan Paapa yashigo saidana bari ya zauna ya jima na kwatanci yagama wasu abubuwa na rayuwa da inya shigo gida yakeyi na fito don in gaidashi.
Cikin ladabi yadda na saba gaidashi inkai gwiwana har kasa ina gaidashi ya amsa yana fadin aam maryam ina ganin gobe zamu kano tare insha Allahu.
Kano kuma antyna ta tambaya cikin mamaki tana kallonshi ya daure fuska yana fadin eeh gara naje da ita ayi komai a gabata zaifi don masu nemanta da zasu zo gida ranan jumma,a idan Allah ya kaimu.
Okey zasu shiga gida ke nan a wanan satin ta tambaya yace eeh har ta juya tana daukan ruwa ta kara tambaya amma Oga Aliyu dinne ko zasu zo ?
Shine mana ya fada kamar a hasale tare da gajiya da tambayanta a lokacin ya juyo gareni yana fadin kinji menace ai gobe ki shirya jirgin yamma zamu bi zuwa kano insha Allahu.
Amma Paapa kasan nima ya kamata aje dina don Allah yaya zaka dauki maryam kaje da ita ita kadai ba tare da rakiyana ba ai hakan ba tsari gara dai muje din tare da ita zaifi ?
Ba komai na soma tunawa sai idan anyi hakan kamar an badani ke nan a garesa hakan na nufin aure ya kusan tabbata a tsakanin mu.
Wanda a gaskiya har yanzu ba zance waye Oga Aliyu ba a fili dan wanan haduwan namu mai kama data bariki shine a yanzu yake kokarin juyewa ya zama aure a tsakanin mu kuma ?
Abinda na sani Aliyu mutumne mai zuciya da saurin fushi yana da saurin hasala kan abu saidai baida wuyan hucewa kuma nake gani.
Ni kuma nasan banda saurin hasala irin hakan amma akwai tsiya akwai fitina nima da daukan zafi idan an tabani ko anyi min ba daidai ba.
Ba zance ga yan uwan Aliyu dana taba gani ba inba wanan Abdul din dana taba gani a gidansa ba lokacin haka bansan wani abokinshi ba ko wani can daya sanshi balle nayi tambaya akanshi ?
Yanzuma meya saura yanzu da iyayye suka riga da suka shiga zancen ai kuma har an wuce wanan gabar ko ke nan a yanzu.
Sallah magariba na mike nayi tare da isha i bayan na idar ina shirin kwanciyane kiranshi ya shigo min na dakatar da abinda nakeyi na dauki wayan inda ya soma fadin .
My daughter amarya yanzun nan uncle dinki ya kirani ashe tare zaku kano dashi gobe amma naga sai jumma,ane ai sukace zasu je gidan naku ?
Baki da lectures ne all those day da zakije kano din nace ina dashi mana gobe idan nashiga zan dauki excuse daga school don kasan dai ba zan iyawa Paapa musu ba ga yadda yace za ayi.
Ku nawane masu tafiyan a nan naji ya tambaya nace dagani sai antyna da Amira ce zamu tafi saishi Paapa din yake fadin okey kince dayan matar shi na kano ko ?
Tana can da jima acan take zaune yanzu okey ticket din mutum ukku dana yarinya za a saya ke nan ba matsala zanwa sulaiman magana a sayo ticket din ku .
Aida ka barshi yace naji amma dai kinsan saboda ni za ayi wanan tafiyan ko ?
Don haka ki barni please ga yadda na tsara abina don Allah ayi hakkuri na fada yace fine nikan wanan hali na Aliyu nasan akwai aiki a gabana don zanyi fama da masifa gaskiya amma kuma so ya kawar da komai akace.
Don hakane na kawar da wanan zancen nashiga hiran wani abu daban dashi har zamuyi sallama don yace yaga Abbanshi ya kirashi a lokacin.
Ina kokarin kashe layin ya soma fadin nayi waya da yusuf akan ya fito da mota yakai service wace zakuyi amfani da ita idan kunje can .
Mota kuma na tambaya cikin mamaki naji yace zakuje ku dinga shiga motar kasuwace a can dole sai an aje maku motar amfani mana don zuwa unguwa so nacewa yusuf ya kai mota a duba kafin ku iso ya kai maku tunda uncle dai ba zaije da motarahi ba kin sani.
Amma kamar da mota zai tafi don dazun naji yana maganan zai fita yakai a duba motarshi No mun yi magana dashi bada ita zai tafi ba.
Bari na duba Abba inji zan kiraki may be kafin na kwanta ya fada nace a gaida Abban yace kinsan ai zan iya fada mai tunda sako kika ban gareshi.
Kayi hakkuri don Allah na fada ina kashe wayan don nasan hakan karamin aikinshine tunda ya taba yi min hakan da mahaifiyarshi ai ya barni da kunya.
Tunane na soma daga kwance ina tambayan kaina me zaisa yace zai aje min motan tunda yasan gidan mu dai kowa yasan karamin karfine damu ai zaice kuma wai zai kawo min motar shiga a kano idan munje.
Wanan daya saya min don nan gashi ya zama min alkakai ina boyonshi kada aji a sakani a baki balle kuma naje kano ina amfani da mota a can me mutane zasuce a kai idan nayi hakan.
Shidai Oga Aliyu baudaden ra,ayi gareshi wallahi abinda yake gani ba komai bane shi mutane suke gani komai a wajensu hakan ya isheni tsegumi kuma a can ai ?
