Showing 372001 words to 375000 words out of 395027 words

Chapter 125 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

gwaggona su kuma sisters din nan nashi suna bayansu kadan itake fadin ai dazun da muka shigo naga mijinki a waje nazata kina ciki kina barcine ai ?

A,a nazo na samu dakinki a rufe sai na wuce wurinsu saudat muna hira aina zata kina barcine kin sanku amarene sai banji dadin hakan data fada min ba sobada naji nauyi da yawa na mika hannun don in karbi kayan dake hannunta, ina karban kayan naji yaya sahura na fadin anty da kanki kuma ?

Ta wasance da fadin keko sahura amaryace da angonta fa za a hanasu amarcine banyi ba ke nan ana zargin muna hakan ina anga nayi aisai a samu na bada labari.

Shi daine na kula tun faruwan hakan a kanmu sai nake ganinshi kamar yana da dan damuwa dani tunda bai iya nuna min ba sai ban dauki abin sosai ba a raina nabishi da hakan nima.

Mukai ziyaran bankwana muna dawowa gida muka dauki haraman tafiya makka a ranan kusan mune karshen fitowa dani dashi daga guesthouse din.

Abayace a jikina farasol da gyalenta dana daure har wuyana dashi hakan ya kara fito da fuskana kadai sabone a lokacin na fara sakawa a jikina muka fito tare dashi yana jan yar troler dina nashi jakkan kuma ya rataya a bayanshi.

Haka muka fito hankalin mutane a kan,mu inda ya dan tsaya yayi sallama da mutanen wajen da akai sabo na dan lokaci.

Kujeran mu aka nuna min kafin ya shigo na fara zama yazo ya sameni bamu dade ba motar ta tashi muka fara fitan birnin madina yayin da kowa ke jin abinda yakeji a zuciyarshi na bankwana.

Mun isa makka cikin dare ana magariba mukaje dawafin umurah bayan mun dauki niyar hakanba zuciyar mu a makka an raba masauki .

Don ba kamar wancan na madina bane wanan akwai dan bambancin hawa a can din mazan suna kasanmu hawa biyar muna hawana nagoma sha daya nidashi su kuma sauran matan na hawa na tara.

Kamar zaman madina haka muka bawa ibadan mu muhinmanci sosai don mu samu rabo a wajen Allah kamar yadda ko wani musulmi ke fatan haka.

Aka fara haraman dawowa gida a wanan lokacin muke dan fita zuwa wasu garuruwan da ba kowani mai zuwa aikin hajja ko umurah yake zuwa ba irin su Riyadh jedda nan ne biranen saudiya muka dinga shiga muna sayayya wani lokaci muje da yaya sahura da anty wani zubin da sister dina da nashi.

Banyi mamakin ganin bai kara irin kula wanan ba tunda ba canza min fuska yayi ba don haka ban damu ba don banga fashi ko damuwa a kaina ba balle in dauka ina da matsala dashi da zai iya shiga tsakanin mu.

Haka muka dawo gida a cikin farin ciki kowa na godiya da wanan tafiyan a airport yake zolayana shida yusuf akan gidansa zan wuce ai bansan lokacin dana hararo yusuf din ba ina fadin namu gidan ba gida bane halan.

Sai cewa da yayi me nake nufi ai daga nan gidanshi nayi ba wani sauran jira a tare kuma yanzu meya rage na wani tsayawa tarewa kuma ?

Allah yasa yusuf ne kadai a wajen don da naji kunya a ranan sai mutum ya dauka ai komai na tafiya irin na ma,auratane a tsakanin mu a saudiya din .

No daddy don Allah kada muyi haka dakai ya shareni ya wuce ba tare dayace min komai ba muka nufi wajen motocin da suka zo daukan mu.

Motan mu guda dashi da Yusuf sai driver muna baya hannunshi yana a cikin nawa tunda muka zauna zamu fara zuwa gidan mu mu gaidasu .

Abinda ya fada ke nan idonshi a rufe lokacin banyi magana ba don wajen shiga motar mota guda yasa a dauki su anty zuwa gida.

Yayin da su Saudat ke tare da sisters dinshi a dayan motan muka nufi unguwarsu kai tsaye ke nan yayi hakane don su rakani gidan nasu mu gaida iyayyenshi.

Jin banyi magana ba yasa ya dan motsine yana fadin bakiji bane ki kira sahura ki fada mata zamu biya nan gidan mu don kada aga su saudat sun jima ?

