Showing 57001 words to 60000 words out of 395027 words
Chapter 20 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
wanda tas nake jin me suke fada.
Tana fasin ita kan in hakane zata koma gida sai anty din ta zauna da mu amma ita bata isa tasa yaro aikiba yakiyi.
Bab dai san ya sukayi ba anty ce tazo dakin tana fadin in fito in wuce tunda nace ina da test ranan da yake ina son karatu ban tsaya ba na fito da saurina ta ban kudin nape din kada in kara makara .
Naje naje na samu har an zauna yin test din haka na zauna na zana gabana sai faduwa da yakeyi har aka kammala muka fito.
Rayuwan gidan Alh yakubu a yanzu komai ya kara cakudewa don har yakai gaba daya Alh din ya daina fita kasuwa ko yaushe yana gida a zaune yanzu.
Kamar ko wani gida da ake samun kariyan arziki gidan yake komawa kamar makabarta sai jefi jefi zakaji sallama daga waje haka wanan gidan dake fuskantar jerabawan ubangiji a yanzu suka kasance.
Dan dama dama hjy Hauwa data tsiro kullawa yaran unguwa da almajirau kankaran kulli suka dan shigo su saya a wajenta jefi jefi ita kuma tana samun kudin yi dan biyan bukatun yau da kullum a bangareta tunda mijin dai babu yanzu.
Dan labarin data tsunta wajen yan uwanta shine wanan gidan da suke zaune wanda in anyi rantsuwa ba kaffara kamar shine ya ragewa Alh yanzu a matsayin kaddara.
Yasa gidan nasane a kasuwa don ya karkare biyan kudin bashin dake kanshi na mutane dan sauran ya nemi ana,a kota zaune ya somayi.
Sai fashi tashin farko abokin sa na kud da kud ne ya taya gidan amma tayin wullakanci yace ba zai sayar ba tunda a zatonsa shine mutum na farko da zai sheda nawa aka kashewa wanan ginan gidan sai gashi kuma shine ya soma tayawa a nakashe din.
Hjy hauwa tana duke da safe tana gyara jera kankaran da yara suka kulla taji muryan maigidan akanta yana fadin.
Waini hauwa yaron nan sam bakiji labarinsa ba kema koga wani ni wanan abin na yaran nan yana daure min kai dan dama dama shi wanan ma yanzu ansan inda yake shiko Aliyu tunda yabar kasan nan ko sako babu daga wajensa ko ?
Dagowa tayi cikin mamaki don wananne karo na farko da zatace tun baein danta gida mahaifin nasa yayi zancensa a cikin dadin rai ba tare da aibantawa ba duk da dai kalamansa na karshe akwai muzanci a cikinshi.
Alh ina zanji tunda bai taba kiran kowa ba tunda ya bar kasan nan ikon Allah sai mutum ya shige cikin duniya kamar baida iyayye yayi shiru.
Aliyu Aliyu dama nasan za ayi hakan don miskilancin Aliyu yayi yawa shi gashi nan banda zuciya bai aje komai ba a rayuwanshi .
Allah dai ya kyauta uwar tace don bata da abin fada har ya juya zai tafi ya tuno ya hango mamaki karara a fuskanta yasa ya dakata yana fadin.
Alamu ya nuna min bai cikin wani wahala a can din don sau biyu ke nan ina mafarkinshi a cikin yanayin walwala atare dashi wanan ne danayi na karshe abun ya tsaya min a rai.
Ajiyan zuciya ta sauke tana fadi a fili Allah yasa hakan kasan halinsa dubaga yadda yabar gidan nan ba cikin dadin raiba nasan ya tsayane sai ya kammala ga baki daya ya waiwayo gida lokacin.
Kamar zaiyi magana sai kuma yasa kai ya bar wajen tabishi da kallon tausayi yadda ya koma a yanzu yau ko yar ciki bai saka ba hakan kuma yake da niyar fita waje take gani.
Kudi wani lokaci masifane ga mutum ga dadi idan sun soka idan sun gujeka kuma ka koma a bin tausayi a cikin al,umma su dai hamshim bai kyautawa rayuwansu ba gaskiya.
