Showing 225001 words to 228000 words out of 395027 words

Chapter 76 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

Na soma karanta mashi din ya rage tafiya da motar ya dauki number din a wayan ina ganin lokacin daya tura masu kudi ta account din Saudat din.

Ance mata kunfi tausayin iyayye saidai ni ban yarda da hakan ba da ake fadi banda wani buri a duniya bayan naga na kyautatawa iyayyena don haka ba wata macen data fini tausayi ke nan.

Abindaya fada din yasa na danyi murmushi a fuskana banda amsan bashi a lokacin kanshi kawai ya sani baisan na wasu ba bazai kuma iya gane abinda bai sani ba din.

Kamar yadda yace ni nasan burina a yanzu shine farin cikin iyayyena inga basu wahala a rayuwa yadda na barsu a baya ba.

Amma yake fadin wanan maganan kamar wanda na tambaya ma,ama ke nan har ya fassara ni da ban damu da iyayyena ba ke nan ko me ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[9/15, 9:11 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊6️⃣9️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

A wanan ranan har kofan gidan mu ya saukeni na yunkura na fita motar ina godiya yake fadin kayanki fa wa zai shiga maki dasu ciki ?

Cikin mamaki na juyo ina dubanshi zakice bashinema yayi magana ba a wanan karon don ko kallon inda nake baiyi ba.

Illan zaman da yayi ya rike sitiyarin motan da hannayeshi biyu ya nema wani abu a motar wasu kaya ke nan na dan tambaye a sanyaye ?

Kada kimin hanliku na mata kayan da kika sayo a wacan shagon fa kin dai san ni ba komai zanyi dasu ba duk nakine .

Kuma kina tambayana kansu yazu ya bude motan ya fita suna sit din baya yaje ya bude ya fara jida yana jingine min a kofan falon mu.

Ina zaune kamar gunki har ya tara min ledojin a kofa ya dawo ya shiga motar ya sameni yana fadin.

Madam na sauke saiki fita ko kada aga na makara ban dawo gida ba yau kisa ai min fada na dan kalleshi na yunkura ina fadin thank you very much nagode kwarai da wanan dawainiyar taka gareni.

Good night kawai ya fada ba tare da amsa min godiyan ba ya tayar da motan na dan jaye daga wajen yayi ribas tare da horn ya tafi ina tsaye ina binshi da kallon mamaki kala da kala nashi a zuciyana.

Ajiyan ziciya na sauke mai dan karfi ya najuya ina karewa tarin kayan kallo cike da mamaki zakice ba tare dani aka sayo kayan ba a lokacin.

A hankali na taka zuwa wajen kayan na duka ina dauka zuwa ciki dasu nayi sallama gidan kamar ba kowa da mamaki na aje na koma na karasa kwasa har nagama banji motsin kowa ba a gidan.

Dakina na nufa duk da nasan mommy tana ciki nayi sallama nashiga sai wayau nagani bata dakin saidai dakin kaca kaca yake ga tsami yana tashi ga zarni da bashi haka na daure na kwaso kayan na dawo dasu daki bakin ciki dana wuni dashi ya dada karuwa min bayan wanda nake cikinshi game da gidan mu.

Duk da nasan kona gyara tana dawowa zata batashi kafin safe ban tsaya ba haka na kwane na fara tsabtace dakin ko ina na zuba izal da roomfresh kafin na samu dan sukunin gyaran dakin .

Lalai tunda banga mommy ba itama anty bata gidan ke nan lokacin tunda dole tare dai zasu fita da yarta .

Nayiwa dakin kwal nayi dacen muna da wutan nepa na sake fanka tare da kware window din dakin iska na shigowa tako ina mai dadi.

Bayan na dan rarage har na fita na dora muna girki wai sai bayan ina kokarin tuka tuwo hajja yabi ta fito daga dakinta tare da danta da suke barci wai tun rana ?

Ni dai mun gaisa dasu nake tambayanta anty fa naji tana fadin tana ganin dai kamar sun fita amma ita ba dai sani ba.

