Showing 369001 words to 372000 words out of 395027 words

Chapter 124 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

rikede ya zamo babban zance zuciya ta kasa daukan matsalan ka saika fitar da abinda zuciyanka ke nasawa a ciki kowa yaji.

Bashir bai yarda ta kwana a gida haka ba dole asibiti aka wuce da ita gashi shi kadaine ya rage a lokacin duk suna umura shi kuma habib ya ketara ya fita yaje sarin kaya.

Itako wanan yar uwar nata tunda ta samu tashigo dakin hjy hauwa ta zauna take fadin ba inda zata a nan zata kwana sai kiran waya takeyi tana shedawa yan uwa ciwon Naito ya juya hauka kuma a yanzu fa ?

Bs zata iya ba ita dole sai yan uwa sunzo asan abinyi tana asibitin dawanau yanzu haka annkwatar da ita a can an bata gado.

A cikin hsusan nasu na yan kauyen zaria ta kira wanan tace ba lafiya ta kira wanan duk ta ruda yan uwa a gida hankalinsu ya kara tashi.

Wata yar uwarsu ta daga wayan babban yar naito din mace da muke saudiya tare take tambayan ta da Rukkaiya ashe abin dake faruwa ke nan ciwon hjy ya juya ya zama hauka yanzu kuma.

Umma ta kiramu tace tana asibitin dawanau an bata gado a can dip Rukkaiya din ta dauke kafin ta saka kuka tana kokarin ihu ina kusa dasu a lokacin nake fadin haba hankalin mutane zai dawo kanki ai daki daure ko menene har mu koma gida kinji ina ta bata hakkuri da baki a cikin kulawa dako meyema ya same ta din a lokacin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[11/2, 10:07 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊1️⃣0️⃣0️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Sai bayan mun dawo masaukine muke jin kus kus din abindake faruwa nima yaran na su saudat da suka hade da Amira da Na,ima sune suke kyankyasa masu gulman abindake faruwa.

Wai ai mahaifiyarsuce ta samu laluran tabin kwakwalwa a bayansu gasu kuma gaba dayansu basu gida sunzo tare damu wanan tafiyan.

Gaskiya na tausaya masu sosai wanan kulawanan dana bata shine yaja raguwan kallon tsarguwan da suke min don bayan mun dawo masauki da dare saida na nemi dakinsu naje kara mata jajen abinda yasamesu din mukai mata Allah ya bata lafiya kafin muji kan zancen.

Sai gashi mun dawo dakinsu saudat suna fada muna cewa ai kishiyan mahaifiyar oga Aliyune ashe abin shima ya shafeshi ai.

Naji wani irin ba dadi a wanan zancen tunda bansan ainihin abindake nan ba koma nasani lalura ya samu dan uwa haka ai dole ka tausaya mai yadda addini ya koyar damu yi.

Saida darene bayan ya shigo na samu yi mashi jajen abindake faruwa a gida yake fadin na rasa sakaran data kirata da wanan zance ?

Aibaka fadawa mutum zance haka kai tsaye ni naji tun da asuba muna hanya kiran da sukai min ke nan gasu asibiti da ita amma ban fadawa kowa meya faru ba don gudun haka.

Yana shirine yake wanan maganan na kawar da kaina gefe daya don abinda yakeyi din na kimtsa kamshi a lokacin.

Allah ya gyara ai mijinki taso da hakan Allah ya mayar mata da abinta kanta bata san mijinki yana cikin tsoron ubangiji Allah bane da batayi gigin aikata min hakan ba koda da wasane.

Kai kuma daddy akan me zatayima hakan yake fadin kan bata kaunana ko kadan a hankali ya kai kwance ya soma ban labarin irin rayuwan daya taso a cikinsa.

Sai naga nawa ashe wasane don wanan kamar ta cunawa mama wajen kishi duk da kusan abinsu dayane da juna suna hada zafin kishinsu da diyan miji duk macen da bata iya controlling din kanta akan dan miji kishinta ya zamo na bala,i tayi gagawan rokon Allah ya rage mata wanan kishin tun bata kai ga aikata barna a rayuwanta ba.

