Showing 243001 words to 246000 words out of 395027 words

Chapter 82 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

lokacin don ganin iyakan mace sai ki hakkura ki daure ki fita zancen su shida kishiya ki nemi abinda zai dauke maki hankali daga garesu ki maida hankalinki kan yayanki da sana,anki da yan uwanki ki daina wanan cika mizanin ki na maunin hawan siradi da nauyin kishiya .

Idan yazo gunki miji idan ya tafi gun kishiya kuma a zauna lafiya amma ina shedan bai bari mata su hango hakan a zukatansu ko yaushe dashi da iyalinshi suna yawo a kawunan mu suna zugamu tare da kawata muna sheri da mugunta a kasan zuciyar mu kan abokan zama kada dai kushiya ta fika tako ina ke.

Wanda abin ba haka bane a wajen Allah don ba a taruwa a baka kai kadai dukka dole idan an fika wani abin kaima ka fita da wani abin sai ki duba ki auna ta ina aka fiki ki gyara wanda kika fita kuma ki kara kaimi a kansa sai a zauna lafiya a tsakani.

Dan guntun tsoki naja ina fadin dama maza duk haka suke nina rasa me mata ke tsayawa suna hauka akai kan namiji guda wani mijin ma inka ganshi saika rainawa matan dake tsayawa yin hauka akanshi.

Wani ba ko sisi saiku matan ne ke wahala amma a hakan kishin juna akeyi kamar a cinye yar uwa danya wani kuma akwai kudin da komai amma sai aki kwantar da hankali a ci arzikin a dadin rai Allah ya bamu wanda muke iya dauka na fada a karshe tare da tunanen mafita a kasan zuciyana.

Don wanan tambada na mata wai kishi ba wai ga hausawa bane kadai ko wani kabilane keda wanan haukan bambamcin shine ko wani kabila da nasu kalan kishin dai ke nan hakan halittane tun farko ga mata sai mace ta roki Allah ubangiji ya bata daidai da abinda zata iya dauka a rayuwanta.

A karshe dai tun a wajen na yankewa kaina shawara da zan bishi kawai a yadda ya daukeni in fitar da zancen wani son da zai wahal da rayuwana kanshi in barshi da iyalinshi su zauna lafiya fakat .

Wanan yasa bayan haka da kwana biyu na daga wayan na kirashi har sau biyu bai dauki waya ba na barshi nasan yana wani uzurine idan ya gani zai kira kamar yadda yake min.

Ba a kira din ba sai washegari ina kwance a daki kiranshi ya shigo min da safe na daga wayan ina sallama wanda ya amsa min a wayan ya karba na sheda ba muryan shi bane.

Don inshine zai soma da maryam ya akayine ko my daughter ya akayi kin kira ina wani abin ban samu dagawa ba sai naji wanan yana amsa sallama ya dora da ina kwana.

Lafiya na karba ina fadin ina mai wayan yake cewa dani yana kwance baida lafiya tun shekaran jiya daya dawo shine yace in fada maki hakan kada kiga bai daga wayan ba.

Innalillahi na fada da dan karfi a cikin damuwa nace ya jikin nashi yana ina yanzu mai muryan yake sanar dani cewa yanzu likita yai mashi allura ya kara kwatawa barci.

Kuna inane a cikin garin nan na tambaaya hakan cikin damuwa iya abinda yace in sanar dake kenan hjy mutum ya fada na rigashi kashe wayan kit.

Ido na lumshe tare da tunanen mafita a kaina daga yadda nake kwance din na jawo wayar dana aje gefe daya na fara neman layin oga sulaiman da na dade banyi magana dashi balle na ganshi tun barina office dinsu.

Layin na danna ina tunanen ko zai shiga a lokacin ko iya office yake amfani dashi kawai ina dannawa kiran ya fara bumming alaman ya shiga.

Aka dauka aka soma magana na kara a kunnena ina sallama tare da fadin morning oga sulaiman ya amsa da fadin .

Ahh maryam so kina nan ashe, kina lagos ko kina kano najiki shiru kwana biyu kin bar wajen mun daina jinki yanzu.

