Showing 204001 words to 207000 words out of 395027 words

Chapter 69 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

ta dawo muci namu.

Nabude dankalin arish ne sai naman koda na kaza da kwai sai kamshin ganyen hadi yakeyi na danci na turawa amira sauran na dan kishingida bakin gado.

Amira ta dauki ledanta zuwa waje can sai gata ta dawo tace anty na kirana hakan yasa na mike na nufi waje don amsa kira almost five thirty lokacin.

Wai sai a lokacin take min zancen girki saboda tayi jigilan asibiti ta gaji bata iya dora girki ba dama kota dorama ba ciwo zaiyi da dadi ba kuma taki tsayawa ta koya tsakani da Allah ta iya.

Banyi magana ba na juya don inje in dora lokacin ne naji uwar na fadin harma rokonta kikeyi tana kyalewa sariya ?

Bata kyale ba zata dora min ne ai ke kike bada dama ga duk abinda ya sameki Sariya ga ita wanan daya kwasa maki gida ba dadin gani abu haka kamar kato .

Ita kuma wanan daya dauko maki da sunan aiki tun farko gashi yanzu yadda ta koma ko aikin zatayi maki saikin roketa tazo tayi maki ita bata sanda aikin bane takoma daki ta kwanta ?

Ina jin muryanta har lokacin dana gama aiki tana magana guda da harshen yarbanci a falon nagama an jima da kirab sallah na koma daki don sauke farali.

Ina idarwa na mike na gyara kayana da kyau tunda Paapa a dakin anty zai kwana ana iya cewa a nan dakin nawa zata kwanta.

Ina kwamce har barci ya soma daukata naji muryan anty a kaina tana fadin har kin kwantane yau da wuri haka kin san mommy da hira tana can tana min hiran kubura ne.

Ido na bude ina fadin ban iya fadan mommy ne naji ta soma fada dake ina fita nima fadan zata soma min kyale mommy tana ganin ban iya tsara gidana bane yasa uncle dinki har ya karo min kishiya.

Ni ban damu da zamanshi da Yabi ba maryam d onlything da bana so shine kazanta da wanan sherin nata na makirci kuma naga hakan halintane ita ?

A nan dakin zata kwana kinsan Paapa idan ya dawo dakina zai kwana yau so zasu zo nan ita da Amira ku kwana tare dama nayi tunanen kin kwanta ?

Jin hakan yasa na soma yunkurin mikewa daga kwamcen don in gyara mata gadon a kasa nayi shimfida zan kwanta take fadin gadon ba zai isheku bane tare ?

No ita sai ta kwanta a saman gado ita da Amira nikuma zan kwanta a nan ai jikinki zaiyi ciwo mana ta fada nayi dan murmushi don har lokacin Allah yagani banji dadin zuwan dattijuwar nan ba don nasan ba a wanyewa da dadi da ita a wanan zuwan.

Ba,a jima ba naji shigowansu da yar nata tashigo tana fadin ehh dakin na maryam ne ya koma haka kamar na wata matar gida ?

To ya kike son kiga dakin mum a yakuce tana mace kan tana gyara ai dole kiga dakinta ya koma neat ya koma kamar haka.

Ga bayi nan idan zaki kewaya kin daiga wajen tsarin dakin kamar na dakina yake ta dai gama ta fita ta jawo muna kofa don naki tashi a lokacin i was pretend like nayi barci ko ina jin tana jan tsoki tana yare da yarbanci tana fadin bansan lokacin da yarinyar nan zatayi hankali ba.

Ina jinta ban motsa ba harta gama ban motsa ba har barci ya daukeni tana zaune tana muku muku da kayanta saida safe dana tashi daga barci zan shiga bayi naga irin abinda ta shuka min don a kasa tayi fitsari kamarma ba sau daya ba.

Wani irin ba dadi naji a raina ban iya yin alwala ba dole dakin na shiga tsarkakewa na samu nayi wanka na dauro alwala.

Ina tsaka da sallah kuma ta tashi kafin ta shiga bayin ta sake min fitsarin tun a kofa kodana gama shiryawa nayi ban tsaya binta kan abinda tayi ba na shirya nace mata zan fita.