Ta tuno irin facakan da sukeyi da uwarsu a lokacin komai saidai su gani ita da yaranta a wajensu idan kuma tayi magana ya zama masifa wani lokaci Alh ya mara masu baya.
Yace bai hana danta ya tsaya aci dashi ba saboda lalaci ya zabi zuwa karatu ya bar kasan gashi can aiga karatun daya kwallafawa rai.
Don haka ta barsu suyi abinsu tunda su uwarsu tafi karfin yayanta irin wanan ranan takan shigo uku da hjy Naito a gidan don haka zata sakasu gaba tana tsina tana fadin bataga ranan zuwa bokon wahala ba banda tambadewa da lalacewa wani boko zai tafiyi har kasan waje halan shi yafi kowa son karatu.
Ai gashi nan idan ana zance ace jikan malamai su basu tabuwa su za a gwadawa malunta ai karya dai wallahi badai ita Naito ba da bata zama jikan hajara ba ?
Yanzu ko ta daina akin magana saidai tace ko dai danta yayi sanadin salwancewan kudin mahaifinsu bai dai tafi yawon duniya inda ba a jin labarin shi ba.
Yauma din da Alh yayi magana tasan halin abokiyar zaman nata sarai saita samu abinda ta tofa a wanan zancen don tasan komai a kunnenta akayinshi.
Aikinta tacigaba da yi a cikin damuwa aikuwa kamar jira hjy keyi maigidan ya fita taji muryan hjy na fadin ato nidai na sani dama .
Ba za a kyale mutum yaji da abindake gabansa ba sai anyi mai tsubbo da surukulle don aga iyakarsa.
Oho dai ko da kasuwa ta watse dan koli ya riga da ya kasa ya sayar ko son ko wani yaro ya figi rabonsa a lokacin a hankali ta dago tana fadin kaiya yaya.
Keda bakinki kike fadan wanan magana sunci kayan sata sun gurgunta mahaifinsu har kika samu bakin fadan hakan ?
Yau ina kudin da kike zance yaya babu ko a lokacin banyi kishin ba balle yanzu don ko banga anzama wani abu da zai tsone min ido.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/10, 10:16 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
2️⃣0️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15- HAWAYEN KADA🐊 1000.
_Account No._
_*ZAINAB IDRIS MAKAWA*_
2254380105
ZENETH BANK
PHONE NO.
08036959257
Kamar ko wani buki ango yana rawan kai hakama amarya balle auren da aka hadashi akan soyayya zaki samu ango da amarya cikin ujula ko yaushe don ganin abubuwa sun tafi daidai wajan sha,anin bukin nasu.
Saidai wanan buki na Salma ya dan saba ga hakan bayan kai ruwa rana da akayi da ango ana gab da buki daya aiko cewa ya fasa.
Don ya samu wata a can Abuja inda yake aiki a yanzu kai tsaye ba tare da shawara da iyayyensa ba ya bugowa salma din waya yace idan ta samu wani miji tayi aurenta donshi ya fasa ya samu wata kalan matar da yake son aure.
Zaune take bakin gadon dakinsu jin abinda yake fada yasa ta saki wayan ya fado daga hannunta tana sakin wani kara hakan ya dawo da hankalin yan uwanta kanta.
Ke lafiya meya faru suke hada baki wajen tambayanta dalilin hakan shiru tayi tana hawaye ba abinda ke mata yawo akai lokacin sai zancen anty Fati da sukai fada da uwarta take fadin auren cin amana da zakiwa yarki shi kike dauka da aure ai karshen maci amana kasa wallahi don sai Allah ya sakawa yar mutane kanku.
Ganin ta kasa magana a lokacin sai abu takeyi kamar me iska a gabansu yasa yar uwar fita zuwa dakin mahaifiyarsu ta sheda mata halin da yarta ke ciki lokacin.
Tare suka garzayo zuwa dakin nasu suka sameta saidai zuwa lokacin lubuna yar uwarta ta dauki wayan suna zage zage da Bello din cikin waya.
Wai me ya faru Hjy tani din take tambaya a cikin damuwa banda wanan dan rainin wayau din bello mama wai ya bugo waya yana fadin shiya fasa idan ta samu wani a daura mata aure dashi.