Shirun da nayi ina wanan tunanen ya zata ko barci nayi a lokacin naji saukan hannunshi saman kaina hakan yasani sauke ajiyan zuciya ina fadin.

Abu kamar almara idan kaji wani abin saika dauka kamar shirin film ba gaskiya bane wai kuma ya faru da gaske kowa fa kuma yana son aljannan nan amma kuma zuciya yasa ana aikata abinda bashi ba.

Na soma bashi labarin mama da irin abinda tayi ta aikata min a rayuwana har tafiyana lagos da farkon zuwana gida abinda tace min.

Ina kawowa nan ya kwashe da wani dariya yana fadin tayi gagawan tambaya ita ai ta jira idan mun koma yanzu ta tambaya da goyo kika dawo koda ciki zam fada mata ince ciki dai muka samo garin rahama zaki haifeshi a nan kano gabanta.

Yanzu ai itama mama ta kanta takeyi wanan lalurar hawan jini daya kamata yasa bata iya komai a yanzu saidai ido ga kowa yanzu.

Dama ita harda yayan mu suke wanan rayuwan nan nabashi labarin ya murja yadda muka kwashe da itama kafin muyi wanan tafiyan.

Lalai ashe kema kin dandana naki irin kalubalin saukinki daya shine ba,a rabaki da mahaifinku ba don a cikin labarin nan naki shi yana tare daku bai yarda an zugashi akanki ba ?

Amma ni rabani da nawa mahaifin akayi fa maryam kwata kwata an cire mai kaunarsa a kaina lokacin itama ummah hakkurine da samun magabatan kwarai da suka zaunar da ita gidan har wanan lokacin.

Irin wanan matan sukan danbala namijine ya koma wani iri sai abinda sukace dashi kadai zaiyi amfani yana karkashin juyawansu ko wani lokaci.

Haka su malam suka fada a lokacin suka rikeni tankar su suka haifeni komai sai suke min laluran rayuwata har gidan namu ya fita raina ga baki daya.

Saida kyar yanzu na dan saba da Abba ai har muke dan zama muyi magana mai mihinmanci a tsakaninmu amma yanzu ai ba wanan zance kuma .

Banyi aune ba naji ya kwanto min a jiki wanda hakan yasa na dan zabura ina kokarin kare kaina daga gareshi amma na kasa hakan saboda nauyinsa daya sakar min wanda yasa a hankali na tuntse idona tare da make jikina daga abinda nake jin yana kokarin min a lokacin.

Bansan meya gani ba son kanshi naji ya mirgina gefe daya yana sauke numfashinsa wani iri tare da huci yayi ringingine yana kallon saman dakin a hankali na motsa hannuna da nakai ina gyara gaban rigana daya budeshigaba daya na saya ta hanyar kokarin mayar da botton din.

Iska mai dan sauti ya furzo daga bakonshi kafin ya mike zaune can naji ya mike gaba daya daga shimfidan zuwa bayi ya jima a ciki kafin ya fito ashe ruwa ya dan watsawa jikinshi.

Kwance nake na lafe har ya gama abinda zaiyi ya sake hawan gadon wanan karon jinayi ya rungumeni zuwa jikinshi yana sauke numfashi a hankali tare da kaiwa tsakiyan kaina kiss.

Dole a haka barcin ya daukemu tare don nasan ba yarda zaiyi yadda ya rikeni din nan in zare jikina daga nashi ba don haka sai asuba shiya tayar dani don zuwa masallaci.

Haka mukai rayuwan madina cikin jin dadi da ibada don ko yaushe muna a cikin masallaci saida darene da kuma safiya muke samun dan hutu a masaukin mu kafin a fara haraman zuwa makka kuma.

Ina kallon suna sayayya nikan oga yace min kada nayi tarkace nan din Allah haka yasa ko mun taso daga sallah yayin komawa masauki suke samu suyi sayayya ni ban tsayawa nakeyi ba.

Don biyoshi nakeyi mu dawo gida tare dasu tunda har yayi magana akan in dakata da sayayyan nan da yaga sunayi duk abinda nake so zan samu a makka.

Amma sai naji sisters din shi suna fadin ai kayan madina sunfi quality shiyasa suke saya duk da sun fadi hakan baisa na saya ba gaskiya sukance basu dakatawa ai ni ina tare da Ogan tafiyan.