Dole na fara laluben wayana ina neman layinta na samu na soma fadin yaya kada kuga mun jima zamu dan biya gidansu daddyna.

Baida matsala ta fada tare da fadin a gaidasu sai kunzo na kashe wayan ina mayar da watata jikin jakkata yake fadin ummah ta matsa tunda muka sauka taga yaranta ?

Shiyasa nake son in kaiku tare dasu ku gaisa da ita kaina gyada kawai don ba abinda zance a lokacin kan hakan nayi shiru an dan taba tafiya muka iso kofan gidan nasu unguwar kamar ko wace unguwace a kano don suma cike yake da jama,a kamar tamu unguwan saidai banbancin gine gine don nan din kabo ginan zamanine ko ina ka duba .

Har cikin get motocin biyu suka shiga damu aka soma fitowa ina jin wani iri a zuciyata lokacin ba ba zance ga yanayin da nake ji ba dai a lokacin.

Allah yasa bakar jallabiyace irin na matan egypt a jikina mai kwaliya da kuma fashion dinsu dinkisu haka yake suna fitar da surar mace a wajen dinki.

Mun samu wasu mata a tare da ita guda ukku ashe daya yar aikintace biyun kuma aminantane na cikin unguwa sukazo mata kara.

Yaran gidan su sisters dinshi su hudu sune a gaba saini da nawa sister din a baya tare dashi mukai sallama muka shigo.

Da murnanta na ganin yayan nata suka taresu nasan Na,imace ke fada mata ai tare muke dasu gaba dayan mu yasa suka soma natsuwa.

Shida yusuf suna gaba mukai sallama zuwa cikin gidan muka mara masu baya iya fuskanane kadai a fili duk da haka kaina a kasa muka shigo.

Ba zance ga mahaifiyar nashi ba a cikin matan saidai ganin yadda take zaune da Amira yasa nagane itace mahaifiyarsu da innan mu zata samu waje haka itama murjewa zatayi ace ba itace ta haifo mu ba.

Don ba zakice itace ta haifi wa yan nan yayan ba dake gabanta izuwa yanzu su Saudat sun saba da gaisuwana ga manya don muna zuwa ban zauna ba yadda suka zauna gwiwa biyu nakai kasa ina gaidasu suka amsa tare da yi muna an dawo lafiya.

Dayan matar na fadin mu tashi mu zauna mana kafin mu gyara zama nan a kasa muka zube ba tare da hauwan kujeran ba.

Malam Ali ya hanya dai kunsha saudiya dayan matar data fisu dan manyanta take fadawa Aliyun hakan a daidai lokacin kuma sauran sisters dinshi su biyu

Suka mike suna fadin part din hjy a bude yakene shiru kowa yayi yana kallonsu ?

Naji tana fadin key din yana hannum Bashir amma kamar ba nisa yaje ba don bai jima da shigowa ba gidan nan yake tambaya kun iso ?

Abinci wanan matan nan ta mike ta fara daukowa cikin katse zancensu tana fadin ai kuci abinci kafin ku tafi can din don a nan aka zuba gaba daya.

Bamu san har amarya zakuzo nan ba iya kune muka zubawa ki bata nawa Larai ya fada yace kinsan ba yadda za ayi amarya tazo gidan nan bataci abinci ba ?

Daka fada muna tare zakuzo aida nayi mata girkin da yafi wanan din dadi baki son kije gidana ta girka maki ke nan kici ai tare zamu tare gidan naku .

Hjy bari muje muna son mu dan hutane muje gurin mummy mu dubata suka kara fada ku bari mana kuci abinci sai mu tafi tare mu dubota tunda nima zanje kuma inkai wanan ta duba jikin nata itama da cewani ?

Zama sukayi ba don sunso ba matar daya kira da Larai tana ta hidimar kwaso a bincin zuwa gaban mu tana girkewa duk yadda suka matsa naci na kasa cin komai a gidan ina zaune a cikin takura don na matsu mubar gidan a lokacin

Duk da dai ba wani abinda akai min amma naga kamar mahaifiyarsu na katse mata farin cikin ganin yayanta a lokacin saidai idan zarginta nakeyi ga hakan zato zunubi koda ya zamo gaskiya.