Wani irin kallon banza tayi min nidai nasa kai nafice daga dakin abina ina mamakin rayuwa irin na mommy din mace kamarta ace bata ibada don koda na fito banga ta maida hankali tayi sallah safe ba.

Ba abin mamaki bane don in antashi za a iya hadesu lokaci daya ayisu ko kuma ace ai babu lafiya don haka sallah ba dole bane a wajenta yanzu.

Ina gyara gashin kaina daya dan zubo min ta hanyar mayar dashi gefen fuskana tsuwayana nasake gyarawa ina facing din titi inda abin hauwa suke zirga zirga a titin Okenah yaja ya tsaya gabana da motarshi dayake ji dashi.

Yana fadin Omo hausa ina zuwa da wanan safen ko baki gaji da school bane ke ya fada cikin zola donshi dan son barkwancine dama.

Na dan taka zuwa gareshi ina fadin aiki zani ya juyo da sauri ya kalloni duk da kokarin parking din da yake gyarawa yace wani irin aiki kuma kike fita na zata kina arewane fa ?

Aiki ina aiki tare da wasu uncles dina ne nan Apapa can nake zuwa a cikin hutun nan bai dauki abin serious ba ya zata irin dan buga buga din nan ne nake fitayi yace muje ya saukeni a can din duk da ba can ya nufa ba ya fito zaije airport road ya dubo wano uncle dinshi.

Shiya kaini wajen aiki a ranan sai dai muna zuwa bakin company ina nuna mashi wajen ya juyo ya kalleni yana fadin ina nufin a cikin nan nake aiki wai ?

Na fada da eeh mana ina daukan jakata dana laptop dina dake gefen motan yace nan fa yana cikin ma,aikatan da kowa ke son aiki dasu a yanzu don su tsarinsu da banne a nan.

Anan din nake temporary work dasu na dan lokaci yake fadin how lucky your Meiram wani conection kike dashi da har kika samu suka daukeki haka ba takardu ?

Akwai wani dan uwana dayaso wajen nan sosai masters ne dashi amma sunki accepting dinsu ya gaji ya hakkura iam sure koda karamin ma aikaci suka dauleshi zai yarda da hakan don suna bada kudi sosai akace.

Wait don Allah baka da zance sai kudi kudi kudin nan idan ka samu me zakayi dashine haka Okenah wanan zance da nayi shiyasa muka dan wasance a lokacin aka mayar da abin wasa na fita ina mashi godiya don nasan ba karamin taimaka min yayi ba a lokacin.

Na kula da matan ma,ailatan duk da basu da yawa sosai yan tsirarune sai jefi jefi zakiga mace a cikin ma,aikatan suna tsegumina duk nazo shigewa don ban tsayawa kulasu har lokacin akwai akidan nan ta tsanansu a raina suma din dai shigana yana boye masu asalina sukanyi tsegumin koni wata yarece ba kuma wanda zasu tambaya a kaina kowa cewa yake bai sanni ba baisan daga ina nazo nan ba.

Nazo zan shiga office dina wanan dan bayeraben mai dan kwale kwale ke fadin miss oga yace idan kin iso ki sameshi office now now har na murda hannun kofan na tsaya na dakata ina saurenshi shawara nayi in shiga in aje jakata da sauran tarkacen dana riko a lokacin .

Hakan yasa nashiga na aje na nufo offoce din nashi na dan tsaya ina knocking daga waje aka amsa min daga ciki yana zaune yana facing din kofan shigowan shi kuma wanan Sulaiman din yana zaune yana mashi bayanin wani abu.

Karasawa nayi a hankali zuwa gaban table din ina fadin ina kwana bance sir ba ko wani suna can sai shi sulaiman din ne ya juyo yana fadin maryam kin karaso ke nan ?

Eeh ina kwana lafiya ya fada ya dan juya gun mutumin yana fadin shike nan zan iya tafiya ya daga mashi hannu alaman ya tafi din.

Ina tsaye inda nake ban motsa ba har ya fice daga office din ina tsaye banyi magana ba shina haka yama nuna baisan da ina wajen ba a lokacin.

Gani ance kana nemana idan na shigo yanzun nan baki iya gaisuwa bane ke kinyi min tsaye haka kerere a kai ?