Cikin irin hakan na barsu gaba daya matan a baya na nufo masauki tare dashi saura kwana biyu mu wuce makkah wanka nayi tare da brush bayan na fitone na zauna don in gyara jikina in kwanta ina laluben mai nazaro wanan kamshin da malama ta bayar in hada saudat ta hada minshi da wani guntun turarena da nake so.

Sai kawai na dauka na murja a duk inda ya kamata indan goga a jiki har kayan dana fitar zan saka saidana dan goga turaren ba tare da wani tunane ba a lokacin.

Na dai gama yan al,addun mu na mata na shafe shafe zama nayi na karya naci abinci wanda kwaine sunyan can sai arish shine dai abincin dama na safe.

Hamman dana soma yasa na tashi na kwanta don dan barcin da nakanyi wanda bamu samun issashen barci da dare sai irin wanan lokacin mu dan rama.

Nasan suna tare da wanan kamal din wanda kamar sunsan juna da dadewa dashi akwai kuma harkan business din da suke hadawa nan nake gani bandai san meye a tsakaninsu ba dai dashi ?

Koda yashiga harna soma barci jin motsinshi yasa na dan bude idona bayanshi nabi da kallo zai shiga bayi nasam shima ruwan zai watsa a lokacin na mayar da idona na rufe a cikin barci.

Bayan ya fito ya zauna yaci abinci ya mike zuwa bakin gado inda ya tsaya ya kura min ido na dan lokaci tare da jin wani sha,awa na kara rufe mai zuciya a game dani din.

Allah ya gani duk kwanankin nan da muke kwana daki daya ba karamin kokarin tausan kanshi yakeyi da hakan ba ?

Don a baya baijin komai game da mace No matter how closed he is da mace baya jin komai game da ita amma a yan kwanakin nan abin ya soma fin karfinshi kuma sai yaji baya iya control din kanshi duk lokaci irin haka shike sa yana yawan sawa mu zauna a masallaci na wani lokaci.

Amma a ranan tunda ya shigo wanan kasalan da bakon yanayin dake ziyartanshi baijin zai iya karfin halin kama kanshi din a kaina lokacin.

Koda ya kwanta ya jima yana kokarin ganin ya taushi kanshi kan abinda yakeji a lokacin amma ya kasa hakan saima jin da yake kamar lamarin yana karuwa mashine.

Ga kamshin jikina daketa juya mai lissafi yana kara saukar mai da wani irin kasala wanda bai taba jin irinsa ba a tare dashi ?

A hanlali ya mika hannunsa zuwa jikina ya fara dan shafa a hankali wanda hakan yasani bude ido a cikin magagin barci na dan sakar mai murmushi tare da fadin daddy bari mana ina jin barcine sosai wallahi na ina mayar da idona na rufe .

Sannu a hankali nake jin bakon lamarin dake ziyartan rayuwana a ranan wanda hakan yasa na soma kokarin bude idona don intabbatar.

Saboda wanan yanayin da nake ji a lokacin ba a mafalki nake jinshi ba kamar a zahirine lokacin.

Tabbas ba mafalkin bane hakan zahirine don kuwa yakai gaban da ban iya dogon motsi ko in samu wani zarran kwanto kaina daga yanayin dana sameshi din ciki.

Gwargwadon sani bangaren ilimi da bangaren shekaruna nasan da hakan hakkinshine a gareni yake kokarin saukewa a kaina lokacin.

To amma kuma ba zanso hakan yakansance ba a lokacin tsakanin a yanzu ba a lokacin daban tashi karban hakan ba.

Saidai abinda zai shiga tsakaninmu a lokacin ina fatan kada ya wuce irin makamancin hakan ayanzu da yake min ?

Dadai yayi hakkuri din har zuwa lokacin da zan tare a gidansa lokacin nake ganin kamar free ga komai.

Don sai nake ganin ba saka ido ko wani abu makamancin hakan dan ba irin yadda muke a nan cikin taro da bin idanun mutane a kanmu ba.

Saiga zance ya canza min a bazata don ya sauya lokaci guda ba zakice shine ba duk da idona nidai a runtse suke har lokacin amma duk abinda ke faruwa a lokacin ya fara wuce wuce sanina.