Shiya samu kalan matar da yake so aiko bai isa ba wallahi uban kuturu yayi kadan balle na makaho shi har ya isa ya rainawa mutane hankali ?
Wayan yar ta nuna mata alaman Bello din yana kan layi a lokacin banshi nan ta fada yana jin haka yayi saurin kashe bangareshi ta manna a kunne tana fadin.
Bello sake maimaita zancen ka taji shiru aiya kashe wayan mama ni dama na fada maku yaron nan dan iskane baida kunya wallahi.
Da kun barshi da maironsa don gaskiya akasi za aita samu irin wanan aure ni dama bai wani kwanta min a raiba gaskiya.
Rufa min baki Lubuna ke maganan ki ba dadi a kullum yaron nan koke kika sameshi zaki so ko bakin ciki kikewa yar uwarkine wai ?
Bakin ciki kuma mama akan me zan tsaya yiwa Salma bakin ciki shi dai yaron ne baida alkilbila gaskiya haka kawai zai kira yarinya da safen nan yana fada mata maganan banza haka don Allah.
Idan baiyi Allahbya bata wani mana aiba shi kadai bane namiji ni tun farko banso wanan hadin ba wallahi tunda kowa na ganin anyi cin amanane wajen nan.
Ai kinji zancen toba za a barshi ba shi din me an kama wanda ya fishima balleshi karamin alhaki barni dashi kawai ta kuta tana juyawa don barin dakin.
A,a mama me zakiyi mai har yaushe salma take da za a wani tsaya ana wanan zancen a kanta don Allah ku barta kawai Allah ya bata wanda ya fishi.
Uwar bata tsaya ba ta fice daga dakin cikin bacin zugun zugun sukayi kafin uwar tasu ta kara turo kofa tashigo binsu tayi da kallo ta sauke akan Lubuna tana fadin.
Karki sake zancen nan in jishi a waje ya tsaya iya munan sai naga abinda ya turewa buzu nadi zan gwada mashi niba sa,an uwarshi bace.
Tajuya tafice daga dakin dan shiru ya biyo baya a dakin kafin Lubuna din ta sauke ajiyan zuciya ta soma fadin ke yanzu ba zaki hakkura dashi ba ke nan ko ?
Nima shina gani wallahi ta fita zancenshi kawai tun ba ai aure ba ya fara nuna shi dan iskane karshe wahala zakiyi a gidansa.
Haba anty Asiya kuyi min fatan alheri mana don Allah ina son Bello kamar in mutu wallahi idan ban aureshi ba zan iya shiga wani hali wallahi.
Aiki ja keda bakinki kike fadan hakan Salma kawarki da kikaiwa kwance ashe ta fadi ta mutu ni ban mata kwance ba ta fada tana turo baki gaba.
Waye baisan meya faru ba a tsakani ku nidai shawaran da zan baki shine ki rabu da yaron nan tunda ya fara nuna maku hakan banga abinda kika gani kika nace mashi ba wallahi.
Kamar yadda hjy tace zuwa yamma sai gashi ya kira yana bata hakkuri yace wasa yake mata yana son gwadatane dama tayi hakkuri don Allah.
Da yar murnanta take fadawa yan uwan yadda akayi tsuki lubuna taja tana fadin jiki magayi ai salma wani wasa dan iska ko kin manta yadda mukai zage zage nan dashi da safe.
Anyi hakan an lafa wanan zancen saida bukin yazo gab kuma aka turo daga gidansu bello din cewa suyi hakkuri don mata biyu zai aura a rana daya.
Nan,ma hankali ya dan tashi karshe dai aka sulhunta zancen kowa yayi hakkuri da yadda abu yazo da kaddara a cewan manya don ita salma dai ta nuna tana so ko a hakan.
Rana daya akai masu aure ita da yan uwanta aka kai kowa gidan mijinshi ni ina lagos lokacin a gidan mu mamace take shige da fice gidan bukin don inna bata leka ko ina ba ga bukin.
Don ko anty Fati dake gidan ba,ayi da ita ba don zaman kishi akeyi gidan irin mai muni din nan don harda yaya suna hadawa cikin kishin nasu.