Sunci abincin suka mike suna fadin bari su shiga part dinsu suma dai ba a cikin sakewa ba tunda ba a saba hakan ba dama a gidan.

Kowa uwarshi ya sani da ita kuma ya saba ba ruwan wani da wani ko gaisuwa arziki da kula juna sai yanzu aka dan soma dalilin wanan tafiyan da akayi tare din.

Suna fita naji dayan matar na fadin ai gara dai su tsaya su natsu kar suje suga halinda take ciki su kasa sukuni kuma da dawowansu.

Jikin nata sosaine ke nan Yusuf ya tambaya take fadin Allah dai ya kyauta kawai yaba musulmi lafiya amma hjy kan ai abin ba kyau gaskiya.

Duk abinda suke fadi baiyi magana bashi sai ga karamar tadawo tana fadin Aliyu bai dawo ba bari mu fara zuwa can din inkun fito sai ku same mu .

Ba matsala ya dago yana fadi idan mun huta zamu shigo dubata din zuwa anjima insha Allahu don ya fahinci kamar basu son jerawan namu a tare lokacin.

Kaiwa Sani magana ya ajesu ya fada yana kallon yusuf din ya mike ya bi bayansu falon yayi shiru nasan don muna zaune a falon suna can daga gefesu a zaune suna hiransu da nake tsuntar zancen guda guda a lokacin.

Inda wanan matar ke fadin ni naji tsiro da mukaje ai ranan ta firfito da ido waje tana fadin kema kinji ko wai sunce na haukace kuma lafiyata kalau.

Daga nace a kwashe kudin Alh a boye shike nan fa suka kawoni nan ina zan yarda kudin nan fa kudinane kudinane hahahaha karya sukeyi wallahi basu cin dukiyan nan wallahi.

Saudat ku tashi in kaiku gida ko tunda kun huta shiya katse matar mai zancen da naji sunyi shiru sun juyo garemu tana fadin wai har zaku tafine yanzu daga shigowan ku ?

Eeh zan kaisu gida a gansu zuwan mu ke nan mukayo nan direct dasu amma banda amarya ko ita a nan zata zauna dai ko damu ?

Dan murmushi yayi sai yusuf ke fadin a,a hjy ai bata tare ba tukun balle ku riketa yanzun ma kinga ai ta kasa shan ko ruwa gidan nan saboda kunya.

Shi nake son fadi wallahi ince yarinyar nan kuwa taci wani abu ai da kin sake jiki nan yazama gidanku ai yanzu ?

A,a maryam bakici komai ba haba dai da yunwafa kuka sauko tunda kun kwana a hanya kici abinci mana tare da yan uwanki mahaifiyarsu ke fadin hakan gareni sai lokacin na danji sanyi a raina ganin yadda ta nuna damuwa kaina.

Barin kaisu gida baci zatayi ba haka take kamar bafulatana da kunya aiko ga alama tabar muna mungani akwai kunya kan gaskiya .

Su daiyi ya mike don mu tafi din a lokacin na sake jin mahaifiyar nasu na fadin Larai a hada ta tafi dashi tunda taki ci a nan din sai lokacin na dago ina fadin.

Ummah a barshi zamu sama a gida ai a jewa su Amira su kara ke nan yusuf ya fada cikin zolaya Amira din ta dago tana fadin aini bamu hakan da ita saidai Anty Na,ima.

Nikan ai murna nakeyi bataci ba ta rage muna quantity din shi yanzu kuma ummah tace a wani daukar mata na dan kallota ina fadin ke kan ?

Tace nasan baci zakiyi ba ai koda anje dashi din wallahi ummah yar nan taki bata damu da cin abinci ba ko a can muyi ta ciye ciye tana zaune kawai tana kallon mu.

Aita huta ba irinku masu cin tsiya ba ganin ya mike din muma muka mike Amira ke fadin zaku asibitin ne yayya mu biku ?

A,a Amira zan kai su gidane su huta suma kafin dai jibi mu koma insha Allahu zan kaita tagaida ita din ki bari anjima da magariba muje mu gaidasu.

Dayan matar tace jibi jibin nan zaku koma lagos ke nan tun baku huta ba yace da mun dawo ajiya gobe ya kamata mu koma don tana da jerabawa ranan monday.

Au har yanzu da saura karatun nata ashe nikan har na fara takawa zuwa can din inda suke na tsuguna ina fadin ummah zamu tafi mun gode.