Sam ba a ko jin motsinki yaya kike ya kwana biyu ya karatu kuma na amsa da Alhamdullahi kin kuwa san oga yana kwance baida lafiya.

Tunda ya dawo kano baiji dadin jikinshi ba yana kwance an mashi drip jiya yace ya dan samu sauki yanzu nake zancen zuwa in dubashi.

Wani unguwa yake please na tareshi da tambaya don naga baida lokacin dakatawa da magana yana ta zuba.

Okey baki san inda yake ba yana nan a cikin Apapa Crystal omoshola road house no 33 yana fadin hakan na mike tsaye da wayan a hannnuna.

Ina fadin okey oga sulaiman nagode sai anjima ya amsa da okey bye ban karasa jin abinda yake fadi ba na kashe wayan.

Ban daki nashiga na watsa ruwa a jikina nafito na shirya a gurguje na fito anty bata falo a lokacin yasa na leka dakinta ina fadin zan dan fita Amira dake kwance tana kallon cartoon ta mike tana fadin zata bini uwar tace zasu fita tare da ita zuwa gidan mommy.

Wanan yasa na kama hanya ni kadai zuwa taron aradu don saida nakai Apapa na soma tunanen idan naje matarshi tana gari fa me zance dasu lokacin.

Tsorone ya rufeni ina shawara in koma inda nafito asirina rufe idan yaji sauki ya fito office inje ingaidashi a can mai taxi din dana daukone ya katseni da fadin muna layin dana fada mai nace house number 33 yace okey sai kofan gidan ya tsayar da mota.

Ginan gidajen kusan iri dayane a wajen kina shiga kinsan kinzo layin manya don zaki dauka a kasan waje kike komai neat kamar ba garun lagos kike ba.

Ga unguwar shiru sai jefi jefi zakiga kittawan mota kodon ya kasance weekend ne ranan wajen yake tsit haka oho ?

Sauka nayi dole har lokacin ina wasi,wasin har idan na bari mai motan nan ya daga samun abin hauwa in koma haka kai tsaye zai min wuya a wajen nan.

Kaina daga na a hankali na dubi katon get din gidan yana rufe a lokacin tunane nayi yaya za a san ma nazo wanan wajen ?

Cikin karfin hali na taka zuwa kofan gidan bayan nasa mai taxi ya jirani a wajen na kai hannu ina kwankwasa get din gidan ba tare da nasan abinda ya izani hakan ba.

Sau daya na kwankwasa na juya da sauri da niyar komawa wurin mota karan bude karamin get din gidan da akeyine ya dakatar dani.

Na juyo mukai ido biyu da maigadin daya leko don ganin ko waye ya taba masu kofan gidan don gudun zargi yasa na juya gareshi ina fadin nan ne gidan Oga Aliyu mutumin kano ?

Ya amsa da nan ne nake tambaya don Allah ko yana ciki shida iyalinsa ?

Iyali gaskiya kila ba wanda kike nema bane amma nan din gidan Aliyune kuma mutumin kano na tareshi da tambayan yana ciki don Allah ?

Nazo in dubashine da jiki don ya kirani baida lafiya dazun yadan kada kai yana fadin lalai shine yana ciki baida lafiya kuwa kwana biyu.

Don Allah zan iya ganinshi na tambaya yace gaskiya yana da wuya ki ganshi yau amma tunda har kince kunyi waya shiya fada maki baida lafiya bari na shedawa na tare dashi zuwanki.

Har ya juya zai tafi sai kuma ya bude get din gidan yana fadin shigo daga ciki ki zauna har in fito yana fadan hakan ya kara dan bude min kofa din .

Wajen zama ya nuna min na shiga na zauna shi kuma ya nufi wani dan dogon hanya a cikin shuke shuken gidan kai tsaye ya tsaya daga kofa yana latsawa.

Sai can aka bude Abdul ya leko da kai yana tambaya yake fada mai watace tazo ganin oga na fada mata baida lafiya tace shine tazo ta gaidashi.