Duban kaina nayi kafin nace ai na gaidaku da nashigo ke wace irice wai anya kina shiga arewa kuwa da wanan rayuwan naki haka ?

Kada ki dauka kin ari rayuwan wasu kin yafa kina ganin hakan da kikeyi shine daidai by the way wani yaro ya saukeki yanzu ?

Meye matsalan kike da kike son zubur da kimarki da Allah yayi maki matsayinki ya mace kuma musulma yar kabilan hausawa ?

Ni na nuna kaina a cikin mamaki wata zuciya daga gefe tana fada min in juya kawai in fice daga office din wanan dan rainin wayau din meya daukenine wai ?

Saidai wata zuciya ta gargadeni da hakan da kar in fita ban fada mai irin abinda shi ya fada min ba ido rufe na dago na dubeshi ina fadin.

Allah sarki irin kallon da nake ma shi kake min ashe nima kallonka nake wani wanda bai rike addininsa ba ko girmansa .

Allah da Annabinsa sunyi gaskiya da suka hanemu zargi ko zato akan dan uwan mu musulmi yanzu gashi kai kayi min mumunan zato a zuciyarka.

Nima haka irin wanan kallon nake maka na mutum mai shishigi da da rashin imani kashiga rayuwata kana matsa min nayi bibiya ga hakan tunda ka biyo ta hanyar uncle dina.

Hakan bai maka ba sai ka saka ido a duk wani movement dina kana zargina akan abinda ban taba tunanen aikatawa ba a rayuwana.

Kasani tun kan nazo lagos iyayyena suke saka min albarka kuma albarkan su yana biye dani a duk inda nake don daidai da second ban taba mantawa dasu ba balle tarbiyan da suka bani na islama.

Dont judge a book by it cover sai ka shiga ciki kaga abinda ya kumsa kadin kayi alkalanci a kai don Allah, na barka lafiya na fada na juya zan fice daga office din a fusace.

Karki fara ki motsa daga nan ya fada yana mikewa tsaye saina fita a rayuwa na tsani zargi ko sa ido ina abina ba tare dana damu da damuwan wani akan komau ba.

Tabbas yanzu nasan yadda kike kwata kwata kin sauya daga yar hausa fulani zuwa roget dinnan na garin lagos don idon ki babu kunya ko tsoro a cikinsa yanzu ?

Dan murmushi na sake na juyo da kyau na fuskanceshi nace kayi min zargin da ban iya yafewa duk wanda yai min irinsa a duniyan nan .

Motar da kake zance na shigo motan dan course mate dinane da muke tare a school a hanya ya ganni ina jiran mota ya ban lift quaty sure ni ba yar kowa bace ban kuma taba cewa ni din wata bace.

Banda mota hakama ubana baida ko keke hawa balle inyi karyan rayuwa ince ban shiga motan haya kota lift don haka kayi min mumunan fahinta a yanzu.

Speechless ya zama don shi ba gwanin iya magana bane haka yadda na tareshi ya kasa fadin komai sai dan rankwafowan da yayi sama table din.

Okey fine motace matsalan ki yanzu yasa kike shiga motar kowa haka anyhow ba tare da kare mutuncinki ba ?

Kinsan irin mutuncin da Allah yai maku diya mata look ina da kanne mata biyu da muka fito ciki daya dasu yadda banson wani abu ya samu rayuwansu haka duk inda naga ya mace nake son kare daga yaudaran duniya.

Allah shehi aida saika koma ka dauku loudspeaker kabi gari kana ina mata ga mai tausayinsu yazo.

Ga laptop din ku nan zan aje maku a office abawata ko wani ba zan iya wanan aikin na zargi ba akaina na juya muka hade da wanan sulaima din .

Ya shigo a gigice yana fadin ke maryam ya haka kuma ogan kine fa you have to obey him koba aiki kinsan ya girme maki nisa ba kusa ba why zaki tsaya kuna haka kina fada mashi magana ?

Zo zo zo ya fada ya kokarin kama min hannu na zille shima yace sorry please don Allah yi hakkuri zo muje offfice dina please.

Ya bude na fita kafin shi ya biyoni yana fadin muje office dina don Allah kiji Allah da yace yasa na bishi zuwa office di nashi muka shiga.