Naja bakina nayi shiru itama ta juya zuwa dakinta don yadda na hade rai nacigaba da aikina.

Wai kishi dai haka yake ke nan ko ina indai akace mace tafi daya a gida wanan gidan zaman lafiyanshi manajine ga mazauna gidan daga matan har miji kuwa why ake hakane wai a rayuwa kuma duk akan namiji.

Zuciyatace taban amsa don tuno da abinda ya rabani da salma kawata da nafiso take sona itama barcine kadai yake raba mu a lokacin .

Amma Bello yazo ya shiga tsakanin mu haka muka rabu hayatan hayantan da ita akan namiji muke nan fa da ba aurensa ma nayi muka hada kishi ba inagasu da an zama daya.

Ni dai ko Allah zai ban mijin aure ina rokonsa karya ban me mata na fada don wauta take kuma a wajen na tuno idan bayan na shigane ya karo min kishiyan fa irin na antyna ?

Ya Allah kada ka jarebeni da abinda ban iya dauka na fada da sauri ina runtse idona ni macece dole sai hakan ya kasance dakai in ba ai maka ba aiwa yar uwarka haka abin yake dama .

Kishin gidan Paapa a gani da hajja yabi zata yi irin na antyna zasu zauna lafiya sosai don ita sam bata damu da irin kishin nan na hauka ba indai kinji fitina gidan to daga hajja yabini matsala ya taso.

Itake nan a kullum an mata laifi bata ko la,akari da halin antyna da sam ita hakan bai dameta ba sai yadda zataji dadin rayuwanta ita shine a gabanta.

Ina lure ko mijin bata damu dashi ba a yanzu irin da da zatace yiwa Paapa abu kaza maryam bari muyi kazan nan don Paapa yanzu sam ba wanan zancen a wajenta ita kuma nata kalan sallon kishin ke nan ta basar da miji sai ya koma binta don gaskiya antyna mace ce ta gaske.

Matsalanta daya shine raguwace gayu kawai da duniyance irin na rayuwan kabilu shike a zuciyarta sutura ko nawa yake zata saye ta sakawa jikinta haka kuma a zaune din take taba sana,anta na kayan mata bata daina ba har yanzu don har sari ake zuwa yi a wajenta.

Har falo duk na gyara na fito da abinci na aje masu daki na koma nayi sallah bayan na idar da addua na kara gyara dakin kwal na saka kamshin da tun shigowan ka gidan zakaji.

Muryan anty naji ina sallah isha,i ta leko dakina tana fadin har kin daw kinyi girki maryam yau da wuri kika dawo ke nan ganin ina sallah yasa ta juya zuwa cikin dakin ta....

Na idar nayi addua na mike zuwa falo din ingaida mummy kada inyi laifin hakan saidai ba kowa a falon yasa na nufi dakin antyna din ina fadin sannu da dawowa na dora da fadin mummy fa ?

Ita nakai gida ai yau ta koma gida da kyar yakai sati muna jidali da uncle dinki ta koma gida kinsan halin mummy tace ba zata koma ba a nan zata zauna shi kuma yace bai yarda da hakan ba.

Why uncle zaiyi haka kuma ai kinsam halin mummy fada sukeyi dashi da matarshi kullum kika fita gidan nan yazo gaida ita sai ta haushi da fada ko kuma tayi ta zaginshi kan Yabi ita kuma idan taji tace zata rama bata san wanan ciwon ne ya kara maida mummy din haka ba ?

Ke meye batayi maki gidan nan baki taba nuna abin ya dameki ba kuma nasan yana bata maki rai shanyewa kawai kikeyi don ni amma yabi ta kasa duba min laluran mummy a gabana zataciwa mummy mutunci yasa naga gara dai din ta koma gida tunda gasu hansai a gidan ai zasuci gaba da dubata.

Yanzuma zuwan nan yau na samu wata da zan dinga biya tana mata komai kinga anhuta ai sai na dinga zuwa ina duba lafiyanta a can din kwana bibiyu.