Nan naga wanda ya leko din ya dago yana kallona daga inda nake don ban zauna ba tare suka tako don cewa yayi da maigadi macefa kace shine dalilin da naga yana lekoni din ashe.

Suka karaso yana wani kare min kallo na kara daure fuska yake fadin sannu da zuwa ance oga kika zo nema na amsa da eeh sorry yana barci ya ban amsa a takaice.

Ok idan ya tashi kace dashi maryam ce tazo duba jikinshi da sauri ya juyo yana fadin Sorry ban sanki bane don Allah kiyi hakkuri kece mukai waya dazun da safe dake ?

Nice na fada a cikin hausa sai naga dagashi har maigadin sun kalloni suna fadin hjy ashe ke ba hausace nasha ke yarece ai da farko.

Nikan nayi mamaki sanina da Oga ba wata mace data taba zuwa gidan nan nemashi sai wanan ranan jin maigadin zai soma zuba na tareshi da fadin don Allah zan samu takarda in bar mashi sako ?

Ko zaki iya jira ya dan tashi don tun dazun da mukai waya dinnan akai mashi allura ya kwanta bai tashi ba.

Jikina yayi sanyi tayaya zan tsaya har lokacin daya tashi nasan tsawon lokacin da zai dauka yana barcinne ?

Ai kawai dai tunda nazo barin tafi nake anyanawa a kasan zuciyana na dan kalloshi ina fadin.

Ba matsala barin tafi kawai idan ya tashi ka sheda mai nazo duba jikin nashi na samu yana barci Allah ya sauwaka yasa kaffarane .

A ciki kuma yana kwamce din mafalkin da yayine yasashi zabura ya bude ido yana kiran Abdul baiji ya amsa ba yasa ya fito zuwa falo nan ma ba Abdul din shine ya nufo waje da niyar tambayan maigadinsu inda Abdul din yaje ya barshi kwance a gida.

Yana fitowa ya hangosu tsaye muna magana tun daga nesa yasawa Abdul din kira da sauri ya juya yana fadin gashima ya fito.

Dan jayewan da Abdul din yayi a wajen yasa ya hangoni yana saye da wandon maza irin crazy din nan iya gwiwa fari mai aljifaiya a gefe sai yar riga karama shima fara a jikinshi.

Gaba dayan mu karasa wajenshi mukayi sau daya na daga kai na dan dubeshi ya kara zama min yaro karami sosai a indona wanan saima ince bello ya girmeshi nisa ba kusa a shekaru yau dana ganshi haka nake fadi a kasan zuciyana.

Muryanshi naji a kunnena yana fadin maryam yaushe kika zo nan din kafin in bashi amsa kuma har ya juya wajen Abdul yana fadin shine kuka barta a waje tsaye ?

Ya sake juyowa wajena ya maimaita tambayashi yaushe kika zo nan waya nuna maki gidana ?

Ban jima da zuwa ba ance kana barci shine zan tafi don ina barci ba zasu tasheni su fada min kinzo ba ?

Zoki shiga ya fada yana jayewa a hanya ya juya gun Abdul din yana fadin ya zaka barta a waje haka tsaye ka taba ganin wata tazo nemana gidan nan ?

Kaje ka tasoni mana bana son irin hakan mutum yayo tafiya zuwa dubanka ace wai kana barci ba a ganin ka bana son irin halayan nan don Allah .

Ganin na tsaya ban motsa ba yasa yace dani shigo mana ciki na dan girgiza kai ina fadin No ba sai nashiga ba tunda na ganka ya jikin Allah ya bada lafiya.

Da mai mota nake yana waje yana jirana na barshi zai koma dani inda ya daukoni sai in biyashi.

Ya tafi kawai za a mayar dake ai mu shiga a gaisa tunda kinzo niko da yasan tsoro nake ji a lokacin dan kada in shiga matarshi tace waceceni da baice min inshiga din ba ai.

Hakako naki shiga na aje mikawa Abdul ledan fruit din da nazo dashi ina fadin ba sai nashiga ba sai anjima tunda naganka.