Dan banbancin kadanne da office din mu da nasu wuri ya nuna min na zauna ya dauko ruwa mai sanyi ya aje min yana fadin sha ruwa please ko zuciyarki zaiyi sanyi.

Na gode ban sha ban karya ba tukunna saboda me ya fada cikin mamaki nace is too ealy now bana kari da safe haka .

Kika kuma tsaya fada haka da oganmu maryam an fada maki ana fada da ogane a office nan fa ba gida bane ko wani wurin wasa ?

Nan aiki mukazo yi gaba dayn mu don cigaban mu shifa ba fada ya tareki dashi ba haka yadda kika dauka kece dai kawai nake ganin baki fahinceshi ba.

Wani irin fahinta malam kullum mutumin nan zargina yakeyi kuma yaki ya fada min manufarshi na sakani cikin rayuwanku da yayi don nasan yana da manufa a gareni ?

Au ke baki fahinci me hakan ke nufi ba har yanzu ke kadaice diyar bahausa a garin nan akwaisu da yawa amma ya zaboki don kece kikai mashi.

Kallon ban fahinceka ba nayi mai yace yes a rayuwana da sanin mr Aliyu ban taba ganin ya tsaya kula wata ya mace ba a rayuwanshi.

Baki na tabe irin ban yarda ba din nan yace wallahi ina fada maki gaskiyane don ki natsu ki dawo hayacin ki kishin ki da kaunarki yaja yake maki hakan ke kuma kin kasa ganewa ?

Ni kishina aka me zai dinga kishina matarshi nake ko kanwarshi saida ya murmusa kana yace dani who,s know ko ,,,,

Haka taku sallon yazo da fada da juna so ke macece don Allah ki gane abinda nake nufi da wanan maganan ki koyi hakkuri da gimama na gaba zaku zauna lafiya iam telling you zaki fada wata rana.

Amma kin haka har wasu su gane komeke tsakani ku kinga za ace oga yana soyayya da wata staff a cikin company shi.

Kaina na dukar kafin na dago ina sauke ajiyan zuciya nace bana soyayya ko wani abu makamancin hakan a rayuwana iyakana da namiji mutunci kawai shine tsakanina da kowa.

Yanzu dai ki natsu don Allah muna matukar bukatanki wajen nan sosai wallahi aikinki yana muna amfani matuka ki nuna ban fada maki komai ba a game dashi zuwa gobe in son samune don Allah ki sameshi ki bashi hakkuri please for my sake na rokeki kada ki dauki hakan wani abu.

Ki taimaka mashi please kada kice zaki fushin zuciya ki daina zuwa shima nasan zai sauka nan da gobe so ki tashi ki koma office din ki please.

Na danyi shiru tare da dukar da kaina kasa ina tunane yake fadin idan kikaji meke damu oga nasan zakiga hakan ba laifinsa bane.

Na fahince ku dukkan ku a yanzu gaba dayan ku hakan bakon lamarine a wajenku so kiyi hakkuri don Allah zan fahintar dake komai daga baya.

Idona yayi ja haka namike tsaye saidana mike nake fadin nagode kada ki damu nike da godiya nida kika taimaka a yanzu daga haka na juya na fita.

Wanan bayeraben sai satan kallona yakeyi ban tsaya kulashi ba nasa kai na shige office dina na rufo kofan da karfin tsiya zaune nakai ina dafe kaina dake juya min.

Suna saka rayuwana a dabaibayi na kasa gane manufarsu ga baki daya wanan mutumi dake zargina koda yaushe hakan shi kauna ?

Kaunama wace iri wai don ban fahinta ba nake tambayan kaina a daidai lokaci aka kwankwasa office din wata yar kabilan yarobace na gane hakan daga magananta da tace good morning mah oga sulaiman say i should bring dis for you

Na daga kai na dubi abinda take ajewa din ko da ban bude ba abincine nace thank you a sanyayye ta dan rusunna tana kara min gaisu.

Ta fita na nisa a raina nace sulaiman din ma yafishi hali kwarai da tausayi tunda yasan darajan mutaneshi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[9/8, 9:27 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊6️⃣4️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login