Duk daba kowane ma yasanni a yanzu ba kano sai an tsaya dogon tunane a kaina wani zai iya shedani tsuki naja ina gyara kwanciyata a lokacin a gaskiya hakan yayi min nauyi inkira kaina a,wa da wanan karyan ?
Uncle ma ai kunyasa nake ji balle can gida ince dasu me idan aka ganni da mota kuma haka dai har barci ya daukeni baikai ga kiran wayan ba dayace.
Washe gari ina shiri naji sako ya shigo min a waya ban tsaya dubawa don a zatona service ne suka turo min sako a lokacin.
Saida aka yi kamar mintuna biyar saiga kiransa na duba ina fadin daddy da safen nan na dauka ina fadin my daddy lafiya ko da safe haka ?
Sai naji ya amsa a muryan barci dakw nuna alaman bai tashi bama daga gado lokacin yana fadin my baby darling lafiya kalau kinga sako dazun ?
Baby darling kuma kamar wata jaririya can dani meya saura a yanzu idan kince min daddy ke kuma in kiraki da baby darling dina.
Amm kudi na nan na turo maki ki gyara jiki kiyiwa yan uwa tsaraba da saura naso muje tare amma gaskiya ina da aiki a yau ba zan samu rakaki ba ya fada.
Mamakine ya kamami a zuciyana a fili kuma nace dashi amma daddy kasan aiba da mota zamuyi tafiyan ba balle in dauki kaya masu yawa.
Kada ki damu da wanan nagama solving dinshi ko na basu sunanki idan kun isa airport din komai yawan kayanki zasu auna a fada min na tura kudi.
Zama nayi a bakin gado ina mamakin bawan Allah nan a zuciyana ashe gaskiyane da ake kiran maza da innuwan giginya.
Na tabbatar da wanan abinda yakeyi a kaina yanzu ba zai tsaya yayiwa yar uwarshi hakan ba amma sai gashi ya tsaya yana bauta akan mace har abinda banyi tunane akai ba yana min tunanenshi shi.
Irinsu Oga Aliyu dole mace taso sosu ko bata shirya ba don sun iya takon matan zamanin nan sosai na son karyan rayuwa irin na nuna isa saidai kash shi kuma yazo a inda ba,a saba da hakan ba kuma.
Duban lokaci nayi naga na kusa makara hakan yasa na mike nakarasa shiri a gurguje nafito dakyat na samu na isa school ba tare dana makara ba ranan.
Bayan na fito lecture safene na fito nayi duk abinda zanyi na daukan live din kwana ukku a school din ban koma aji ba na fito kai tsaye ina duban time kada in makara don Paapa ya fada min karfe shidda zamu daga daga Lagos zuwa kano na yamma.
Sallon na fara zuwa akai min gyaran kai dana jikina na biya na fito na nufi shago don hada tsaraba yadda yace din don dole inyi tunda ya turo min da kudin.
Tun daga su Abdul din mu har kan innan mu zuwa baba da mama da kowa nagidan har anty fati da danta na hado masu tsaraba daidai dasu.
Hakama wanda zan rabawa mutane shima na hada wanda dai ba a saye a kano din sai naji raina ya ban shawaran inwa salma tsaraba itama ba tare da dogon tunane ba na sayo mata less da dogon riga haka yaranta suma har malama kawar innan mu.
Ina hanya dawowa gidane ya kirani yana tambaya ina ina yanzu nace ina hanyar komawa gida a lokacin ki biya nan Pilamigo mu hadu ina daidai wajen yanzu haka .
To kawai na amsa mai dashi don nagaji sosai a lokacin ga yunwa da nake ji ko karyawa banyi ba tun safe dana fito daga gida.
Anan Falamingo muka hadu yana tsaye jikin motarshi yana waya jikinshi saye da bakaken suith har takalman kafanshi bakine na samu waje a hankali na sauka na parker motar nafito .
Ina karasowa duk da yana waya idoshi yana a kaina ina takon nan nawa mai kama da ina kunyar taka kasa nazo gefenshi na tsaya.
Juyowa yayi yana fadi kinkoci abinci yau kaina girgiza mai sam bansan da mutum a motar ba saida naga ya juya yana fadin hamza fito don Allah ka kai motan nan gidansu.
Ita zan tafi da ita taje ta samu abinda taci jin abinda ya fada yasa na dan kalloshi sai naji yace dani nasan idan kinje gida haka ba zaki zauna ki ci wani abin ba so muje a samu abinda zakici yanzu.
Daddu banfa ko shirya ba har yanzu ga kayana nan dana sayo a mota idan na tsaya zan bata lokacine a nan okey bashi key din sai yaja mu biyoshi a baya.
Dole haka din nayi har mun soma tafiya naji yaja tsuki yana daukan waya ya soma magana Hamza ka tsaya a hanya kasai manyan jakkuna da zata saka kaya a ciki don Allah kadai gane wanda nake nufi.
Ni yanzy yar kalloce don ban iya cewa komai a lokacin shi dai irinane komai na rayuwa irin na baya bai bar komai daga halin rayuwan malam bahaushe ba.
Karfe tara dai dare saura na rana muna kofan gidan mu wanda naga ba gidan mu ba har unguwar ya canzawa sanin da nayi mai a baya.
Ni sai gaba daya naga wajen ya canza min a fuska kamar irun mutum yaje wani kauye nake wa garin mu duba a yau don jimawa da nayi banzo garin ba .
Tun