Na juya abina na tafi na barshi a tsaye yana bina da kallo cikin mamaki bai iya cewa dani komai ba a lokacin har na bude get din gida nafice da sauri nasha cajin kudi ga dan taxi din dana dauka din hakan kuma bai dameni ba.

Saidai kasan raina ina tunanen idan akwai mace me zaisa yace wanan guy din ya tayar dashi koma dai yaya zancen yake dai na nuna kulawana a gareshi kuma ya gani.

Na karasa gida a kasalance lokacin rana yayi sosai a garin don wajajen karfe dayane na rana don haka kwamciya nayi kafin sallah don indan samu barci in huta.

Cikin mamaki ya juya zuwa ciki baiyi yunkurin tsayar dani ba ko wani abu ya samu kujera ya zauna yana dafe kanshi tare da tunane don yadda ya ganni kamar banda natsuwa a lokacin ?

Wani irin haline ga yarinyar nan haka kamar zararra da ita kinzo kuma kice baki shiga hakan yasa ya danja guntun tsuki a fili yana gyara zaman shi .

Kamar jira ake don ko kirane na mahaifiyarshi ya shigo mai a lokacin Abdul ya nufoshi da wayan dake ta ringing a daki.

Ya karba yana karawa a kunne tare da fadin ummah ina wuni tace babana ka tashi ke nan na kira ance kana barci har sau ukku Abdul ke dauka idan na kira ?

Na tashi ummah yaya kuke yaya jariri kuma ta amsa da lafiya lau ince dai jikin da sauki yanzu ya amsa da sauki ummah ya jama,a kuma ?

Jama,a Alhamdullahi Alh yace min saida aka kara maka ruwa yau ai shine nake ta kira inji ya jikin da sauki ummah ya fada a dan snyayye gareta.

Ga hjy Ku gaisa ta fada ta mikawa matar yayan nata waya suka fara gaisawa da ita take tambayanshi karfin jikin yace da sauki.

To Allah ya baka lafiya baba ai Alh da malam sunce saidai a dage sunan nan jibi tunda baka da lafiya kada kace zaka biyo hanya kuma haka.

A,a mama don Allah a fada masu kada su dage don ni zan aiko da komai daga nan idan ban samu zuwa ba ai ayi kawai Allah ya raya munashi bisa sunna ta amsa da amin amma kasan tunda sun fada haka din zasuyi ai yanzu dai sai kunyi waya dasu ai.

Ta mikawa mahaifiyar nasa waya yake fadin ummah don me za a daga sunan nan a satin nan ai kafin nan naji sauki zan shigo kano din insha Allahu amma don kada a daga wanan abin ?

Zancen Alh daine kasan ba wanda zai hanashi hakan a yanzu yayi shiru kafin ya sake tambayan yana dai lafiya ko naji ana cewa yayi karami yaron ?

Lafiya kalau yake gashi nan a hannun maman ku hjy tana mashi farsa sun danyi magana kafin suyi sallama ya kashe wayan tare da dafe kanshi da hannun shi wani irin sanyi ya soma ji a lokacin cikin jikinshi.

Abdul ne ya danzo gabanshi yana fadin a kawo maka wani abune ko zaka iya ci hakan yasa ya dago kai ya girgiza kai yace banjin cin komai a yanzu Abdul.

Abdul din ya tsaya dan shiru saman kanshi kafin ya juya da niyar barin wajen yaji muryanshi yana fadin me yarinyar nan ta kawone akwai fresh lemo a ciki ka bare min in sha ?

Barin duba ya fada da sauri ya nufi kitchen dinsu inda yakai kayan ya bude akwai lemo a ciki fresh da kankana su ya wanke ya bare ya kawo mashi inda yaken ya dafe kai da hannu yayi shiru a zaune wajen.

Yasha sosai har Abdul din yana mamakin hakan kafin ya mike zuwa daki daurewa yayi ya dauro alwala yazo yayi sallah yana idarwa kuma ya koma ya kwanta sanyi ya rufeshi lokaci guda .

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[9/21, 9:56 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊7️⃣5️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login