Hankalina bai kwanta ba saida naji ya mirgina yana sauke numfashi a wahalace nasan insha Allahu na samu kaina ke nan saboda naji lokaci guda ya daina komai da yake min.

Amma duk dai har lokacin idona a rufe suke saidai ina kokar8n neman abinda zan saya jikina dashi don kunya.

Ji nayi da kansa ya saya min jikina tare da mikewa ya shiga bandaki ya jima a cikin bandakin kafin ya fito ya sameni na dan dunkele kamar mai tsoro.

Sorry tashi kinyi wankan kema iya abinda ya fada min ke nan lokacin ya fice daga dakin sai lokacin na bude ina ina binshi da kallon mamaki ?

Abubuwa da damane sukazo a raina lokacin na mike din duk da bansan wankan da yake nufi inyi ba a lokacin amma dai banki ba nayi din saidai kasan zuciyana suna da tambayoyi masu yawa a kan hakan lokacin.

Ina goge kaina a gaban mirro tambayan karshe ya zo min kasan zuciyana kodai ina da matsalane bai sameni yadda yake zato ba yasa ya kyaleni ba tare da aikata komai a kaina ba ?

Dammmmm gabana ya fadi matsalam me kuma na sake tambayan kaina ance ko wani namiji da akwai abinda yakeso a jikin matarshi wanda ke matukar burgresu koya kasance ni banda wanan abinne yasa ya barni a yanzu din ?

A gabar nan da muka kai a lokacin inba wani abu kwakwara ba babu namijin da zai iya kai wanan matakin yabar mace a lokacin ba tare daya shigeta ba .

To kila ninawa mijin dabanne ko kuma dai din da matsalan kamar yadda nake tunane haka nagama shirina don ba zancen komawa barci a gareni lokacin saboda barcinma ya gudu a idona sai tunane.

Gashi ya fice daga dakin gaba daya ba tare da furta komai a kaina ba lokacin haka yasa nafito daga dakin don nasan zuwa lokacin su Saudat sun dawo dakin antyna na fara murdawa kofan ta a rufe yasa na nufi nasu saudat din kuma.

Inda na samesu yare da Amira kanwarshi a dakin tun kan in karaso nake fadin ashe kun dawo tun dazun yaya muna nan muna kallon kayan nan ne ai take nuna min kayan nakai zaune ina jawowa gabana.

Na dan duba nace amma suna da kyau tace Amirace sukace mu saya wai suna da matukar tsada a can gida mutum bai iya sayanshi a can din kuma babushi sosai sai wa yanda sukaje ,,,,

Anty kayan nada matukar tsada sosai ninaga yayi saukine na saya har biyu nace su saya zai masu rana kinsan abayan matan pakistan ba,a samunshi sosai haka su dinkinsu daban yake.

Nabi kayan da kallo ina juyawq nace suna da kyau matuka amma dai zasuyi tsada ko ta fada min kudinshi na dago da sauri na dubi Saudat a cikin mamaki.

Kafin inyi magana ta noke kanta tana dariya nake fadin ba zakiwa su inna tsaraba bake nan tunda kin kwashe kudin akan riga daya ?

Haba dai Anty maryam kan wanan rigan zata kasa saiwa mama tsaraba rigan nan zai mata rana sosai idan mun koma gida fa.

Nabi jakkunansu da kallo ina fadin wai yaran nan kuna cin abinci kuwa da kudinku munaci mana kanwar tashi ta fada tana dariya da alama ita din tafi yar uwarta saukin kai sosai a yadda nake ganinsu .

Zama nayi dasu muna hiran yadda garin yake daban da garuruwan da muka saba gani koda a cikin filmne inda baka sanin ina mutanen garin suke rayuwa tunda ba wani fita mukayi ba andai kaimu ziyara wurare munyi addu,a munyi abubuwan da addini yace ayi.

Ganin lokacin firan mu sallah ya kusa yasa na mike don komawa dakin mu alokacin muka hade dasu anty dake dawowa da ledoji a hannunsu alaman abinci suka karbo lokacin.

Itada yaya sahura da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login