Allah ya sawaka amma dai da an barta ta dan kara samun sauki waye bai san halin tsoho ba ga kuma ciwo No haka yafi min maryam yabi bata da mutunci kinga da ace muna da wajene enough of saita zauna damu nan din ban damu amma kema tana takura maki da wanan laluran fitsarin nata ai.

Ga abinci can falo idan kun huta na katse zancen da fadin hakan don magana take min ranta a bace na juya na dubi Amira yarta dake kwance ina fadin Amira tayi barcine haka ?

Tace tun a hanya kinsam go slow dun nan na Lagos take ta barci da kyat muka kawo gidan nan da ita muna shogowa shine ta kwanta a nan.

Na dan taba yarinyar na juya zan fita nake fadin yau gidan mu su inna ba lafiya fitina sukeyi tun safe har baba ya saki mama ta koma gida akace.

La,ila ilah ta fada irin na yaroba nace wallahi nima banji dadi ba anty da tsufan mama haka kuma ace ta rabu da miji ai hakan ba dadi gaskiya.

No kada kice haka idan kaga babba yayi abu da kake ganin bai dace ba yafi ka sanin haka mukkadarime abin ko kuma ya gaji da halin meshi ya sauwaka mai kinga ko wanan matar nasan karshe haka za ayi don fitinan yabi yayi yawa wallahi .

Dan murmushi nayi na juya na fita daga dakin dakina na koma akwai sabon zanin gado dana taba saye shina dauko na bude na goge bakin gadon da ruwan izal na fasa air fresh na sake kakkabe ko ina na dakin kafin na shimfida zanin gadon dakin ya fito fes dashi kafin hankali ya fara kwanci da dakin.

Sai goma na samu nagama gyaran daki na fito falo da wayana a hannu ina zama na tuno da zancen saudat na daga waya na kirata nake tambayanta taga kudi a account dinta take fadin yanzun nan taga wani Aliyu Abdullahi yakubu ya turo mata kudi take nunawa inna bata san ko waye ba kuma har dubu dari biyu.

Nerver mind ogan mune ya turo maku yana wajen da inna ta bugo min waya dazun shine yake min fada wai meyasa nake barin innan mu ba kudi ?

Shiya karbi account dinki wajena ya turo maku a cire dubu ashirin aba yaya Sahura taje asibiti dashi don Allah don inna tace min bata da lafiya tana kwance.

Gama yaya din mavai in tabata wayanne ku gaisa da ita ?

Wani iri naji a raina banda yadda zanyi nace bata din ta mika mata ta amsa murya wani iri kasa kasa muka soma magana a tsakanin mu wanda gaisuwane nake tambayanta yaya jikinta take fadan ai taji sauki ya nake nan lagos din ?

Na amsa da lafiya anty nace kudi na nan na turo Saudat zata baki kisai magani ace baki jin dadin jikinki dazun dana tambayeki kai haba dai mairo ta fada nace ba komai yaya aiki nake da karatu fa kinsan dan tallaka bai zama wuri daya.

Haba kin gani ko nikan nace dama nasan ba banza ba kan ance wanda ke karatu yana wanan abin haka shiyasa nace a dai bincika ?

Godiya ta fara min tana tagode tagode nace ba komai yaya ai na kusa gama karatuna in dawo gida ta amsa da Allah ya nufa mairo nima ina shawaran fara karatune ai yanzu don zaman nan haka ya isheni mairo.

Haka nada kyau yaya sahura saiki bincika kiga wanda ya dace dakiyi sai kinje ki ji ko nawane kudin sai ki bugo min waya naji.

Kai haba mairo babama yace idan na tashi in fada mashi don muyi maganan kwanaki dashi mun dan taba hiran zumuci mukai sallama da juna.

Saudat ta karbi wayan mukayi magana nake fadin ki tabbatar duk abinda bamu dashi dakin nan kin sayowa inna kada ace za a je kudin nan don Allah budan bakinta sai cewa tayi taliya ko ?