To maryam sannu ku nagode a gaida mutanen gida Allah ya karba yasa makasudiyace a wurin Allah aka amsa da amin nima na karba a hankali na mike.

Su Amira suka rakomu tare da matan zuwa get a nan mukayi sallama dasu suka koma mu kuma muka tafi koba komai naji dadin irin karban da sarakuwan nawa tayi min daga baya din.

Muka fito muka tafi suka koma a nan dayan matar ke fadin hjy hauwa yarinya mai hankali haka da ita baban gida kan baiyi zaben banza ba gaskiya.

Da alama yarinyar nada hankali sosai don ko a waya muke gaisawa haka take magana aikine a gareta.

Wanan kam bata da matsala gaskiya don nidai har mukaje muka dawo banga wanda yace ga matsalanta ba a cikin mu.

Har su yaya Sadiya da basu son sakewa damu dole suka sake har suna jerawa wani lokacin da ita an saba sosai da juna gaskiya tasan darajan manya sosai wallahi .

Sai dai yar gayu ce sosai kam ga turanci kamar ruwa idan ta juya baki zakice bata iya hausa ba a bakinta kamar ba yar arewa ba wallahi.

Na,imace ke fadin hakan ga iyayyen nata ai kuwa tunda Na,ima ta yaba to kowa zai yaba wa na taba jin Na,ima na yabo haka a gabana ?

Gayu kuma ai tunda kikaga yayanku ya nace a kanta ninasan ba banza dama irinsu yake so ai yasa yake fadin tsarinshice ita don haka ita zai aura .

Abinda nake tunane ke nan hjy hauwa saidai diyarku ta nunawa wanan arzikin iyayye amma ba komai ba in kaga namiji ya dage a kan mace akwai abinda yakewa shine nan auren nan nasu.

Wa zaice irin bude idon yarinyar nan zata zamo mai kunya haka da ladabi ki duba ko ruwa ta kasa sha a gidan nan balle abinci da watace saita sakw ta kwashi abinta ba kunya komai a tare da ita.

Su kuma yayan hjy Naito suna zuwa akace ba lokacin ganin mara lafiya bane saida suka matsa aka bari su ganta dole da kuka suka fito asibitin gidajensu suka nufa a cikin bacin rai.

Don sun sameta a kwance an daure mata hannu da kafafuna tana barci a lokacin wanan yasasu tashin hankali tun a mota suke fadin basu yarda ba don anga basu nan Abba yasa ai mata haka a mayar da ita mahaukaciyar karfi da yaji ke nan suka fito a cikkn bacin rai daga asibitin.

Ganin kai tsaye hanyar gidanmu yusuf ya dauka yasani jin dadi ina dan kwanto mai a motan murmushi yayi yake fadin kema kinsan badake bace ai su saudat za a sauke.

Nasan sun matsu suga inna ke ko ga innan ki can a yanzu yasa na fara kai mata ke ta ganki ai ban yarda nayi wani maganan da zai sa yaja min aji ba sai cewa da nayi dashi kuma naji dadin hakan sosai wallahi.

A kofan gidan mu dayasha gyara motar mu ta tsaya gaba dayan mu muna mamakin hakan daya faru lokaci guda mun dai san ana gyara din amma ba irin hakan ba da akayi din.

Dubanshi nayi ya lumshe idonshi kafin naji yace dasu saudat idan kuje ku gaida inna kuce zamu shigo anjima ko gobe idan maryam ta huta aida sauri na zabura ina fadin a,a wallahi .

Rike ni naji yayi yana fadin wallahi me sai kin shiga kome nace haba dai daddy don Allah kada muyi haka dakai please ?

Naga ya bude kofan gefen da yake zaune ganin hakan yasa nima na bude nawa na fito da sauri daga cikin motan yan unguwar mu da suka taso taron mune aka tsaya gaisawa yasa na sulale zuwa cikin gida da sauri kafin duk ya juyo na shige ciki.

Su Abdul suka tareni a cikin murna muka rungume juna dasu yaran na inna kamar tagwaye don ko shigarsu iri daya ake masu duk da Abdul ya dan dara shi murtala ga girma amma shiga daya inna kewa yaran ko wani lokaci.

Inna kan yaranta take taro matar yaya ibrahim ta rugumeni a cikin murna da yaranta nima na rungumesu take fadin a,a mama ga babba zaki wuce taron su


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login