Don dan da Anty fati ta haifa a gidan daga uwar har yaran ba wanda ke daukanshi ko kallo yaron bai ishesu ba daga uwarshi sai mahaifinsu ke kula yaron yanzu zaman yakai kowa tana nata bangaren ba mai shiga sha,anin wani a cikinsu.
Hjy Tani ta hau itama Anty Fati din tace muje zuwa sai gidan ya kasance baida dadin zuwa koga yan uwan maigidan don da mutum yaje wani fitinane kuma zai taso a tsakaninsu ko ace anzo anki shiga part din wance.
Koda bukin yayan nata duk dangi yan uwan miji da suka zauna part din anty Fati hjy Tani taki kulasu balle ta basu abin buki yadda taba yan uwan .
Dama anty fatin da shirinta haka na baiyana tana da tanadinta akan hakan sai gashi ta fito da wasu robobi data aika aka sayo mata don ba mutanen ta tunda tasan kalan kishin abokiyar zaman nata dama.
Roban da kudin sayen ya fito daga uban gaiya don mijin shine ya bata data fada mai ga abinda zatayi don yan uwa bai jira komai ba ya cire kudin ya bata.
Sai gashi yan uwa sun dare suna tururuwa a bangaren Fati din akan manyan roban da take rabo da abinci a take away a wasu robobi masu kyau da tayi na yan daurin aure masu kyau lokacin sai hakan yaba hjy Tani haushi kuma da kyat mutanenta suka tausheta ta lafa ba ai fada ba amma duk da haka saida aka dan taba kadan.
Anyi an watse kowa ya kama gabanshi haka anty fati ta aikowa innan mu da katon roba har guda biyu tare da kayan buki don yan uwana da sukaje tayata aiki a lokacin bukin su take samu suna rike mata yaro tana kuma aikensu ko ina suke son zuwa.
Koda inna ta tura ai mata godiya yaran suka dawo dauke da dan anty din da kusan gidan mu yake wuni wurin kaunata suna fadawa inna sun samu ana fada a gidan da mijin da matan yasa basu zauna ba suka fito.
Ina taga lokacin da mama ta yafa ta fita ta dan jima bata dawo ba sai can ta shigo tana fadin Allah ya rabamu da kishiyar zamani maiwa mutum zagon kasa.
Ke bake keda buki ba amma kinfi mai buki cin riban bukin don iya kissa ta kalalame miji da dadin baki komai na buki itace tayishi a bangaren miji duk hjy bata sani ba.
Ai koda yake itama hjy ai maganin ta ke nan ai hatta da abincin da zata ba mutane ta boye sai bayan buki aka zubar saboda bakin hali irun nata ai gashi nan ta hadu da yar bana bakwai tazo ta kwace mata jama,a akan mako irin nata.
Har tayi ta gama ba wanda yace da ita taci kanta a lokacin su inna suna daki basu fito ba saidai suna jin tana mayarwa baba yadda akayi.
Saida ta gama fada baba ke fadin ko kowa baici ba aike kinci tunda kune manya a wajen kinga kuwa sai yadda kukayi don nasan halinki Rakiya.
Nikan ai nasan yadda zan shamaceta malam mun diba tun ba akai mata ba mun dibi namu mun kawo gida muka kai mata sauran har ita yar saka idon nata Lami.
Allah ya kyauta ya fada ganin kaunata khadija ta fito da dan anty Fati goye a bayanta yasata fadin sunan muna can ne amma ai yan ba ruwana sun fimu cin riban bukin don mu ko plate din roba bamu samu ba.
To ai shiya kamun kai yake da kyau gashi kin fada da bakinki yanzu wanda baije ba yafiki cin moriyan abin don mu muna nan aka aiko muna da abinci cike da kula kowa yaci ya koshi a gidan nan.
Ai kun fimu dabaran boye ta fada ta mike zuwa dakinta don ta fahinci baba ya gane me take nufi da zancen nata har takai kofa ta juyo tana fadin .
Ai malam baka sani ba bakin yarka mairo ya kama kawarta fa don yarinyar nan bayan kishiya kuma ashe ita dayan matar daya aura wata babban mace ce mai zaman kanta can abuja kaidai bari ai akwaita a kasa Allah ya rufawa mairo asiri da shegen yaron nan baka ganshi ba