Okey taliya du kuke so ke nan ki sayo tace sai mai baba yana yawan fada muna mashi barnan man miya idan ya sayo yaya.

Murmushi nayi ina fadin dole yai fada mana Saudat ku rage barnan kayan abinci mana zata tsaya min dogon bayani na katseta da fadin duk abinda kuke so nace ki saya don Allah ki sayowa yaran nan su Abdallah dan drinks na zuwa school ki hada masu dashi.

Wani guntun ihu tayi min nace kibawa innan mu waya in mata bayani ta mikawa inna din na fada mata komai ga yadda zasuyi din ta karba da fadin ke yarinya idan mukace muyi karya haka ai kudin sai mu kasheshi a bakin mu ba tattali ko ?

Haba inna da yaran nan su gani wajem wani ya basu sha,awa inna ba gara tunda Allah ya kawo a saya ba wanan kudin ogan office din mune ya bada zan turo maki wanda zaki rika a hannun ki.

Ta dinga saka albarka da neman tsari daga Allah garemu har mukai sallama da ita na sauke ajiyan zuciya na dan jima a kwance wajen na rufe kofan daki sai lokacin na samu sukunin bude kayan da nashigo dasu din don ba zan iya cewa ga abinda nashigo ba a yanzu gaskiya.

A nan na fara tunanen uban kudin daya kashe min a wanan ranan na jima a zaune ina kallon kayan tare da tunane kafin in nisa ina yunkurin tashi na fara kwasan kayan ina adanawa can cikin wardrobe din kayana irin na da dinnan da ake mannawa a ginashi lokacin gini.

Ina idarwa na koma na kwanta dakin sai tunane a haka barci ya daukeni a wajen ban falkaba sai safe.

Can gidan mu kuma tashin hankalin a gidan kakannina yake don labarin mama da dawowanta gida ya yadu ko ina a cikin yan uwa.

Inda wasu sunji ba dadin faruwan hakan wasu kuma sukace ai baba din yayi hakkuri ma don mama ba dadin zamane da ita ba don ko yinin buki aka taru a gidan yana da wuyane a watse batayi fitina da wani ba a wajen.

Dole dakin dija mahaifiyarta ta zauna ga yaya murja da tunda ta kawo mama din gida ta sakai ta fita tana fadin tana zuwa bata sake dawowa gidan ba har yamma.

Sai tsohuwar ke fadin cewa ga murja bata dawo ba balle ta sayowa mamanta magani ta dansha don mama din tunda ta shigo haka take kwance ba lafiya ta dunkule a waje daya.

Ga yan uwanta maza dake gidan biyu kowa aka fadawa zancen dawowanta gida saiyace Allah ya kyauta tunda haka ta zabawa kanta ai iya kan hakkuri kowa yasan ai Ali yayi hakkuri da Rakiya a zamantakewa.

Hakan ya kara dagawa mama dake kwance hankali don tana jin lokacin da suke magana da iya dije din mahaifiyarsu.

Ba abinda takeyi daga kwancen sai mamaki yau ita Rakiya itace baba ya furtawa saki abinda bata taba zaton zai iya faruwa a tsakaninsu ba.

Inma sakine tafi danganta hakan ai akan mama don itace take gani har gobe zata bar mata gidan mijinta ta koma inda ta fito.

Sai gashi ganwo ya birkice da kaya itace wai yau baba yayi tsaye yake fadin ita da shegiyar yarta murja daya sheganta mata ita a gaban kowa su fice su bar mashi gida ita murja din ya tsameta daga cikin yayansa daga wanan ranan .

Wani abu taji ya tsaya mata akan zuciya dayasa saida ta nade ta dunkule a waje daya tana nishi haka dije data dan amso mata koko da ake sayarwa a layin da yamma don ta kula da bataci komai ba haka suka fito gida tunda karfe tara zuwa goma suka shigo gidan maza suna haraman zuwa kasuwa a lokacin.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login